Farautar Mutunci

Chapter 1

by @oumfatayat

FARAUTAR MUTUNCI


Marubuciya:

Nai’ma Sulaiman Daƙayyawa (Oum Fatayat)



Page: 1


Matsakaicin gida ne mai cike da kayan alatu. Ƙamshin tuturaren wutar da ya mamaye ko ina na layin, da yake cikin unguwar Badiko dake Jihar Kaduna ne yasa Mahmud ƙara tsunduma cikin shauƙi, da ƙaunar Nuri don ya san tabbas wanna ƙamshin daga gidansa yake fitowa.


A hankali ya cigaba da tuƙi yana lumshe idanu, zuciyarsa tana alla-alla ya ƙarasa gidan, don yin tozali da ruhin rayiwarsa, sannu a hankali har ya ƙarasa. Dakiɗo mai gadi ne ya buɗe gate ɗin gidan da sauri, cikin nutsuwa Mahmud ya tura kan motar farfajiyar gidan.


A tsaye take ta sha doguwar rigar shadda wanda ta ji ɗinkin surfani, ta naɗe hannayen ta a kan ƙijinta, taku ta fara sannu a hankali kamar mai tausayin ƙasa, fuskarta cike da fara’a ta nufi inda Mahmud ɗin yake tsaye kamar wanda aka dasa shi.


Hannayensa ya buɗe, alamun ta taho,tana tq kwanta a cikin ƙirjinsa, kai tsaye gare shi ta nufa, inda ta lafe a ƙirjinsa kamar wata mage, ƙafafunsa ne suka kasa ɗaukarsa,ƙoƙari yayi ya jingi na a jikin motarsa, tare da sauke ajiyar zuciya a lokaci guda.


Ganin ba shi da niyyar sakinta ne, yasa ta ɗaga kai ta kalle shi, sai dai idanuwansa arufe, gyaran muryat ta yi, shima dai taji shi shiru, daidaitar lebansa tayi takai bakinta ta ta kamo da haƙorinta ta ɗan masa cizon wasa, yar ƙara ya saki, “Wash” Dariya ta yi kana ta shiga cikin falon da ɗan gudu-gudu.


“Wai ni kika ciza? Aikuwa sai na rama”.


Shima da gudun ya shiga falon,nan suka fara zagayayeniya a tsakanin kujeru, gwalo ta ke masa, ganin ya kasa kamata ne yasa ya faɗi ya riƙe cikinsa alamun yana masa ciwo, da sauri ta ƙaraso inda yake. 


“Hubbina mai nene kuma ya same ka?” 


Kafin kace kwabo ta matso kusa da shi, tana jijjiga shi amma shiru, kuka ta fara sosai har ta kai ga cire ɗankwalin kanta a gefe guda, baƙin gashinta da ya zo mata kusa da gira, ga shi da tsayi duk ya barbazo mata a fuskarta. Ɗan buɗe ido ya yi kaɗan,y ganin tayi masa kama da bebin roba ne yasa shi fashewa da dariyar da baiyi niyyaba.


Bori ta fara yi tana mumurzaƙafa akan Carpet, cigaba tayi da kukanta wiwi, kamo ta ya yi ya haɗe bakinsa da nata, tsawan awa guda suka kasance a haka, sarrafata ya fara yi cikin salo na nuna ƙauna da bayyana tsantsar soyaya, bayan wasu a wanni kuma ya ɗauke ta cilak zuwa ɓangaransa.


Sarrafa ta yake cikin salo na ƙwarewa, wanda hakanne ya ke ƙara nutsarda su cikin bege da shauƙin juna, ba su ankara ba suka ji muryar ladani na kwaɗa kiran Sallah magrib, adole ya yaƙyaleta ba don ya soba. Wanka suka shiga cikin farin ciki da nuna kulawa, daga nan ya jasu Sallah don ko ya fita massalaci ma ba zai samu jam’iba.


fitowa suka yi, kai tsaye wajen dining table Nuri ta nufa, langwaɓe kansa ya yi 


“Gaskiya Nuri ni dai kawai ki sakko da kayan abincin nan ƙasa muci, so nake na zauna akan cinyarki”. zaro ido ta yi kawai ta fashe da…



 بقلم أم فتيات 👧👧👧 ✍🏼…