BIYU A ƊAYA

Chapter 8

by @barista

BIYU A ƊAYA 

***
YOTA 13 
TEAM OF FIVE INK LEGENDS 

Dedicated to princess Nimcyluv Sarauta 👸🏻


Page 8


Nigeria Maiduguri KIRAWA'S FAMILY 

Ringing wayarsa ce ta tashe shi, a hankali ya buɗe idanunsa da su kayi masa nawi saboda gajiya da rashin bacci da bai ishe shi ba. Ya kurawa screen na wayar idanu, ganin kiran Daddy ne yasa ya ɗauka kamin yayi sallama yaji sauƙar muryar sa..

"Ka same ni a palour nah"

"Ok Daddy.....

Kan ya ƙara magana Daddy ya kashe wayar, ya mik'e jiki ba kwari ya shige toilet ya wanke fuskarsa ya fito tare da ɗaukar wayar sa ya fito, kai tsaye ya wuce side na Daddynsa...

Ya tadda su zaune suna cin abincin kari, ganin harda Alhaji Babba yasa ya fahimci kiran na musamman ne, ya zauna cikin girmamawa ya gaida su, suka amsa Abbie ya ce

"Zo Waahab, matso kai ma ka yi kari"

"Abbie bani da yunwa"

Alhaji Babba yayi magana 

"Ban sani ba ko da surukinka a cikin mu"

Murmushi Dr Waahab yayi ya ɗan gyara zamansa a lokacin Abban Ashfat ya jera masa abinci a gabansa tare da cewa 

"Ai yanzu ba a yayin wannan kunyar surki, ka zage ka ci abinci"

Murmushi kawai Dr Waahab Waseem KIRAWA ya yi, ya ɗan ci abinci kaɗan babu yawa, yayi zaman jiransu har suka kammala nan Daddy ya faɗa masa akan fitar da Mommie outside ne sun gama magana da Alhaji Babba cikin sauƙi yayi magana da babban hospital dake Egypt isowarsu kawai yaje jira.

Dr Waahab ya sauke numfashi cikin farin ciki ya ce

"Alhamdulillah komai yazo ƙarshe da izinin Allah"

Suka haɗa baki wajen faɗin 

"In sha Allahu"

Alhaji Babba ya ce

"Nan da jibi ma kawai a wuce Abuja, daga cen kuma sai a wuce Egypt ɗin"

"Hakan ma yayi"

Cewar Abbie, Dr Waahab ya ce

"Daddy gobe za mu wuce Abuja mu yi kwana biyu daga cen mu wuce Ghana"

"To da wuri haka?"

"Eh fah muna yau aka sanar damu"

"Wannan tafiyar Mommie babu kai a ciki, abin da za ayi shine da Nazeefa da Maimuna za a tafi ko a haɗa da Sa'eed"

Cewar Alhaji babba, Daddy ya ce

"A bar Maimuna a tafi da Suhaima hakan zai fi in yaso shi Sa'eed yayi musu jagora"

Suka amsa da 

"Wannan shawarar ta yi"

Sun tattauna sosai akan larurarta da kuma abubuwan da za a kashe na nema mata lafiya, kamin su tashi sai da suka ware kuɗaɗen da za ayi amfani dasu sannan suka fice. Daddy ya kalli Dr Waahab tare da cewa 

"Abdulwahab tashi mu je kayi min rakiya unguwa"

"To Daddy"

Ya amsa ba tare da ya tambayi ina za su je ba, wannan ɗabi'ar sa burge kowa yake baya shiga hurumin da ba na shi ba. Yana da sauƙin dabi'a amma sai an fahimce sa, muddin ba a fahimta ba, sai mutum yayi ta wahalar da kan sa.

Ya yiwa Daddy rakiya sun jima a inda suka je sannan suka dawo gida, Daddy baya shakka ko kokwanto akan Dr Waahab ko'ina ne yakan shiga dashi baya ɓoye masa komai, duk sirrukansa ya sani.

Bayan sun dawo ne Dr Waahab ya wuce ɗakinsa ya ɗauko luggage nasa ya soma shirya kayansa, duk wani abin da zai buƙa duk ya zuba a cikin sannan ya fito ya wuce ɗakin Mamie........

*********************************

GHANA 

Alaja restaurant 

Ta kaɗu da jin abin da suka faɗa, a hankali ta soma girgiza kanta alamun a'a cikin tashin hankali, jikinta na rawa haka ma muryarta ta furta

"Cutar da ita za ku yi?"

"Bai shefe ki ba"

Cewar cewar Laraba, Jummai ta ɗaura da

"Babu ruwanki da abin da za mu yi mata, iyaka shine ki yi abin da za mu saka ki"

"Uhm"

Ta sauke numfashi tana sake bin su da kallo, a hankali ta sauke ajiyar zuciya ta tambaye su

"Me yasa sai ni ce zan yi muku?"

"Saboda Bilqees tana son ki"

Jikin Majada yayi sanyi, jin har sun fahimci Bilqees na sonta, to me suke shirin aikatawa ne?...

"Kun shaku sosai, kuma kin fi kowa kusanci da ita"

Cewar Jummai ta buɗe mata ƙofa tayi mata alamun ki fice, Majada ta kura mata idanu tana kallon ta...

"Ki ci gaba da shige mata jiki, sauran aikin ki bar mana"

Cewar Laraba, sauke numfashi Majada tayi sannan tayi sauri ta fice daga ɗakin, ta koma kitchen ta tadda Bilqees da Server's suna magana da alamu akwai abin da ake buƙata cikin gaggawa, maybe customer's suna buƙatar wani abun ne..

Majada ta wuce ta kama aiki, Bilqees tana gama sauraron waiters da suka ɓanɓaro mata aiki ana buƙatar abincin gargajiya kuma kada ya dauƙi lokaci, da sauri ta soma haɗa kayan girke-girke nan ta baje komai ta fara aiki, ita kaɗai take yi, Laraba ta kalli Jummai suka raɓe baki alamun to ƴar iya tana aiki, nan Majada ta haɗa idanu dasu su kayi mata alama da ki taimaka mata don sake samun kusanci. Majada ta iso inda Bilqees ke aikinta cikin nutsuwa da kwarewa ta zauna tare da cewa 

"Bilqees dame zan taimaka miki?"

"Na kusa kammalawa ma"

"Ai kamar da saura"

Bilqees ba ta ce komai ba, Majada ta taimaka mata, nan da nan kamshi ya baɗe ko'ina, suka kammala, Server's suka shigo suka fitar da shi. Bilqees ta wanke hannayenta ta sami wajen zama ta zauna, majada ta zauna kusa da ita tare da cewa 

"Special chef me yasa ba ki son yi min magana?"

"Ba komai"

Ta bata amsa a takaice, Majada tayi murmushi ta ce

"Ai na baki hakuri, ko har yanzu kina fushi dani?"

"A'a bana fushi dake"

Alaja ta shigo fuskar nan sai fara'a take, tana 

"My Bilqees! My Bilqees"

Bilqees ta mik'e tare da cewa 

"Yes Maa"

"I'm so proud of you"

"Me too Maa"

"Yawwa go and serve our customers"

Kura mata idanuwa Bilqees tayi, ita kuma tayi saving ita da bata so ana yawan kallon ta...

"Oya dress as server and go there"

Jiki a sanyaye, ta koma ciki inda ake ajiye riguna dake ɗauke da tambarin Alaja restaurant...

Tana shiga Alaja ta ce

"Majada da ta fito ki ce ta kai min wannan plate"

Ta nuna mata sadadden plate da Alaja ke amfani dashi kuma tana son plate ɗin, musamman aka bata a wajen Award da aka taɓa bata na karrama Alaja restaurant...

Alaja tana fita, Laraba da Jummai suka matso kusa da Bilqees tare da cewa 

"Ke aiki za ki yi mana yanzu"

Waro idanuwa waje Majada tayi tare da cewa 

"Wane aiki?"

"So mu ke ki lalata wannan farin cikin dake fuskar Alaja"

Baya Majada tayi cike da tsoro tayi magana da ƙarfi 

"Kamar ya?"

"Ki zuba mai a daidai ƙofar dining areas, ki tabbatar ta taka man da takalminta tana wucewa ki goge wajen don gudun kada a kamaki, muddin aka kamaki da laifi kika furta sunan mu zamu yi miki illa"

Jikin Majada na rawa, cikin tashin hankali ta ɗebo mai ta fito daidai hanyar shiga dining area ta zuba mai yadda Bilqees zata taka, ta koma da gudu a daidai lokacin Bilqees ta fito, tana ƙoƙarin barin kitchen ɗin, Majada ta ce

"Bilqees"

A hankali ta tsaya ta juyo bata amsa ba ta kalli Majada, alamun ina jin ki. Majada tayi mata nuni da plate dake kan drower ta ce

"Alaja ta ce ki tafi mata da plate wancan"

Bilqees ta tako zuwa inda plate ɗin yake ta ɗauko, cikin sauri ta fito don kada ta ɓatawa Alaja rai wajen jinkirin fitowa. Tana fita Laraba da Jummai suka tafa suna dariya.

Bilqees cikin sauri ta taka mai da bata san dashi ba tayo cikin dining areas, customers cike da wajen suna cin abinci hankali kwance, har an kammala serving nasu, ta juyo da niyyar kaiwa Alaja plate tsantsi ties ya ɗebeta ta faɗi ƙasa nan take plate ya tarwatse, nan yayi ƙaran da ya janyo hankulan customer's suka ɗago suna kallon ta...

Alaja ta fito da jin wannan ƙarar, cikin tashin hankali take bin plate nata da tafi ƙauna ya tarwatse, ta maida kallonta kan Bilqees dake ƙoƙarin tashi tana mamakin ya aka yi tsantsi ya kadata bayan babu ruwa ko wani abin da zai sa hakan ya faru, tayi sauri ta kalli Alaja da idanunta suka yi ja don ɓacin rai tana so ta sauke mata masifar amma gani da tayi customers suna zaune yasa ta danne zuciyar ta koma ciki, da sauri cleaners suka gyara wajen, Bilqees jiki a sanyaye ta koma ta fito don ta san a yadda Alaja take muddin taje mata sai ta kusa cinye ta ɗanye.

A hankali take kallon hanyar da ta biyo ko za ta ga ruwa ko wani abu amma babu, ta fito ta zauna a waje ta rafka tagumi, tana jin bata kyauta ba da ta zama silar fashewar plate ɗin da Alaja tayi ƙauna a duk cikin abubuwan dake kitchen.....

"Dole ki zo nan ki zauna Bilqees"

Cewar Laraba, ta ɗago ta kalleta ba ta ce komai ba, ta ci gaba da cewa

"Ya za ki yi interrupting customers?"

Bilqees shiru ta rasa abin cewa, haka Laraba tayi ta mata faɗa, sannan ta bar wajen, Majada da ta ɓuya daga gefe tana jin yadda ake yi wa Bilqees rashin mutunci akan laifin da babu alhakinta a ciki.

Customers sun ragu Alaja ta fito ta zazzagawa Bilqees rashin mutunci, sai da ta wanke ta tas sannan ta kyaleta ban da hakuri ba abin da Bilqees ke iya furta wa, har da ƙwalla.


**********************************

Wasa suke yi yau ma kamar kullum, tun suna wasan guje² har suka gaji suka zauna suna jiran isowarta, yau ta jima bata iso ba, ko me ya faru, anya za ta zo ma...

Shine dai abin da suke ta sake² cikin ransu, Muneef ya yi magana 

"Kun ga mu koma gida tun da mun tara kuɗaɗe masu yawa"

Jamal ya ce

"A'a sai mun jira ta kawo mana biscuits da Alawa"

"Wa ya ce maka zata zo?"

Cewar Madina...

"Za ta zo mu dai ƙara jiranta"

In ji Jamal, suka zauna jigum, suna zaman jiran ta....

"Lah! Ga kyakkyawar Aunty"

Aiko a lokaci guda suka ɗago suka kalleta a lokacin tana sallaman me mashin, tana sauri har ta cire ran taddasu a gurin ga mamakin ta suna zaman jiran ta, don ta san tabbas zaman jiran ta suke...

Tana isowa su kayi mata oyoyo, suka kewaye ta, tayi murmushi tana me jin farin ciki, tare suka iso suka zauna sai ganin take sai nan nan da ita suke, tayi magana cikin siririyar muryarta 

"I'm really really sorry, na jima ko?"

"Tin (kin) jima"

Cewar Aicha, ta ɗauke ta sannan ta zaunar da ita kan cinyarta ta ce

"Naje wani waje ne sai yanzu na dawo"

Aicha tayi murmushi ta ce

"Tin (kin)kawo mana Alawa?"

"Na kawo, kowa yayi kayi na raba muku"

Nan ta sauke Aicha ita ce ta farko sauran su kayi layi a bayanta ta raba musu Alawa da biscuit suna murna suka rungume, a hankali ta zubda ƙwalla tana jin tausayin yaran har cikin zuciyarta, ta ce 

"Kowa ya zauna"

Suka zauna ta ce

"Zan dinga zuwa ina duba ku, kun ji"

"To mun ji amma ki daina daɗewa"

Cewar Muneef, ta ce

"Na zan sake jimawa haka ba"

"Suka haɗa hannayen su waje guda, suka ce ita ma ta ɗaura nata akai tayi musu alkawari, tayi murmushi ta ɗaura tare da cewa 

"Nayi alƙawari"

Nan suka saka ihu suna murna, Madina ta ce

"Kyakkyawar Aunty me yasa kike rufe fuskar ki"

Ta sauke numfashi, a hankali ta lumshe idanunta ta buɗe su, bata son ta dinga tunano wasu abubuwan, don zuwanta wajen ba ƙaramin taimaka mata yayi ba, za tayi magana Jamal ya ce

"Ko mijin ki ne ya ce ki rufe"

Da mamaki ta kalli yaron, ta ce

"Wa ya faɗa maka hakan? A ina kaji ana faɗin haka?"

"A TV na gani, a drama mijin ta ya ce ta rufe fuskar ta in zata fita"

Ta dinga bin su da kallo tana mamakin irin abin da yake ƙwaƙwalwar yaran...

"Aunty kyakkyawa bye"

Cewar Muneef, haka ma sauran, mamakin sunan da suka kirata dashi tayi "Aunty kyakkyawa" ta furta a hankali tayi murmushi tana zaune har suka ɓacewa ganinta, a hankali ta sauke numfashi tana jin yaran cikin ranta sosai, taji zuciyar ta wasai kamar ba ita ba, ta tana ƙoƙarin tashi wayar ta dake cikin jakarta tayi ringing ta buɗe zip ta fiddota ganin sunan dake jiki yasa ta sauke ajiyar zuciya har kiran ya tsinke, aka sake kira ya ta ɗauka ba tare da ta ce komai ba, shiru me ana kora mata bayani, cikin ɗaga murya ta ce

"Stop calling me Abraham"

Tana faɗin hakan ta katse wayar.

Ta mik'e ta iso bakin titi ta hau mashin ta bar wajen....

************************************

Alaja SPECIAL RESTAURANT 

Wunin ranar Bilqees bayyi mata daɗi ba, kwata-kwata, ji tayi restaurant ɗin ya gundure ta a daddafe ta kammala aikinta na ranan, cikin damuwa da tashin hankali, ai ta taɓo tsuliyar Dodo Alaja ba zata bar wannan fashewar plate ɗin ya tafi a banza ba, ko ta cire cikin salarynta ko kuma tayi ta mata bala'i tana tada zancen, don ita abu baya wuce ta.

Za ta tafi gida ta sanar da Alaja zata koma gida amma Alaja bata tanka mata ba haka ta fito ta wuce gida....




Comments and share fisabilillah