Waiwaye
JA DA BAYA...
Book 1
Page 3✍️
Meelah Bazata
***
MAI RABO ESTATE shine sunan da yake rubuce a katon get din da zamu iya kiransa da kofar gari, domin estate ne mai girman gaske. Kowa yasan family din Mai Rabo domin kuwa ba boyayyen family bane. Alhaji Yusuf Mai Rabo shahararren dan kasuwa ne wanda duniya ta sanshi ta fannoni da dama. Mutumin kirki ne, sannan hamshakin dan kasuwa. Yanada mata guda biyu; uwar gidansa mai suna Yagana, sai kuma matarsa ta biyu mai suna Saadatu.
Asalin Alhaji Yusuf Mai Rabo dan jahar Taraba ne, yankin Gembu, Mambila. Asalin su acan yake, iyayensu su uku suka Haifa; yayansa Aminu, sai kuma shi, sai kanwarsu Karimatu. Tun tasowarsa yanada nasibi akan nema, hakan yasa yake son makaranta, sannan iyayensa sun bashi goyon baya. Yana zuwa karatu can cikin Taraba, ahaka aka yiwa kanwarsa aure, Karimatu, inda take auren wani acikin nan Mambila din, wani kauye Mayo Salbe. Alokacin da yake shirin kammala makaranta, wani iftila'i ya same su inda ya dawo gida ya tadda gobara ta kama a gidan iyayen sa, da kuma yayansa duk sun mutu. Sun yi kuka sosai da sosai, yana ganin yanzu bayida kowa sai Karimatu, sai kuma yan uwan wadanda ba za a rasa ba.
Bayan lokaci kadan zaman garin ya ishesa, hakan yasa ya tattara ya koma Kano da zama, kasuwanci suke acan inda uban gidansa yana jin dadin aiki da shi, kasantuwar yanada sani akan kasuwanci yasa komai ya taba sai abin yai albarka. Ya zamana ya dogara da kansa, duk yanada abokan kasuwanci. Inda acan kasuwanci ya kaisa Maiduguri, inda wanda suke turawa kaya shima kamar uban gidansa yake daga Kano zuwa Maiduguri. Shine ya fara yabawa da hankalinsa, yace zai bashi auren yar sa Yagana. Mutum ne babban mutum ne, ya dauki Yusuf amatsayin da ko dan, sabida amanarsa bai yi musu ba, ya amsa hannu bibbiyu. Ba a dau dogon lokaci ba akayi aure inda amarya ta tare a gidan mijinta, anan garin Kano. Yagana ta kasance mai hakuri, sannan batada shiga abinda bai shafeta ba. Zaman su suke hankali kwance.
Shekara hudu da aurensu sunada yara biyu: Sulaiman da kuma Bello. Alokacin ne Yusuf suka tafi Saudiya shida Yagana. Su Yagana an zama Hajiya ga arziki yana ta habbaka kasantuwarsa mai nasibi. Bayan dawowarsa, ya tafi Mambila duba yar uwarsa Annane, Allah ya hada sa da Saadatu, kyakykyawar Bafulatana ta hakika. Alokacin yarinya ce mai tsananin kyau, marainiya ce sannan ba ta samu riko mai kyau ba, hakan yasa ta taso cikin wani kadaici da sanyin hali. A kallo daya Allah ya daura masa kaunarta mai tsanani, bai ja da nisa ba ya tambaya yar uwarsa game da ita, take bashi labarinta inda kuma ta bashi goyon baya akan auren Saade. Be bar garin ba seda iyaye suka shiga ciki kuma aka bashi, hakan yasa ya je ya samu mahaifin Yagana ya gaya masa, kuma harda shi aka shige masa gaba gurin neman auren. Yagana tana da kishi, amma fahimtar mijinta yana son Saade sosai yasa ta hakura. Ya auro Saade, zaman su suke hankali kwance.
Saade tana son yaran sosai har akai shekara biyar Allah bai bata haihuwa ba, domin sau biyu tana samun ciki sai tayi bari. Sai acikin shekara ta shida, ba wanda yasan tana da ciki ma. Wanda alokacin Yagana tana da cikin wata bakwai, ma haihuwar Yagana da wata daya, Saade ta haifi danta namiji mai tsananin kama da mahaifinsa. Hakan yasa kowa yayi mamakin haihuwarta domin ba wanda yasan tana da ciki, sedai ciki ya isa haihuwa. Sun yi murna sosai inda dan Yagana mai suna Aliyu, sai dan Saade Muhammad kenan. Bayan haihuwar Muhammad da shekara uku Allah ya kara ba Saade ciki, ta haifi danta namiji aka sa masa suna Ahmad. Still dai yaranta sun fi kama da mahifinsu domin Saade Bafulatar Mambila ce, haka shima Yusuf haka.
Bayan haihuwar Ahmad, Yagana ta haifi danta namiji aka sa masa suna Umar. Tsakanin Umar da Ahmad ba wani tazara, hakan yasa suka tashi atare, komai tare suke yi. Muhammad ne ma ba wata shakuwa tsakaninsa da sauran, suna ganin kamar mahaifinsu yafi son shi, shiya suke kyararsa daga zarar ya matso su. Haka kuma ko shi Ahmad din, kawai dai dan suna da sawa da Umar ne. Muhammad da Ahmad akwai shakuwa mai karfi atsakaninsu domin burin mahaifiyarsu kenan taga kansu ahade, suna matukar kaunar junansu. Yaran duk sunyi wayau inda kowa yana zuwa makaranta. Yaran Yusuf guda shida duka maza.
Bayan wani lokaci, Yagana ta samu ciki inda cikin ya bata wahala sosai, ahaka kuma cikin yazo da laulayi sosai, hakane yasa cikin ya bata wahala. Bayan cikin ya isa haihuwa, ta haifi yarta mace Masha Allah, mai kama da mahaifinta. Sun yi farin ciki bada wasa ba kasantuwar ba su da ya mace, barinma Saade sabida ita ba ta kara haihuwa ba ma. Yarinya taci suna Halimatu. Haka suka taso, girma ya kama su, kowa yanzu ya mallaki hankalinsa. Inda alokacin Alhaji Yusuf suke kiransa da Alhaji Baba, Yaganah kuma Hajja, Saade kuma Inna. Alhamdulillah rayuwa tai albarka inda babu wanda baisan Alhaji Yusuf Mai Rabo afadin kasar da kewayenta ba. Sannan kuma ya gina wani katon estate me girman gaske, domin kuwa misalta girman estate din bata lokacine, domin shi mutunne mai son yaga iyalensa akusa, kowa akwai bangaren sa. Haka kuma gurine wadacce bayan shekara sha biyar abubuwa sun canza, dayawansu sun yi aure.
Sannan Alhaji Baba alokacin yayansa duk sun yi aure, Halimatu tana auren wani minister, bama a kasar suke zaune ba. Sulaiman wanda suke kira Daddy yana da yara biyar da mata daya mai suna Hawwa, yaransa uku maza, biyu mata. Khalid shine babba, sai Haidar, Ammar, sai yan biyu duka mata Najlah da Najmah. Sai Bello wanda suke kira Baba, yana da yara uku, namiji dayane sai mata biyu: Umair, Fadeela, sai Khairah. Aliyu wanda suke kira a Uncle Ali yana da mata biyu, yara biyar; uwar gidansa tanada yara biyu Hanifah da Hanif, amarya kuma tana da yara uku: Hafiz, Muhibba sai Mufidah. Sannan Umar shima yayi aure, yayansa hudu, maza biyu mata biyu: Sadiq, Anwar, Beenafah, da Hibba.
Muhammad sun rigasa aure domin seda suka fara haihuwa ma kafin Allah yasa yayi aure, kuma sun yi aure rana dayane tare da kaninsa Ahmad. Haka kuma matansu kawayen junane. Wata tafiya dasukai zuwa Abuja, acan suka hadu. Maleekah ainayin mahaifiyarta Balarabiya ce, mahifinta kuma dan Yola ne acan ya aureta, mahaifiyarta ta rasu sedai yan uwa. Sannan su biyu iyayensu suka Haifa da kanwar Sameerah. Tana wurin babanta anan Abuja, aiki ya kaisa. Ita kuma Ameenah sun hadu a makaranta, suna matukar kaunar juna hakan yasa koyaushe zaka gansu tare, har yan uwa sun san juna. Muhammad ya fara son Maleekah inda kaninsa ya fada soyayyar Ameenah, hakan yasa sun yi farin ciki ganin zasu zauna a gurin daya. Sannan anyi aure an kaisu suma Mai Rabo Estate a rana daya. Zuwan da sauran matan da yawa suka ware su, ganin sun darasu a abubuwa da yawa.
Muhammad Allah ya sa ba haihuwa, sedai aranar dan ya koma sun ji ba dadi sosai, amma haka suka dangana. Bayan wani lokaci Allah ya ba Maleekah ciki inda suka haifi yarsu mace suke kiranta Jauhar. Sannan seda Jauhar tayi shekara biyar aka haifi Ayzaan (kyautar Allah) wanda yaci sunan kakansa wato Yusuf. Kuma haihuwarsa tazo da wani al'amari mai girma, dashine silar komai a cikin wannan family. Yana dira a wannan duniyar ubangiji ya daurawa mutane dayawa kaunarsa, haka kuma ya daurawa mutane dayawa kiyayyarsa.
Maleekah wato Ummee babu dan da take so a duniya kamar Ayzaan, haka mahaifinsa. Sedai har alokacin Ahmad matarsa bata haihu ba. Tsananin farin ciki da Ameenah tayi bata baki ne, hakan yasa gaba daya Ayzaan a gurinta ya tashi. Soyayyar da take nuna masa ko Mahbub bata nuna masa ita ba, domin Ayzaan nada wata biyar Ammee ta haifi Mahbub. Hakan yasa suka taso tare da Ayzaan, sedai Mahbub yafi wuni ma abangaren Ummee domin Jauhar tana son daukarsa kasantuwar baya kuka. Shi kuma Ayzaan indai ba Ummee ko Ammie ba, to babu mai daukarsa, ya yarda shi. Kuma Mahbub yana da karafniya tun tasowarsa. Ayzaan kuma miskili ne na hakika wanda seda kowa yai zaton ko baida lafiya ne, domin baya magana se a wuni indai ba a gurin Ammee yakeba, ko kuma Alhaji Baba, to bazaka ji maganarsa ba. Sedai yana matukar kaunar yayarsa Jauhar wacce suke kira da Didi. Ayzaan da Mahbub sune suka sa mata Didi.
Alhaji Baba yayi matukar shakuwa da Ayzaan wanda yake kira da Zaki, hakan yasa suke jin tsanarsa ganin ya dau soyayyar duniya ya daurawa Ayzaan. Ummee bata sake haihuwa ba har Ayzaan yayi shekara goma. Awannan lokacine Allah ya ba Ammee ciki, ya Allah farin ciki a gurin Ummee bata baki ne! Murna take kamar itace mai cikin haka. Ahmad wanda Ayzaan yake kira da Abbie, Abbie yafi kowa farin ciki da wannan ciki domin shi kam yana son yara sosai. Cikin ya ba Ammee wahala sosai, wanda har seda aka yi tinanin ko a cire cikin. Ikon Allah ta haifi ya mace, ya Allah yarinyar da wasu da yawa a gidan suka danganta da aljana domin yarinyar tazo da wani sabon al'amari sabida wani irin kyau da kuma fari, farace har tana daukar ido. Sekuma gashi Wanda gashin kanta har yana rufe mata fuska.
Ayzaan yafi kowa kaunar yarinyar domin babu wanda ya isa ya tabata. Asalima dayawansu seda aka haifi yarinyar suka taba ganin dariyar Ayzaan. Akanta ze zauna yaita kallonta yana murmushi. Sun yi fada sosai da Mahbub amma Mahbub bai isa ya taba yarinyar ba, tunda aka haifeta yake ce mata "Chuchu". Sannan shine wanda yasa mata suna INARAH, taci sunan kakarta wato Sa'adah. Hakan yasa Ayzaan yasa mata suna INARAH.
INARAH kuma haka ta taso a duniya babu abinda takeso kamar Ayzaan, in yatafi makaranta tadinga kuka kenan. Ta taso da surutu sosai, shi kuma Ayzaan miskili, amma ahaka dole dan ita yake mata magana. In kaga yana magana to an taba Reehal. Kasantuwarta me tsokana yasa take cin duka a gidan. Ahaka duk wanda ya taba ta, to a ranar babu zaman lafiya a gidan. Gashi har yayyenta shakkarta suke, yasha yiwa sauran yaran gidan duka akan Inarah, wanda ko Ammie ba ta isa ta duki Inarah ba. Sun yi shakuwa sosai wacce takai ko bacci ma ba ta yarda tayi se atare da Ayzaan. Har ta kai shekara biyar inda Ayzaan ya shirya mata wani gagarumin birthday. Kuma a wannan ranar ne mummunan abinda ya faru da ita wanda ba za su taba mancewa ba. An yi shiri sosai da sosai, ga yara saanninta Khairat, Hibbah, Mufeedah sun yi kwalliya sosai, inda Ayzaan ya tafi ya shirya. Ita kuma Inarah Ummee ta gama shirya ta, da saurinta ta tafi tana cewa zata gurin Ayzaan ta nuna masa kwalliyarta. Sedai babu wanda ya san me ya faru da ita a wannan ranar, kawai sun tsince ta cikin jini ne.