10
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_
*Na*
*AISHA ALTO*
*JAMILA UMAR(Janafty)*
M.A JUMARE FOOD AND SPICES
Pure and Natural hygienic tasty.
Muna da garin Ɗanwake da yaji mai kyau dakan hannu, akwai kuka, tsamiya, garin tamba, kuɓewa da daddawa.
Muna aikawa da kayanmu a ko'ina
Anguwan Ma'aji new millennium city kaduna
Phone number ***.
*HIJABS CORNER BY JANAFTY*
*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design, muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*
*BABI NA GOMA*
Ranar barci ko ɓarawo bai Sace Tahir ba, kuka kuwa yayishi kamar Ranshi Zai Fita Daga ƙarshe ya Haƙura ya Fauwalama Allah komai ya kuma Ɗaukeshi A Matsayin Ƙaddararshi, Amma yasan Duk Abunda ya Faru Dashi Farida ce Sila kana Goggo Abu Da'ace Sunyi Duba da Lalurarsa da Irin Halittarsa, Da Duk Haka Bata Faru ba Amma yana Ta Neman gafaran Allah, sai dai Kunya da Nauyi Sun Cikamai Ƙirji Sun Hanashi Sukuni.
Shi yazo ya tashi Bassam Suka Tafi masallaci Sallar Asuba basu Dawo ba sai Wajen Bakwai Saura Koda suka Shigo Iya ta gyara Ko'ina Tana Kichen Tana Musu Abun Karyawa Bedroom ɗinsa ya shige ya Zauna Kawai ya Zabga Tagumin Makomar Rayuwarsa yadda ya Cuci Rayuwar Yarinya kamar Mufeeda.
Su Iya ko tana gama Abun karyawa Ta ɗorama Mufeeda Abunda Zata Tafin mata Dashi Asibiti Tunda Tahir yace in Sun karya Garzali zai Tafi Dasu, Shiko yana Cikin ɗaki yama kasa Fitowa Bawai bayajin Yunwa bane A'a yanaji Domin Rabonshi da Abinci Tun Jiya da Dare, Amma Cikinsa ne A Chushe bayajin Akwai Abunda Zai samu Wajen Zama ga bakinsa ba Tes Kwata kwata Ɗaci ɗaci ma yakeji Shikanshi Damuwa ta Saukar mai Da Zazzaɓi mai Zafi kan gado ya Kwanta ya Lulluɓa da bargo Haka Basma da Bassam Suka zo Suka iskeshi ya Dunƙule yana Hawaye, yanajin Muryansu Suna Kiranshi yayi Saurin Share Kwallah ya Fito da kanshi yana Ƙoƙarin Daidaita kansa.
Basma ce Ta ƙarasa Tana Zama Gefen gadon Lokaci Ɗaya Take faɗin "Daddy jikin ne...? Ta faɗa Cike da Tausayawa, Kai ya girgiza musu kafin yace "No ba sosai bane Basma, nasha magani da nayi barci zan Warware, kun Shirya ne..." Bassam ne ya Ɗaga mai kai yana Zama Shima gefen Basma Fuskarshi ta bayyana Damuwar Dayake Ciki, Cikin Raunin Murya ya Furta..." Daddy What Wrong With you ne? bama jin Daɗin Ganinka A haka in Momy bata sonka Why not ka samo mana Wata Second Mom ko Basma...?" Ya faɗa yana kallonta, Saurin Kuka ne da Ita sai ga Hawaye Shar ta gyaɗa kai tana Faɗin "Eh mana Daddy, Momy tana Barinka kana Wahala bamai kula dakai ka ƙaro Aure plz kasamu Wacce Zata Dinga Zama dakai kullum muma Mu samu Mommy Wacce Zataso mu sosai Fiye da Momy.." Ta faɗa Kuka na Ƙwace mata ta Kifa kanta Jikin Tahir tanayi, Hannu ya saka yana Shafa kanta Dake Cikin Hijabin yanajin Ƙaunar 'ya'yansa Har Cikin Ranshi Duk da ƙananan Shekarunsu Sun Fahimci Damuwar nashi Acikin Ranshi Faɗi yake dama dama ace bai Aikata Abunda ya Aikata ba, Amma yanzu da Wani ido Zai kalli 'ya'yansa yace Shine ya Ketama Mufeeda Mutumci.
Cikin Sigan Lallashi yake Faɗin "Shiii..Is Ok karku damu Kunji na samu Sauƙi Sosai Ku Tashi Ku Tafi Garzali zai kaiku Room 9 Take kunji.." Gyaɗa kai Basma Tayi kafin Ta mike Tana Share Kwallah Hannunta Bassam ya Riƙo Kafin su Duka Dukkansu Su Sakarma Tahir kiss a Goshi, Lumshe ido yayi Idanuwansa Sun Cika da Kwallah Cikin Raunin Murya yace "Take care..." Suka Fice Suna Ɗaga mai Hannu Suka Fita Wani Kuka yazo mai ya Shige Cikin Bargo yanayi kamar ya Shiɗe Saboda Takaichi So yake ya Buɗe Ido yaga Duk Abunda ya Faru mafarki ne Amma Ina bakin Alƙalami ya Riga Daya bushe, Abunda yasa Ma ya bari su iya suka Tafi Asibitin bashi da mafita ne don ya cigaba da Hanasu Zuwa Zasu Zargi Wani Abu, shiyasa yakira Dr Hadiza da Safen nan, dayake sun karɓi Numbarn Juna, ya Roƙeta Akan Don Allah mahaifiyar Mufeeda Zatazo Dubata koda Wasa Kada Ta mata Narrated din Abunda ya Faru da Mufeeda baya son Hankalinta ya tashi Sai daga baya zai sanar da ita, jin Haka yasa Dr Hadiza ta Amince da Roƙonsa suka Rabu Akan sai Anjima zai Shigo Asibitin.
Su Basma Sun Iske Jikin Mufeeda da Sauƙi Tana ta Barci ga Nurses nata kula da Ita sai Wajen 1 ta Farka taji Daɗin ganinsu Iya dasu Basma Ta dinga Murmushi, ta daina Kukan yanzu, Tunda Ta fara jin Sauƙi Gasata Suke bana Wasa ba ga mgaunguna gashi tana samun Hutu Dr Hadiza Da Tazo da Safe Haka ta Dinga Tambyar Mufeeda ko Zata Tuna Fuskar Wanda yayi mata Wannan Aiki Ko Zata Taimakesu Su Nemar mata Hakki, Acikin Ranta Kuka Take Har Asarari, Saboda Bazata iya Buɗe baki ta Furta Wanda ya Inganta Rayuwarta ne ya Aikata mata haka Bazata iya karya Alƙawarin da tayima Daddy ba Koza'a Kasheta Akaro na Farko Zata saka mai da Abunda yayi mata Arayuwa, tana kuka take Cemata bata sani ba Dole ta kyaleta.
Sun Daɗe sai Wajen Uku Suka Tafi bayan Iya Ta Zuba mata Faten Waken Data Zo mata Dashi Abakinsu ma Takejin Wai Daddy baida lafiya, Tana Shan Faten Waken Tana Sharan Kwallah Na Tausayin kanta Dana Daddy Domin Dukkansu Sun Faɗa Cikin Wata Jarabawa, koda suka koma gida Tahir na Kwance Ba yadda yake Ishaq ne da yayi ta Kiran Wayarsa bai samu ba yazo gidan nan ya iskeshi Kwance Zazzaɓi ya Rufeshi Batare da Tunanin Komai ba ya Taimaka mai ya Fito Suka Tafi Asibiti.
Iyali Hospital Ishaq ya kaisa Suna Zuwa Suka Riƙeshi Saboda Jikinsa ba ƙwari ga Jininsa ya Hau Gado Suka bashi bayan Sun Sakamai Drip, Ishaq kamar yama Tahir Kuka yana Tunanin Duk Damuwar Farida ce Sai da Aka gama Komai aka kawoshi Ɗakin Hutu kana ya samu Sararin Kiran Farida yana Sanar da Ita Tahir bashi da lafiya gashi Anyi Addmiting Ɗinsu, Taji ba Daɗi Sosai Ta Dingama Ishaq din kame kamen batama san Bashi da lafiya ba, Nan tace Insha Allah gobe Zata Dawo Daga Haka Suka Rabu, kafin ya kira Zahra yana Sanar da Ita ta Turo Direba da Abinci yana Asibiti Zai Kwana da Tahir, Su Basma kuwa Jin Shuru basu Dawo ba yasa Suka saka Garzali ya Kawosu Asibitin nan Suka Iske Daddynsu Kwance Kuka Sukayi Tayi Ishaq na lallashinsu bai Tashi ba Har Suka Koma gida, Iya Tayi Tagumi Tana Jimamin Wannan lamarin Gefe Ɗaya tana Tir da Halayyar Farida.
Sai Wajen yamma Farida Ta Dawo, Tun Agida ta samu labarin Itama Mufeeda na Asibiti ga Tahir Abu Lokaci Ɗaya sai ta Fara Zuwa Asibitin Inda Tahir yake Ta Dubashi, taji Tsoro Ganin yadda Tahir ya Faɗa yayi Wani Sukuku Dashi nan ta Iske Ishaq da matarshi da 'ya'yansu, Alokacin ne yake Shaida mata Likita yace Damuwace Tayi mai yawa Sosai Shine ta galabaitar dashi gashi bayason Cin Abinci, Tagumi Farida Tayi Tana kallon Tahir Cike da Tausayi, Yau ne Rana Ta Farko Dataji bata kyauta ba, Shiko Tahir bayama son ganin Fuskar Farida Saboda Duk Itace Silan Shiga Wannan Halin Shiyasa ya Kulle ido Yayi mata barcin karya, Da Farko Ta karɓi Ishaq Jinyar Shi ya Koma gida Amma Sai Tahir ya Hana yace Ta Koma gida Saboda Mufeeda Shi Ishaq ɗin ya cigaba da Zama Dashi bata da yarda Zatayi Hakan ta Haƙura suka Fito da Aliya Kowa ya Shiga Motarshi Zuwa Gida.
Bata samu Zuwa gaida Mufeeda ba sai Washegari dasu Innaro Suka zo Da Ashe da Hakimi Sun Zo Duba Tahir bayan sun Dubashi ne Farida Ta ƙarasa Dasu Suka Duba Mufeeda wacce Ta samu Sauƙi Sosai, Koda Suka Haɗu In Farida zata Lura Mufeeda bata iya kallonta Saboda gani Take kamar Zata Fahimci Abunda ya Faru, Amma ita Farida ba Wannan bane agabanta Damuwarta yadda Tahir bayason kallonta balle yimata mgana sai ya zama Dole.
Washegari ne Umma Tazo Daga Kano, itama Ta Jinjina Ramar da Tahir yayi da Zata Tafi, tayi tama Farida Faɗa lokacin Data Zo Rakata, Akan ta kula da Mijinta Taga dai Halin Dayake Ciki Haƙuri Farida tabama Umma Inda Tamata Alƙawarin gyara Kuskurenta, itama bata Wuce ba sai da ta biya ta Duba Mufeeda, kana Direba ya Wuce Da Ita Kano.
Tahir Kwana Huɗu yayi A Asibiti kafin asallameshi ya Dawo Gida, Mufeeda ko Sai da ta Kwana Takwas Cur ta Warke kamar babu Abunda ya Faru kana Dr Hadiza Tayi Discharging Ɗinsu Tahir da kanshi yaje ya Taho Da Ita Shida Farida Wacce yanzu ke Wani Rawan Jiki Dashi Shi kuwa kallonta kawai yake Acikin Ranshi yana Faɗin Lokaci ya Ƙure miki Farida, Baya son ma Haɗa Ido da Mufeeda Amma itako Tana ta Satar kallonshi ganin yadda ya rame yayi ƙasumba kamar ba Daddy Ɗan Gayu ba, ita kaɗai Tayi ta Sharɓan Kwallah Acikin Ranta Tana Faɗin Ta yafema Daddy Duniya da lahira kuma Har Abada ba Wanda Zaiji Labarin Abunda ya Faru.
Gida yayi Daɗi da Dawowar Mufeeda mussaman ma Basma da Bassam da Iya, Tahir ko yanzu kwata kwata ya daina Sakewa kamar da ko ya'yanshi Sun Fahimci Haka dama kuma baida yawan magana Amma yanzu Abun nashi yayi yawa Tun balle Farida Data zage tana Kula Dashi Amma Sai dai ya Bita da Ido Abun ya Fara bata mamaki da Tsoro ko Ta Tambayeshi sai yace mata ba komai ta bashi Haƙuri Kuma yace ba komai amma ya kasa Sakin Jiki Da Ita Babban Abunda ya bata mamaki Shine bai Nemeta ko Sau Ɗaya ba, Shi ko Gaba ɗaya Sha'awarshi bata Zuwamai Saboda baya Cikin Natsuwarsa, Abunda ma ya ɗan Lafamai Shine ganin Mufeeda ta samu lafiya ta Dawo Walwalwarta Har Ta koma School Shi kaɗai sai ya Riƙa Fita Ta Ƙofar baya Daga sama yana Hangensu in Zasu makaranta ganin Ta Saki Jikinta yasa Hankalinsa ya fara Kwanciya.
Sati biyu ya kwashe Agida yana Hutu kana ya koma Office Wanda ko Alokacin Sai Ahankali Ishaq yasha Kamashi yashiga Zurfin Tunani Akwai Ranar daya ganshi yana Kuka Abun yabashi Tsoro, yayi kuma Tambayar Duniyar nan Amma Tahir yaki Sanar dashi sai ma Murmushin Kuka Dayayi mai yana Faɗin karyayi Fatan Jin Abunda ya Aikata Domin Har shima in yaji Sai ya Tsaneshi, Abun yabashi Tsoro Sosai Sai ya Dinga Fatan Allah ya yayema Tahir Duk Abunda Ke Damunshi Tunda yaƙi Sanar dashi koma menene.
Ita kuma Farida takasa gane kan Tahir yadaina Fitowa Dining Cin Abinci sai dai takai mai Ɗaki, shima bawani ci yake Sosai ba, koda yaushe ya dawo yana Ɗakinsa yana karatun Qur'ani ko Kuma ka ganshi Zaune yayi Tagumi duk ya Chanza kamar ba Tahir ba, bashi da Wata Walwala Komai na Duniya ya Fita kanshi gani yake Watarana Za'a gane Komai yana ji Ajikinsa Asirinsa bai Rufeba Wata rana Komai Zai Fito Sarari, kowa kuma Zaiji yazaiji Da Kunyar mutane Dawani Ido Zai kalli iyayansa yace Shine da kanshi ya Aikata Wannan Aiki, Abun yana Ranshi ya Hanashi Sukuni.
*****
Yau ɗin Takama Weekend ne Sunday, Tun safe Farida ke Lura da Tahir yayi Zurfi Cikin Tunani Ko Ruwan Wanka Data Hadamai bai Shiga yayi ba, Tana Lura Dashi yayi Zaune Kawai yayi Shuru agefen Gado ya zabga Tagumi da Hannu Bibbiyu.
Shigowarta Bedroom d'in yasa Ta Bishi da kallo kafin ta ƙarasa Kusa Dashi Zama tayi Gefenshi Kafin ta sanya Hannu Ta dafa Kafaɗarshi Tana Faɗin "Abban Basma..." Ta faɗa Lokaci Ɗaya Tana Girgiza Kafaɗarshi, Ɗagowa yayi yana kallonta Kafin ya saki Ajiyar Zuciya, yana Lumshe ido Lokaci Ɗaya yana Furzar da Iskar bakinshi, narai narai Tayi da Ido kafin tace "Meke damunka ne..? Tunda Kadawo Daga Asibiti Ka Chanza kadaina Walwala kamar baya baka sakin Jiki da Kowa, Baka da Aiki sai yawan Zama Shuru da Tunani, kuma kasan Cewa Likita yace kadaina yawan Zama Cikin Tunani Saboda Jinin Ka yayi Sama.." Ta faɗa Cike da Tausayawa.
Ƙura mata ido Yayi kafin ya saki Ajiyar Zuciya, Kawai ya Miƙe bai ce mata komai ba, sai da ya Nufi Hanyar Toilet kana ya Waigo yana Faɗin "Bafa komai Tun Ranar Nake Faɗa miki karki Damu.." Ya faɗa yana Tura Ƙofar Toilet d'in ya Shiga Da kallo Ta bishi Jikinta Duk yayi Sanyi A iya Tunaninta ta kasa gano Abunda ke Damun Tahir Ta tambayeshi ko Itace Amma yace karta damu Bakomai Amma Koda yaushe Abun nashi ƙara gaba yake ba Wani Chanji, tana nan Zaune ya Fito Wanka Ɗaure da Towel a ƙugunsa yazo ta gabanta Zai Wuce Da Hanzari Ta Miƙe ta faɗa Jikinsa Ta Rungumesa ta baya ta Fashe mai da Kuka Tana Faɗin "Nidai don Allah ka sanar dani Abunda ke Damunka..? In nice na maka laifi Tunda na Dawo nake baka Haƙuri Bai ci ka Haƙura ba? Don Allah kadaina Wannan Tunanin.." Ta faɗa tana zagayo da Hannuwanta Ta Cikinshi Runtse Ido yayi Jikinsa Duk yayi Sanyi kafin ya Buɗe ya Juyo da Farida Suna Fuskartar juna, Hannu ya sanya yana Share mata Hawaye kafin yajata Jikinsa yana Faɗin "Shiiii..Nace miki ba komai ko? Ki daina Damuwa..." Ya faɗa yana Shafa bayanta Har Zuwa Tudun Hips Ɗinta, ganin Haka ne yasa ta ƙara Narke mai ajiki kafin Ta Ɗago kanta Ta Haɗa Bakinsu Waje Ɗaya Gefe Ɗaya Kuma Hannunta na saman Faffaɗan Ƙirjinsa Tana Shafawa.
Tahir bai da Wata Natsuwa Biye mata kaɗai yayi Saboda Kada Allah ya kamashi da laifin Danne ma Farida Hakki Har Suka Dangana da gadonsu sai gashi yau Abun mamaki Farida bata gaji da Tahir ɗin ba Amma Shi Round ɗaya Sukayi ya Zame Jiki ya Shiga Toilet ya sakarma kanshi Shower, yana Jin kamar ya kurma Ihu, yau shine bayan ya Sadu da Mufeeda kuma ya koma ya Sadu da Farida Abun yamai baƙin ciki Sosai Wanda yasa ya kasa Sakin Jikinsa yayi komai kamar yadda ya saba, Har yayi Wanka ya Fito Farida na Kwance Tana Binshi da kallon Mamaki Aranta tana Faɗin Tabbas Tahir bashi da lafiya don A Tarihin Aurensu bai Taɓa mata Ci Ɗaya Alokaci ɗaya ba sai yau.
********
_BAYAN SATI UKU_
Bayan Sati Uku da Faruwar Haka Abubuwa Suka Fara Sauki, Domin Mufeeda ta Saki Jikinta Sosai ta Koma kamar da, rainon Naila ya Dawo Hanmunta kamar da, kuma Tana Cigaba da Harkarta sai dai Abun na Cikin Ranta Tayi ta Kuka Ita Kaɗai Acikin ɗaki, Sai Abu na Biyu Daya Dameta ganin yadda Daddy yake Ta Rama Atsaye Duk da bata cika ganinshi bane, Shiko Tun bayan Faruwar Haka Mufeeda Ta Zauna Aranshi Komai yake sai ta Faɗo mai tausayi Take bashi yarinya Ƙarama Ta Zama Abun Tausayi, Da ganga yake gujema Haɗuwarsa da Mufeeda Da Zarar Sun Haɗu Abunda ya Faru ke Dawo mai Duk da yanzu Ya fara Maida Natsuwarsa Amma bawai Don Abun yabar Zuciyarsa ba Kwata Kwata...
Tsakaninshi ko da Farida Kadaran kadahan Domin Tagaji Da Tambayarshi meke Damunshi Ta Haƙura ta Zura mai ido Har ƙararshi Takai Wajen Goggo Abu ta Kirashi yaje ta Turkeshi Daga Ƙarshe Kuka ma ya Fashe mata Dashi Abunda ya bata Tsoro kenan Domin Ita ta Haifi Attahiru, tafi kowa saninshi Bai da Rauni, Amma sai gashi yana mata Kuka yana Faɗin Ta tayashi Addu'a ya Aikata Wani Abu Wanda yakejin kunyar Idon Mutane da Allah Wanda ya Halliceshi, kuma tayi tayi Ya Faɗa mata Amma yaƙi sanar da Ita, ko da ya tafi Ɗaki Ta shiga Tana Tunanin meke Faruwa da Tahir ɗin ne Haka Domin Ko Afuska ya Rame Sosai Duk ya Chanza, hakama Hakimi Yayi mamakin Ramar Ɗan nashi Amma sai ya Danganta Hakan da Rashin Lafiyar Dayayi, Kai Ranar Duk Wanda yaga Tahir yasan Cewa ba Lafiya yake ba Hatta Innaro sai da tayi magana, Toh ba Wanda Zaice ga Abunda ke Damunshi Domin bai yarda ya Sanar ma Kowa Abunda ya Aikatama Mufeeda ba.
Nanny(me reno) Free book ne amma ga waɗanda ba za su iya jira ba akwai completed documemt 1k ne ku tura ta wannan acct ɗin 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK ko tuntuɓar waɗannam lambobin ***
***.
*Aisha Alto...*
*Janafty.*