GADAR TSAUTSAYI 39
by @nusybee143
Page 39
Ƙirjinta ya buga da ƙarfi lokacin da ta ga tarin jama'ar da suka halarci kotun da sunan sun je kallon shari'arta,take kanta ya sake kawo mata cewa za'a yi Shari'a da ita ne akan ana tuhumarta da safarar miyagun ƙwayoyi da kuma satar kuɗaɗen mutane ta yana(Yahoo),take ta ji ta muzanta sosai,bata taɓa jin tsoro da shakkar aikata wani abu ba sai yanzu,sosai ta ji ta shiga razani da ɗimauta, jikinta ya hau rawa sosai
Ɗaga kai ta yi a sanyaye,hawaye suna kwantawa akan ƙwayar idanunta,caraf idanunta suka faɗa cikin na yayanta Muyassar,take ta ji wata kunya da bata taɓa ji ba,wai a gaban Muyassar wanda ya zame mata gata da duk farin ciki za'a tuhume ta da wannan gagarumin laifin!
Magatakardar kotu ta gabatar da ƙara ta gaba, wadda ake tuhumar ROXY ko kuma Fatima Shaheeda da laifin safarar miyagun ƙwayoyi,danginsu cocain da ƙwayoyi,sai satar kuɗin al'umma ta yana da take yi
Har cikin kanta ta ji wannan tuhumar da ake yi mata,tashin farko Ummeey ce ta faɗo mata a rai,ta fara tunanin ya zata ji idan ta ganta a wannan halin?tabbas bata yi mata adalci ba, kafin ta gama tunanin aka bayar da umarnin a kawo ta zuwa kusurwar tuhuma,babu musu ƴan sanda suka rako ta,ta sunkuyar da kai,har yanzu jikinta yana rawa,duk da jarumtar da ta aro
Lawyern gwamnati ne ya fara miƙewa ya gabatar da kanshi,bayan ya gaida alƙali "sunana barrister Sulaiman Yusuf,ni ne prosecutor da yake ƙalubalantar wadda ake ƙara"ya koma ya zauna
Barrister Hibba ta ɗaga kanta, cikin izza da take shigarta a duk lokacin da ta samu kanta a bakin aiki,ta miƙe a dake ta ce"sunana BARRISTER HIBBA IBRAHEEM AIYO,nice lawyern wadda ake ƙara"
Alƙali ya ba wa lauyoyi damar magana, barrister Sulaiman ne ya fara miƙewa ya ƙarasa kusa da Shaheeda da kanta yake ƙasa,ya ce "kotu tana buƙatar jin ainihin cikakken sunanki"
Bata amsa ba, kamar yadda bata motsa ko da kanta da yake sunkuye ba,har sai da barrister Sulaiman ya sake maimaita mata tambayar
Kanta a ƙasa ta amsa"sunana FATIMA SHAHEEDA YUSUF MALIYA!"
Take kotun ta ɗauki hayaniya sosai,sunan Yusuf Maliya da Shaheeda ta ambata a matsayin mahaifinta ya ba wa mutane da yawa mamaki,ko da yake akwai masu zargin Alhaji Yusuf Maliya shine mahaifinta,amma ya fito ya yi hira da ƴan jarida ya barranta kanshi da ita,har wasu suke ganin kamar tana amfani da sunansa ne don tabbatarwa,amma sai barrister Sulaiman ya ce"kina nufin ke yar Alhaji Yusuf Maliya ce?mamallakin MALIYA GROUPS OF COMPANIES?"
Kanta tsaye ta amsa masa da faɗin "eh,kai tsaye ma na ce nice babbar ƴarshi"
Barrister Sulaiman ya jinjina kai ya ce"dama haka na iya faruwa. To Malama Shaheeda!kotu tana tuhumarki da laifin safarar miyagun ƙwayoyi tsawon shekaru uku,da satar kuɗaɗe ta yana wato Yahoo, menene gaskiyar maganar?"
Shiru ta yi da farko, jikinta a sanyaye, kafin ta ɗago a hankali suka haɗa idanu da barrister Hibba, Hibba ta jinjina mata kai alamun ƙwarin gwiwa,don haka ta fara zayyano bayani kamar haka"eh haka ne!
Amma ba shekara uku bane, shekara ɗaya ne!"
Shiru kowa ya yi yana kallonta da tsananin mamakin jin abin da ta faɗa, barrister Sulaiman ya ce"amma menene hujjarki ta cewa shekara ɗaya ne?bayan kowa ya san shekaru uku kika ɗauka kina aikata wannan laifin?"
Shaheeda ta gyara tsayuwarta ta ce"shekara guda na ɗauka ina aikata wannan laifin saboda wata larura da ta same ni, wadda ya zamto bani da mafita sai hakan, tsawon shekaru biyun kuma nemana ake yi kawai ina guduwa,amma ba aikata laifi ba"
Barrister Sulaiman ya jinjina hakan cikin tsantsar mamaki, kafin ya ce"amma kuma duniya ta shaida cewa kin cigaba da aikata miyagun laifukan,har ma ana kyautata zaton jami'an tsaro sun kama ki ne bayan tarko da suka yi miki, menene gaskiyar wannan maganar?"
Ita kanta Shaheeda ta yi mamakin wannan ƙaryar da ta ji an yi mata,kuma zuwa yanzu ta sake tabbatar da maganar barrister Hibba da take ce mata ba don a ƙarfafa doka aka kama ta ba,sai don wani ƙudiri na dabam,don haka kai tsaye ta buɗe baki da niyyar magana,amma sai barrister Hibba ta riga ta
"Objection ya mai shari'a!
Barrister Sulaiman yana so ya ɗora ƙarfin zargi akan wadda ake tuhuma bayan ta musanta hakan,mai Shari'a ya kula da hakan"babu ja mai Shari'a ya yi masa gargaɗi,ya bayar da haƙuri sannan ya cigaba da tambayoyinsa
Ya sake duban Shaheeda ya ce"kina da hujjar abin da kika faɗa? na cewa kin dakatar da duk wani aiki da kike yi a tsawon waɗannan shekaru?"
Shaheeda ta jinjina kai ta ce"eh!
Ina da hujja "
Barrister Sulaiman ya ce"menene hujjarki?"
Shaheeda ta ce"tun a lokacin da aka kama ni a Abuja na dakatar da komai,sai dai Alhaji Sa'idu Wada, tsohon minister a wancan lokacin ya buƙaci na cigaba da yi masa aiki,na fara na ɗan lokaci,daga baya da na ga na tara abin da nake nema,dama ba gaya maka akwai dalilin da ya sa nake yi,sai na daina komai
To saboda na yi masa bore na ce ba zan cigaba da yi masa aiki bane sai ya sa aka fara bibiyata don a kama ni "
Barrister Sulaiman da yake aika mata wani kallo ya ce"wanne Alhaji Sa'idu Wada kike nufi?"
"Alhaji Sa'idu Wada dai wanda ka sani,kowa da yake nan wajen ya sani,wato tsohon ministan ilmi"
Take waje ya kaure da hayaniya,don dama wasu mutanen suna zarginsa da aikata ɓarna,wasu kuma sun yi mamakin bayyanar sunansa a cikin maganar,sai da alƙali ya buga guduma sannan aka yi shiru, barrister Sulaiman ya ce"ko kina da shaidar hakan?"kai tsaye ta ce
"Eh,na turawa lawyerna, barrister Hibba Aiyo evidence,zata nunawa kotu"ita kanta bakinta rawa yake yi ta ƙarasa, saboda bata san me barrister Hibba ta taka ba ta ba ta umarnin ta faɗi haka
Alƙali ya buƙaci barrister Hibba ta fito,ta miƙe ta fito daga wajen zamanta,gaba ɗaya kallo ya koma sama,don an tabbatar da cewa barrister Hibba bata bari a yi nasara akanta tun tana matashiya,har zuwa yanzu da girma ya fara cim mata,ta taso ta dawo gaban alƙali ta fara magana
"Ya mai shari'a,kafin na gabatar da hujjojin Shaheeda a gaban kotu zan so kotu ta ba ni dama na yi mata wasu ƴan tambayoyi"alƙali ya bata izini,ta rissina ta ce"na gode ya mai Shari'a "ta dubi Shaheeda ta ce"a bayananki na ɗazu kin shaidawa kotu cewa akwai dalilin da ya sa kika faɗa harkar safarar ƙwayoyi da Yahoo, shin za ki iya sanar da kotu wannan dalilin?"
A hankali ta jinjina kanta, sannan ta fara ba da labarinta a hankali,bata dakata ba har sai da ta kai ƙarshen labarin, kafin ta kai ƙarshe kusan rabi da quarter da suke kotun sai da suka zubar da hawaye
Bayan Shaheeda ta kai ƙarshen bayanin barrister Hibba, wadda ita zuwa yanzu ta daina kuka akan irin wannan case ɗin ta ɗauko laptop ɗinta ta danno wasu hotuna da Roxy da Alhaji Sa'idu Wada suke tattaunawa,har ma da CCTV footage da ta samu oga boss ya samar Mata na lokacin da Alhaji Sa'idu Wada yake tattaunawa da Roxy,ga bayanai nan raɗau sun fito,ga muryarshi ga hotonsa
Tuni kotu ta sake kaurewa da hayaniya,mafi yawa suna tsinewa Alhaji Sa'idu Wada da suke ganin a matsayinsa na ministan ilmi abin da ya dace shine ya tallafi Roxy ta yi karatu ya daƙile wannan sana'ar tata,to amma bayan munin abin da ya nema a wajenta har ma ya nemi ya yi haramtacciyar tarayya da ita,hakan ya sa mutane suka fara tsine masa,da yawa kuma suka fara yabawa Roxy saboda yadda ta nuna kai tsaye cewa ba zata siyar da mutuncinta akan wani kuɗi ba
Sai da alƙali ya buga guduma sannan aka yi shiru,ya ba wa barrister Hibba izinin cigaba da bayani
"Ya mai Shari'a,abu ne sananne a nan cewa Fatima Shaheeda ta aikata laifukan da ake tuhumarta tabbas,kuma daidai ne ta fuskanci doka,amma kuma ya kamata a ce wanda ya yi silar faɗawarta ciki shima ya fuskanci doka
Sannan ya mai Shari'a,duba da halin da Fatima Shaheeda ta shiga a rayuwa,muna roƙon wannan kotu mai adalci da ta yi mata rangwame,ko babu komai a ba ta wata dama a rayuwa"
Kotu shiru ta yi,kowa yana jiran abin da alƙali zai ce game da shari'ar da ake kan gabatarwa, wadda take a cukurkuɗe, alƙali ya juma yana rubuce-rubuce kafin ya ɗago yana gyara zaman glasses ɗin idanunsa,ya dube su ya ce"kotu ta saurari hujjoji daga dukkan ɓangarori,kuma ta yi dubanta don yanke hukunci,amma an ɗaga shari'ar zuwa takwas ga watan gobe,wato nan da sati biyu kenan
Kotu ta bayar da umarnin a cigaba da tsare Fatima Shaheeda ba tare da beli ba zuwa ranar, sannan ta bayar da umarnin a kamo tsohon ministan ilmi,wato Alhaji Sa'idu Wada,don tuhumarsa bisa ga laifukan da ake zargi ya aikata"daga haka ya buga guduma,mutane suka miƙe suna faɗin "koooootuuuuuu!!!"
Daga nan jami'an tsaro suka fito da Shaheeda barrister Hibba ta tare su, Shaheeda ta ɗago kai a sanyaye ta kalle ta, Hibba ta yi mata murmushin ba da ƙarfin gwiwa,amma zuciyar Shaheeda ta karye, hawaye suka cika mata idanu, Hibba ta goge mata hawayen, cikin kwantar da murya ta ce"khairan in sha Allah daughter!
Very soon za ki fita kin ji? Allah yana tare da mu gaba ɗaya,ki daina zubar da hawayenki a inda bai cancanta ki yi asararsu ba"Shaheeda ta jinjina kai a hankali, Hibba ta dafa kanta, sannan ta wuce ta bar wajen, jami'an tsaro suka wuce da Shaheeda zuwa motar da za su kai ta gidan kaso,duk da ƴan jarida suna ta jefo mata tambayoyi
*NILE UNIVERSITY NIGERIA,ABUJA*
Ɗan murmushi ta yi bayan sun kammala kallon yadda shari'ar su Shaheeda ta gudana, ƙawarta Hanan da take zaune kusa da ita suke kallon tare ta kalle ta ba tare da ta yi magana ba, tana murmushi ta ce"seriously Hanan I'm very proud of this lady, wallahi Abba ya yi asarar brainy girl irinta,ya kasa gane su Mommy da sauran matansa hassada suke yi masa na samun one in town irin aunty Shaheeda,i like her so much wallahi,ba ƙaramin daɗi na ji ba da aka ce ita ce wadda ta rinƙa jijjiga ƴan sanda,ko zuwa nan gaba na san sun gane cewa ba iyawarsu ba ce ta sa suka kama ta ba,ikon Allah ne kawai"
Hanan tana dariya ta ce"gaskiya Na'ima ba ki da mutunci, Mommyn kike cewa tana yiwa Abba hassada?"
"Let's keep joke aside Hanan,kin san wacece Mommy na, saboda yayan mamanki ta aura, which is our father,dukkanmu muna iya tuna yadda ta wahalar da dangin nan namu,da a ce mum ɗinku ce ta wahalar da mu kamar yadda mum ɗina ta wahalar da ku da ba mu isa mu zauna a waje ɗaya ba
I'm very sure su Mommy na sune suka janyo Abba ya kori Aunty Shaheeda
Kin san babban yayanmu Muyassar ya so ya aure ta,tun muna yara, Allah bai yi ba,su Mommy suka hana, suka aura masa wata matsiyaciya,for God sake Hanan na tsani yarinyar nan,bata da tarbiyya ko kaɗan,amma Mommy bata gani saboda tana sonta, shiyasa na zaɓi na koma wajen Mom ɗinki kawai na zauna,ko wajen Uncle Ismail (ƙanin babanta)"
Hanan ta riƙe hannunta, cikin lallashi ta ce"Na'ima,duk lalacewar iyaye fa iyaye ne, ba'a taɓa fushi da su,sai dai a yi ta haƙuri ana nuna musu hanya, ba'a fito na fito da su,yin hakan kuskure ne,kuma ba'a gyara kuskure da kuskure,ki yi duba ga maganata please "
Na'ima ta taɓe baki, Allah ya sani tana jin ciwon halayen mahaifiyarsu,mace mai tsananin son kanta da ƙyashi,tana jin haushin yadda take dakile Abba tana shigarwa Ummeey hanci da ƙudundune,mace ta gari, wadda a kowanne lokaci take sha'awar zama mai irin halayenta
Daga nan Na'ima chanja topic ta yi,amma har yanzu a ranta tana jin Shaheeda ta yi daidai,kuma zata iya zama irinta,banda haka ma sai ta san yadda aka yi yayanta ya aure ta
*ROCKY ESTATE,KANO STATE*
"Ikon Allah!anan nake jin son zuciya, wadda hausawa suka ce ɓacinta"Hajiya Mariya ta dubi Nimra mai wannan maganar tana riƙe haɓa,ta ce"me kika gani?"
Nimra cikin ɓacin rai ta ce"wannan shari'ar da aka canjawa ma'ana mana, wallahi ko kaffara ba zan yi ba duk abubuwan da aka gabatar ba haka suke ba,haka kawai an wani rage mata laifi,an shirya ƙarya da sharri an saka babban mutum kamar Alhaji Sa'idu a matsala?
Gaskiya wannan yarinyar masifa ce,kuma in sha Allahu ba zata gama da duniya da lafiya ba"ta ƙarasa magana cikin ƙunan rai
Hajiya Mariya da take kallonta ta ce"ke menene matsalarki da ita ne?"
Nimra ta ce"ya Haisam ya damu da ita da yawa,bana son na zarge shi akan wani abu dabam, Allah Allah nake yi ta zo ta amshi ɗanta,ni da ban ga kamannin halfcast a tare da shi ba ma da na ce ɗan na Haisam ne,ta shiga rayuwarsa da yawa,babu wata criminal da ya yi chasing da nake ganin yana kallon hotunanta yana murmushi sai ita,why?duk saboda ta yi laifi ne ko me?"
#Nusy_bee