Rabin Raina

9. Coffee, again

by @inkedbynadeerah

Najib bai daɗe da barin gida ba Hasina ta fito daga ɗakin ta ta samu mahaifinsu shi ɗaya a dining area. Ta gaishe shi sannan ta fara cin abinci. 


"Abba ya Najib ya fito kuwa?”


Mahaifinta yace, "Eh, bai wani daɗe sosai da ficewa ba. Akwai wani abu ne?"  


Hasina tace, "Dama zan tambayeshi abu ne." 


"Ki kira wayanshi mana?"


"Ai Abba ba lallai ya ɗauka ba, amma dai zan gwada na gani." 


"To shikenan." Yayi wa 'yarsa sallama sannan ya wuce sama rarrashin matarsa don ya lura kamar ta bar gurin cikin rashin daɗin rai.


Hasina kuma tasha alwashin yau zata dage ko kwanan living room sai tayi don taga yayanta. Amma kafin hakan, ta yanke shawaran kiran Maryama a waya saboda kada taji shiru batun bracelet ɗinta.


****

Maryama ta shafe lokaci mai ɗan tsawo a salon ana gyara mata gashi. Da aka gama ta dubi kanta cikin mirror. Komai yayi yadda take so cikin kyau da tsari. 


Ta ɗan gyara fuskarta da powder sannan tabi lips ɗinta da lip gloss, ta yafa gyalenta ta ɗauki hand bag ɗinta tare da yiwa ma’aikatan salon ɗin sallama. Ta ƙarasa inda motarsu ke ajiye a harabar salon ɗin ta shige, driver yayi shopping mall da ita.


****

Cikin driving Najib yaji wayarsa na vibrating. Screen din wayar ya duba dake manne jikin car vent mount. 


Cousin ɗinsa ce. 


Yatsa yasa yayi swiping screen, yayi receiving call ɗin tareda sawa a handsfree. 


"Fatima amarya.”


Fatima tayi dariya ta ɗayan layin. 


"Ya najib gauro mai karya alƙawari.” 


Shima Najib yayi dariya dajin haka.


"Haba Fatima, you know i am not always like that. Dole akwai dalili.”


"To ya Najib gaskia kayi ƙoƙari kazo before you leave. Habib ya faɗa min kusan kullum kuna haɗuwa, yace yau ma zaku haɗu, kuma nasan ka kusa komawa. 


Nayi mamaki ma wannan karon ka ɗan daɗe baka tafi da wuri ba.”


Najib ya murza steering wheel a lokacinda yabi wata kwana kan titi daya sha shimfiɗa.


"Inn shaa Allah i’ll come and see you very soon.” 


“Yauwa yayana na kaina… 


Sannna kasan dai bazaka taho da hannu empty ba ko? You know my favourite snacks.” Cikin zolaya ta ƙarasa maganarta.


Najib ya murmusa. “Kada ki damu. I won’t disappoint you. Take care.”


Sukayi sallama da juna sannan call ya katse ta wajen ta.


Tabbas, Fatima na ɗaya daga cikin ʼyan uwansa da yake ji dasu. Duk da shi mutum ne marar magana sosai sannan ya girme ta da shekaru, bai hanasu zama kusa da juna ba.


Dalilin hakan ya samo asali ne tun suna yara. Sunyi primary da secondary school ɗaya a gida Nigeria, sannan sukayi attending University ɗaya a ƙasar Canada. 


A duk shekarun da suke makaranta, Najib ne komai nata. Tun tana takura masa yana share ta har ya haƙura ganin bata da wani na kusa da ita sai shi. 


Ƙulluwar soyayyar Habib da Fatima ya samo asali ne da abokantakar dake tsakanin Najib da Habib. Hakan yasa ta san Habib sosai har yakai ga faɗawa kogin son juna zuwa ga maganar aure. 


Najib da Habib sunyi graduating a tare, sannan Fatima tayi nata graduation ɗin bayan wassu ‘yan shekaru


Suna kammala karatunsu bada daɗewa ba, Najib ya fara managing branch na company ɗin mahaifinshi dake Canada, shima Habib ya koma Nigeria ya fara aiki a nasu branch ɗin.


Har a lokacin Najib yaci gaba da nuna wa Fatima kulawa irin na ‘yan uwan jini tsawon lokacin data kammala nata karatun ta koma gida Nigeria. 


Najib ya dubi lokaci dake nunawa kan touchscreen display ɗin motar sa. Sha ɗaya da kusan rabi. 


Kasancewar yau juma'a kuma zai haɗu da abokansa kafin su wuce masallaci yasa ya ɗan ƙara gudun motar, ya nufi shopping mall ɗinda ke kusa ba tareda ya ɓata lokaci dayawa ba. 


Da isarsa yayi parking, ya ciro wayarsa dake manne da vent mount tare da key ɗin motar. Ya fice daga motar ya rufe, sannan ya danna locked button jikin ƙaramar remote. 


Cikin mintuna ƙalilan da shigarsa ƙayataccen shopping mall ɗin ya wuce coffee island, wanda aka ware gefe guda na ƙayatattun packages na coffee masu tsada daga manyan brands na duniya.


A hankali ya fara bin shelves yana duba irin coffee ɗinda yake so. 


*****


Maryama ta gama shopping har ta juya zata wuce gurin cashier, saita tuna tayi mantuwa. Nan ta juya tare da shopping cart ɗinda ke tare da ita, ta ƙarasa gurin da sanitary pads ke jere kala kala. 


Da hangowa irin wanda take so ta ƙarasa daf da gurin tana mai miƙa hannu saman shelf da niyyar ɗauka, amma hakan ya gagara dalilin tsayinta daya kasa kaiwa.


Najib ya miƙa hannu da niyyar ɗaukan kalan pack ɗin coffee da yake so sai ya hango wata dake ɗan kusa da inda yake. Itama a tsaye take, sai dai ta bashi baya yadda bazai iya ganin fuskarta ba. 


Hannunta na dama ta miƙa zuwa sama tana ƙoƙarin ɗauko abu amma ta kasa. 


Duk da baya iya ganin fuskarta, jikinsa yana mishi kamar yasan wacece. Ya sake dubata da kyau yana tunanin meyasa yake jin hakan? Ya mayar da hankalinsa kan abinda yake son ɗauka.


Ana cikin haka wayarta dake ɗayan hannunta ya fara ringing. Cikin ringing na biyu ta saka wayar daf da kunnenta.


"…Na'am, ya kike ya kwana biyu? I hope kowa na lafiya."


Ana iya jin muryarta a hankali, tana ratsawa cikin sararin wurin. 


Da jin kalamanta, wani abu ya motsa cikin zuciyar Najib. Ya tsaya na ɗan lokaci yana ƙoƙarin tuna inda ya taɓa jin wannan muryan.


Tana cikin waya taɗan juyo da gefen fuskarta, sannan ta juyo gaba ɗaya tana murmushi. 


Lokacin yazo dai dai daya ɗago da kallon sa.


Tabbas… Maryama ce. 


Abinda zuciyar shi ta gama saƙawa cikin waswasi ya tabbatar da idanunsa.


Maryama taci gaba da waya a lokacinda ta sake bashi baya yanda ya daina ganin fuskarta.


"Oh, Allah sarki. Har yanzu baki samu bracelet ɗin nawa ba ko? I'm very sorry na baki aiki…”


Ƙaramin murmushi ya baiyyana a fuskarsa. Ya gama ɗaukan abinda zai ɗauka sannan ya bar gurin.


Maryama ta gama wayan, ta sake miƙa hannu tare da ɗage ƙafafunta ko hannunta zai kai, amma abin baiyi aiki ba. Nan ta yanke shawara zata kira wani daga cikin masu aikin gurin ya taimaka mata. 


A hankali Najib ke tafiya, yana tsayawa lokaci lokaci yana yi kamar yana duba tulin kayayyakin da ke jere cikin tsari. 


Amma hankalinsa na inda take tsaye, lokaci mafi dacewa da zaije kusa da ita yake jira.


Daf da ita ya isa sanda take ƙoƙarin sauƙe hannu. 


Maryama dake tsaye taga an zaro hannu mai dogayen yatsu, an ɗauko mata abinda ta gagara ɗaukowa. 


Cikin sauri ta juya da niyyar ganin waye, bata ankara ba goshinta ya kara da wani abu mai ƙarfi, sannan ƙaran faɗuwar wasu abubuwa a ƙasan floor suka biyo baya.


Ƙamsin turare mai sanyaya zuciya ne ya mamaye mata ƙofofin hancinta sanda ta runtse idanu don jin zafin buguwar da tayi. 


Cikin ruɗewa Maryama ta buɗe idanu tare da sa hannu kan goshinta, sai taga Najib ne tsaye a gabanta. 


Ya kalleta cikin fara’a. Ɗan murmushi ya baiyyana a gefen bakinsa. 


Yanayin data shiga ya bashi dariya.


Hannunsa ɗaya riƙe yake da sanitary pad, ƙasan floor kuma coffee packs ne guda biyu, sai wayarta da makullin motarsa. 


Maryama tayi dara dara da idanunta cikin mamakin ganin shi.


Najib ya sauƙe kallonsa ƙur cikin idanunta.


"My coffee, again..."