Shafi na tara
YARIMA BAHJAT 🌏
Na
Harira Salihu Isah
(Uwar Batoorl)
SHAFI NA TARA
⭐️
Wani irin gyatsa TJ ya saki sanda ya sauƙe gorar dumar a bakinsa, sai kuma yayi jifa da gorar dumar, zuwa lokacin yana jin yadda nitsuwa ke ratsa shi saboda giyar da ya sha, haka kuma a sannu a hankali cikinsa ya fara murɗa, wani ciwon ciki ne da duk sanda ya sha giya sai ya ji shi, sai dai jin ciwon baya hana shi sake sha.
...
"TJ!"
Ya ji an ƙira sunansa kamar daga sama.
Lumsasassun grey eyes nasa ya buɗe ya zuba su, a kan yaron da ya zauna a gefensa, wanda idan har shi TJ ya girmewa yaron, to ba zai wuce da shekaru biyu ba ne.
"Dev."
TJ ya ƙira sunan yaron yana mai wadata fiskarsa da murmushi.
"Na ɗauka ba zan sameka ba ai, shiyasa ma ban iyo ta nan da wuri ba."
Faɗin Dev.
"Mu ƙarasa kogon ka ƙara mini karatun, kada dogarawan da muka fito tare su zo ta nan su ganmu."
Dev ya sake faɗa yana miƙewa tsaye, tare da miƙawa TJ hannu, ya kuma kama ya miƙe, sannan suka bar ƙasan bishiyar mangoron, suka yi gaba kaɗan, sai ga wasu duwatsu manya-manya.
Wani kogo suka shige mara girma sosai, sannan a hankali cikin natsuwa TJ ya fara yiwa Dev karatu, bayan Dev ya bita masa karatunsu na baya.
Fatiha, Falaƙi da Nasi da kuma tarjamarsu, haka Dev ya karanto rass kamar yadda TJ ya koya masa, TJ kuma su Maa suka koya masa.
"Yau suratul Iklas za muyi, surar da ke bayyanawa da nuna tsantsar kaɗaitakar Allah, sura ce da duk mai imani idan ya karantata, a zuciyarsa kuma yana kawo ma'anoninta, to ba zai taɓa yin gigin haɗa Allah da wani ba."
TJ ya dakata da yiwa Dev bayani yana jan numfashi.
Sai da ya sauƙe numfashin sannan ya cigaba, "Ƙul huwallahu Ahad, ka ce shi ne Allah makaɗaici, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya."
Cikin nitsuwa Dev yake maimaita duk karatun da TJ ke koya masa, yana maimaitawa yana nanatawa har sai da ya tabbatar ya zauna a harshensa.
"Thank you TJ."
Dev ya faɗa da yarensu na Nasara.
"Ka godewa Allah Dev, shi da ya nufe ka da son gaskiya da bin hanya madaidaiciya."
"Haka ne TJ, amma watarana za ka kaini wajan Maa da Baa ko?"
Dev ya tambaya.
"In Allah ya yarda."
"Allah ya yarda TJ."
Sun ɓata lokaci sosai a wajan, sannan Dev ya fara fita a kogon yayi gida, bayan wasu mintuna TJ ma ya fita ya kama hanyar gida.
..Dev ɗa ne ga Yarima Dodo ɗan Sarki Dungu.
Dev ya fara koyon karatu da addinin musulunci a wajan TJ ba jimawa, watarana sun fito rangaji da dogarawa, sai Dev ya ɓace musu ya cigaba da zagayensa shi kaɗai, a wannan zagayen ne ya jiyo sautin karatun TJ, wanda yake karatu yana maimaita fassarar karatun.
Ba karatun ne abunda ya ja hankalin Dev ba, a'a, fassarar ma'anonin karatun da kuma tsaruwar kalmomin, su suka burgesa duk da kasancewarsa yaro ƙarami, amma ya ji yana son ya koyi wannan karatun, hakan ya sa ya dinga dube-dube har ya samu TJ a wannan kogon yana karatunsa.
Da farko TJ ya tsorata sosai, ganin wani ya jiyo karatun Ƙur'ani da yake yi har ya zo gare shi, wanda ya san hakan da Maa ke gudu shiyasa take hana shi yin komai a waje, kamar yadda su ma ba sa yi.
Ganin Dev yaro sai TJ yayi ƙoƙarin illatasa, domin gudun kada ya ce zai je ya sanar, abinda su Maa suke gudu kuma ya faru.
"Kar..kar..kar ka kashe ni, kawai karatun da kake yi ne ya mini daɗi, ya sa na zo dan ka koya mini."
Dev yayi maganar a wancan lokacin, da shaƙaƙƙen muryarsa saboda shaƙar da TJ ya masa.
TJ bai saki wuyar Dev ba sai da yaga yana ƙoƙarin macewa, sannan ya saki wuyarsa ya koma gefe ya tsaya, Dev kuma yayi ƙasa yana tari gami da neman ruwa, TJ na tsaye daga gefe bai ko motsa ba, sai Dev da idanuwansa suka yi jajayene ya hangi ƴar gorar dumar da ke yashe a gefe, da sauri ya kai hannunsa ya ɗauka ya ɗaga kai ya kama kwankwaɗa.
Sai da ya sauƙe gorar dumar, sannan ya jingina da jikin dutse yana mayar da numfashi.
"Karatun da kakeyi nake so ka koya mini, ya mini daɗi."
Dev ya faxɗa bayan shuɗewar wasu mintuna.
"Who are you?"
TJ ya tambaya da harshen Nasara.
"Dev, sunana Dev, jikan Sarki Dungu......"
Dev ya faɗawa TJ komai a kansa.
"And you?"
Dev ya tambayi TJ.
Sai sannan TJ ya rage tsayinsa ya zauna a nitse, "Tijjani, you can call me TJ, ni yaron Maa da Baa ne, mu Addini daban muke yi da wanda kakanka ya ce ayi, karatun da kaji ina yi ma na Addininmu ne, Addinin musulunci."
TJ ya faɗa kai tsaye idanuwansa a kan Dev, a zuciyarsa yana jin idan yaga alamar Dev zai fallasa su ne, to kashesa zai yi ba ruwansa da kasancewarsa jikan Sarki, tunda dai yana ganin yadda ake kisan, ya san ba zai kasa ba.
"Karatun ya mini daɗi, yadda ma'anonin kalmar ke fita duk mai hankali idan yaji, ya san akwai gaskiya a wannan karatun, ka koya mini please, kuma nima zan yi Addinin da kuke yi da Baa da Maa naka."
Wani kallo TJ ya aika masa, duk da kasancewarsu masu ƙananun shekaru duka, amma ya san maganar da ba zai yiwu ba Dev ke yi, yana cikin gidan sarauta ya ce zai yi Addinin musulunci ai da kamar wuya gurguwa da auren nesa.
"Ka taimaka ka koya mini, ina so da gaske."
"Zan yi magana da Baa da Maa."
Faɗin TJ.
Sai da TJ ya tabbatar wa Dev a nan za su sake haɗuwa, sannan Dev ya yarda ya tafi bayan ya saka TJ ya masa alƙawarin zuwa gobe zai faɗawa su Baa, wani gobe kuma ya fara koya masa.
Bayan barin TJ dajin, ya koma gida sai ya kama kame-kame, ya rasa ta ina zai fara faɗawa Maa yadda suka yi da Dev, musamman da ya san Maa ta fi jaddada masa faɗa, a kan ya kula, to ya san muddin ya mata magana to akwai matsala, tashin hankalinta kawai za tayi, fiye ma da yadda yake a tashe, saboda tunda yayi wayo ya fara fahimtar komai na Buzjar, da kuma rayuwarsa da su Maa, ya fahimci hankalin Maa ba a kwance yake ba.
Baa ya samu ya faɗawa maganar cikin ɗari-ɗari, sai dai a mamakinsa sosai Baa ya nuna jin daɗinsa ya kuma goyi bayan hakan.
"Baa amma ba za'a kashemu ba? Kuma hakan Maa ke gudu, ko da yaushe hankalinta a tashe."
TJ yayi maganar ba dan yana tsoro ba, sai domin gudun damuwa da tashin hankalin Maa ɗinsa.
"Duk wanda aka kashe a tafarkin jaddada addinin Allah, duk wanda aka kashe a ta farkin kare addinin Allah, ko kuwa aka kashe su domin kaɗaita addinin Allah, to lallai-lallai sun mutu ne a tafarkin Allah, kuma duk wanda ya mutu a ta wannan tafarkin, sakamakonsa aljanna ne, dan haka ka koya masa, kada kaji komai, kada kaji tsoron komai, Allah na tare da wanda duk ya riƙi addininsa ya kuma ji tsoronsa, ina roƙon Allah ya baka kariya alfarman kariyar da ya baiwa Annabi Muhammad SAW daga kafuwan Makka, Allah ya tsaremu da kalar tsarewar da ya yiwa Annabi Musa Alaihissalam daga duk wani makirci, ƙulle-ƙulle da kafurcin Fir'auna, idan ka duba yadda komai ya kasance ga waɗanda suka gabacemu, Annabawa da salihan bayi, za ka ga duk wannan namu ba komai bane, domin duk abinda ya faru a baya wata alamace ga mutanen zamanin gaba, dan haka ka kwantar da hankalinka, kuma wannan magana ya zama iya tsakaninmu, kada ma ka bari Maa taji, domin nima ba faɗa mata zan yi ba, kai dai ka cigaba da yin aikin Allah, in Allah ya yarda tun a duniya za ka fara riskar sakamakon kyakkyawar aikinka, ina kuma fata ka zamo dalilin kawo sauyi a Buzjar gaba ɗaya......."
Sosai Baa ya kwantarwa TJ hankali da kalaman ƙarfafa guiwa, da kuma nuna masa misalai da dama, ya kuma saka masa albarka gami da fatan alkairi.
TJ ya samu ƙwarin guiwa sosai a kalaman Baa, hakan ya sa washegari ko da ya fita suka haɗu da Dev, ya masa bayanin komai daidai saninsa da ƙwaƙwalwarsa, daga ranar kuma suka kama karatu, ba tare da wani mahaluƙi ya sani ba bayan Baa, domin a ɓangaren Dev ko dogarawan da yake fitowa da su basu sani ba, balle wani a gidansu.
...Cikin nitsuwa TJ ya ƙaraso ƙofar gidan nasu, inda ya samu Baa ma daidai dawowarsa daga kasuwa kenan.
"Sannu da dawowa Baa."
TJ ya faɗa ya na amsar kayan hannun Baa.
"Yauwa TJ, daga ina haka?"
"Karatu!"
TJ ya faɗa da murya ƙasa-ƙasa, bayan ya duba gabas da yamma ba wani mai kallonsu balle ya iya jiyo abinda suke faɗa.
Fiskar Baa faɗaɗa yayi da murmushi, sannan ya sake yiwa TJ sannu, gami da saka masa albarka ya kuma bi shi da addu'a.
"Baa, na cewa Maa ba zan daɗe ba, amma na daɗe."
"Kar ka damu zan taya ka bata haƙuri."
Da taimakon Baa kuwa TJ ya samu Maa ta haƙura, bayan sun shiga gidan tare xa Baa, da ciwon cikinsa ya murɗesa ba shiri Maa ta mance batun ya jima ta shiga kula da shi, maganinsa ta ba shi cikin kulawa da tausayawa da ƙauna, a fili take faɗin.
"Dama can ba fitarka nake ƙi ba TJ, ciwon cikin da sautari kake dawoaa da shi idan ka fita shi ne ba na so, amma ba komai ya wuce Allah baka lafiya ka kiyaye gaba."
Ta ƙarishe maganar tana shafa kansa.
"To Maa ta."
TJ ya amsa a nitse da muryar shagwaɓa, yana taune leɓensa saboda cikinsa da ya murɗa.
...
"Ƙul huwallahu Ahad, ka ce 'shi ne Allah makaɗaici, shi ɗaya ba shi da abokin tarayya. Allahus-samad, Allah wanda ake nufinsa da buƙata, shi shi kaɗai. Lam Yalid Wa Lam Yulad, bai hafa ba kuma ba'a haife shi ba, Allah shi kaɗai ne. Wa Lam ya....."
"Dev!!!"
Wani irin ƙiran sunansa da aka yi da mugun ƙarfi, shi ya katse masa karatun da yake maimaitawa a zuciyarsa, wanda bai san sanda ya fito fili ba.
Tass!!
Matar da ta ƙira sunansa a tsawace ta zabga masa mari mai zafi, idanuwanta a waje, ƙirjinta na wani irin bugu.
"Moza!"
Dev ya ƙira sunan mahaifiyar tasa a sanyaye saboda marin da ta masa, ba tare da ya san laifin da yayi ba, tunda a iya saninsa a zuciya yake maimaita karatunsa.
"Dev me kunnuwana suka jiye mini kake cewa, Dev wani kalan magana kake yi? What are you reading?"
Moza ta ƙarishe tambayar ta na leƙe-leƙen hannunsa har zuwa gefe da gefensa, ko za ta ga abinda yake karantawa da ta kasa ganewa, amma wani sashi na jikinta na shaida mata is not good thing, ba abu mai kyau yaronta ke karantawa ba.
"Me kika ji Moza?"
Dev ya tambayeta a nitse.
"Something like you're saying, he's the only...."
Moza ta kasa ƙarisawa saboda gudun kar tayi saɓo, ko kuwa ta faɗa abinda zai fiddata a Addininta, domin wani abu a cikin zuciyarta da jikinta suna faɗa mata, Dev na practicing wani abu daban ba Addininsa ba.
"Kiyi haƙuri Moza, ba haka nake faɗa ba."
Dev ya faɗa cikin girmamawa.
Moza kuwa hakan bai wadatar da ita ba, sai da ta solle shi tass, ta kuma yi masa ƙaƙƙarfar warning da ko ita ba ta son ta sake jin kalar sumbatun da yake yi, balle wani daban ya ji.
Dev alƙawarin hakan ba zai sake faruwa ba ya mata, sannan ya mata sannu da shigowa, domin ta shaida masa tun da ya fara wannan sumbatun ta shigo.
"Ka shirya za'a je wajan Father(pastor),domin akwai abinda zai bayar na shirye-shiryen bawa Babanku kujerar King, and you'll be the crown Prince....."
"To Moza."
Dev ya amsa cikin girmamawa bayan da Mamansa ta gama bayaninta, sai da ta sake yi masa gargaɗi sannan ta fice, hadimanta da suke jiranta daga bakin ƙofa suka mara mata baya.
"Allahu Ahad!"
Dev ya furta a ƙasan maƙoshinsa ya na dafe kansa, gami da koro addu'a da fatar wani sanadin ya hana shi halartar zuwa wajan Father, ko kum naɗin Babansa, shi kawai ji yake komai na masarautar Buzjar na fice masa a kai.
Haƙar Dev bata cinma ruwa ba, domin haka Moza ta tisa ƙeyarsa a tare xa sauran ƴan uwansa, yaran Yarima Dodo har zuwa wajan Father.
A kwanakin da suka biyo baya wani irin bidiri ake yi a Buzjar, shagali na gani na faɗa komai free kawai.
Ranar da ta kasance ranar naɗi wasu tamfatsa-tamfatsan randuna aka cika da giya ga wasu ƙwaryu masu kyan gaske marassa adadi, a gefe ga gasassun namu, na karnuka na shanaye na aladu ba irin naman da babu, kowa kawai ya zo ya ɗiba son ranshi ya ci ya sha yayi hani'an.
A babban filin taronsu na Buzjar aka ƙawata ake gudanar sa bikin.
Kujerar Sarki Dungu ne da matansa biyu, Magajiya Tadoga da Magajiya Tubali, an haɗa wajan zaman nasu an ƙawata shi.
Daga nan sai wajan zaman Yarima Dodo da matansa biyu shi ma, Moza da kuma Mother, su na an ƙawata musu da ado na musamman, kasancewar Yarima Dodo Sarki na gaba, matansa kuma za su koma Sarauniyoyin Buzjar.
Daga nan sai sauran yaran Sarki Dungu da matayensu, sai kuma jikokinsa wato su Dev, akwai gefen baƙi waɗanda suka kasance, Hakimai, dakacai da manyan wasu ƙauyukan da ke ƙasan Buzjar.
Taro dai yayi taro ga manyan baki ga ƴan gari, sannan an wadata kowa da Giya da gasasshen nama.
Naɗin aka fara gabatarwa inda aka sadaukar da jinin mutane goma, sannan aka damƙawa Yarima Dodo sarautar, aka dinga ihu ana shewa wanda kana ji ka zan na shayayyu ne, daga nan kuma aka naɗa Dev a matsayin Yarima, wanda idan da nisan kwana shi ne Sarki na gaba, nan ma aka dinga shewa da ihu da ƙiran sunan uwa, ɗa da ruhi mai tsarki.
Daga nan fa taro ya ɗau zafi, aka fara gabatar da wasa, wani ƙaƙƙarfan namiji aka kawo aka baje masa zafafan mata goma, aka umurci da ya kusance su duka, ire-iren wasannin kenan, ga giya ga namomi ga mata sai wanda ka zaɓa, ana komai ana shewa da ihu.
MASARAUTAR BAHJA
⭐️
"Abdi!"
Magajiya ta ƙira sunansa da kakkauran murya.
****