HAYAT NAZLI

12

by @maryamannour71


Chapter.12 

 

Ƙifta idanu take a hankali tamkar ɗan sabon jaririn da ya fara zuwa duniya, da sannu a hankali ta soma buɗe har ta samu nasarar buɗewa gaba ɗaya sai dai hasken ɗakin da ya dake ta a ba za ta ya sa da saurin maida idon ta rufe. A karo na biyu ta sake koƙarin buɗe su a hankali har ta buɗe su tarr kan ceiling fan ɗin ɗakin da ke kaɗawa tana bada iska mai daɗi, ƙurawa ceiling idanu ta yi cikin dawo da nutsuwarta da kuma son fahimtar inda take. 

 

Ta ɗan muskuta daga kwancen da take tare da kai hannu kanta tana furta sunan Allah can ƙasan zuciyarta jin yadda kan ya ke wani tsara mata, ta ɗago da idanunta da suka mata nauyi sakamakon daɗewar da suka yi a lumashi ta kalli jikinta. Mamaki ne ya kamata ganin ba kayanta da ta sani bane a jikinta ba wata 'yar riga ce kalar na shan iska ƙatuwa da har ta yi mata girma a jiki. 

 

Tunani ta soma na ina ne nan? Ya a ka yi ta tsinci kanta a nan, me kuma ya same ta? Ta maida kallonta ga hannunta na dama da ya ɗan riƙe ya kumbura yana ɗan yi mata zugi saboda ƙarin ruwa da ke saƙale a ciki. 

 

"Maddallah kin tashi kenan?" Ta tsinkayi muryar Dr da shigowarsa kenan domin duba patient's, bata amsa ba ta kalli gefen gadon ta a nan ta fahimci ba ita kaɗai ce a ɗakin da wasu marar lafiya. Nurse da ke biye da shi a baya ce ta soma duba ƙarin ruwan da ke hannunta yayin da shi kuma ya ke mata 'yan tambayoyi tana amsawa a hankali cikin yanayi na rashin lafiya. Bayan ƴan bincike da tambayoyi Dr ya koma ga next patient yayin da ita kuma nurse ke monitoring na ta. 

 

~~~~~~~ 

 

da taimakon nurse ta shiga restroom ta sauke nauyi tare da taimaka mata ta koma ta zauna. Kuma har zuwa lokacin tana cikin ruɗun inda take, waya ya kawo ta nan ina yan gidansu? Kamar kuwa nurse ta san me take saƙawa ta ce. "Sorry Maman ki ta tafi gida amma na san yanzu haka tana hanya ba za ta ɗau lokaci ba za ki gan ta, i know you must be hungry, kina buƙatar saka wani abu a baki kafin ki sha magani." "Mama?" Ta tsinci kanta da tambaya cikin rashin fahimta. "Eh wacce ta kawo ki ba, ta shiga damuwa sosai a lokacin da kika ɗau lokaci ba ki farka ba. Gaskiya kin yi sa'a  sosai da kike da mahaifiya me kaunar ki da damuwa da ke." Nurse ta faɗa tana manta murmushi cikin gyara mata gashin kanta da ya dan fito daga hular kanta. Babu wanda ya faɗowa Nazli a zuciya a wannan lokacin sai Mom, take ta ji sanyi a zuciyarta da zumuɗin haɗuwa da Dad ta san idan ya ganta cikin yanayen nan dole ya hakura ya saduda ya yafe mata su koma gida. 

 

Dan ta san duk abin da ya yi cikin fushi ne da Kuma zuciya amma ba wai har haka bane cikin zuciyarsa. "Amm Nurse, tsawun wani lokaci na ɗauka a kwance ne na ji kin ce ban farka da wuri ba." "Ai kwanan ki biyar a asibiti." "What? Garin ya ya?" Kamar Nurse ba za ta ce komai ba sai kuma ta ce. "Saboda buguwar da kika yi a kanki kin zubda jini sosai bayan ƙoƙarin ceto rayuwarki da a ka yi likita ya saka miki allurar bacci saboda kwakwalwarki ta huta domin gujewa labarin da zai taɓa zuciya." 

 

Sai a lokacin Nazli ta kai hannu ta taɓa kanta jin da bandage yanzu ta gane dalilin sarawan da ya ke mata. "Apart from my mom babu wanda ya zo?" Ta tambaya cikin hope ɗin zuwan Daddy da Zaid da har yanzu take jin zafin sa kan abin da ya yi amma can ƙasan zuciyarta akwai wani rare of hope a kansa ko ta ce a kansu tare, maybe just maybe komai zai daidaita su ta gyara kuskurenta na baya su koma cikin inuwar aure ɗaya. 

 

Sallamar da a ka yi cikin ward ɗin a ka shiga ne ya jawo hankalinta, murmushi Nurse ta yi. "Kin ga ma yanzu muke maganar ta ashe tana kusa." Fadin nurse a daidai lokacin da kyakkyawar bafulatanar matar da a shekaru ba za ta haura arba'in ba sanyi da purple hijab har ƙasa hannunta rike da basket din abinci ta shigo ward din, cikin girmamawa suka gaisa da nurse ta nemi kujera da ke kusa da gadon na masu zuwa dubiya ta zauna. 

 

Nazli da tun shigowar matar take bin ta da kallon rashin sani, maganar nurse kuma ya sake dilmiyar da ita kan wacece ita. Ina ta santa? A iya sanin ta dai bata taɓa ganin koda mai kama da ita ce, sai dai murmushin da ta ga tana sakar mata ne ya sa ta sakar mata murmushin ita ma ba tare da ta san tana yin ba.  

 

Ita ba mutum ce mai saurin sabo shi ya sa ma bata da ƙawaye ƙawarta ɗaya ce wato Elherm ita ma ita ce ta manne mata ta nace da son abota da ita tun bata kulata har ta soma biye mata suka ƙulla abota. Sai dai da wannan matar da bata gama sanin wacece ita ba is different ji ta ke kamar tana da wani connection da ita. 

 

Murmushi matar ta yi tare da tambayar ya jiki? A hankali kamar baki na ciwo ta amsa da "Da sauki." "To Allah ya ƙara lafiya." ta jawo basket ta fito da abincin da ta kawo, kunun gyada ta fara zubawa ta miƙa mata, da kamar ba za ta amsa ba sai kuma ta cire hannu ta karɓa har zuwa yanzu bata dena kallon matar ba, ko ba a faɗa mata ba ta tabbata ita ce wacce ta kawo ta asibitin bi ma'ana ita ta cece rayuwarta tun da har ma'aikatan asibiti ma sun ɗauka mahaifiyar ta ce. 

 

Cike da ɗari ɗari ta kai cufin baki kamar wacce a ka cewa za'a yi poisoning ɗinta, sai dai the moment ta kurbin kunun bata sanda ta yi sama da cufin ba saboda daɗi da garɗin kunun, sai ga Nazlin ku ta saki jiki tana sha kunu harda ƙari. Nazli ganin matar da har yanzu bata san ko da sunan ta ba tana ƙoƙarin buɗe cooler abinci za ta zuba mata ya sa ta faɗin. 

 

"No ya ishe ni." To ta ce ta maida cooler ta rufe tare da matsarwa can gefe, daga nan suka yi zaman kurame. Shiru shiru cikin su babu wanda ya yi magana Nazli dai lokaci zuwa lokaci ta ke daga kai tana satan kallonta, zuciyarta cike da tambayoyi amma ta kasa buɗe baki ta yi magana. 

 

======= 

 

Ganin shirun ya yi yawa ya sa matar kallon Nazli cikin nutsuwa da kamali ta ce. "Ni sunana Batoola amma anfi sani na da mai Koko a anguwa, na fito da safe kamar yadda na saba ne a kullum na kai niƙan wake na na kosai na ci karo da ke a bakin hanya kusa da kwalbati bakya numfashi ga kuma kanki da ke zubda jini. Da farko na ɗan tsorata kasancewar safiya ce gari bai gama wayewa babu yalwar mutane amma ganin halin da kike ciki na buƙatan taimako ya sani na dake duk da yadda zuciyata ke gargaɗina ga yin hakan. Na ƙira wani ɗan ɗakina Mahmuda shi ya taimaka min muka kawo ki asibiti Nan suka ƙarbi ki tare da baki agajin gaggawa. Ba mu san daga ina kike ba balle mu yi ƙoƙarin sanar da 'yan uwanki makusanta, amma alhamdulillah yanzu da kika farka lafiya sai ki bada number ko addressing gida a sanar da su dan na tabbata yanzu haka suna cikin damuwar batan ki." 

 

Sai a lokacin komai ya soma dawo mata daki daki barin ta gida da yadda ta yi walagigi a titi har zuwa saceta da a ka yi wanda shi ne makasudin kawo ta asibitin nan. Take idanunta suka cika da kwalla, ta tuna abin da Habu ya faɗa mata last a sanda ya taimake ta ya kubutar da ita a lokacin da ta cire ran tsammani da rayuwa. Lokacin da ta sallama rayuwa da sake ganin Daddyn ta da Kuma sauran ahalinta gabaki daya. 

 

      *Flash back.* 

 

A lokacin da su Goje suka yanki hanyar barin gari da ita, bayan umarni da Mom ta basu suka yanke hukuncin daɓa mata wuƙa a ciki kawai su kashe ta tare da turawa Mom shaidar aiki da ta buƙata daga nan kuma kowa ya wake abunsa. Sai dai 

 

tunanin yadda za su yi da gawar ya dakatar da su, sun san waccece ita kuma yard gidan waye. Tabbas idan suka yi haka to kamar sun cakawa kansu wuka ne dan tabbas yan sanda za su shiga lamarin za su yi bincike idan kuma a ka yi tracing dinsu fa? Komai ya zo musu karshe dan ba shakka makomarsu gidan yari karshe a masu daurin rai da rai. 

 

Hakan ya sa suka gaugauta changer plan whiski ya bada shawarar kawai su babbakawa motar wuta su cinna ta hakan ne kaɗai there will be save ba za'a san ina take ba ma balle a samu prove a kansu, da wannan kowa ya gamsu suka tsaya kan kashe ta cikin motar kawai ba tare da an samu shaidar komai a kansu ba. 

 

Lokaci guda Habu ya ji zuciyar imani ta shige sa, haka kawai ya ji ba zai iya yin abin da suke ƙoƙarin aikatawa ba don shi har ga Allah yarinyar ta shigar zuciyarsa. Don haka da kansa ya ƙarbi fetir ya babbakawa motar ganin hankalin su Goje bai kansa don lokacin yana waya da Mom ya ke faɗa mata change of plan na su, shi kuma whiskey ya dan zaga ne zai kama ruwa. Da wannan damar ya buɗe motar a hankali cikin sanɗa ya fito da Nazli ya kunce mata hannu da baki cikin ƙasa da murya ya ce. 

 

"Idan kina son kanki da kuma rayuwarki to ki yi nesa da wurin nan daga garin ma gaba ɗaya kar ki saki ki dawo, domin a gaba ba lallai bane ki samu kubuta ba wannan ita ce damar ki na tsare rayuwarki idan ko ba haka ba rayuwarki na cikin babban hatsari don wannan kaɗan ne daga abin da zai tunkaro ki." Fuskarta ta carbe da hawaye ba inda bai rawa a jikinta domin ta ɗan ji daga abin da suka tattauna na kashe da za su yi kuma a yadda ta ji suna magana ba sato ta suka yi ba saka su a ka yi Wanda Kuma Bata san waye shi ba. Sosai jikinta ke rawa gaba ɗaya ta sare ta cire rai da tsammanin sake yin wata rayuwa a lokacin da bata da ikon yi ko hanawa sai gashi Allah ya buɗe mata hanya. "Na gode na gode ba zan taɓa manta abin da ka yi min rayuwa ba, bani da abin da zan biya ka sai addu'a ubangiji Allah ya shirye ka dawo hanya mai kyau ka gane abun da kuke ba daidai bane ka shiryu Mamar ka da kowa na duniya su yi alfahari da kai." Ya yi murmushi.  

 

"In sha Allah na miki alkawarin daga wannan na dena rashin zan koma gida na nemi yafiyar mahaifiya ta da ma kowa da na batawa." Har ta bude baki za ta tambaye shi wanda suka sa a kawo ta Nan a kashe ta suka ji motsin sawun kafa. "Ki gudu kar su ganki duk abin da za ki ji ko gani kar ki tsaya ki tabbatar da kin yi nisa da garin nan kuma karki kokarin dawowa ba yanzu domin rayuwar ki na cikin hatsari." Daga haka ya tura ta cikin ciyayi jin sahun ƙafafun na karasowa. 

 

Sosai Nazli ke gudu cikin bakin daji tana gudu tana kuka ba ta yi wani nisa sosai ba ta ji ƙara bom da hansken wutar lokacin da suka kunnawa motar wuta. Ai bata san sanda ta fashi da wani iron mai ban tausayi gudu kawai take gaba ɗaya ta galabaita karfin ta ya ƙare, amma hakan bai sa ta tsaya ba dan da tuna maganar Habu sai ta ƙara ƙarfin gudunta tun tana yi cikin hayyacinta har ta zo bata sanin inda take jefa ƙafarta. Idanunta ne suka soma rufewa bata yi auni ba sai jinta yi karo da wani abu mai karfi da ya sa yi baya baya sai kuma komai ya soma juya mata Bata yi auni ba ta ji ta kasa, daga nan kuma bata sake sanin ina take ba sai farkawar da ta yi ta ganta a asibiti. 

 

  *END OF FLASH BACK.* 

 

Wata nannauyar ajiya zuciya ta sauke tuna abin da ya faru, tsintar kanta da boye kanta musamman da maganar Habu ta fado mata. "B..ba.ban sani ba, ba.. San komai ban kuma iya tuno da komai sai suna." 

 

~~~~~~~~ 

 

Kwanan su biyu a asbiti a ka sallame su, Batoola (Mai Koko) ita ke kula da ita, kullum idan ta zo da safe bata komawa gida sai yamma ta dawo da abinci. Sosai take kula Nazli kamar yadda uwa za ta yi wa ɗanta. Domin sosai Nazli ke bata tausayi na rashin tuna komai na rayuwarta ta baya, bayan maganar su da ita sai da ta samu likita inda ya kara jajdada mata lallai hakan na iya faruwa duba da yadda ta samu rauni amma in sha Allah da taimakon makusantan ta da Kuma magani a sannu za ta tuna komai na rayuwarta na baya. Sosai ya bada shawarwaren matakan samuwar lafiyarta.....