NANNY(MAI RENO)

7

by @jamilaumarjanafty

*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Na*

*AISHA ALTO*
*JAMILA UMAR(Janafty)*


*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*

*Sanyi flusher!* 
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. 
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta  dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.

*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa  da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.

       *BABI NA BAKWAI*

Duk da yaran Sun Tashi Zuciyarsu ba Dadi bai Hanasu Shirin Tafiya mkaaranta ba,Suna bisa Dinning Suna Breafsat,Kowa ka gani Fuska ba Walwala Don Daga Tahir din Har Faridan ba Wanda Sukaji Motsinsa Har Gwarashi yazo da Asuba ya Tashi Bassam sun Tafi masallaci.

Batare da Sun saka iyayen nasu a ido ba garzali ya Kwashesu Zuwa Mkranta Naila Kuma dama Wajen Tahir Ta Kwana,Sun Fita ba Dadewa Farida ta fito Daga Cikin Bedroom Dinta Dauke da karamar Trolly dinta Fuskarta ta Kumbura Idanuwanta Sun Chanza kala Saboda Kuka Tana Sanye da Riga da Sikat na Wata Atamfa Holland,Daurin Dankwalin dai gashi ga kamarshi,sai karamin Gyale Vail Data Yafo Bisa kafadarta,karamar Jakarta na Hannunta Hade da Wayarta sai Key din motarta Dake Hannunta.

    Ahaka ta Sauko Har Zuwa Main Falo din Tana Tafiya tana Share Hanci da Iya taci karo Wacce Tafito Daga Kichen,cikin mamaki Take kallonta kafin Tace"Hajiya lafiya Kuwa..? Wata Uwar Harara Ta maka mata kafin Ta Saki Tsaki takama Hanyar Fita Daga Falon,iya bata Dandara ba Tace"Haba Hajiya gaskiya Wannnan ba girmanki bane,Ina Zaki Tafi ki bar mijinki da ya"yanki Kefa ba yarinya bace Yaji bai kamace ki ba,kin kai Munzalin Da Zaki ma Wata Fada bama Kanki ba..."Tafada Cikin Nuna Alamun Abun bai mata Dadi ba.

Juyowa Farida Tayi Afusace kafin Tace"Wlh iya sai na Tafi nagaji da Irin Tozartanin Da Tahir yake yi nagaji..!kina gani Jiya gabanku gaban ya"yana Ya Tsinkeni da maruka har biyu Saboda ga baiwarsa ko,Allah sai na Tafi Sai ya Zauna Shi kadai.."Tafada Tana Sharbe Kwallah kamar Wata yarinya.

Iya tayi kasake kafin Tace"Hakuri Ake Hajiya,Kowa fa kikagani yana Zama lafiya agidan Mijinshi karki Tambayeshi Hakuri,Kema Kiyi Hakuri Don Allah In kika Tafi Gida Kicema su Umma Mene Don Allah.."?Tana Sharan Ido Tace"Ai ba Kano Zani ba Danbatta zani Wajen Goggo Abu taga Shaidan Yatsun Tahir Akan Fuskata..."Tafada Tana juyawa da Sauri Ta Fice Daga Falon Tana kara Rike zaman karamin Akwatin Dake Hannunta Iya Dake Tsaye ta Yunkura Zata Bita sai Taji Muryan Tahir Daga Sama yana Fadin"kyaleta iya..."yafada Cikin Halin ko Inkula 

Iya ta Waigo Jiki asanyaye kafin Ta Rusuna Tana gaisheshi,Shiko yana Daga saman Benen ya amsa mata Fuskarsa na Nuna Alamun baida Damuwa yana Sanye da Amarican Suit,Ash colour,Yar jakar Briefcase dinsa ne Ahannunshi da alamun Fita Zaiyi Tana Kokarin Barin Falon ya Karisa Saukowa yana Fadin"Naila tana Room Dina iya Ta Koma barci plz ki Haura ki Daukota Ta Zauna Kusa dake.."Ya Fada yanq Nufar hanyar da Zai Sadashi da Haraban Gidan Lokaci Daya yana kallon Agogon Fatan Dake Hannunshi.

Iya tabi bayanshi da kallon Tsausayi kafin Tace"Insha Allahu Adawo lafiya Alhaji.."Bai Jita ba Don ya Riga yaFita Daidai Lokacin Kuma Garzali ya Sawo kan Motar Cikin gidan ya Dawo Daga kai Su Basma mkranta batare da bata Lokaci ba ya Shiga ya Juya Dashi Zuwa Office don Ya Makara gashi Kuma Meeting garesu Suna Tafe yana kallon Agogon Dake Tsitsiyan Hanmunshi kafin Wayarsa kirar iphone 11 promo,tadauki Tsuwa Sunan Ishaq ya Fito baro baro Afuskar Wayar Dauka yayi Da Hanzari suka gaisa kafin Su Cigaba da mgana Cikin Kulawa da Tsantsan Ilimi.

********

*D'ANBATTA*

Goggo Abu Sai Dai Taga Farida Kwatsam Tazo Tana Mata Kuka Wiwi kamar Wacce Aka yanka Ko Akace Uwarta ta Mutu Lokacin Data Iso Ashe na gidan,nan Goggo Abu Ta Rude Ta Shiga Tambayanta Abun ya Faru,Farida na Kuka tana Zayyanama Goggo Wai Tahir ya mareta Har guda hudu Dukkanta ma yaso yi sai da iya mai aikinsu Ta Shiga Tsakani Farida na Kuka Tanama Goggo Abu Rantsen Rantsen Cewa Tahir yace ma bata da Wani Amfani Acikin Rayuwarshi.

Ran goggo Abu ya baci Ta Dinga Sauke Numfashi Takaichi Attahiru na Damunta Ashe ce Tace"goggo Kada ki yanke Hukunci Cikin Fushi yakamata Shima yayan Ki kirashi ki Fara jin Ta Bakinshi Tukunah.."Tafada Da Sigar Lallashi,Cikin Kuluwa Farida Ta Dago Tana Hararan Ashe kafin tace"Eh mana Akirashi mana ai ba karya namai ba Jiya agaban ya'yana Da yan Aiki ya Tozartani nidai kam goggo Ki kirashi na Gama zama da Tahir kamar yadda yace banda Wani Amfani Acikin Rayuwarshi Nima Tahir baida Amfani Awajena ya"yana yaje ya Rike na barmai Dama badasu nazo ba..."Tafada Tana Shesshekan Kuka Lokaci Daya Tana Hararan Ashe din Domin Dama Jininsu baizo Daya Saboda yadda Tahir yake matukar ji da Ashe Ita Kuma Duk Abunda ya Shafi Dan"uwanta bata Wasa Dashi.

Ashe bata mata mgana ba illah kallon Goggo Abu Datakeyi kafin Tace"Kinji goggo Don Allah Kifara Kiranshi Tukunnah.."Jin Haka yasa goggo Ta Mike Ta Shiga Ciki Ta bar Ashe da Farida Anan Cikin Falonta Kowa na kallon Kowa Cike da Takaichi Mikewa Ashe tayi ta Fice Zuwa Shashen Innaro Tana Fadin"Allah ya kawo maka mafita Dan"uwana..."Tafada Cike da Habaici da Kuluwa,Da Ido Farida Ta Bita kafin Ta Rakata da Tsaki Tana Share Kwallah.

Fitowarsu kenan Daga Meeting yana Hanyar Komawa Office ya Fito da Wayarshi Wacce Tun Shigansu meeting din ya sakata A Silent Hankalinsa ne ya Tashi Ganin Misseds Rututu Na goggo Abu gabansa sai dai ya Fadi yana Bude Kofar Office din ya Na Kokarin Kiranta gabda zata Katse Ta Dauka yana Kokarin gaisheta ta katseshi A Fusace Tana Fadin"Dagata min Attahiru Nagode da Abunda Kamin in Har na Isa dakai kazo gida yanzu ka sameni mutumin banza kawai..."Tafada Cikin Fushi kafin ta yanke Kiran,Dafe kai yayi yana salallami,Domin yasan Cewa Farida Tagama Hadama goggo Abu Famfo shi bama Wannan ya Dameshi ba Irin yadda Ta Dau Zafi Dashi Allah ne kadai Zai Kwaceshi.

   Office din Ishaq ya Tafi Agurguje Sukayi mgana Sama sama Kafin Suyi sallama ya Fito bai Tsaya bata Lokaci ba yace ma garzali Su kama Hanyar Danbatta sai da Sukayi Nisa ne Garzali ke Tunamai dasu basma Ba Wanda Zai Daukosu Daga Sch,Dafe kai yayi yana Salati kafin ya Dauki Wayanshi Shugaban mkrantan Su Basma ya Fara Kira inda yabada Umarnin Indan Antashi Daga Mkranta Basma da Bassam Su bi Sch Bus Su Dawo gida Saboda Dukkansu basunan bamai Zuwa ya Daukesu,Daganan sai Shugaban Mkrantar su Mufeeda Itama Abunda yace Kenan Kafin ya Katse Kiran,yana Sakin Numfashi kadan yasan yau sai sunyi Rashin Islamiya Saboda baita yarda Sun Fita Waje Su kadai ba Duk inda Zasu sai dai garzali ya kaisu Kuma yana Da Tabbatacin Tunda Sukaga babu mai Kaisu bazasuyi gangancin Fita ba.

Wajen 2pm suka iso Kofar gidan Hakimi,Shikanshi Hakimi da Jama"arsa Sunyi mamakin ganinshi don Akasari bai Cika Zuwa Cikin Sati ba Sai karshen Sati,Hakimi bai yi mamaki Sosai ba Saboda yaga Zuwan Farida Hartazo ta gaisheshi Yaga Fuskarta ta Chanza kamar tayi Kuka Daya Tambayeta sai tace bakomai tatashi Ta Shiga To Tunda yaga Zuwan Tahir sai yasha Jinin Jikinsa Ammh Dayake yana da Miskilanci sai bai Nunama Tahir din Komai ba Wanda Sai da yagama gaisawa da Jama"ar Wajen kafin ya Karisa garesa yana Kwasan gaisuwa,bayan Tambayi Aiki da yara,bai Zauna ba ya Mike yacemai Zai Shiga Cikin gida,Hakimi yayi Mirmishin su na manya kafin ya kalli Tahir din yana Fadin"Attahiru yau kazama Mara Hakuri ko...? Akullum ina maka Nasihan ka Rika kai Zuciyarka Nesa Domin Akasari mata akarkarce suke Kana Kokarin Daidatasu Suna kara famdarewa ne,Toh Dole sai munyi Hakuri Dasu kaji...?"Yafada kasa kasa Wanda Inba Tahir din ba Wanda yakejin meyake Fada,Sadda kanshi yayi kasa yana Fadin"Naji Hakimi Insha Allahu Zan Kiyaye.."Kai ya gyada kafin yace"Tashi ka Shiga Ciki Allah yayi maka albarka.."Da Ameen ya amsa kafin ya Wuce Zuwa Cikin Gidan...

Sheshen Innaro ya Wuce Direct nan Suka Ci karo da Inna Fulera ta Zube Tana gaisheshi ya amsa Cikin  sakin Fuska Kafin ya Wuce Zuwa Babban Falon Innaro Dake Shashenta,Nan ya iske Innaro da Ashe Suna Hira,Ashe Dataji Dadin ganin Dan"uwanta sai da tatashi ta Fada Jikinsa Tanamai Oyoyo Riketa yayi yana Dariya Lokaci Daya yana Shafa Kanta,Tare Suka Zauna gaban Innaro,Tahir yafara gaisheta ta amsa Cikin Sakin Fuska da Fara"a Tana Tambayanshi su Basma ya amsa da Suna Mkranta,Yadade Awajenta Suna gaiswa da Hira kafin ya barota Zuwa Shashen Goggo Abu Ashe bata biyoshi ba Saboda tasan Goggo Abu Korarta Zatayi.

Lokacin Daya Sawo kanshi Falon goggo Abu Da sallama Abakinshi da Farida yaci karo Tayi Rashe Rashe Atsakiyar Falon Tana Shan Fura,Suka Hada Ido,Daure Fuska yayi kamar bai Taba Dariya ba yana karisowa Cikin Falon Goggo Abu Tana Fitowa Daga Uwar Dakinta Suka Ci karo,Takalmin kafarsa yacire kafin ya Zauna yana gaishe da goggo Abu Wacce Ke Dankaramai Harara kafin Tace"Tashi Tsaye bana Bukatar gaisuwaarka Attahiru,domin ka gama Nunamin Iyakata..."Tafada Cikin Kakkausan Murya.

Kasa yayi Dakai yana Jin Wani Daci Acikin Ransa,Dagowa yayi yana Kallon Farida Wacce Ke kallonshi gabanta ne yafadi ganin Irin Kallon Dayake Jifanta Dashi bai iya mgana baa,sai ma Sauraran Goggo Abu Dayayi Tayi Ta Inda Take Shiga batanan Take Fita ba Sai da Tagama Wanke shi Tas Kamar Zata Dakeshi Ta Koma Gefe Tana Haki,sai da yaga Ta gama kana ya Dago yana kallon Goggo Abu kamar yayi kuka yana Fadin"Goggo Ta Fada miki Fita Take bada Izinina ba,Ta sanar dake batamin Kallon Mijinta Dauka na Take tamkar Wani yaronta ko Ma"aikacinta Ta gayamiki Wannan Ko bata gayamiki ba.."?Yafada kamar Zai Fashe da Kuka.

Daga Farida Har Goggo Abu Jikinsu yayi Sanyi Saboda yadda Tahir din yayi mganar,Sai goggo Abu Ta Koma Da Kallonta kan Farida tana Fadin"Kinji Abunda Mijinki yace In Hakane To Tabbas baki kyauta ba,Taya zaki Dinga Fita bada Izininsa ba Ai ba Zaman kanki kikeyi ba Ko Farida,Gaskiya ki gyara Kina Cikin Fushin Allah da Tsinuwar mala"iku matukar baki Roke Mijinki Gafara ba.."

Farida ta kanta ke kasa ta Fashe da Kuka,Jawota Jikinta goggo Abu Tayi Tana lallashinta Lokaci Daya Tana Fadin"Yi Shuru kibar Kuka,Ki bama Mijinki Hakuri Kune mi gafaran Juna Don Allah bana Jin Dadin Wannam Rashin Jituwar naku,kufa ba yara bane Kune fa Kuke da yara kamar basma da bassam Haba Don Allah Farida Don Allah Ku Sansanta kanku.."Tafada Cikin Sanyi Dagowa Farida Tayi Tana Share Kwallah kafin tace"Toh Goggo.. "Muryanta ta Dishe Sosai...

  Mirmishi goggo Abu Tayi kafin Ta Mike tana Fadin"Yauwa Naji Dadi bari naje na Karboma Atrahiru Fura Wajen Innaro yanzu zan Komo ."Tafada Tana Ficewa Don ta basu Waje bayan Fitanta Falo ya Dade Shuru kafin Farida ta yanke Shurun bayan Ta Dago Tana kallon Tahir Daya Tsurama Cafet din Goggo Abu Ido Fuskarsa ba Annuri ko Kadan Duk da gabanta na Fadi hakanan ta Daure Ta Furta.."Srry...'Tafada Muryanta na Rawa Ko kallonta baiyi ba,ganin Haka yasa sai Jikinta yayi sanyi Tatashi Ta Koma Side din daya ke kallo Ta Sake Furta"Am Srry..."Kauda kai yayi Yana Neman Tashi sai Ta Riko Hanmunshi Da Sauri ta Fashemai da Kuka bayan ta Dora kanta bisa  Cinyarsa,tsayawa yayi yana Kallonta Kukanta na Dakarmai Zuciya,Runtse ido yayi kafin ya Dora Hannunshi bisa kanta yana Tapping cikin Ajiyar Zuciya yake Fadin"Shiii...is ok.."..

Jin Abunda yace ne yasa Ta Dago Da Sauri Fuskarta Jage jage da Hawaye,tana kallonshi Mirmishi ya sakarmata kafin ya Zaro Wani Farin Hankey Daga Aljihunsa,yana Share mata Hawaye yana Fadin"Nace komai ya Wuce ko..? Kece fa kike ja muna Fada Farida,in da bakiyi Saurin Zuwa Wajen goggo Abu banayii Regreating din marin da nayi miki zan baki Hakuri,plz Farida..."Bai karisa ba goggo Abu Ta Shigo Dole yayi Shuru ganinsu haka sai ya sanyayamata Rai,Furar ta mikamai ta sake Ficewa,yana kallon Farida kasa kasa yafara Shan Furarsa,yana gamawa ana Kiran sallar La"asar nan yafice Zuwa Msallaci Ita Kuma goggo Abu Ta Dingama Faridar Nasihan bayan Suma Sun Idar da Sallar.

Bai komo dakin Goggo Abu ba sai da ya sallami kanwarsa Ashe,Har gida ya karata akafa suna Tafe Suna Hiransu gwanin ban Sha"awa,sai da ya Dawo ya Shigo bangaren Goggo Abu yace Farida tataso Su Tafi,nan ma goggo Abu Hadasu Tayi tana musu nasiha Sosai kafin Su mata sallama Shashen Innaro Suka Koma Suka mata sallama nan Tabada Sakon Fura mai Dadi Tace akaima basma da Bassam,Awajema Sallama Suka ma Hakimi ya bisu Shima da Sanya albarka.

Tahir shi ya Tukasu Shida Farida Acikin Motarta Shi Kuma garzali ya Tuko ta Tahir,acikin Motan Ma Hannunshi Farida Ta Damke tana Fadin"Shine ni baka bani Hakuri ba.."Tafada Cike da Shagwaba,Hankalinsa na Wajen Tuki ya Waigo yana Fadin"Ah...Waht Are u Eating na baka is Fooling Down,Zan baki mana ammh ai kinsa nawa Is so Special ko.."Yafada yana kallonta Lokaci Daya yana Kashe mata ido,Dariya tayi tana Kwantar da kanta Cikin kujeran Mota batace komau ba Ammh Hannayesu Sarke da Juna Jefi Jefi suna Hira Har Suka Kariso gida.

  Abun mamaki Haka yaran Suka ga Iyayen nasu Sun Shigo Hannuwansu Sarke da Juna,Saboda Jin Dadi basma da bassam Suka Ruga suka Rumgumesu suna Ihun Oyoyo momy da Daddy,Hatta Iya da Mufeeda Sunji Dadin ganin Farida da Tahir Da Alamun Komai ya Wuce,Ranar dai gidan Gabadaya yayi Dadi Dukkansu tare Sukayi Dinner Suna Yi Suna Hira Fuskar ya"yansu cike da Farinciki,Da Suka gama Cin Abunci Suka koma Falo Suna Hira da ya"yansu Hatta Naila Taji Dadi Sosai ganin yadda Take Tsallake Tsakanin Cinyar Tahir dana Farida,sai Wajen Goma Kana Suka Umarcin yaran da Su Tafi Dakinsu su kwanta Naila Kuma Farida Ta Mikama Mufeeda.

Awannan Daren dai Farida ta Hakura ta bama Tahir Ahakkinshi nan Suka Fahimci Duka Sunyi Kewar Juna,Farida tagayama aya Zagi,domin Tahir dai sai da ya Fanshe,koda Asuba ma Daya Dawo masallaci sai da Ya Dora Farida Tafara gajiya Sosai Sai Tura baki Takeyi Domin Abunda Ke Hadata Tahir kenan Jarabarsa.

*HIJABS CORNER BY JANAFTY*

*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design,  muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*


*Aisha Alto..*
*Janafty*