13
Chapter 13
Tunda a ka sallame su take baza idanu ta ga me Koko amma shuri, tun tana saka ran zuwan na ta har ta saduda ta soma tunanin ko ita ma gajiya ta yi da ita ta tafi abun ta kamar yadda kowa ya juya mata baya, ta kifa kanta da guiwa ta soma kuka abun ban tausayi, shi kenan kowa baya sonta kowa ya juya mata baya kan abun da bata san hawan sa ba bare saukan sa ba. Hatta Daddy da shi ya kamata ya tsaya mata a ko wani yanayi na rayuwa da za ta tsinci kanta a ciki ma ya barta ina ga kowa, a dan zaman da suka yi da mai Koka sosai ta dan shaku da ita duk da babu wata magana da ke hada su sai idan ta kama amma hakan bai hana shakuwa shiga tsakanin su ba don zuwa yanzu sosai take jinta har cikin zuciyarta. Idan tana tare da ita tana ganin yadda take nuna kulawartw a gareta sai take tuna mahaifiyarta Ishiraqa.
Cak ta tsaya da kukun jin an dafa ta daga baya, dago da kai ta yi a hankali tare da goge hawayen fuskarta. Me Koko ce tasye a gabanta hannunta rike da farar leda irin ta chemist da suke bada magunguna a cikinta. "Ya dai yar nan ya da kuka Kuma?" Cewar me Koko dai dai lokacin da takewa kanta masuguni a bakin gadon, bata yi magana ba sai tagwayen ajiyar zuciya da take saukewa a jajjere don ba karamin sanyi ta ji ba ganin ta da ta yi gaba daya sai ta nemi damuwarta ta rasa. "Kin ga na je siyo magungunan da a ka rubuto ne na tsaya tsaida mana adaidaita sahu kin ga yamma ta yi suna wahalar samu ga kuma yanayen ki ba za ki juri tsayuwa ba."
=======
Mai Koko da kanta ta hada kayansu ta rika hannunta suka fita, inda suka samu mai napep da ta tsaida na jiransu. A hanya ma haka ta baza idanu tana karewa yanayen garin kallo, tunani ta soma ko nan ina ne? Dan bai mata kama da inda ta baro ba, kasa hakuri ta yi ta kalli mai Koka ta ce. "Amm.. nan muna wani gari ne?" "Abuja." Dan sahun ya bata amsa. "Abuja?" Ta tambaya cikin mamaki ganin ko kusa wajen bai yi kama da Abuja da ta sani na yan gayu ko ina manyan gidaje da plaza's akasin nan da ya ke dan kama da kauye a na ta tunanin. "Ehh Abuja amma mu muna waje wajen gari ne amma tsakanin mu da cikin gari ba babu nisa." Fadin Mai Koko, kai ta gyada cikin fahimta daga nan bata sake magana ba har suka isa.
Suna sauka yaran gidan da ke wasa a bakin kofa suka yo kan su suna ma mai Koko oyoya tare da karbi kayan hannunsu suka yi ciki da shi, tsaye ta yi tana karewa yar karamar anguwar kallo, tana mamakin yanzu a nan wasu ke rayuwa? Bata tashi mamaki ba saida suka shiga cikin dan madaidaicin tsohon gidan da ko arzikin kofar kirki bashi da shi. Gida ne maidaici na haya da ya kunshi sassa har hudu kuma duk da mutane a cikinsu.
Daki na farko da shi za ka ci karo da idan ka shigo shi ne na Maman Khadija, yaran ta uku, Khadija yar shekara goma sha biyu sai Abubakar dan shekara goma da auta Amani mai shekara biyu. Daga dakin Maman Khadija sai daki na kusa da shi wanda shi kuma na Maman Sadiq ne na gaba kuma na wata amarya ce da ba su dade da zuwa gidan ba. A dan gefe kadan kuma shine bangaren mai Koko, daki daya ne da dan kitchen na sa a tsikiyar gida. Sai dai na ta sashe an yi anfani da kwanon langa langa an zagaye baranda da kitchen sai yar tsakar gida da a ka cire mata, waje tsakiyar gida kuwa katuwar bishiyar mangoro ce wacce ta kawata gidan tana busar da iska mai sanyi da kuma taimakawa wajen bada inuwa idan rana ta fito, mutanen gidan kan fitowa su zauna kamar dai yanzu gaba dayan su suna waje sun hallara sun baza majalisa suna hira.
Suna shiga mai Koko ta tsaya suna gaisawa da mutanen gidan yayin da Nazli ke tsaye a bayan ta tana karewa gidan da daga yanzu ya zamo na ta inda ta za ta shinfide sabuwar rayuwa a ciki, sabuwar rayuwa sabon waje da kuma sabin mutane, ko ya rayuwa za ta yi da ita a gaba? Allah masani amma tana fatan rayuwa mai dadi da inganci.
Suna shiga mai Koka ta bude kofa suka shiga ciki cikin yar tsakiyar gidan da a ka zaga da langa langa. Kujera ta nunawa Nazli ta zauna kafin ita kuma ta shiga ciki ta bude daki tare da daga labule ta kutsa ciki.
Bayan yan mituna ta kakkabe dakin tare da kuna maganin soro ta sauke labaule tare da kunna hasken fitila kana ta fito, ganin an soma kiraye kirayen sallan magrib ya sa ta nufi randa ta debo ruwa cikin buta ta mika ma nazli. Ganin Nazli na dauro alwala ne ya sa ta fadin. "Ba za ki kama ruwa ba?" Bayin na waje." "A'a bana jin fisari." To ta ce ta juya ta zuba wani ruwan a buta ta nufi bandaki da ya kasance pupplic toilet ce tana can waje tsakiyar gidan. Lokacin yan gidan kowa ya yi ciki masu dauro alwala na yi wanda ke kan murhu kuma na kai.
=====
Suna daura alwala suka shiga ciki, a hankali da Bismillah a baki ta saka kafar ta cikin dakin. Dan maidaicin daki ne da babu wani tarin tarkace a ciki, katifa ce shinfide da ma tashin kai (pillows), sai mirror da ke gefe saman ta mayuka ne da turaruka wanda suka hada na shafawa a jiki da na wuta, a dayan bangare kuma a kwatunan kayan sawa ne da Ghana most go sa shima ya kunshi tsummokarai, sai dayan side da kuma kayan kitchen ne da ya hada bokatai kaflask a jere su wurin bakwai sai manyan tukwana da dai sauran tarkace kitchen. Dakin a tsaftace ya ke ko ina tsaf staf komai yana ma'adanarsa sai kamashin turaren humra da kulacca kamar dai kamshin da take ji a jikinta a kullum.
Dadduma ta shinfide masu suka tada sallah, bayan sun iddar Mai Koko ta mike ta fita waje. Kitchen ta shiga ta jawo dan karamin gas dinta ta kunna, ta daura ruwa cikin tunkuya tare da wanke shinkafa ta zuba kana ta koma ciki. Wata yar jaka da ke rataye cikin gusta ta dauka tare da fidda kudi ta fita, a waje ta samu yara ta aika suka kawo mata kayan shayi da kwai. Dama tana da yar jan miyar ta da ta rage ta wanke kwai biyu ta saka cikin shinkafar, sauran kayan shayi kuma ta adana su a daki cikin daya daga bokatan saboda gujewa bera.
Shinkafar na yi ta daura miyar ta dumama kana ta zuba masu abincin a tare, tare suka ci abincin, da kanta ta balla magani ta ba na Nazli ta sha. Da lokacin sallan isha ya yi suka tashi suka iddar, mai Koko ta sake daura ruwan zafi a tukunya yana zafi ta juya a bokiti tare da sirkawa da ruwan sanyi ta kai bayi kana ta samu Nazli da ta je ta watsa ruwa za ta ji dadin jikinta. Ba musu kuwa ta mike dan dama zafin ya ishe ta, ta cire kayanta yayin da mai Koko ta fidda mata kaya mara nauyi daga cikin na ta.
Tare suka fita ta nuna mata bandakin kafin ta koma ciki ta bar Nazli tsaye tana kallon bayin cikin kyankyami, ya ma za ta iya zama ta tsaya cikin bayin nan bare har ta tube ta yi wanka bayin da ba shi da ko kofa illa buhu da a ka daura a maimakon kofa wanda iska na sama da shi za'a ganka tsirar.
Bayan sake saken zuci da ta dinga yi ba lafiya ya sa ta yi shahada ta tube ta watsa sharp sharp ta fito cikin sauri tun kan wani ya fito ya ganta dan jinta take tsirara kamar a tsakar gidan take wanka ko ina a bude bayi babu rufi bare kofa.
lokacin da ta dawo ta samu har mai Koko ta daura gidan sauro ita take jira, tana zuwa ita ma ta tashi ta shiga wanka, bayan sun gama komai ne suka yi shirin bacci suka soma hira jefi jefi har bacci ya dauke mai koko. Amma Nazli idon ta biyu har sha biyu da rabi ta kasa bacci, tunani kawai take ta tuna rayuwarta ta baya da ganta da komai na ta Bata rasa komai ba na rayuwa, sai gashi yau an wayi gari ta rasa komai ba iya dukiya da jin dadin rayuwa ta rasa soyayyar iyayenta da komai. Ta rasa Zaid dinta me kaunar ta, da a ce wata daya baya wani zai fada mata za ta tsinci kanta a wannan yanaye da sai ta karyatar da shi karshe ta danganta shi da ciwon hauka, amma sai gashi ba zato ko tsammani rayuwarta ta canza duniya ta yi mata juyin waina. Lallai duk wanda ya dau duniya da zafi to kuwa za ta kona shi.
Tunani ta soma ko ina Daddy yanzu? Ya yi bacci ko bai yi ba? Yana gari ko baya nan, shin ya damu da rashin ta ko a'a? Tunani ta soma kala kala haka ta soma tuna rayuwarta da Zaid da kalar soyayyar da ya ke mata karshe ta tuna da Nadiya? Ko ya take? Shin ta fara makarantar ne da ta saka ta?