Chapter 10
Ilham ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba lokacin da Momy ta sanar da ita an bawa Saddik izinin fara zuwa zance wajenta. Ta san tunda har Dady ya amince masa tabbas ya yi shawara da su Yaya Sudais, kenan hakan na nufin duk roƙon da ta yi masa bai amince ba? Sosai take kuka kamar ranta zai fita, wayar ta ɗakko ta kira Zahra, bugu biyu ta ɗaga, cikin kuka ta ce "Zahra Yaya Sudais baya sona. Duk magiyar da na yi masa bai sa ya saurare ni ba, yanzu shikenan haka za a aura mini wanda ba na so? Zahra ya zan yi da soyayyar Yaya Sudais dake cikin raina, wallahi ji nake yi ba zan iya rayuwar aure da wani ɗa namiji ba in ba shi ba" ta kai ƙarshen maganar numfashinta na sarƙewa. Ita ma Zahra cikin kuka da jin tausayin ƴar uwarta ta ce "Ki yi haƙuri Aunty Ilham, wata ƙila aurenki da shi ba alkhairi ba ne shi ya sa Allah ya haɗa ki da Saddik, amma kuma Ulcer ya ce da amincewarki".
"Haba Zahra taya zan amincewa wani bayan ga wanda nake so? Wallahi wannan duk shirin Momy ne" Ilham ta faɗa tana sake fashewa da kuka.
Cikin mamaki Zahra ta ce "Ikon Allah, to me ya sa Momy ta yi haka? Ke kuma sai ki yarda? Ai da kin sanar da Uncle gaskiya". Ilham ta ce "Ta hana ni yin magana ne, ta ce idan na ƙarya ta abin da ta ce sai dai na nemi wata uwar".
Zahra ta ce "Subhanallah! Ki yi haƙuri Aunty, in sha Allah za ki ji daɗinsa, sannan duk wannan abin idan Allah ya ƙaddari Yaya ne mijinki sai ki ga kin aure sa". "Ubangiji Allah ya ƙaddara Zahra, Allah ya sa shi ne mijina ba Saddik ba" Zahra ta amsa da "Amin" nan ta shiga ba ta haƙuri tare da kwantar mata da hankali, har ta samu ta ɗan saki jiki.
****
Bayan kwana biyu an sallamo su Inna sun dawo gida. Alhamdulillah jikin Abida da sauƙi, ƴan dubiya suka ci gaba da zuwa gida suna duba jikin. Halima gabaɗaya ji take yanayin jikinta ya sauya kamar ba na ta ba, komai cikin sanyin jiki take yinsa, wani lokacin dauriya ne kawai take yi tana yin aiki saboda jikinta babu ƙarfi, ji take kamar an zare mata lakar jiki.
"Inna"
"Na'am Ma'una".
"Auren ƙawata Hadiza saura sati ɗaya".
Inna ta ce "Ma sha Allah, ashe har abin ya ƙaraso?".
"Eh Inna, ai saboda kina asibiti ne ya sa ban sanar dake ba, gashi ban samu yin anko ba". Ma'u ta yi maganar tana maraice fuska alamar rashin jin daɗi.
Inna ta ce "Haba Ma'u ana ta abin da za a ci wake zancen anko? Kina ganin yadda muke lallaɓa rayuwarmu, ki yi haƙuri da zancen ankon nan, ki na da kayanki masu haske, ki saka abinki ki je ku yi hidimar bikin". "Inna shikenan ina matsayin babbar ƙawar amarya sai na ƙi yin anko?".
Fusata Inna ta fara yi ta ce "Kin ga wallahi idan kika matsa mini zan saka Gadanga ya hana ki zuwa bikin nan. Dan ubanki an ce miki saka anko dole ne? Wai Ma'u sai yaushe ne za ki yi hankali? Kullum gaki nan sai girma kike yi amma abin da kike yi Abida ma ba za ta yi shi ba, bari na sake jin kin yi ƙorafi a kan ankon nan sai na yi mugun saɓa miki, idan ba za ki je a haka ba ki haƙura da zuwa a yi bikin da ke". Inna ta ƙarasa maganar cikin ɓacin rai.
Ma'u na tunzura baki ta ce "Inna ki daina haɗa ni da waccan yarinyar kar ki sa na karairayata, ba ruwana da ba ta da lafiya tsaf zan zane ta". Ƙin kula ta Inna ta yi, nan Ma'u ta ƙarasa hasala ta koma waje ɗaya ta zauna ba tare da ta kula kowa ba.
*****
Ilham ta tarbe Saddik ba yabo ba fallasa, ba ƙaramin yaƙi ta yi da zuciyarta ba wajan ganin ba ta yi masa wulaƙanci ba saboda gargaɗi da jan kunne da Momy ta yi mata, bayan ya zo ne da kwana biyu iyayensu suka tsayar da ranar aurensu nan da wata uku. Sosai Momy ta yi farin ciki da hakan, sai dai da aka sanar da mahaifiyar Saddik cewa ta yi "Ya yi yawa, idan da hali tana neman alfarma a dawo da shi nan da wata ɗaya, saboda za ta aurar da ƴar ƙanwarta da take riƙo tana son a haɗe auren. Ko da Alhaji Bashir ya yi Uncle magana nan ya nuna masa babu damuwa ko nan da sati suka ce za a yi. Ilham jin an dawo da auren nan da wata ɗaya ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, lokaci ɗaya wani azababben zazzaɓi ya rufe ta. Momy kuwa tuni ta fara kiran ƴan'uwa da abokan arziki tana sanar da su.
****
"Hanif"
"Sudais"
"Hanif ina cikin damuwa, gabaɗaya narasa me yake yi mini daɗi, abubuwa sun yi wa kaina yawa, ga harkar business ɗin nan, ga yanayin aikin nan ina shan wahala ba ƴar kaɗan ba. Narasa ya zan yi" Sudais ya kai ƙarshen maganar yana dafe kansa.
Ajiyar zuciya Hanif ya sauke, ya dafa kafaɗarsa ya ce "Abokina ni kaina na san kana matuƙar ƙoƙari, kuma kai jarumi ne, ka ci gaba da gudanar da abubuwanka kamar yadda ka saba, ka da ka bari ka sare, in sha Allah Allah zai ci gaba da dafa maka, sannan aikin da kake magana wannan kai ka yi niyyar yinsa. Sudais ka na da arzikin da ko jikokinka ba za su yi talauci ba, amma ka ɗorawa kanka cewar sai ka yi wannan aikin, albashin da kake karɓa a cikin ma'aikatan akwai waƴanda ke karɓar fiye da shi. Amma ka dage dole sai ka yi". Sudais ya ce "Hanif ba za ka gane ba, wannan aikin shi ne burin mahaifina tun ina yaro, akwai tabon da yake zuciyata wanda ta dalilin wannan aikin ne zan samu warakarsa, ba zan taɓa manta mahaifina ba, haka kuma ba zan taɓa manta kalamansa na ƙarshe ba, ba zan manta sautin ƙarshe da ya fito daga bakin mahaifina ba. Hanif ba zan iya haƙura da wannan aikin ba, in sha Allah sai na binciko duk wasu azzaluman ƙasar nan. Sai na binciko su waye suka cutar damu kamar yadda Abbana ya faɗa, sai na gano wace irin cuta ce aka yi mana, wannan ƙudurin da shi na taso a cikin zuciyata. Kuma in sha Allah sai na cika burina". Hanif kallon Sudais ya yi da idanunsa suka kaɗa suka yi jawur, jijiyoyin kansa duk sun tashi. Ya ce "Shikenan Sudais, Ubangiji Allah ya taimake ka ya ba ka nasara, Allah ya kare ka daga dukkan wani abin ƙi da sharrin masu sharri". Shiru Sudais ya yi yana jin yadda zuciyarsa take tafasa, a duk lokacin da zai tuna Abbansa sai ya ji tamkar ya kurma ihu saboda damuwa. Ƙyale shi Hanif ya yi, ya tashi ya bashi guri saboda ya san ba kula sa zai sake yi ba, yana fita Sudais ya kwantar da kansa a jikin teburin dake gabansa ya lumshe idonsa.
*****
Alhaji Sango ne ya tura ƙofar ɗakin da take ciki ya shiga cikin isa da gadara yake faɗin "Amaryata, ina fatan dai kin tashi? Ga angonki ya zo ku yi ganawar saf..." Maganarsa ce ta maƙake sakamakon ganin ɗakin wayan babu kowa a ciki, murza idonsa ya yi yana sake kallon ɗakin bai ga kowa ba, dubansa ya mayar inda ake ajiye yaron nan ma babu sh. Da sauri ya tura ƙaramar ƙofar toilet ɗin dake cikin ɗakin nan ma babu kowa, a mugun firgice ya fita daga ɗakin yana ƙwalawa Zaki kira, harabar gidan ya fito in da masu gadin gidan ke tsaye, ko wanne fuskarsa babu alamun rahama a tattare da su. Cikin hargagi ya ce "Kai! Ina yarinyar nan ta tafi ne? Na duba ba ta ciki ita da yaron nan". Zaki ya ce "Oga ban gane ba ta ciki ba? Tana nan ciki mana, ko ɗazu sai da na duba ta". "Yi mini shiru" Sango ya ce yana zazzaro ido waje, ya ce "Ba ta cikin gidan nan". Ciki Zaki ya wuce da sauri, Sango ya bi bayansa, ko ina ya duba a cikin ɗakin bai ganta ba, idonsa ne suka sauka a kan tagar ɗakin. Ya ga tagar a buɗe an cire ƙaramin gilas ɗin dake kai. Babu shiri Zaki ya ce "Kan bala'i, Oga yarinyar nan ta gudu, tabbas guduwa ta yi, kuma ta nan ta fita" ya yi magana yana nuna masa tagar. Mutuwar tsaye Sango ya yi, cikin ihu ya ce "Me ye amfanin ku da har za ku yi sake ta gudu? Wallahi na baku nan da awa biyar maza duk in da yarinyar nan take ku dawo mini da ita tare da wannan yaron. Na san tana cikin dajin nan ba za ta iya fita ba".
"An gama Oga tuba muke" daga haka Zaki ya juya da sauri ya fita. Alhaji Sango ma barin gidan ya yi zuciyarsa na bugu da ƙarfi, idan yarinyar nan ta gudu ai ya kaɗe.
*****
Aliyu ya dubi Halima da kyau ya ce "Wai me yake damunki ne kwana biyu naga yanayinki ya canza gabaɗaya? Ko ba ki da lafiya ne?".
Halima ta sauke numfashi ta ce "Nima ban san abin yake damuna ba haka kawai ba na jin daɗin jikina". Aliyu ya ce "Kefa ba yarinya ba ce da za ki ce ba ki san me yake damunki ba". "Haka ne, amma dai wannan na kasa tantance me nake ji, amma tabbas ba ni da lafiya a jikina". Ta bashi amsa, shiru ya yi yana kallonta kafin ya ce "Allah ya sauwwaƙe" ta amsa da "Amin".
***
Tun wajen ƙarfe goma na safe suke bulayin nemanta amma ko mai kama da ita basu gani ba. Gabaɗaya sun karaɗe dajin nan ba su ganta ba, cikin takaici Zaki ya ɗaga waya ya kira Sango, bugu ɗaya ya ɗaga yana faɗin "Kun same su ne?".
"A'a Oga, wallahi mun duba dajin ko ina bamu ganta ba" cikin tsawa Sango ya ce "Ban son maganar banza, kar ku yarda ku dawo mini ba tare da su ba. Duk inda suka shiga ina son ku nemo mini su". "An gama Oga" Zaki ya faɗa tare da kashe wayar suka sake kutsawa cikin dajin.
***
Da ƙyar da wahala ta ƙaraso bakin titin. A lokacin ta gama galabaita tafiya ma da ƙyar take yinta, ga yaron dake goye a bayanta yana ta faman kuka saboda azabar yunwar da yake ji, ga wahalar da ya sha ta gudun da aka yi da shi. Wata rukuɓaɓɓiyar mota ce akori kura ta zo. Ɗaga mata hannu ta yi, motar har ta yi gaba ta dawo baya, dattijon dake jan motar ya ce "Yarinya me kike yi wa tsayi a cikin wannan guri mai haɗarin gaske?" Cikin ƙarfin hali ta ce "Ka taimaka muna ka bar gurin nan damu, idan suka kama mu za su kashe mu". Da sauri ya fito daga cikin motar ya karɓi yaron ya buɗe motar ya saka shi, sannan ya ce ta shiga. Shiga ta yi tana sauke ajiyar zuciya. Da sauri ya shiga motar ya ja suka bar gurin.
Har yamma suna nemansu ba su gansu ba, Alhaji Sango hauka ce kawai bai yi ba. Zagi ta uwa ta uba yake yi wa su Zaki, tare da basu umarnin kar su dawo inda yake har sai sun nemo su duk inda suka shiga.
Amanarcool
***