MARTANI BY RUKAYYA YUSUF IBRAHIM (A. Y. M Creatives)

Episode 4

by @aymcreatives


Jim yayi yana tunanin ina ya taɓa ganin fuskar dan ba zai iya tantancewa ba. 

____ 

 

 

Episode 4 

 

Juyawa tayi da sauri don barin gurin yayi saurin dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa . 

Cak ta tsaya tana dubansa, yayinda shi kuma ya tunkaro inda take yana watsa mata wani kallo. 

Sai da yazo daf da ita ya ja ya tsaya yana kallonta, ta sunkuyar da kanta zuciyarta na dukan uku -uku. 

" Kamar nasan wannan fuskar taki " kalamansa su ka dawo da hankalinta gare shi. 

Gyara tsayuwarta tayi ba tare da ta ce masa komai ba. 

Ya ci gaba da cewa" gara da na ganki a falo domin bazanje inda kike ba. 

Zan kafa miki sharadi ne, na farko in har ina cikin gidan nan , bana son ganin fuskarki a falon nan. Na biyu kuma ina so ki tsaya iya matakin ki, domin ban shirya haɗa zuri'a da kowa ba a yanzu, sai na tabbatar da wa aka daura min. 

Domin bana son ahalin kwadayayu a cikin sati da maganar aure tsabar kwadayi har anyi auran an kawo ki , to ki tsaya iya matakin ki ko kwadayinku ya koma ciki, don ni mai iya sakin ki ne a daran nan ". 

Murmushi mai sauti A'isha tayi tana kallonsa ido cikin kana ta ce " ka sake ni yanzu ba tare da na kwana a cikin gidan nan ba? Na rantse da Allah da salloli biyar da nake a rana sai na saka a addu'a Malam. 

To yo ni ai wannan shine burina, a da naji a raina zan iya hakuri na zauna da mijin da su Kawu suka aura min, amma tunda na dora ido naga kaine mijin naji dama kashe ni sukayi da wannan auran naka". 

Galala ya tsaya kallonta don baiyi tunanin akwai ƴa macan da zata tsaya tana masa waddan nan maganganun ba . 

Tsintar kansa yayi da cewa" daman bake kika  ce kina son auran ba kenan?". 

"Wa? Ni? Allah ya rufan asiri. Hala baka gane ni ba, ko da yake daman ni bazaka san ni ba , tunda bana cikin mayun da suke nuna sonka. 

Ni daya daga cikin daliban da kake koyarwa ce level 1 nursing student. 

Baka burge ni kuma ba ka cikin mazan da nake burin aura ". 

Shuru tayi na dan mintuna da alama wani abun ta tuna, ta su sauke numfashi ta cigaba da cewa" kayi hakuri dan Allah Sir , nakasa dan control din kaina da na ganka a matsayin Mijina. 

 Don Allah ka sauwaƙe min kamar yadda ka fada, mu rufawa juna asiri please, nasan maganganun da nayi  suna da zafi ka yafe min". 

"Me ne ne sunan  ki?" . 

"A'ishatu Aliyu Usman " ta ba shi amsa. 

" Kamar yadda na faɗa ki ja rayuwarki bana son ki dinga shiga sabgata". 

"Idan na shiga sabgar taka saki na zakayi?". 

"Malama karki sake  ki fusata ni, kuma tunda saki kike so wallahi a gidan nan zaki mutu ko in na mutu ki bar gidan shasha . 

Wai bana burge ki , bana cikin maza da kike burin aura ko. To wa cece ke , me kike takama da shi ? Kyan sura ko ilimi ko kuma dukiya? . 

To bari kiji dole ki bi umarnina ko kina so ko bakyaso. Shasha yarinyar ko kunya baki da ita, a ranar farkon a gidan miji kina sa'insa da shi . 

San nan kada ki kuskura ki nuna kin sani ko a makaranta ko a waje koma a ina ne domin ni abun kunya ne na nuna ki a matsayin matar Ashraf ". 

Murmushi tayi tana kallonsa ido cikin ido ta ce" babu komai Sir daman ni ban fadawa kowa anyi min wannan jalllararan auran ba. Na yi matuƙar farin ciki da jin wannan sharadi domin nasan nan kusa dole a sallame ni zuwa gidan mu ko kana so baka so. 

San nan ina mai baka shawara kaja girmanka don Allah, karka ce zaka dinga faɗa min magana any how, don ni a yadda nake son rabuwa da gidan nan babu abunda zaka faɗa min ban mayar maka da MARTANI ba". 

Ashraf kasa magana yayi a zuciyarsa yana aiyana ko ina su Kawu suka samo wannan jarababiyar yarinyar oho. 

Ta murguɗa masa baki tayi shigewarta daki . 

Ƙwafa yayi ya haura sama yana aiyana irin matakin da zai dauka a kanta. 

A'ishatu tana shiga daki ta saki kuka, bazata juri auran dole ba da kuma cin mutunci, don haka ta daura aniyar zama da shi a duk yadda ya tsara zaman nasu. 

Wanka ta shiga yazo ya saka daguwar riga ya bacci tayi addu'a ta kwanta amma bacci yaki zuwa sai tunani-tunanin wannan rayuwar da zata fara take , wai Sir Ashraf shi ne mijin. 

" Kai!  impossible " ta faɗa a fili. 

Tuna yadda ake roshing akansa , ga Summayya ƙawarta da ita ma take mugun son sa. 

___ 

Washe gari A'isha tunda ta tashi da asuba bata koma ba, karatun Alkur'ani da addu'a ta dinga yi har rana ta fara fitowa. 

A ƙa'ida yau suna da lacca amma tasan ko ta ce zata bazai yiyu ba don haka tayi wanka ta shirya cikin riga Three quarter da siket. 

Wasu hawaye ne suka zubo mata da ta kai idanunta kan akwatunan da aka mata a matsayin lefe. 

Cin mutumcin da Kawu Sani yayi ma Ummanta ne ya faɗo mata, da yake cewa" Hadiza ga sadakin yarinyar dubu dari uku ga kuma lefe nan iya ganinki. Karki yi halin tsiya ku kwashe mata kaya domin ko tsinke kuka taɓa sai sun gane, a daure akai zuciya nesa. 

Domin tabbas Shatu me kashin arziƙi ce, miliyan daya suka bani Ni da ƴan uwana na shirin biki don haka bazan bari a taɓa musu komai don na san ku ke da danginku baku gaji arziki ba". 

Hawaye ne suka zuba a idonta ta zauna ta kasa daurin dan kwallin dake kanta. 

Sadakin da Umma ta bata ta duba jakarta ta gansu muraran . 

Take ta shiga tunanin me ya kamata tayi da su. 

Sallamar Yaya Rumana ce ta dawo da ita ga tunanin da take , tayi saurin maida kudin ta fito falo. 

Yaya Rumana ce rike da Breakfast a maidadaicin kwando ta tsuguna har kasa ta gaida A'ishatu. 

Cikin sauri A'ishatu ta miƙar da ita tana cewa " haba don Allah, karki sake durƙusa min bana so Please". 

Murmushi Yaya Rumana tayi ta ce" ai dole na durƙusa miki Hajiya tunda a karƙashinku nake aiki". 

Numfashi A'ishatu ta sauke ta dagta ta ce" Yaya bana so don Allah, karki ƙara durƙusa min. Ni ba ƴar kowa ba ce ban saba inga babban mutum na durƙusawa na kasan sa ba kinji". 

Wata boyayyar ajiyar zuciya Rumana tayi kafin ta ce" daman na kawo abun karyawa ne, san nan zan yi shara da mopping ". 

A'ishatu ta kalleta kafin ta ce" ki koma ki huta, zanyi da kaina ". 

Cikin waro ido Rumana take kallon A'ishatu ta ce" don Allah ki rufa min asiri Hajiya ai wannan  aikina ne". 

Bata tsaya jiran me zata ce ba ta shiga kitchen don dauko tsintsiya. 

Takunsa daga sama ya dawo da idonta inda yake daga kallon kofar kitchen din da Yaya tayi. 

Zuba mata ido yayi yana watsa mata harara har ya sako. 

Duban kayan Breakfast din yayi ya ja kwandon zuwa saman dining, budewa yayi dankali da ƙwai ne sai ruwan tea. 

Gajiya tayi da kallon sa ta bi Yaya kitchen ganin har yanzu bata fito ba tana cewa" na ce kizo ki huta, zanyi komai don Allah". 

Yaya Rumana kuwa ta dage tana goge saman dorowar kitchen tana cewa" Allah ba ruwana sai nayi aikina Hajiya". 

Shiru A'ishatu tayi mata har ta kammala ta fito da niyyar gyaran falon ta tarar da Ashraf na breakfast. 

Saurin dauke kai tayi tunawa da tayi A'ishatu na bayanta ta tsuguna tana cewa " barka da safiya Alhaji" da mamaki yake kallon Yaya Rumana harda miƙewa. 

Ita kuwa ganin yana shirin rusa musu plan ta yi gaba tana kaɗe kujeru da duster hannunta. 

Idonsa ya kai kan A'ishatu yana maka mata wani mugun kallo ya ce" me nake gani haka? Ba dai aiki take miki ba?". 

Ita ma kallonsa tayi kafin ta gyara tsayuwarta ta ce" ga shi kana gani kuwa". 

A fusace ya ƙaraso inda yake yana cewa " don baki da tarbiyya kamar wannan zaki tsaya tayi miki aikin gida?" . 

Saurin dakatar da shi tayi da cewa" Sir don Allah ya isa, bani na ce tazo tayi aikin nan . Tun jiya Aunty Zeenah ta kawo ta a matsayin mai aikin da zata dinga taimaka min. 

Ni  har a zuciyata ma bana son kowa yayi min wani aiki, shiyasa da tazo na ce ta tafi amma taƙi". 

Murmushin kin raina min hankali yayiwa A'ishatu ya ce" tun muna shaida juna ki sallameta, kuma ba ita ba karna sake naga wata a cikin ɓangaran nan da sunan mai aikin ki , idan kuma ba haka ba zan nuna miki asalin kalata". 

Yaya Rumana ce ta ce" kayi hakuri yallabai don Allah, laifina ne ba nata ba". 

A'ishatu ta kalle ta kafin ta ce" kinga jeki abunki, babu abinda ya isa yayi min duk kuri yake ". 

Cike da mamakin kalaman A'isha Rumana ta fita daga part din nasu tana tambayar kanta" ko dai daman sun san juna ne?  Me yasa daga jiya zuwa yau har sunyi sabon da zasu dinga sa'insa da juna haka ". 

A ɓangaran Ashraf da A'isha kuwa kallonsa tayi ta ce" ka riƙe girmanka Malam na faɗa ma, mu muddin baka ji kunyar faɗa min magana a gaban wani ba, to ni ma ba zan ji kunyar maida maka da MARTANI ba". 

Hannunsa ya miƙa da niyyar kwaɗa mata mari, ai kuwa ta tsaya tana kallonsa ido cikin ta ce" lallai ashe ragon namiji aka liƙa min , duk namijin da zai daki mace ai maza ya rako balle kuma namiji mai dukan matarsa". 

" Kar ki sake kiran kanki da mata ta Malama , banza ƴar ƙauye kawai" ya juya ya dauki car key dinsa ya bar gidan. 

 

___ 

Yaya Rumana babban falonsu ta shigo tana waige Zeenah da Labib na breakfast suka tsira mata ido. 

Zuwa saman dining tayi tana ajiyar zuciya Labib ya ce" me ya faru ne Yaya?". 

"Matar Ashraf Labib anya ba muyi kuskure ba?" Cewar Yaya Rumana.