SAUTIN KARSHE

Chapter 11

by @amanarcool323

Kusan kwana huɗu su Zaki suna nemansu lungu da saƙo amma ko mai kama da su basu gani ba, Sango ya yi bala'i da masifar har ya gaji. A dole ya haƙura su Zaki suka dawo masa saboda ba zai samu waƴanda za su riƙa gudanar masa da aikinsa ba kamar su ba. Haka suka sake nemo masa wani yaron ya gudanar da baƙin aikinsa a kansa. Sai dai duk da haka bai haƙura duka da neman yarinyar ba. Yana nan a kan bakarsa na a cigaba da nemanta duk inda aka ganta a ɗakko masa ita.

A cikin kwanakin nan Halima ta yi wata irin rama ta ban mamaki, juyin duniya Aliyu ya tambaye ta me yake damunta amma ta ce masa "Babu komai". Ga Abida tana samun sauƙi sai dai jikin mahaifiyarta ya koma abin tsoro. Inna ta ƙare mata kallo ta ce "Anya Halima wannan rama taki ta lafiya ce? Ko dai juna biyu ne dake?". Sunkuyar da kai ta yi ta kasa magana, Inna ta ci gaba da faɗin "Abin ya yi yawa, mutum a tsaitsaye duk ya rame? Idan dai har ba juna biyu ne dake ba to tabbas ba ki da lafiya, ke ma akwai ciwon da yake damunki". 

"Inna ni fa babu abin da yake damuna, kawai bana jin daɗin jikina ne". Inna ta ce "To ai shikenan, koma dai mene ne Allah ya kawo mana sauƙinsa". Halima ta amsa da "Amin". 

****

Sudais sun fara shirye-shiryen gudanar da gine-ginen da za su yi. Duk wani abin buƙata da gudummawar da ya kamata kamfaninsu ya bayar ya yi, an fara tsara komai cikin tsari mai kyau. Sudais duk abin da suka buƙata yana yi musu ba tare da ɓata lokaci ba, sai dai duk da haka yana nan yana bincike ta ƙarƙashin ƙasa a game da su. 

Yana zaune a office ɗinsa yana tunanin saƙon da Ilham ta sake turo masa ɗazu ya ji kira ya shigo wayarsa, ko da ya duba Alhaji Sardauna ne, cikin nutsuwa ya ɗaga kiran tare da yin sallama. Amsa masa Sardauna ya yi ya ce "Adam ya kake? Ya fama da jama'a?". 

Sudais ya ce "Alhamdulillah Alhaji ya naku hidimomin?". 

Sardauna ya ce "Alhamdulillah da godiya, kwana biyu na ce bari in taɓo yarona" ya yi maganar yana murmushi sannan ya ɗora da faɗin "Na ji kun kai ƙarshe sa mutanenka har kun fara aiki, Ubangiji Allah ya taimaka ya shiga cikin lamarin, ya sa ku amfana da juna". Sudais ya ce "Amin ya hayyu ya ƙayyum muna godiya sosai da sosai".

"Ah babu komai ka daina yi mini godiya" Sardauna ya ce, kafin ya ci gaba da faɗin "Adam ya batun waccan maganar da na yi maka ta a kan ƙanwarka Zuhura? Na ji shiru ba ka ce komai ba, ko dai ba ka son tayin nawa ne?". Sosa kai Sudais ya yi, ya sunkuyar da kai kamar yana gabansa ya ce "Am ban manta ba Alhaji, in sha Allah gobe zan zo da yamma ka turo mini address ɗin gidan". 

Cikin jin daɗi Sardauna ya ce "Ah ma sha Allah, to Allah ya kai mana rai, zan sanar da ita ta shirya tana da babban baƙo". Daga haka suka yi sallama. Sudais ya sauke ajiyar zuciya yana tunanin ta yadda zai je gurin wata budurwa da sunan zance.

****

Yau Ilham jikinta da sauƙi ba kamar kullum da take fama da rashin lafiya ba. Hakan ya sa ta ce wa Momy za ta je gidansu Mammy, kasancewar a gaban Dady ta yi maganar ya sa Momy ta amince mata ba don ranta ya so ba. Ilham ta shirya da kanta ta yi driving ta tafi. Kasancewar yamma ce ya sa ta tarar da su a falo gabaɗaya hadda Sudais, cikin farin ciki Zahra ta tarbe tana yi mata sannu da jiki. Zama ta yi tana gaishe ɗaya bayan ɗaya, da ta zo kan Sudais ta yi zaton ba zai amsa mata ba sai kuwa ta ji ya amsa. 

Mammy ta ce "Sannu Ilham, Zahra ta ce mini ba kya jin daɗi. Ya jikin ina fatan da dai sauƙi?"

"Eh Mammy Alhamdulillah da sauƙi" Ilham ta ba ta amsa tana sunkuyar da kai ƙasa. Tashi Sudais ya yi ya haura sama, bayan kamar minti goma da shigarsa Ilham ta miƙe ta ce "Zahra ina zuwa".

"Ina za ki je?" Zahra ta tambaye ta.

"Gurin Yaya Sudais zan je an bani saƙo ne a gurinsa". Daga haka ta bar gurin. Girgiza kai Mammy ta yi ba ta ce komai ba. 

Faruk ya ce "Saƙon da zuciyarta ta aiko ta da shi ne za ta sanar masa, Allah Sarki Ilham wallahi Mammy yarinyar nan ba ƙaramin so take yi wa Yaya ba, amma shi kwata-kwata ba ta gabansa". 

Mammy ta ce "To ya muka iya da shi, ni kaina ba ƙaramin tausayinta nake ji ba". "Kai gaskiya Yaya bai haɗu ba" Faruk ya yi maganar yana barin falon.

A bakin ƙofar ta tsaya tana knocking, babu za to ta ji ya ba da izinin a shigo. A hankali ta tura ƙofar ta shiga, yana zaune saman gado ya sauko da ƙafafunsa ƙasa hannunsa riƙe da wayarsa yana dannawa. Zama saman kujerar dake ɗakin, ta tsura masa ido ba tare da ta ƙifta ba, wata irin ƙaunarsa ce ta ji tana fizgarta. "Lafiya kika tsare ni da ido? Ki faɗi abin da ya kawo ki". 

Numfashi ta sauke, ta fara in da in da, "Am dama... Dama..." 

"Dama me? Ki yi magana ba na son shirme". Idonta ne suka ciko da ƙwalla ta tsare shi da su tana kallonsa. Ɗago da kansa ya yi idanunsu suka sarƙe cikin na juna, da sauri ya kawar da kansa tare da faɗin "Ya Allah!". 

Haka kawai Ilham ta fara kuka, shiru ya yi yana sauraren ta, kusan minti biyar sannan ya kuma cewa "Ilham idan ba za ki yi magana ba ki tashi ki fita ba na son hayaniya". Ƙara sautin kukanta ta yi, muryarta na rawa ta ce "Yaya Sudais wai me ya sa ka tsane ni ne? Me na yi maka da ba ka sona? Shin laifi ne don na ce ina sonka a matsayinka na Yayana wanda na san akwai aure tsakanina da shi? Why Yaya? Ka san irin halin da zuciyata take ciki? Ka san irin ƙunci da damuwar da nake ciki na shirin aura mini waninka da ake yi, Yaya me ya sa ba za ka ji tausayina a matsayina na ƴar uwarka ba? Ko ba za ka so ni ba na yarda ka amince ka aure ni wallahi zan iya zama da kai a kowane irin hali, ko da ba za ka yi mini magana ba, ko ba za ka zo inda nake ba, kai ko ba za ka ba ni duk wata kulawa da ta dace miji ya bawa matarsa ba na yarda na amince zan iya zama da kai a haka. Ban ce dole sai ka so ne ba a yanzu. Alfarma nake nema da ka yi wa Dady zancen aurena, wallahi na san zai amince". 

"Shi kuma wanda waccan ɗin ya kike so a yi da shi? Bayan ke kika bayar da damar ya zo". 

"Ba ni na bayar da damar ya zo ba, Momy ce ta ce na amince, kuma ta gargaɗe ni a kan haka, amma ba na sonsa kai nake so". Ta kai ƙarshen maganar tana kuka mai ratsa zuciya.

"To koma dai ya ne tun da har an bashi dama ni ba zan tunkari Uncle da wannan zancen ba, saboda haka ina ba ki shawara da ki haƙura kawai ki aure shi". Sudais ya yi maganar yana ci gaba da danna wayarsa. 

"Haba Yaya yanzu shikenan sai a...." Ɗaga mata hannu ya yi, ba tare da ya ɗago da kansa ba ya ce "Ilham tashi ki bar ɗakin nan, ba na son shirme". Ganin babu alamar wasa a tattare da shi ya sa ta tashi jiki a sanyaye ta fita tana ci gaba da kukanta. 

A hankali ya ɗago da idonsa ya kalli ƙofar ɗakin, shiru ya yi yana kallon ƙofar kafin ya kawar da kansa ya ci gaba da dannar wayarsa.

Ilham na fita ko da ta sauka ƙasa ba ta tarar da kowa a falon, kai tsaye fita ta yi harabar gidan ta shiga motarta ta bar gidan.

*****

"Zuhura" 

"Na'am Abbi"

"Idan Allah ya kai mana rai ki shirya gobe za ki yi baƙo" Zuhura ta ce "Baƙo kuma Abbi? Waye?". 

"Eh baƙo, kuma ina son ki yi masa tarba ta mutunci saboda babban mutum". Sardauna ya faɗa yana kallonta. "Abbi kar dai tsoho za ka aura mini? Ni fa ina da wanda nake son aura, ka yi haƙuri zan kawo maka shi ba sai ka aura mini tsoho ba" ta kai ƙarshen maganar tana yamutsa fuska. 

Murmushi ya yi ya ce "Ki kwantar da hankalinki ba tsoho ba ne yaro ne shar, kawai dai yana da dattako ne da kamala irin na manya, sannan na tabbatar idan kika gan shi ko da kina da wanda kike so ɗin da gaske za ki iya canza ra'ayi". Zuhura ta ce "To fa, ikon Allah Abbi waye wannan kuma?". 

Sardauna ya ce "Ai na san kina da labarin matashin yaron nan mai kamfanin Global Holdings wato Adam A Adam ko? To shi ne zai zo gurinki, idan Allah ya nufi kun daidaita kanku nan da ɗan wani lokaci za mu sha biki". Ƙwalalo ido waje ta yi tana kallon Sardauna, kafin ta ce "Abbi wannan yaron da na ji kana maganarsa? Wanda na taɓa ganin hotonsa a cikin wayarka?". Sardauna ya ce "Ƙwarai kuwa shi". 

Cikin zumuɗi ta ce "Ai kuwa ina maraba da shi, wannan kyakkyawan saurayin ai ba wadda zai ce yana so ta ƙi amincewa". 

Dariyarta ya dinga yi yana faɗin "Au ba ma ki jin kunyata a gabana kike faɗar wannan maganar?" 

Zuhura ta ce "Sorry Abbi na kasa ɓoye farin cikina ne" daga haka ta tashi da sauri ta shige ɗakinta tana jin wani irin farin ciki a cikin zuciyarta. Sardauna ya murmusa ya ce "Allah ya tabbatar da mana da alkhairi". 

*****

Zaune take saman tsohuwar tabarmar da duk ta cashe saboda tsufa, ta tsurawa yaron ido tana kallon yadda yake cin abinci. Wani irin tausayinsa ne ya kamata. "Allah Sarki, ko ina iyayensa suke da ya taso a gidan marayu?" Ta yi maganar a hankali hawaye na zuba saman fuskarta. Inna Lantana ce ta shigo ɗakin da sallama, da ƙyar ta buɗa baki ta amsa sallamar. Zama ta yi kusa da ita "Ƴata kin tashi daga bacci ne?" Jinjina mata kai ta yi ba tare da ta yi magana ba. Inna Lantana ta ce "Haba ƴata ya kamata ace zuwa yanzu kin saki jiki da mu. Yau fa kusan kwananki biyar a gidan nan amma ko sunanki bamu sani ba, ai ya dace a ce ko sunanki ne mun sani". Shashekar kuka ta fara yi, Inna Lantana ta ce "A'a yi haƙuri kar ki yi kuka, ni ba takura miki zan yi a kan sai kin saki jiki da mu ba. Ki bari duk sanda kika ji hankalinki ya kwanta damu sai mu yi magana". Ta kalli yaron dake zaune yana cin abinci ta dafa kansa tana faɗin "Ɗan albarka abinci ake ce?". Ya kalle ta ya yi dariya, ita ma dariyar ta yi ta ce "Allah ya yi maka albarka". Daga haka ta bar ɗakin. Ajiyar zuciya ta sauke ta bi bayan matar da kallo, Allah ya sani tana son yi musu magana amma sai ta ji bakinta ya yi mata nauyi, tana jin kunyar sanar da su abin da ya same ta.

****

Washe gari, ƙarfe huɗu da rabi Sudais ya yi parking ɗin motarsa a harabar gidan Alhaji Sardauna. A hankali ya fito daga cikin motar yana bin gidan da kallo. Babban gida ne da a ka gina sa cikin tsari mai kyau, an ƙawata shi da adon furanni masu kyau da ɗaukar hankali. Sardauna ne ya fito fuskarsa ɗauke da fara'a yana faɗin "Oyoyo Adam sannu da zuwa". Murmushi Sudais ya yi ya gaishe shi cikin girmamawa, Sardauna ya ce "Yau muna da babban baƙo, bismillah zo mu shiga ciki mana". Bin bayansa ya yi, ya kai shi falon tarbar baƙi, cikin ƙanƙanin lokaci ma'aikatan gidan suka cika gabansa da abinci kala-kala. Nan suka ƙara gaisawa, Sardauna ya ce "Adam ci abinci mana" Sudais ya yi murmushi kafin ya ce "Afuwan, ina azumi ne" .

"Ah ma sha Allah, Allah ya karɓa ya ba da lada, ka yi kyaun kai Adam Allah ya biya buƙata, bari na turo maka Zuhuran ku gaisa" . 

Sudais ya ce "To shikenan" daga haka Sardauna ya bar falon. Sudais ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya fara dannawa.


Amanarcool
***