GAJERIUN LABARAI

AURE NA KE SO

by @jikankaila2014

*AURE NA KE SO....*

*Sadaukarwar ga Abokina Faisal Haruna Alhunqawee* 

*Daga alkalamin Jibrin Yusuf Kaila* 

"Ta yaro kyau take bata karko" haka kullum Uncle Auwal yake faɗa, ni kuwa a duniya na tsani kalmar nan, ji na ke kamar shine ya ƙirƙiro ta, saboda yadda yake alaƙantata da zance aurena, duk sanda na ce *AURE NA KE SO...* Ga kuma abokina Faisal yadda ya dame mu da wata nasiharsa da yake a walafawa a kafar yanar gizo,sai na ke zargin da ni yake wai cewa yake "Zaman aure bai dogara da kalmar (I LOVE YOU ) kawai ba... " Duk lokacin da na ci karo da rubutunsa sai na masa ta maguzawa.Don dakinmu daya yana jin taɗin mu da Safiyya.. Soyayyarmu ta yi nisa da bama jinkira " Har mun daina faɗin *I LOVE YOU* sai dai mu ce *I HATE YOU* sunan da ake kiranmu kuwa shi ne *Rome da Juliet* .....

Bari dai na kai wannan abun gida, wanda masu iya a zanci suke masa kirari da Kadangaran bakin tulu, don ya zame kowani magidanci dole, tamkar lomar mu ke sanya wa a baka, babu ranar dainawa sai ran da mutum ji shi kukkuba, wanda Hausawa kan ce masa Cefane...... Daga baya na karasa muku dambawar da mu ka yi ni da wannan ja'irar matar nan tawa Safiyya.......