GADAR TSAUTSAYI 38
by @nusybee143
Page 38
Kallonta Haisam ya yi fuska babu walwala, kafin ya yi magana Abba ya ce fuska a ɗaure "shine ya so hakan,ya kawo shi da radin kanshi don ya inganta masa rayuwa,idan zai yiwu ki bi shi da addu'a kawai,idan ba zai yiwu ba kuma ki yi shiru,amma ko da a ce kina so ko ba kya so yaron nan yanzu zai fara zama a gidan nan da izinin Allah"
Shiru Hajiya Mariya ta yi ba tare da ta yi magana ba,ita kuwa Nimra ji ta yi kamar ta kurma ihu
Haisam ya dubi Abba ya ce"na gode Abba, Allah ya saka da alkhairi
In Sha Allah zuwa next term idan an fara enrolling yara a makaranta zan saka shi a makarantar su Amna"
Abba ya jinjina kai ya ce"hakan yana da kyau, Allah ya taya riƙo, riƙon maraya akwai lada da alfanu mai tarin yawa ,fatan shi ne Allah ya raya shi ya albarkaci rayuwarsa "Haisam ya amsa da"Ameen "
Daga nan hira suka fara,suna tattaunawa akan abubuwan da suka shafi kasuwancinsu shi da abban, Nimra ganin ba'a yi batunta ba ya sa ta fara zungurin Hajiya Mariya, fuska a ɗaure Hajiya Mariya ta dubi Alhaji Abdulmalik ta ce
"Ni ko Alhaji ba mu ƙarasa Maganar da muka fara kwanaki ba"
Alhaji ya dube ta ya ce"wacce maganar ce?"
Hajiya Mariya ta ce"maganar ya kamata a haɗa Haisam da Nimra aure mana,tunda dai yanzu ga ka ga ni,gashi kuma ga Nimra ɗin kawai gwara a yi a gama ko?amma kai ya kake gani?"
Alhaji Abdulmalik ya kalli Nimra ya ce"da izininta kika yi wannan maganar?"Hajiya Mariya ta ce"da izininta ne,ka sake tambayarta ka ji"Alhaji Abdulmalik ya jinjina kai ya ce"to kai Haisam ya kamata ka ware lokaci ka san abin yi, tsawon lokacin da ka ɗauka baka yi aure ba ya kamata ko me aka yi maka zuwa yanzu a ce ka huce, riƙo a wajen ɗan musulmi ba shi da amfani sam, ballantana ma wadda ta yi maka laifin dabam da wadanda kake hukuntawa,ya isa hakanan Haisam "jinjina kai ya yi,a sanyaye ya ce"to shikenan Abba,komai ya wuce, Allah ya shige mana gaba ya yi mana jagora "
Alhaji Abdulmalik ya ce"Ameen Ameen!
Yanzu ga Nimra, menene ra'ayinka akanta?
Ka ga dai ita ka santa,kuma ina da yaƙinin ba zata ba ka matsala ba in sha Allah,kuma zata riƙe maka yaran da kyau,amma kai me ka gani?"
Haisam ya ɓoye mamakin rashin kunyar nan,ya ce"Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi,amma ya kamata ta ƙarasa karatunta, idan ya so sai a yi maganar auren"
Cikin zumuɗi Nimra ta ce"za'a iya yi min transfer ma na dawo Kano,ba dole sai a Abujan zan yi karatun ba"
Haisam ya watsa mata wani mugun kallo,tuni ta nutsu, fuska a ɗaure ya ce"za'a yi auren bayan ta kammala makaranta in sha Allah, Allah ya bada sa'a "
Abba bai damu ba ya ce"Ameen Ameen, Allah ya sa albarka "Haisam ya miƙe ya ce"sai da safenku"ya fice daga sashen zuwa nashi
Washe gari ko cikin gidan bai shiga ba ya shirya ya ɗauki Mubarak da yake bacci ya kai shi sashen Nanny shi kuma ya fice daga gidan zuwa office ɗin sa,akwai wani aikin bincike da zai bayar akan wani mutum da ake zargin yana safarar ƙwayoyi,har da samfurin cocain,da kuma muggan makamai,amma duniya tana yi masa kallon mutumin kirki,don yanzu ma shirye-shiryen fitowa takara yake yi
Ɗaga kai ya yi yana kallon Awwal da yake shigowa, kafin ya ce"Awwal ƙaraso,ina son yin magana da kai"babu musu ya ƙaraso ya sara masa yana faɗin"morning Sir!"
"Have a sit Awwal "ya faɗa ba tare da ya kalle shi ba
Waje ya samu ya zauna yana kallonsa, Haisam ya ɗaga kai ya kalle shi ya ce"ya ake ciki game da case ɗin Alhaji Yunusa Datti ne?me kuka gano akanshi?"
Awwal ya ce"Sir da farko dai mun gano yana bincike da wasu manyan mutane a guest house ɗin sa, waɗanda ya kamata mu san me suke tattaunawa da suke yawan zama cikin dare,da yiwuwar ba hannunsa bane kaɗai a cikin wannan badaƙalar,akwai waɗanda suke yi masa aiki,ko kuma suke aiki tare"Haisam ya jinjina kai cike da gamsuwa ya ce"ya kamata a duba kuwa,amma ba yanzu ba, saboda na fuskanci kamar ana sanar da shi sirrin aikinmu,zai iya mamayarmu ya yi nasara akanmu"ya ƙarasa magana yana kallon Awwal
Ɗan murmushi ya yi ganin alamun razani a fuskar Awwal duk yadda ya so ya ɓoye hakan, Haisam ya cigaba da magana "don mun yi magana da Roxy,ta tabbatar min da cewa akwai waɗanda suke taimaka mata,duk da dai bata faɗi sunansa ba,amma tabbas akwai na yarda,kuma ka ga zai iya ɓata mana aiki ko?"
Dakewa Awwal ya yi ya ce "haka ne sir!"
Haisam ya ce "very good!
Yanzu sai a je a fara shiri, very soon zan iya nemanka akan maganar"Awwal ya ce "okay Sir!"
"You can leave"Awwal ya sara masa ya juya ya fice daga office ɗin
Murmushi kawai Haisam ya yi,ya san yadda zai yi ya kama shi da laifinsa ba tare da wata matsala ba,sai ya cire masa sha'awar cin amana da izinin Allah
Lawyer ɗin da suka yi magana ce ta kira shi a waya,kai tsaye ya ce mata ta jira shi gashi nan zuwa,kuma ba tare da ɓata lokaci ba miƙe ya fice daga office ɗin
Kai tsaye chamber ɗin BARRISTER HIBBA IBRAHEEM AYYO ya nufa,(barrister Hibba Novel 😍kada ku sake a ba ku labari💯)bayan an yi masa iso ya shiga,ya gaishe ta ta amsa, sannan ta nuna masa waje ya zauna
Barrister Hibba ta ɗago tana kallonsa, cikin jimami ta ce"akwai matsala sosai a ƙasa officer "Haisam ya gyara zama ya ce"menene matsalar barrister?"
Barrister Hibba ta mayar da kanta jikin kujerar da yake zaune, cikin jimami ta fara faɗin "yarinyar nan tana cikin matsala fa,seems like akwai manyan da suke da hannu akan kamun nan da aka yi mata, Haisam me kake ɓoye min ne?
Ka yi min bayani bana son nuƙu-nuƙu,ka san wacece ni"
Ɗan murmushi ya yi kanshi a ƙasa,a hankali ya fara yi mata bayanin gaskiyar batu game da laifukan da ake tuhumar Shaheeda da shi,wani kallo ta yi masa cikin ɓacin rai ta ce
"Ban taɓa tsammanin jami'in tsaro mai gaskiya da riƙon amana irinka zai so na kare mai tarin laifuka irin wannan ba,why ba za ka bari a hukunta ta ba, wannan yarinyar barazana ce fa ga ƙasarmu,ta yaya kake so na yi defending ɗinta bayan ka san abin da ta yi?kana son ta fito ta ɗora daga inda ta tsaya ne?
Why not ka bari doka ta hukunta ta?"
Haisam ya gyara zama ya ce"I'm sorry Ma'am!ba zan iya bari a hukunta ta ba, musamman ga laifinta, saboda....."ƴar dariya barrister ta yi ta ce"saboda ka faɗa soyayyarta ko?
Wow! very interesting!zan so na ga yadda wannan soyayyar zata tafi"girgiza kai ya kama yi yana murmushi,ya ce"ba soyayya bane barrister,tausayinta nake ji,bari na ba ki labarin yadda rayuwarta ta tafi,har ta samu kanta a wannan halin "a hankali ya warware mata komai
Murmushi ta yi hawaye suna cika idanunta,a sanyaye ta ce"Allah sarki rayuwa!kowa da irin tashi jarrabawar,ita mahaifinta shine mafarin jarrabawarta,ni kuma rashin mahaifina shine mafarin tawa jarrabawar
Shikenan babu komai, yaushe kake so na tattauna da ita?"
Haisam yana murmushi ya ce"ko yau ne,kin ga ranar Monday za'a shiga Court"
Jinjina kai barrister Hibba ta yi ta ce"a ƙa'idar doka hukuncin life imprisonment ne hukuncinta, saboda safarar miyagun ƙwayoyi da take yi, wadanda suka haɗa har da cocain,kuma tana importing,shine babbar matsalar,ga hukuncin da za'a yi mata na hacking da take yi,abin da yawa
Zan yi magana da ita, za'a san yadda za'a ɓullowa lamarin,amma fa dole zata yi zaman prison ko da na shekara ɗaya ne ko biyu"cikin rashin jin daɗi ya ce"okay Ma'am!
Thanks for your effort"barrister Hibba ta sauke numfashi mai nauyi ta ce"to yanzu ina ɗan nata yake?"
Haisam ya ce "yana wajena,na mayar da shi gidana yanzu"barrister Hibba ta yi murmushi ta ce"Haisam wato ya fara yin gaba kafin uwar tashi ta biyo baya kenan, Weldon!"Haisam ya yi murmushi ya ce"Ma wai ba ki yarda bane? believe me kawai ina son na zame mata wani bango ne na taimake ta,amma ba wai soyayya ba ce tsakaninmu, I promise you"barrister Hibba ta ɗaga kafaɗa ta ce"alright then!
To Allah ya dafa ya yi mana jagora,anjuma kaɗan ka zo mu tafi can inda aka rufe ta,da buƙatar mu tattauna da ita,don na san ta inda zan fara "Haisam ya rissina ya ce"I'm grateful Ma'am "daga nan suka yi sallama,ya fice daga office ɗin
Bayan wasu awanni Haisam da barrister Hibba suka isa zuwa jail ɗin da aka rufe Shaheeda,tare suka shiga bayan kowannensu ya nuna ID card ɗinsa,kai tsaye suka buƙaci ganin Shaheeda
Babu jumawa aka fito da ita,kanta a ƙasa, Hibba ta zuba mata idanu a ranta tana jinjina tsantsar yarintarta
A sanyaye ta rissina tana gaishe su,suka amsa,ya dube ta da kulawa ya ce"to Shaheeda,ga barrister Hibba,na san kin taɓa jin labarinta ko?babbar lawyer ce,kuma shugabar ƙungiyar lawyers kuma shugabar ƙungiyar tallafawa marasa galihu "Shaheeda ta ce"na sani duka
Ina matuƙar godiya da karamcinki Mommy!"Hibba ta yi murmushi ta ce "never mind dear!
Na ji duk abin da ya faru, I'm so sorry,but still za ki iya amending mistakes ɗinki,you still have a time"
Kallonta Shaheeda ta yi a sanyaye ta ce "it's too late for me Ma!na san ke ma kin san da haka, saboda Ni kaina na san laifina ba irin wanda ake yafewa bane,ko da a ce a kan ɗaya aka tsaya ballantana....."
"Amma kamar jiya mun yi magana da ke ko?
Na gaya miki ki mayar da lamuranki ga Allah,hala kina ganin ba mai yiwuwa bane?ko idan na yi alƙawari ba zan cika bane?"girgiza kai ta yi a sanyaye,a hankali ta ce"I'm sorry "
Hibba ta yi murmushi tana kallonsu, kafin ta ce"yanzu kwanaki uku suka rage a shiga Court in sha Allah,duk abubuwan da na tsara miki shi za ki je ki faɗa,kar ki kuskura ki yi min ba daidai ba, saboda ni ina hukunci "sunkuyar da kanta ta yi a hankali, Hibba ta fara tsara mata duk yadda take buƙatar ta yi a Court ɗin
A hankali Shaheeda ta ɗago da confused face tana kallonta, kafin ta yi magana Hibba ta ce"bana son taurin kai,just do as I say, okay?"Shaheeda ta jinjina kai
Kwantar mata da hankali Hibba ta cigaba da yi cikin sigar lallashi,har Shaheeda ta saki ranta,da za su tafi Haisam ya bata izfi sittin ɗin da ya fansar mata a hanyarsu ta zuwa jail ɗin
Shaheeda ta yi farin ciki sosai,ya jadadda mata ta dage da addu'a,in sha Allah za'a yi nasara,ta tabbatar masa da in sha Allah zata yi addu'a
*RANAR ZAMAN COURT*
Kotu ta cika maƙil da mutane,kuma yawancin mutanen sun zo ne don ganin wacece wannan Roxy ɗin da ta firgita ƙasa ta tsayar da tunanin jami'an tsaro waje ɗaya,da ake tunanin wata babba ce ta a zo a gani?ko ƙarfin ƙwaƙwalwa kawai gare ta? tunda da yawan mutane har yanzu ba su santa a hoto ba
Wasu kuma al'ummar Alhaji Sa'idu wada ne,da ya turo su su ga yadda shari'ar zata kaya,ya shaida faɗuwa ƙasa wanwar da zata yi, wanda ya alamta hakan a matsayin sakamakon butulcin da ta yi masa
Yana sane da shiga maganar da BARRISTER HIBBA AIYO ta yi cikin case ɗin, wanda hakan na nufin zai iya zama ƙila wa ƙala,nasara ko saɓanin hakan a gare shi,don ya daɗe da sanin wacece BARRISTER HIBBA AIYO,wasu shekaru can baya sai da ta yi silar shigar abokinsa Alhaji Adam doguwa jail,kusan shekaru sha biyar yanzu kenan amma har yanzu bai fito ba
A ɓangaren barrister Hibba itama ta je tare da tawagarta ta lauyoyi,duk inda ta wuce sai an dare an ba ta hanya cike da girmamawa,ko ba don kanta ba,ko don mijinta wanda ya kasance ministern lafiya a halin yanzu
Babu jumawa aka kawo Shaheeda da take cikin matsanancin tsaro,dama tun can a tsarin doka bayan jami'an tsaro da lauyoyinta babu wanda ya isa a bari ya ganta
#Nusy_bee