Shafi na takwas
YARIMA BAHJAT 🌏
Na
Harira Salihu Isah
(Uwar Batoorl)
SHAFI NA TAKWAS
⭐️
FULANI HAJARA
A hankali-hankali jikinta ke motsawa alamar kuka take a sujjadan, sautin muryarta ma a hankali ya fara fitowa.
A lokacin da sautin kukanta yayi yawa har ya isa kunnen Mai martaba Sarki Ahmad, nauyayyar numfashi ya ja ya sauƙe, sannan da kamammen muryarsa cikin kulawa ya ƙira sunanta.
"Hajara!"
Maimakon Fulani Hajara ta sassauta kukan, sai ƙaruwa da sautinta yayi, addu'ar da take yi cikin sujjadar ma dakatawa da shi tayi, kuka take yi da gaske bilhaƙƙi, da wani irin sauti da ke bayyana daɗaɗɗen ciwon da ke danƙare a zuciyarta.
"Hajara!"
Sarki Ahmad ya sake ƙiran sunanta, amma a wannan karon ya sanya hannayensa ya ɗago kafaɗunta, wanda hakan yayi sanadin ɗagowarta a sujjada, bai tsaya ɓata lokaci ba kuma ya haɗata da jikinsa ya kama lallashinta da kalaman natsuwa, gami da ba ta misali da ba ita ce ta farko da ta fara fuskantar jarabawar ba, kamar yadda ba lallai ta zama ta ƙarshe ba.
"Kiyi haƙuri Hajara, ina baki haƙuri ne ba dan kin fini jin ciwon rashin Tajuddin ba, sai domin kin fini nuna ciwon da kike ji a fili, amma a zuciya na fi ki jin ciwo Hajara, domin gwanda ke Hajara, kin zauna da Yarima a cikinki har tsawon watanni tara, kin saba da shi a hakan da motsawar da yake a cikinki, Hajara ba ko yaushe nake samun dama da lokacin saka ki a gaba, naga yadda Yarima ke motsawa a ciki ko ma nayi hira da shi ba, saboda sha'anin mulki, a lokacin da nake cikin ɗauki da farincikin zan ga gudan jinina, zan ɗauke shi, sai kuma wata ƙaddarar ta gifta, a ranar da lokacin sai da naji komai na duniyata ya tsaya, wanda har zuwa yanzu banji komai ya koma daidaita ba, nayi ƙoƙarin nunawa mahalaccina na amshi Ƙaddarar ɓacewar Yarima Tajuddin, kamar yadda Annabi Yaƙub alaihissalam ya karɓi ƙaddarar rashin ɗansa mafi soyuwa, wato Annabi Yusuf alaihissalam, kuma kamar yadda Annabin Allah bai cire tsammani da dawowar ɗansa ba, haka nima ba zan cire rai da rahamar Ubangiji ba, muddin Tajuddin na raye a doron ƙasa, in sha Allah watarana zai dawo garemu da yardar Allah, a yanzu dai muyi haƙuri Hajara, haƙuri mai kyau, in sha Allah watarana za mu ga Tajuddin."
"Allah ka yarda, Allah ka bayyana mini yarona cikin lafiya, aminci da kariyarka."
Fulani Hajara ta faɗa da muryarta da har sannan da yanayin kuka.
Waɗannan addu'o'i ne da tun sanda ta rasa abinda ta haifa take yi, tare da addu'ar kariya da shiryar Allah su tabbata a gare shi a duk inda yake, Allah ya tsare mata shi, kada Allah ya bari wani abu ya ɓata mata rayuwar ɗanta.
A haka Sarki Ahmad ya cigaba da lallaminta da tausasan kalamai, sannan har ya samu ta daina kukan, suka kuma yin addu'a suka shafa, ya taimaka mata ya yane mayafin da ke kanta, sai da ya tabbatar ta kwanta, sannan ya koma wajan da suka ida nafilfilun ya naɗe darduman da mayafinta, daga haka ya ƙarisa kan gadon shi ma, ya jawota jikinsa gami da cigaba da rarrashinta, a haka har bacci yayi gaba da su duka.
Bayan shuɗewar kwanaki biyu, kamar yadda Daleesha tayi magana da Abbinta, wanda za'a iya ce masa shawara, a yau da za su tafi sashin Fulani Hajara da Umminta, ta ƙuduri aniyar cire abinda aka wa Fulani Hajara na rashin haihuwa.
Suna tafe Ummi na ma Daleesha faɗa, a kan ƙin zuwa wajan Fulani Hajara da take yi, domin sam ba ta jin daɗin hakan.
"Daleesha kinga idan za ki ke ƙin zuwa wajanta, to za ki bar biyo ni, ki zauna can da Abbinki."
"Kiyi haƙuri Ummi."
Daleesha ta faɗa a sangarce.
"Muna shiga kije ki tsugunna ki gaisheta kuma idan ta ƙiraki kije."
"To Ummina."
Daleesha ta amsa.
Ummi na gaisawa da Hadimai ƴan uwanta, suna kuma tambayar lafiyar Daleesha, wacce da idanuwa kawai take bin kowa bayan ta ce ma mutum "Ina kwana."
"Ke dai Allah ya yaye miki wannan ƙuya Daleesha, mutane na sonki kina gudunsu, kinji daɗin halinki kam."
Faɗin Ummi.
Da sallama suka shiga sashin Fulani Hajara, sai dai ba ta palour, sai sauran hadimanta da ke kai komo, hakan ya sa Ummi ma ta kama nata aikin, kafun Fulani ta fito su miƙa gaisuwa.
Sai da aka ja lokaci sosai sannan Fulani Hajara ta fito, hadimai suka dinga miƙa gaisuwa, ta amsa musu da sakakken fiska.
"Ina yarinyata?"
Fulani Hajara ta miƙawa Ummi tambayar.
Kafun Ummi ta ce wani abu, sai ga Daleesha ta shigo, hakan ya sa duk suka murmusa.
"Barka da safiya Rankishidaɗe."
Yanayin yadda Daleesha tayi gaisuwar sai duk ya ba su dariya, domin ita idan an barta to tayi yadda hadimai suke yi ne.
"Yauwa ƴar gidan Fulani, barkanki dai, fatan kin tashi lafiya?"
"Eh."
Daleesha ta amsa, sannan ta miƙe daga durƙushen ta ƙarisa gaban Fulani, ta tanƙwashe kafafuwanta ta zauna daidai ƙafar Fulani.
Fulani Hajara murmushi tayi gami da shafa kan Daleesha.
"Allah ya miki albarka Daleesha."
"Amin Ya Rabbi."
Ummi ta amsa cikin murmushi, na jin daɗin albarkar da Fulani ta sakawa Daleesha, da kuma zuwa wajan Fulani da Daleeshan tayi.
Fulani ƙoƙarin jan Daleesha da hira tayi, har dai ta miƙa hannu ta kamo na Daleesha domin ta tashi a ƙasa, wanda da wannan damar Daleesha tayi amfani wajan riƙe hannun Fulani Hajara cikin nata, sannan a hankali ta lumshe idanuwanta, laɓɓunta suka fara motsi duk da ba mai jin abinda take faɗa.
**
Wani irin rantsttsen fada ne haɗaɗɗe, wasu ƙarfafa kuma manya-manyan halittu ke riƙe da wani halittar wanda komansa irin nasu ne, sai dai shi baƙiƙƙirin ne saɓanin su da suke da haskensu, sannan shi wanda suke riƙe da shi ɗin jikinsa duk gashi ne, hatta da idanuwansa gashi sun rufe.
Da wani irin yare suke magana.
"Za ka ƙyale wancan bil'adaman ko ba za ka ƙyaleta ba?"
Wanda ya kasance shugabansu a wajan yayi tambayar ga wanda aka rirriƙe.
"Shugaba ba'a ce in bar jikinta ba, asalima ina jin daɗin zama a jikinta sosai, domin abinda aka aikani nake zuƙewa a jikinta, ban taɓa jin abu mai daɗinsa ba, a duniyarmu ta aljanu da ma tasu ta bil'adama."
Wanda aka rirriƙe yayi maganar da wani irin sauti mara daɗin sauraro, da ma firgita duk bil'adaman da ya saurara, amma da yake duk jinsin su na aljanune a wajan wannan sautin ba komai bane, saboda sautinsa bai kai na saura firgitarwa ba, balle ma ta sugabansu.
Shugaban nasu bai sake cewa komai ba, sai umurni da yayi na azabtarwar da za'a yi wa wannan baƙin aljanin, ba ɓata lokaci kuma dakarun shugaban suka fara tsige masa gashin jikinsa da wani irin ƙarfi, cikin salon azabtarwa da ladaftarwa.
Ihu mara daɗin sauraro wannan baƙin aljanin ya kama yi, cikin sautin da ke nuni da azaba da raɗin da yake ji.
"Zan fita jikinta, zan ƙyaleta shugaba, zan barta, kar ku rabani da gashin da shi ke suturta mummunan halittata, iyalina za su gujeni idan na fito a ainahin surata babu suturtar wannan gashin."
Abinda baƙin aljanin ke faɗa kenan cikin sautin ihu da neman agaji.
"Na fita, na fita shugaba, na fita, ko yanzu mijinta ya kusanceta za ta samu ciki, dama ni ke lalata duk wani abu da zai shiga jikinta da har zai samar da ciki, ba zan sake ko waiwayar masarautarsu ba, shugaba kar a cire mini sutura, jinsinmu ba kaman na bil'adama ba, balle nayi wani shigar naje ga iyalaina, ko ya na sauya za su ganeni kuma za su guje ni...."
Duk magiyar wannan baƙin aljanin, shugaba badakire bai bawa dakaru damar ƙyalesa ba sai da ya tabbatar da an gana masa azaba kalar tasu ta aljanu, da ko zuwa nan gaba wani ya ba shi aikin cutar da wata halitta, ba zai cutar ba, ba iya bil'adama ba, ko da kuwa dabba ne.
"An gama Gimbiya, Allah ya raya ki ya miki albarka, kariyar Allah na tare da ke, kuma muma muna a tare da ke daga nan har zuwa inda Allah ya so."
Shugaba badakire ya faɗa ya na sakar wa Daleesha murmushi.
***
Daleesha da idanuwanta ke a rufe har sannan, ita ma murmushin ta saki sai lokacin kuma ta saki hannun Fulani Hajara.
Fulani Hajara tayi baya luuu ta faɗa kan tattausan filon da ke saman abun zamanta.
"Ummi ki bawa Fulani ruwa."
Daleesha ta faɗa kamar wata babba, tana gama maganar ma ta fice da hannayenta riƙe a bayanta.
Ummin Daleesha da sauri ta nufi inda Fulani Hajara take, ai sai taga Fulani kamar sumammiya kamar mai bacci, da sauri ta ɗibo ruwa ta shafa wa Fulanin a fiska gami da yin bismilla.
"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un!"
Fulani ta faɗa tana dafe kanta da ya mata nauyi.
Da taimakon Ummi ta tashi zaune, Ummi na ta jera mata sannu, Fulani ta amsa, a zuciyarta tana mamaki da tunanin me ya faru.
Bayan da ta miƙa hannu domin taso Daleesha daga ƙasa, sai taji ta kasa ɗago Daleesha, ko da tayi ƙoƙarin janye hannunta, nan ma taji tamkar an manne hannun nata ne da na Daleesha, magana ma ta kasa, lokaci ɗaya kuma ta ji tamkar ana zare wani abu daga cikinta, azabar hakan da take ji har fatar cikinta, ya sa ta fice a hayyacinta, daga nan ba ta sake sanin me ake ciki ba, sai yanzu da Ummin Daleesha ta shafa mata ruwa.
Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauƙe, tana ƙoƙarin haɗa ɗaya da biyu ko za ta fahimci me duk hakan ke nufi, sai dai ta kasa gane komai, asalima kanta ne taji ya mata nauyi.
..Daleesha ko da ta bar sashin Fulani Hajara, sashin Fulani Samira ta nufa, tana tafe kamar wata babbar mace har bakin ƙofar turakar Fulani Samira, daidai Fulani Samira ta fito kenan suka yi kiciɓus, hakan ya haddasawa Fulani Samira wani mummunan faɗuwar gaba, musamman da idanuwanta suka sauƙa cikin na Daleesha.
MASARAUTAR BUZJAR
⭐️
"Maa zan fita."
TJ yayi maganar yana marairaice fiska.
"Ina za ka je TJ?"
Maa ta masa tambayar da tasan shi yake gudu har ya marairaice fiska.
"Nan ɗan bayan gari ba nisa, kuma ba zan jima ba ma, nayi alƙawari."
Faɗin TJ.
"Ka dawo lafiya, kariyar Allah ta kasance a tare da kai, kuma ka kula sosai, ko kalmar da bai kamata aji ba kada ka furta balle wani ya ji, har hakan ya zame mana damuwa, kake komai a zuciyarka, sannan ko da wasa kada ka ce za ka yi salla a waje."
Maa ta ƙarishe maganar sallar da murya ƙasa.
"To Maa."
TJ ya amsa cikin ladabi, sannan ya juya ya fice a gidan bayan ya sake mata sai ya dawo.
Rumfar Baa ɗin sa na ƙofar gida a rufe, saboda Baa ya shiga kasuwa nemo wasu daga cikin kayakin da yake aiki da su, dan ƙawata sana'ar ƙwaryar shi.
TJ cikin nitsuwa yake tafiya, sai da yayi nisa da gidansu, sannan ya sa hannunsa ya janye roberband da Maa ta kame masa yalwataccen gashinsa, sanya roberband ɗin yayi a aljihunsa, sai kuma ya fara tsalle-tsalle ya na jujjuya jikinsa da kansa, gashin na rufe masa har idanuwansa, sai ya kai hannu ya tattare gashin ya na sakin lallausan murmushi.
Duk inda ya wuce, muddin mutanen wajan sun san shi, sai sun ƙira sunanshi TJ, shi kuma ya amsa gami da ɗaga musu gaisuwa yayi gaba, daga inda ake buga caca, sai inda suke hira kamar majalisa kowa da ƙwaryar giyarsa, har shi ma ya tsaya ya amsa a wani ɗan madaidaicin duma yayi gaba.
Daji sosai ya shiga, can ƙarƙashin wata bishiyar mangoro dake da wadataccen ganyayyaki da suka sa har ƙasan bishiyar tayi duhu, a wajan ya samu waje ya zauna, tare da jawo wannan duma da ya amso na giya, ya riƙe a hannunsa yana kallo, duk da ba wannan ne karonsa na farko da ya fara shan giyar ba, amma kuma kusan ko yaushe idan zai sha, a can cikin zuciyarsa tunanin Baa da Maa ne, ranar da suka san yana sha me zai faru? Ya za su ji? Me za su masa?
Tunda yake ko Baa da yake namiji bai taɓa ganin ya sha giya ba, balle kuma Maa da take mace, duk da a Buzjar kowa kwankwaɗa yake ba babba ba yaro, ba mace ba namiji, tamkar ruwa haka aka ɗauki giya.
Cikin ƙarfin hali yake ƙoƙarin mallakar kansa, domin fasa shan giyar, amma sai yake jin ba zai iya ba, ba kuma zai samu nitsuwa ba sai ya sha.
Hannunsa na rawa ya ɗaga dumar hannunsa ya kai baki, yadda ya ɗaga sama ya kama kwankwaɗa, shi ne bai sauƙe ba sai da ya shanye tass.
****
Follow my page's
●WATTPAD
@Uwarbatoorl96
●AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
●TIKTOK
@Uwarbatoorl96