GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 37

by @nusybee143

Page 37



Haisam ya yi ɗan murmushi ya ce"Mubarak yana hannuna a yanzu haka,idan za ki bar min shi ma ina so, because I love the boy so much,kuma ina fatan watarana mahaifiyarsa ta dawo gare shi ta cigaba da riƙe abinta"

Murmushi ta yi sosai,duk da hawayen fuskarta ta ce"na bar maka shi,kuma ina fatan watarana idan ya girma ka ba shi horo ya yaƙi mutane masu irin sana'ar da nake yi, maganar rainonsa kuwa kai ma ka san ba abu bane mai yiwuwa a gare ni a yanzu dai"

"Babu abin da ba ya yiwuwa da izinin Allah,ke dai in sha Allah za mu dawo mu tattauna akan batun shiga kotun 

In Sha Allah za ki fita daga nan,kuma za ki sake ganawa da ɗanki,amma ina so na yi miki wata tambaya ɗaya"jinjina kai ta yi ba tare da ta yi magana ba

Kai tsaye ya ce "a Labarin da kika ba ni,ba ki sanar da ni cewa kin yi karatun addini ba, menene gaskiyar lamarin?"kai tsaye Shaheeda ta ce"na fara ba ka labarina ne tun sanda na kammala secondary,amma na haddace Alqur'ani tun ina SS2,na karanci littafai da yawa, dalilin haka ya sa na daina zuwa islamiyyar ma"

"To duk lokacin da kika ji damuwa da ƙunci,kin taɓa ɗauko Alkur'ani kin karanta?ko kin taɓa tashi cikin dare kin roƙi Allah ya duba ki ya ba ki maslaha akan matsalolinki?"shiru ta yi tana kallonsa, don tabbas bata taɓa yi ba,ya ce"to kin gani ko?

A duk lokacin da kika ce Allah zai yi miki to tabbas zai yi miki ɗin,amma idan kika gwada dabara da iyawarki to tabbas Allah zai bar ki da iyawarki "
A hankali ta jinjina kai cike da gamsuwa,ta yi ɗan murmushi ta ce"na gode sosai da karamci,na gode,ka yi abin da iyayena ma suka kasa yi min"Haisam ya ce"babu ta inda iyayenki suka rage ki,sun yi dukkan ƙoƙarin da za su yi miki,ke ce a yanzu suke bi bashi"

"Ni kuma?ta yaya zan iya biyansu bayan ka san a yanzu tawa ta ƙare?"

"Weather taki ta ƙare ko kina da sauran dama lokaci ne zai bayyana haka,shekarunki nawa a yanzu, ashirin da nawa?"

Shaheeda ta ɗaga yatsunta guda uku ba tare da ta yi magana ba, Haisam ya zaro idanu yana murmushi ya ce"har yanzu ke ƙwaila ce Shaheeda,yarinya ce ke sosai,kin yi ƙoƙari sosai,na jinjina miki yadda kika rinƙa gwara kanmu da ƙananun shekarunki,I salute you Ma'am "ya faɗa yana sara mata yana murmushi 

Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa tana kallon handcuff ɗin hannunta tana murmushi ita ma, Haisam ya ce"alright then,ni zan tafi,sai na dawo zuwa gobe "ta sake yi masa godiya,suka yi sallama 






*MALIYA ESTATE*


Izuwa yanzu al'amura sun sake rincaɓewa a gidan Alhaji Yusuf Maliya,don a wannan karon Ummeey ta kasa jure halin da ƴarta take ciki, da gaske ciwon da take ciki ya taɓa ta,kuma kallo ɗaya za'a yi mata a gane hakan 

Hakan ne ya sa Alhaji Yusuf ya fita daga sha'aninta,don a ganinsa saboda ƴarta tana son ta fara karya masa doka 

Hakan ya sa ta fusata ta fara shiryawa don komawa gida,don ita ta gaji da wannan auren da tunda ta yi babu abin da take samu banda baƙin ciki da ɓacin rai 

Tana shirin fitowa daga sashenta sai ga Hajiya Atika,tana yi mata wani kallo ta ce"Hajiya sai kuma ina?"

Bata amsa ba, Hajiya Atika ta sake faɗin"dama Alhaji ne ya ce na yi masa kiranki "tana kai wa nan ta juya ta bar wajen 

Bata yi niyyar zuwa ba,amma sai ta canja ra'ayi ta tafi, tana zuwa ta samu Alhaji Yusuf a tsaye, fuskarsa a ɗaure 

Bata nuna ta gane halin da yake ciki ba ta ce"Barka da warhaka Alhaji"

"Samu waje ki zauna Zainab"ta manta rabon da ya kira ta da wannan sunan,amma ko a fuska bata nuna damuwa ba,ta samu waje ta zauna

Daga nan ɗaga waya ya yi ya yi kira,ana ɗagawa ya ce"Ruƙayya ku taho tare da Arfa,ki cewa Sa'adatu itama ta zo,ina buƙatar ganinta"sannan ya kashe wayarsa

Babu jumawa suka iso,sau ɗaya Hajiya Zainab ta kalle su ta ɗauke kai,daga amsa sallamar da suka yi ba ta sake magana ba, musamman da ta ga ko sashen da take ba su kalla ba

Alhaji Yusuf ya ɗaga kai ya kalle ta,a ɗan fusace ya fara magana "Zainab an kawo min ƙararki a gidan nan,ban san menene matsalar da take son ta canja ki ba,ko don kina ƙoƙarin ki nuna min ban isa da Shaheeda bane ya sa kike yin haka ban sani ba"

Hajiya Zainab ta ɗaga kai ta kalle shi ta ce"Alhaji me kuma aka ce na yi?"

Alhaji Yusuf ya ce"ina Muyassar ya je?"

Hajiya Zainab ta dube shi sosai ta ce "Muyassar?

Alhaji ta ina zan san inda ya je?"

Alhaji Yusuf ya kalli Hajiya Sa'adatu,kamar jira take yi ta fara magana a fusace "ɗana tunda nake da shi ban taɓa ba shi umarni ya kauce ba sai akan ke da ƴarki,me kuka taka ne haka?

Da me kika fi sauran mutane ke da ƴarki?

Har ga Allah zuwa yanzu na fara gajiya,na gaji da yadda nake tarbiyya kuna rusawa,don haka ki saka ɗana ya dawo gida kawai ya mayar da matarshi Kamar yadda kika saka ya sake ta,don na san ke ce kika saka shi ya sake ta sannan ya yi nisa da ita, saboda an kama gallafiriyar ƴarki "

Kallonta kawai Hajiya Zainab take yi har ta kai aya, sannan ta yi murmushi ta ce"hattara dai Hajiya Sa'adatu!

Me ɗa ba ya yiwa wani gorin lalacewar ɗa idan da tunani, babu uwar da zata so ɗanta ya lalace ko da ace ita lalatacciyar ce kuwa, kin ga......."

"Saurara Hajiya Zainab!

Ai lalacewa kuma sai dai ki ganta akan ƴarki wadda take zuba rashin tarbiyya da rashin mutunci tun tana ƴar ƙanƙanuwarta amma kin kasa tsawatar mata,idan ma wani asirin kika yi don lalacewar yayanmu to Allah ya mayar miki da masifar kanki,amma yayanmu sun fi ƙarfin lalacewa da ikon Allah "

"To madalla!

Da kika san da haka,na cewa ƴaƴanki suna jin maganarki ai da ɗan naki ya yi nisa shi za ki tunkara ki ce ya dawo,ba ni za ki zo kina zaƙalƙalewa ba,ƙaddarar Shaheeda kuwa idan Allah ya so zai iya mayar da ita ba komai ba,ni fatana koda yaushe Allah ya shiga rayuwarta ya zama gatanta "

Wani kallo Alhaji Yusuf ya yi mata, cikin ɓacin rai ya ce "wato kina nufin da na ce a manta da ita a gidan nan ba ki manta ba kenan ko me?"miƙewa ta yi tana kallonsa cikin idanu ta ce

"Ko zan manta komai,ai ba zan manta cewa Shaheeda ce ta mayar da ni uwa,nake tuna cewa na haihu ba tare da na ji zafin wani gori ba,a lokacin da kowacce uwa take ƙyamatar na nuna ɗanta na ce nawa ne a lokacin ne nake alfahari saboda na tuna cewa ina da Shaheeda,kuma ban taɓa nadamar haifarta ba,don haka ka ma cire a ranka cewa akwai ranar da zata zo har ta wuce ban yiwa Shaheeda addu'a ba,ko kuma ban ji ta a raina ba"

Arfa da Hajiya Ruƙayya da mamaki suke kallon Hajiya Zainab wadda iya tsawon zamanta a gidan ba'a taɓa jin ta mayarwa da wani amsa ba saboda tsananin haƙurinta,amma sai gashi yau ga tana mayar da magana 

Hajiya Sa'adatu ta kama haɓa da mamaki tana kallonta ta ce"ke yanzu idan banda rashin kunya da rashin ɗa'a irin na wasu mutanen yanzu har Shaheeda ta kai a yi tutiya da ita?

Wallahi ni dai a nawa ganin da haihuwar irin su Shaheeda gwara zama babu haihuwar ma gaba ɗaya,me ake da ɗa irin Shaheeda,haka kawai a haifarwa duniya Annoba?"

Hajiya Zainab ta yi murmushi ta ce"idan kin tashi haihuwa ki haifo limamin harami bisa wayonki da dabararki,Ni wannan ba matsalata ba ce

Allah shine ya san hikimar ba ni Shaheeda ba tare da yan'uwa ba, sannan ya jarrabe ni da halayenta,amma a hakan na godewa Allah,kuma har yanzu ban cire rai zata zamar min abar alfahari ba watarana,ban cire rai zai sake haɗa mu ba"daga haka ta juya da sauri ta fice daga parlourn tana mayar da zazzafan hawayen da ya fara cika mata idanu,da wanne zata ji ita kuwa?

Da halayen Shaheeda?ko da baƙin cikin korar da mahaifinta ya yi mata wanda shine tushen komai,ko da abubuwan da aka ce ta aikata?ko da kamun da aka yi mata?ko da wadannan surutan da ake yi mata,da baƙaƙen maganganun da ake gaya mata dare da rana

Daga sashen Alhaji kai tsaye parking space ta nufa ta shiga motarta ta tayar ta fice daga gidan,tana tafiya a mota tana share ƙwalla, aranta tana ambaton dukkan sunan Allah da ya zo mata rai 

Kai tsaye gidan Hajiya Saudat ta nufa,a bakin gate ta tsaya ta kashe wayar ta sannan ta shiga cikin gidan,a ranta tana ganin gwara ta ba wa kowa hutu kawai, ita ma ta samu nata hutun






*ROCKY ESTATE*


Sai da ya yi sallar isha'i sannan ya shiga sashen Nanny ɗin su Amna,yana shiga da sallama Amna ta taso da gudu ta ɗane shi tana murna,ya rungume ta yana murmushi,ya mayar da kallonsa ga Mubarak wanda yake raɓe a gefe guda 

Sauke Amna ya yi, Nanny tana faɗin "Barka da zuwa ranka ya daɗe"ya yi murmushi ya ce"Barka dai Nanny,ya na ga yallaɓai a zaune ya takure?"

Nanny ta yi murmushi tana kallonsa ta ce"wai nan fushi yake yi saboda na ba shi magani,ka san baya son magani ko da wasa"Haisam ya yi ƴar dariya ya ƙarasa inda Mubarak yake zaune yana kallonsu, fuskarshi duk hawayen da bai gama gogewa ba,ya sa hannu ya ɗago shi yana faɗin "abokina ya dai?

Wa ya taɓa min abokina ne?me yake faruwa? Nanny ce ta ba ka magani?ba ka so ko?"ya gyaɗa kai fuskar nan a ɗaure, Haisam ya ce"ai tafiya ma zamu yi mu bar mata sashenta ko?"ya sake gyaɗa kai yana shagwaɓe fuska, Haisam ya yi murmushi ya ce"Weldon my friend,zo mu tafi ko?"Nanny tana murmushi ta ce"tafiya za kayi ka bar ni?"ya juyo ya kalle ta ya ɗauke kai, Amna ta ce"Daddy nima zan bi ku"

Daddy ya ce"ba yanzu ba tukunna, sai da safe sai ki zo, yanzu ki zauna a wajen Nanny "ya ja hannun Mubarak suka bar sashen 

Ya ɗan ɗauki lokaci yana yi masa wasa,har shima Mubarak ya fara sakin jiki yana ba shi amsa,shi dai kallonsa kawai yake yi,ganin exactly fuskar Shaheeda, babu inda ya bar ta,sai hasken fata da ya fi ta

Wajen ƙarfe tara Haisam ya samu Mubarak ya yi bacci,ya kwantar da shi sannan ya miƙe ya nufi sashen iyayenshi,don Abba ya yi masa magana yana son su gana

A parlour ya same su a zaune,ya yi mamakin ganin Nimra da ya fara gajiya da ɗan banzan nacinta,amma ko a fuska bai nuna ba, bayan ya gaida su abbansa ya nuna masa kujera yana faɗin"zauna Haisam "

Babu musu ya zauna, Abba ya ce"har yanzu baka cewa kowa komai ba game da yaron da ka kawo gidan nan,gashi mu kuma ba mu san shi ba"

Haisam kai tsaye ya ce"Abba ba ku sanshi ba,amma yanzu ya zama ɗaya daga cikinmu, ɗan criminal ɗin da na kama ne, kasancewar ba shi da kowa sai na kawo shi ya zauna a cikinmu"

A kusan tare Nimra da Hajiya Mariya suka razana, Abba ya ce"menene hikimar hakan Haisam?na san dai baka yin abu sai da dalili"

Haisam ya gyara zama ya ce"haka ne Abba!

Akwai ƙwaƙwƙwaran dalili kuwa, saboda shi yaron ba shi da kowa,asalima"ya ba su labarin Shaheeda a taƙaice yadda za su fahimta 

Abba ya tausaya mata sosai,su kuwa Hajiya Mariya da Nimra kallonsa kawai suke yi sun kasa magana, Abba ya ce"Allah sarki!

Dama a rayuwa ba kowa bane za ka ganshi da wani hali ya zama laifinsa ne,wasu trauma ce,wasu kuma dole ne,to ina yi mata fatan Allah ya fito da ita lafiya ta riƙe ɗanta,don bai kamata abu irin wannan ya shafi rayuwarsa ba

Allah ya kawo mafita,shi kuma yaron Allah ya raya shi ya yi masa albarka "

Haisam dama ya sani zai samu goyon bayan Abba, dattijo mai nutsuwa da hangen nesa,mai tsananin tausayi da mayar da duniyar ba komai ba, kafin Haisam ya sake magana Alhaji Abdulmalik ya cigaba da Magana 

"Akwai kuskure sosai a tozarta rayuwar ƴa mace a lokacin da ta aikata kuskure,da ba'a tozarta ta ba an sallama ta da yanzu wataƙila ta zama wata mai amfani,amma hakan da aka yi mata gashi nan baiwarta ta zama barazana ga al'umma 

Muna buƙatar yara irinsu a society ɗin mu,bai kamata mu yi musu haka ba"

Haisam ya yi murmushi yana gyara zama, kafin ya yi magana Hajiya Mariya ta kasa haƙuri ta ce"Haisam ni kuwa sai na ga kamar baka yi dabara ba

Me zai hana ka kai shi gidan marayu?amma menene amfanin kawo shi nan?mu da ba mu da alaƙa da uwar tashi?"






#Nusy_bee