GADAR TSAUTSAYI 40
by @nusybee143
Page 40
Hajiya Mariya ta yi murmushi ta ce"oh Allah!
Nimra meyasa abin da ya zama damuwa da wanda bai zama ba duka saka shi kike yi a ranki?
Ba kya tsoron wani ciwon na zamani?
Ki kwantar da hankalinki ki cirewa kanki damuwa,tunda ya zaɓe ki a matsayin macen da zai aura ai komai mai sauƙi ne
Allah na tuba ko da a ce ya ce zai aure ta ne ke ba mace ba ce?ba ki san yadda za kiyi kissa irin tamu ta mata ki mayar da abin tarihi ba?
Ni ba ki ga yadda nake zaune a gidan ubansa ni kaɗai ba?ko an gaya miki haka kawai a banza nake zaune?"
Nimra ta jinjina kai, Hajiya Mariya ta ce"ko ke fa!
Mace da ta isa bata taɓa yin hayaniya akan namiji,idan kika ga mace tana hayaniya akan namiji to kucaka ce"
Nimra ta yi shiru tana jin huɗubar yayar Tata,kuma tana shiga kanta,a ranta ta ƙudurce tabbas sai ta koyawa Shaheeda hankali muddin bata fita sabgarsu ita da Haisam ba
*HAISAM*
Sun sake tattaunawa sosai shi da barrister Hibba,duk da ya ji relief na alamun cewa za su yi nasara a zaman kotun to amma ya ji babu daɗi da barrister Hibba ta tabbatar masa ko yaya ne zata yi zaman kaso,amma ganin babu wata mafita sai wannan ya sa ya haƙura
Bai koma gida ba sai wajen ƙarfe takwas na dare,kuma kamar yadda ya saba yau ma sashen Nanny ya nufa
Ya sha mamaki da ya shiga sashen ya ga Nimra a zaune tana kallon cartoon tare da su Amna,amma fa Amna ce a kusa da ita, Mubarak kuwa yana kusa da Nanny wadda take goge musu kaya zata jera musu a wardrobe
Da fara'a ta fara gaishe shi da yi masa sannu da zuwa,ya amsa fuska babu yabo babu fallasa, Amna ta miƙe ta tafi da gudu ta ɗane shi,ya ɗaga ta ya sauke, sannan ya kira Mubarak,ya taso fuska babu yabo babu fallasa,ya ɗaga shi ya dire yana murmushi, kafin ya ce"abokina ya ne?
Ka ci abinci kuwa?"Mubarak ya ɗaga kai, Amna ta ce"Daddy ɗazu ma ya yi kuka yana kiran mamana!mamana!!"ta faɗa tana kwaikwayon yadda Mubarak ɗin yake faɗa
Murmushi Haisam ya yi,ya ɗauki Mubarak da yake kallonta,yana faɗin "abokina yanzu fa kai babba ne,ya kamata fa a ce ka daina rigima"
Nanny ta yi ƴar dariya ta ce "tsokanarsa ƴar'uwar ta yi,shine dalilin kiran maman"
Haisam ya harari Amna,ta sunkuyar da kanta da sauri,ya ce"wato kuka kike saka friend ɗin naki ko?
Sai na ɗauke shi na mayar da shi tunda ba kya so"
Da sauri ta ce"I'm sorry Daddy ina so"ya ce"Weldon!
Sai ki daina tsokanarsa"ya kalli Mubarak ya ce"kana jin bacci?"
Mubarak ya gyaɗa kai a hankali, Haisam ya ce"yawwa mu boy!mu je mu kwanta ko?"nan ma ya gyaɗa kai yana kwantar da kanshi a kafaɗar Haisam
Abin ya yiwa Nimra ciwo sosai,ganin ko kallo bata ishe shi ba,sai ta wannan matsiyacin yaron yake,a ranta ta ƙudurci sai ta raba shi da shi su huta, tunda gashi yanzu ma ko ta yar cikinsa baya yi
Har ya juya baya ta ce"Good evening yaya Haisam!"ya juyo ya ce"evening Nimra!"sannan ya kalli Nanny ya ce"Nanny na manta, Mubarak ya sha maganinsa kuwa?"
Nanny ta ce"ai bana yi masa wasa ko kaɗan Alhaji,na ba shi tun ɗazu "Haisam ya yi murmushi yana sake rungume Mubarak ya ce"Weldon Nanny muna godiya sosai,sai da safe ko?"Nanny ta ce"Allah ya tashe mu lafiya Alhaji"
Amna ta ɗaga masa hannu tana murmushi tana faɗin "Daddy Good night"ya ce"Good night angel"ta ce"Mubarak Good night"
Kamar yadda Nimra ta yi zato sai kuwa ta ga Haisam ya ja ya tsaya yana murmushi yana kallon Haisam,ya ce"ka ce"mata good night "da farko kamar ba zai faɗa ba,amma sai ya ce"good night!"da yanayin gwaranci a maganarsa
Dariya suka yi su duka banda Mubarak da Nimra, sannan Haisam ya fice daga sashen
Yana fita Nimra ta kalli Nanny ta ce"Nanny yaron ba shi da lafiya ne?"
Nanny cikin jimami ta ce"wallahi kuwa Hajiya!
Yaro abin tausayi,wai ciwon asma,jiya da numfashin ya riƙe ai sai da na kusa faɗuwa,don na ɗauka barin duniyar zai yi"
Nimra cikin fuskar tausayi ta ce"Allah sarki!
Allah ya ba shi lafiya"Nanny cikin jimami ta ce"Ameen Hajiya!
yaron abin tausayi wallahi,gashi sam ba shi da saurin sabo da mutane"
Nimra bata sake magana ba,ta cigaba da kallonta, ƙarshe ma da ta ga Amna ta fara jin bacci ta raka ta ta kwanta sannan ta miƙe ta fice zuwa sashen Hajiya Mamie
*MUYASSAR*
Yana tsaye a jikin windown ɗakin da ya kama a katafaren hotel ɗin yana leƙen titin da yake bayan hotel ɗin,gaba ɗaya duniyar ta yi masa zafi,damuwa ta ishe shi sosai,a yanzu yana jin ba shi da wani farin ciki ko walwala sama da mallakar abincin ruhinsa wato Shaheeda,amma jiya a gabansa aka gudanar da wata zazzafar shari'ar da yake kyautata zaton cewa Shaheeda ba za ta fita ba, sai ta yi zaman kaso
Sau uku yana zuwa don ganinta, amma abu ɗaya ake sanar masa shine babu wanda zai ga Shaheeda,daga jami'an tsaro sai lawyer ɗin ta, hakan ya sake tabbatar masa da case ɗin babba ne tun a wancan lokacin, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba
Duk wannan dambarwar ba ita ba ce ta dame shi kamar rashin damar auren Shaheeda, mafi girman tashin hankalin kuma shine rashin soyayyar da Shaheeda take yi masa, kenan hakan ya nuna cewa dakon wahala yake yi? Nooooo! Impossible ya san Shaheeda ko bata so shi ba yanzu zata so shi wataran
Arfa ce ya faɗo masa a rai,wani baƙin ciki ya tokare masa maƙoshi tuna yadda Arfa take ƙare masa zagi shi da iyayensa don kawai tana taƙama ba zai sake ta ba, saboda umarnin mahaifiyarsa, yanzu gashi nan ya sake ta ɗin,ta je can ta shirya duk makircin da zata shirya,shi yanzu ma nan da shekara guda ba za'a sake ganinsa ba, don yan kwanakin da ya ɗauka babu Arfa a tare da shi har ya fara samun nutsuwa ya dawo hayyacinsa
Kira ne ya shigo wayarsa,bai damu da ganin mai kiran ba ya ɗaga wayar,kamar yadda ya zata kuwa haka ɗin ne, Na'ima ce
"Yaya!kana tare da Ni?"
A hankali ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce"ina tare da ke Na'ima,ya school?"
"Yaya!ka kalli shari'ar su aunty Shaheeda kuwa?"
Muyassar ya ja numfashi ya fesar ya ce"na kalla Na'ima,in fact a gabana aka yi komai,sai mun dage da addu'a sosai, don Shaheeda tana cikin gagarumar matsala"
Na'ima ta yi murmushi ta ce"yaya kenan!
Kana kallon Shaheeda a matsayin wadda ta faɗi,ni kuma ina kallonta a matsayin jarumar da ta jijjiga ƙasa baki ɗaya da kaifin ƙwaƙwalwa da fikirarta, wallahi ko a yau aunty Shaheeda ta bar duniya tarihi ba zai manta da ita ba"
"Ke bana son shirme!
Ba fa abin a zo a gani ta yi ba, ƙwayoyi ta siyar, sannan kuma Yahoo girl ce, menene abin alfahari a nan?"
"Yaya yahoo ai na masu basira ne,Ni na yi mana,ko kai!
Sannan abu ka gaba kar ka manta yaya, manyan ƙasa waɗanda ya kamata su tallafi rayuwarta da sana'ar yi da ƙwaƙwƙwaran ilmi su ne suka ba ta hanya,ko na ce suka yi amfani da ita don aiwatar da wannan muguwar sana'ar,a wannan lokacin ahalinta sun watsar da ita,sun nuna ba sa buƙatarta, not even her,ko ni idan na gamu da wannan trauma ɗin ban ce zan iya riƙe kaina ba, musamman da ya kasance kana jin tarihin da ta bayar ai,ta ce ta nemi aiki a kamfanoni,amma ko'ina daga mai neman takardu sai me nemanta,kuma ƙarin alfaharin da nake yi da aunty Shaheeda shine rashin siyar da mutuncinta,ta yarda ta amsa sunan criminal amma bata yarda a yaga mata rigar mutunci ba,yaya aunty Shaheeda ta dabam ce "Muyassar da ya yi shiru yana sauraren maganganun Na'ima da ya ɗauka shirme ya ce"na ji Na'ima,Ni dai sai anjuma kar ki saka ni ciwon kai da wannan surutan naki "ya kashe wayar yana jin ta tana ƴar dariya
Sai kuma ya zauna yana nazarin maganganun ƙanwarshi Na'ima, ya tuna lokacin da Shaheeda ta dawo gida bayan rasuwar Arnold,da alamun nadama masu yawa a tare da ita,ga ciki,ga babu,amma hakan bai hana Abba ya kore ta ba, ba tare da tunanin a wanne hannu zata faɗa?ko wanne hali zata shiga ba?
A ina ta cigaba da rayuwa?ta haihu?me ta haifa? tabbas ya tuna ƴan sanda sun fitar da rahoton cewa da ɗanta aka yi mata tarko, kenan wannan ɗan na Arnold ne kenan?
Ya aka yi yan sanda suka san da zamansa da za su yi mata tarko da shi?
A ina ta ajiye shi take kasuwancin nata?ko da shi take tafiya?ya dafe kai cikin ruɗewa, gaba ɗaya sabgar nan tana kulle masa kai, gashi an hana shi ganinta ballantana ya je ya ji dukkan bayanai daga gare ta,har da tambayar ina yaron ya shiga?
Kwantar da kanshi ya yi a jikin kujerar da yake zaune ya lumshe idanu, tabbas Shaheedansa tana cikin matsala,amma matsalar da yake hangowa a gaba ta fi wadda ake ciki yawa
*RANAR KOTU TA BIYU*
A yau kam kotu ta cika ta tumbatsa fiye da zaman baya,kuma yawancin mutane dalilai biyu ne ya kawo su,na farko ganin hukuncin da kotu zata ɗauka akan Shaheeda,na biyu kuma ganin Alhaji Sa'idu Wada, kamar wancan karon, yau ma Muyassar ya samu zaman kotun, Hakazalika Haisam da tawagarsa
Bayan an shigar da Shaheeda don fara zama,a can ta hango Oga boss da Azeema a cikin mutane,suna haɗa idanu da Azeema ta ga hawaye sun fara wanke mata fuska,ta yi murmushi tana girgiza mata kai
An fara zama kamar dai wancan karon,an sake karanto gaɓar da aka tsaya a zaman baya, Shaheeda ta sake tabbatar da cewa eh lallai ta aikata, sannan alƙali ya buƙaci ganin Alhaji Sa'idu Wada,a nan yan sanda suka tabbatar da cewa ya bar ƙasar tun kafin a gama zaman baya, da alamu ma a shirye yake da hakan
Hakan ya sa alƙali ya bayar da umarnin gani da kamu a duk inda yake, sannan ya duƙa ya cigaba da rubuce-rubucensa,kotu ta yi tsit tana jiran hukuncin da za'a yankewa Shaheeda, wadda a wannan lokacin da za'a tsaga jikinta bai zama lallai a ga jini ba saboda yadda ta daskare tana jiran ikon Allah, duk da cewa a yanzu ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali sosai sakamakon karatun alƙur'ani da take yi a yawancin lokuta
Alƙali ya ɗago ya fara magana "kotu tana tuhumar Shaheeda da safarar miyagun ƙwayoyi,wanda ta amsa ta yi hakan da kanta, sannan tana tuhumarta da sata ta yana,wato yahoo,bayan ta yi hacking asusun mutane
Don haka kotu ta yanke mata hukuncin shekaru bakwai a gidan gyaran hali bisa samunta da laifin safarar miyagun ƙwayoyi, rangwamen hukuncin ya samo asali ne saboda halin rayuwa da ta samu kanta,da kuma wanda ya zama shine mai alhakin hakan
Na biyu kuma kotu ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan kaso bisa samunta da laifin satar kuɗaɗen mutane ta yana wato Yahoo, sannan kotu ta ƙwace dukkan abin da ta mallaka na dukiyarta da kadarorinta,idan bata yarda da hukuncin ba,tana da damar ɗaukaka ƙara zuwa kotun gaba nan da kwanaki talatin"daga nan ya buga guduma,mutane suka miƙe suna faɗin "koooootuuuuuu!!!!"
Tirƙashi!!!
(Yanzu wani wasan zai soma!!!"
*Wannan shine ƙarshen book one,akwai ragowar chakwakiya masu ɗimbin yawa a gaba,ni kaɗai ce nake tunanin akwai wani abu tsakanin prisoner ɗin da wanda ya yi arresting ɗinta?😁baya ga haka shin ya rayuwar Shaheeda zata kwashe a prison tsawon shekaru goma?
Ga Ummeey da ta kasance abar tausayi kuma wadda take cikin ƙunci da damuwa,shin damuwar tata zata tafi a banza ne ko zata samu sakamakon haƙurinta?
Nice dai Nusaiba Ibrahim Rimi (Nusy bee)ku kasance da ni a littafi na biyu don jin yadda zata kaya
Book one shine Free, Book 2 Paid ne both Whatsapp and Arewa pen,ga mai buƙata ya tura #500 kacal ta wannan account number 8125952284 Nusaiba Ibrahim Rimi moniepoint,sai a tura shaidar biya ta wannan number ***,kada ku sake a yi babu ku,ina iyalan Roxy da na yallaɓai CSO Haisam ne?
Sai na ji ku.
#Nusy_bee