20
by @gureenjoh
A hankali kuma sai ya janye idanun ya miƙe ya fice daga ɗakin, ba'a jima ba ya shigo da likita har kuma lokacin hiransu suke tsakaninsu ita sai ya kama take saka baki, yana mamaki a ce mace ce bata da lafiya amma maza ne zagaye da ita, yadda bata nuna ta sanshi ba shi hakan faranta masa yayi don bai san ta ya ma zai nuna wata alaƙa ko min nisanta tsakaninsu ba iyayenshi na wurin don abin Sam ba tsari, bai taɓa cin karo da marar lafiya bai yi masa gaisuwa ba ko fatan waraka daga rabbi ba sai a kanta haka kawai sannu ba ya so ya ji ya haɗa su.
Likitan ya duba hoton da aka karbo ya tabbatar ba wani matsala yace za su iya tafiya da ita kawai a kula da kafan Sossai bayan sati biyu a zo a cire POP da aka saka mata.
Goggo hindatu ta tattare komai wasu nurses suka zo suka taimaka musu wurin ɗora ta kan wheelchair Goggo hindatu ta tura ta a tsorace suke da su Diva din don a yanzu sun ƙaru hakan yasa ko Daddah da ke son yi mata Allah ya kara sauki bata yi ba suka fice da ma shi ya jima waje yana jiransu.
Kofar da suka rufe ta zurawa idanu ba yau aka saba gudunsu ko kiyaye wa inda suke ba hasali hakan na yi mata daaɗi kwarai ta zo wuri a shiga taitayi kuma a natsu har ana kiyaye hasalarta amma a wannan karo ta ji abin babu daaɗi, suna nuna kaman aljana ce ko wata halitta mai muni ba mutum ba hakan ya tsaya mata a rai amma ta basar.
Tana sauraron hiran su Shaly kaman ko yaushe, itama a ranar aka yi hoton hakarkarin aka ci sa'a wukar bai taɓa mata koda ba, daga nan hankalinsu duk ya sake kwanciya amma ban da Jagaban da suka rasa kanshi a kwanakin duk ya zama very busy baya zama sun kuma kasa pinpointing matsalar.
Ta ɓangaren su Shehi yana driving da hannu ɗaya dayar hannun yana riƙe da waya da Abbiey yake magana akan idan sun tashi aiki kar su je asibitin an riga an sallami Daddah ɗin, bayan sun gama ya ajiye wayan yana sauraron hirar Daddah da Goggonshi Dija duk a kan su Diva ne da irin abin da ta sha a ɗakin da kuma rashin tarbiyarsu har suka isa gida bai cewa kowa komai ba. A kofan sashen Daddah din ya yi parking duk ahalin gidan suna tsaye har ta sauka suna yi mata sannu har cikin parlor, Daddah kaka ce wacce bata da tamka, daga jikokin surukanta har yaranta bata yarda ta takurawa kowa ba hakan ya sa ta zama dattijuwar arziki da kowa ke ji da ita a gidan, ta kan kafe akan lamari amma muddin ka ga ta kafe ɗin to abin babba ne, sun jima zaune ana ta hira a parlorn kan suka watse saboda magrib da ya karato kowa ya tafi shirin sallah.
Shi dai Shehi tunda ya sauke su ya wuce bangarenshi wasu ayyuka ya rage Sossai bai tashi ba sai lokacin sallah ya yi alwala ya fito ya saka wa magenshi abinci daga nan ya fice zuwa masallaci.
*****
"Abbiey baka ce komai ba"
Ammie ta faɗa tana ƙarasa tattare kwanukan abincin da Abbiey din ya gama ci, ya ɗan yi murmushi
"Da alama kin matsu ki ga 'yan jikokinki"
Itama tayi murmushi
"Toh ai na ga ne ku babu ruwanku da musu magana akan auren, har yaushe zai mayar da hankali idan ba'a tuna masa? Shekarun suna ta tafiya gwara a yi din muna raye"
Yace
"In Shaa Allah zamu yi magana da ɗan uwana sai mu ga yadda abun zai kasance, amma ya je ya ga yarinyar kika ce?"
Cikin farin ciki marar misaltuwa da ya zo wa Ammie tace
"eh ya je, kuma daga shi har ɗan uwansa Ammar sun yaba kwarai da hankali da natsuwarta Nima kuma na yaba da ita gaskiya"
"Amma kina ganin ba mu tauye shi ba kawai mu ce ya yi aure ba tare da shi ya ganta ya ji yana so ba?"
"Toh sai yaushe za mu jira Abbiey? Tunda bashi da wannan niyyan gwara mu shige mishi gaba kawai matukar nagartar yarinyar ya yi daidai da nashi"
Abbiey ya sauke Numfashi Sam baya son tauye iyalansa amma tunda sun gama yanke hukunci za'a yadda suka ce ɗin.
"Shikenan za mu yi magana da Abbansu mu tsara yadda abin zai kasance"
Ya faɗa yana Miƙewa itama ta miƙe ta bi bayanshi zuwa dakinshi fuskarta cike da annashuwa.
Da daren Ammie ta kasa hakura ta kaiwa 'yar uwarta ziyara suka fara tattauna wa akan abubuwan da za su tsara suna cikin maganan ne ma Shehi da Ammar suka shigo wuraren tara da wani abu.
Sun yi mamakin ganinsu tare Ammar sai da ya tanka
"Yau kuma hirar 'yan uwantaka ne ya tashi har cikin dare Ammiey?"
Maamah tace
"Kin ga wanda ya kamata a yi wa aure don yana bukatar abin da zai ɗauke hankalinsa har ya kashe wannan bakin da ba ya shiru"
Dariya yayi Shehi na murmurshi ya zo ya zauna kan ya gaishe da iyayen nashi suka amsa cikin kulawa kan Ammiey tace
"Rabu da shi Maamah shi waye ya raba shi da nashi ɗan uwan ba gashi kullum suna tare ba?"
"Daga gani dai hirar ta nishadi ce mu zauna ko mu yi gaba?"
Ammar ya sake faɗa yana zama cikin murmushi shima ya gaishe su haka yake don ma ba ya mood ne amma iyayenshi tamkar kakanninshi haka ya mayar da su akwai wannan sakewar da kuma hira Sossai tsakaninsu ba kaman Shehi ba ko don zaman kasan bai yi shi yana ƙarami bane sai da ya girma oho.
"Zancen auren ɗan uwanka ne muke tattaunawa"
Haka kawai Shehi ya ji gabanshi ya ɗan fadi amma bai dago ba Ammar ya amsawa Ammiey
"Masha Allah! Mu fara shirye shirye kawai mu ma da alama ba za'a ɗau lokaci ba"
Maamah tace
"In Shaa Allahu soon za'a yi dama matar ne ake jira ba komai ba"
Sai ta kalli Shehi
"A kawo maka abinci ne Sheikh?"
Ya ɗan dago kaɗan
"A'a Maamah ba buƙata zan sha Laban kawai ya wadatar"
"uhmmm! ka ji Larabawa"
Ammar ya faɗa da zolaya, Irshad ya kalle shi ya harareshi ina ruwanshi dariya kawai yayi sai Irshad ya zuba masa idanu.
Yana mamakin yadda Ammar ya danne yanayinshi yake wasa da dariya, ƙazafi irin na sata ko ya yake babu daaɗi cin rai ne dashi da hana bacci gashi har yanzu Abba ba kulashi yayi ba bare ya fahimci babu hannun Ammar a lamarin ɓacewar kudin companyn.
Maganan Ammiey ne ya dawo da shi ɗan tunanin da ya tafi sai ya kalle su sun miƙe Ammiey za ta tafi Mamaah kuma za ta mata rakiya sai ka ce ba gida daya suke ba, sai da safe suka mata ta wuce sun jira Maamah ta dawo itama suka mata sallama kan suka fice kowa yayi sashenshi.
*****
Tsaye take gaban reception ɗin za ta saka Hannu a wani takarda da aka rubuta record book, Rubutun ta zubawa idanu inda aka shigar da sunanta ranar da aka kawota sai ta ɗan lumshe ido tana tuna yadda ya riƙe ta da yadda muryarsa dake fita daga nesa Sossai a cikin kanta ke Salati da ambaton wani suna da ba zata ce ta ji ba.
"Suhan Muhammad"
Ta maimaita, shi ne rubuce a katin da ya buɗe ya aka yi ya san sunanta? A saninta dai bata tare da kowani identification card da ya bayyana sunanta, babu waya a hannunta ya aka yi ya san sunanta?
Canular da ba'a kai ga cire wa ba ta zubawa idanu kuma har jininshi ya bada a lokacin da nata ke shirin ƙarewa aka sanya mata, yanzu jininshi ne ke yawo surke da nata.
"Waye wannan?"
Ta faɗa chan ƙasa, Jagaban dake tsaye da ita yace
"kika ce?"
Sai ta girgiza kai kawai ta saka hannun, suka karasa nurses station aka cire canular ɗin kan suka fice daga asibitin, da kanta ta buɗe seat na gaba ta zauna ta kwantar da kanta jikin kujerar.
Saboda ita Jagaban ke Driving cikin hankali idan ba haka ba shi ma ya ƙware a rough driving yadda take yi idan na rashin mutuncinta na kusa.
"Waye JJ baba? Meyasa ya nemi kasheni?"
Sai da motar ta kusa kwacewa daga hannun Jagaban, ya samu ya dakatar yana kallon ta don kaman saukar aradu haka ya ji maganan nata, idanu ya ɗan rufe ya buɗe
"Sohana yanzu ba lokacin wannan magana ba ne, ni kaina ban san waye JJ ba da kuma dalilin taɓaki amma na yi alkawari zan nemo shi ko a ina yake sai ya san ya taɓa ki, daga yanzu kuma bana so ko da wasa ki fita ke kaɗai musamman idan cikin dare ne"
Ta koma ta jingina da motar tana zubawa waje idanu a karo na farko ta ji bata yarda da maganan Baban ba, amma itama ba za ta zauna ba za ta yi iya bincikenta wurin sanin menene dalilinsu JJ na zaɓarta ya nemi kashe ta, waye ne wannan da ya taimaka mata? Abu biyu ne gabanta a yanzu.
Har suka isa bata sake magana ba, sun samu gidan cike sai maraba ake mata cikin salonsu na dabanci tayi murmushi tana hade hannaye alamar godiya da haka ta shige ciki Shaly da Zubash suka bi bayanta.
****
"Zainab! Tun muna shaida juna ki fitar da sarkar nan"
Dattijon yayi magana da karfin gaske muryarshi na fitar da gajiya da wani irin yanayi marar misaltuwa.
"Ni dai sharri ne kawai amma ban ɗauki wani sarka ba Daddy a shafa min lafiya..."
Hannu ya kai zai zuba mata mari matar dake zaune daga gefenta tayi zuruf ta tare.
"A'a Alhaji ba za ka dukar min yarinya ba, tace bata dauka ba bata dauka ba to me za ta fitar? Don kawai ta zama kaddarar gidan nan sai aka ce duk wani mugun abu ita ce?"
"Wallahi wallahi Subai'a idan na miki Allah ya isa sai Allah ya saka min akan yaranki, Allah ya gani kuma shine shaida iya kokari na yi wurin tarbiyatar da yarinyar nan amma ke bata taɓa laifi a idanun ki ba, babu wanda ya isa ya hukuntata a duniyar nan baki ɗaga ido kin kalleshi kin rama mata ba, yanzu yadda take yawo lungu lungu da gungun 'yan daba ashe bai zama miki izina ba? Wallahi ko rantsuwa zan yi babu kaffara Zainab ce ta ɗauki sarkar nan don haka ku fitar na gaji da biyan abinda ban ci ba"
Wacce aka kira Subai'a ta kalli Alhajin tace
"Ai dama abin da kake nema kenan kiris ka daura min alhakin lalacewar Zainab, kun kyauta ke kuma suwaiba in karya kika mata ma ke da Allah. Zainab ke tashi mu tafi"
Ta miƙe tare da jan hannun Zainab din suka fita, Alhj ya tafi da baya kaman zai fadi suwaiba ta tare shi suka zauna.
"Ba damuwa Alhj na hakura da sarkar duk da yana cikin zinari na mai tsada amma ba komai, Allah ya shirya mana ita ya sa ta gane don Allah kar ka ɗaga hankalinka"
"Suwaiba na gaji da ganin Subai'a da Zainab a gidan nan na gaji"
"Na sani amma babu ta yadda hannunka zai rube ka yanke ka yar, kana addu'a baka taɓa gajiya ba ka cigaba in Shaa Allah za su chanza"
Ya kalleta
"Kin san dai Ƙarfe ɗaya bai taɓa amo ba dole sai ya haɗu da wani karfen, kina ga Zainab ta cigaba da zama da Subai'a da ta watsar da alhakin tarbiya da Allah ya ɗora mata ta ɗauki soyayya mai muni ta ɗora wa kanta akan yaranta zai bari su shiryu? Ba Za su taɓa shiryu wa ba ina tsoron tambayar Allah akan yaran nan"
Shiru suka yi cikin jimami, tsawon shekarun talatin da wani abu suke rayuwa tare da 'ya'yansu amma duk wanda ya shigo gidan ya san Yaran Suwaiba daban da yaran subai'a, samm bata yarda da abin da zai taɓa su ba, bata yarda ko da wasa sun yi laifi wani lokacin ko a kan Idanunta kuwa za ta mutsuke ta nuna basu yin ba kuma ya sha kenan.
Wannan sakacin ya jefa Zee-zee cikin halin da take ciki har ma take bibiyar Diva dukda kudin mahaifinta, yayi iya kokarinsa har Rehabilitation center ya kai ta Maman taje ta ciro ta, kuma ba ita kaɗai ba har yayyunta biyu duk a watse suke a kan titi babu wanda ya tsaya ya tsinana wa kanshi komai ga yaran Suwaiba har suna iya ɗaga abu da alfaharin nasu ne na ƙashin kansu.
Suna fita Zee za ta fice daga gidan Maman ta riko ta
"Ina kuma za ki je? Meyasa bakya gajiya da janyomin magana ne?"
Kallon yaushe aka fara wannan ta mata kan ta zare hannunta
"Wurin Diva za ni"
Tana kai nan ta yi gaba, a cikinsu duk babu mai daukar abin wani idan ka ga sun yi abu da abin wani to sun lalata ne don Diva bata shiri da ɓarawo bata son sata kwata kwata, basu damu da inda Zee ke samun kudi take saye sayen abubuwan mayenta ba har wani lokacin ma ta sayawa kowa free sanin cewa babanta mai kudin ne ita kuma ta ishe 'yan gidan da dauke dauke duk abin da suka ajiye mai muhimmanci in dai ta gani sai ta dauke shi.