JODAH

21

by @sadisakhna


 

______👑 *JODA* 👑_____ 

 

              

 

 

Na  

 

*Sadi-sakhna* 

 

Ƴar mutan Jama'are 

 

 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

@sadisakhna on Arewapen 

@SAKHNA03 On Wattpad 

*** on Whatsapp 

 

 

LITTAFI NA 1 

 

 

👑*WarÆ™a ta (21)*👑 

 

 

Abin Yabani mamaki ban taba zaton zanga ummu hajar a kaina ba,duk zato na Hammar ne ya dawo daga majalisi sai fara mita akan inason neman ilimi amma nafiye ragwanta,ashe ummu hajar ce,ko mai yakawota nan É—in oho. Gashi nayi wasu maganganu masu wuyar fassarawa,wanda nasan koda nayi yunÆ™urin fassarawar bazata fahimta ba,tunda zuciyarta tagama fassara mata a yanda take son ji. 

 

"Ahah ahah Ummu hajar wlh ba yanda kike zato bane,da karatu nake karatu nake nufi akan ya isheni haka sai gobe mu cigaba na gaji yauÉ—in." 

 

"Kedai kika sani koma menene,ke mai hankalice ai ballantana kice ayi miki tuni,saidai ma ki faÉ—awa wani. Kwadayin na son tara iliminki ma zaisa kije har garken kura nemansa. Tashi ki wanke fuskarki mu tafi wani aikin gaggawa ya taso kuma ke ake nema a wajen. Sannan kiyi taka tsantsan da wannan mutumin,domin dukkan mu babu wanda yasanshi kokuma daga inda yake sai su baba guru kawai,su kuma ko ya zaka tambayesu bazasu fadaba, dan haka kiyi a hankali ku rabu lafiya baya binki bashi kema bakya binsa. Ki shirya kijo muna É—aki mai mutum É—aya na tsakiya bangaren mata" 

 

Tana gama faÉ—in hakan nayi saurin tashi,kowa abinda yake faÉ—amin kenan nayi taka tsantsan,amma nikuma nagagara yin hakan,gabaÉ—aya zuciyata idan ina tareda shi ji take tamkar ta samu wajen mafaka,kuma da alama shima yanajin hakan a tattare dani,ko yaya nayi Æ™oÆ™arin zame masa sai ya nemoni,kuma a yanayin ban tausayi nake kallonsa kaman wanda ya wuni yana gudu. Shiyasa ko naso tafiyar nake fasawa,domin ganinsa cikin wani hali shine abu na Æ™arshe da banaso,wanda bansan miyasa ba. 

 

Gyara kayan jikina nayi sannan na wanke fuskata kafin nabi bayan ummu hajar É—in, yanda na babbaza kayan karatun a haka na barsu ban tattareba,domin zatona yanzu zanje ai na dawo sai na tattare,nasan bazai dawo da wuri ba sai can wajen yamma. Ko abinci ban karbo masa ba saboda ba'a gama ba na bangaren É—alibai masu gasar. 

 

Cikin nutsuwa nake tafiya don bansan mai zan tarar ba idan naje,dan yanzu gabaÉ—aya jinya tafara daina É—agamin hankali kaman da,saboda yana daga cikin karatun ta idan kana jin razani ko rashin nutsuwa to bazaka haifar da sakamakon da ake so a samu ba. 

 

Tun daga bakin Æ™ofar na hango wani matashi sanye da kayan na sarauta,zaikai shekara ashirin da huÉ—u zuwa da biyar. Kallon dayakemin ko Æ™ifta ido bayayi nasa naji tun kafin na Æ™arisa duk yafita akaina. Koda nazo Zagayeshi nayi na wuce batareda nace komai ba. Jin takun mutum nayi a bayana,ina juyawa naga yana biyo bayana idonsa kyam akan kunkumina dayake juyawa har muka shiga É—akin. Jinayi gabaÉ—aya na tsargu,domin tunda nake babu wani namiji daya yimin irin wannan kallon sai shi. Ko Hammar ma saidai ya kalli idanuwana kokuma yaÉ—au hannuna ya É—ora akan Æ™irjinsa inda yake masa ciwo,amma bai taba yiwa surar jikina kallon Æ™urilla ba.  

 

Har muka shiga É—akin ina satar kallonsa,har sannan ni ya kafe da ido ko Æ™iftawa sosai bayayi. Araina nace wannan wanne irin maye ne haka. 

 

Tsunnawa nayi har Æ™asa na gaida babbar matar dana gani akan É—aya daga cikin kujerun da suke É—akin. 

 

Sai wata kuma wacce take jujjuya kanta kwance akan gado da Æ™aton ciki.  

 

"Sannu yarinya ko kece jodan da muke tajin labari kai?" 

 

ÆŠan murmushi nayi har zanyi magana naji muryar wannan mutumin yasaka baki. 

 

"Ganinta har fi jinta ma,koda kallonta dole ta tara wannnan baiwa" 

 

ÆŠan tsuke fuska nayi,ta gefen ido ina kallon lokacinda matar ta watsa masa harara.  

 

Tashi nayi na matsa inda marar lafiyar take kwance,inaso nace su matsa su bani wajen Fasihnman mai mayen kallon,amma kuma ina shakkar hakan saboda ko daga shigarsu ya tabbatar daga gidan sarauta suka zo. 

 

Hannuna na saka akanta na daga tareda rufe idona. Bayan duhu ya lullube ganina da kuma shuru wanda babu motsi a cikinsa,sai kwatsam naji jijiyoyin ta suna gudu kamar zasu tsinke,gudun jininta a cikin jijiyoyin yaÆ™aru sosai,hakan yasa zuciyarta bugawa da Æ™arfi tana watsa jinin a duk inda tasamu,Fasihmman ma cikin kanta. Saurin É—auke hanuna nayi ina ja da baya,share gumin goshina nayi kafin na kalli matar da take zaune,dan nima ji nayi kamar jininnata yana Æ™oÆ™arin shiga nawa jikin,saboda Æ™arfin gudunsa.  

 

"Yayadai yarinya nagana yanayinki ya sauya,ki faÉ—amana mai kika gani a tattare da ita" 

 

"Ranki ya daÉ—e da alama ta É—au lokaci ranta yana baci zuciyarta bata samun hutu saboda aikin rayuka ta takeyi,to saikuma akayi rashin sa'a takalla ko kuma da saurari abinda ya razana zuciyarta,hakan yasa tashiga buga jini da gudu fiyeda kima. Wannan ne ya haddasa mata numfarfashi da matsanancin ciwon kai,yanzu zanje na haÉ—o magani nadawo,kafin sanna a samu tsumma mai tsafta yana shafa mata ruwan sanyi a goshinta da kuma cikinta sannan da ambata mata addu'oin neman samun lafiya daga Allah. Dukkan wani abu da zai sakata cikin damuwa a tabbatar an matsar dashi daga inda take." 

 

 

"Shikenan yarinya za'ayi haka Allah yadawo dake É—aukeda sa'a kuma cikin Æ™oshin lafiya" 

  

Bayan na fita daga É—akin jingina nayi da jikin bango ina tuno abinda naji a jikintan,koma wacece lallai tana cikin matsanancin hali,sannan kuma ga juna biyu a jikinta. Abinda yake damunta ya alaÆ™anta da zuciya,amma kuma ba irin na hammar bane,ita nata jininta ne yake gudu daÆ™arfi sabanin shi da zuciyarsa ce tayi rauni sakamakon abubuwa dasuke yi masa barazana kaÉ—an kaÉ—an yau da gobe. 

 

ÆŠakin ajiyar magunguna na nufa,idan zuciya tana razani tamkar raine dole yana buÆ™atar abinda zai kwantar masa da hankaline. Wata Æ™ararrawa na É—auko wacce ake amfani da ita lokacin yiwa masu fama da tashin hankali ko halin gajiya tausa. Ganyen vanilla da Babunaj na É—auka sai kuma kasko da man vanillar. 

 

Komawa É—akin nayi bayan na taho da bayi guda biyu,wanda nasan da biyan tawa buÆ™atar ne ba lallai su yarda su biyoni ba domin taimakamin,amma dayake yar masu sarautace har ma sun fini sauri. 

 

Shirya duk wani abu danake buÆ™ata nayi har sannan idonta a rufe yake tana jujjuya kai,amma kuma bakaman sanda aka kawota ba. 

 

Turaren na ganyayyakin nafara zubawa a kaskon daddaÉ—an kamshinsu yafara gauraye wajen a hankali. Masu fifita suka fara,sannan nasaka baiwarta tana yi mata waÆ™e a hankali na ainihin Ƙabilarsu,wanda akacemin tana yawan saurarensa, nan da nan na maida É—akin tamkar an so yiwa sairki tausa,saida na tabbatar komai ya saitu kafin na fara shafa mata man a goshinta ina murzawa a hankali Fasihmman duk wani waje danaji jijiyar waje ta tashi kuma ta dunÆ™ule. An É—auki kaman minti talatin munayi wata nayi mata tausa a sauran gangar jikinta. Inajin wasu na  mamakin aikinnawa,yaza'ayi mutum bashida lafiya amma kuma a fara yi masa tausa,sannan ba'a bashi komai yasha ba saidai inda yake kwance akeyiwa hidima. Nima kaina banida tabbacin abinda nakeyi É—in zayyi,kawai yaÆ™ini ne da kuma neman taimako daga Allah. 

 

Sunkia Madina na zaune a can gefe tana kallonmu,amma wannan mai mayen kallon shi ya fita baya nan. 

 

Cikin ikon Allah dukka jikinta ya saki,bacci yafara É—aukarta,don su kansu wanda muke aikin dasu har sun fara gyangyanÉ—i,hayaÆ™in dayake jagayawa yafara sakasu bacci. A hankali na sallami kowa daga É—akin sannan na Æ™ara itacen turaren a É—akin,da kuma garin hodar saka bacci. Bayan kowa ya fita Babbar matar ce ta Æ™irani É—akin da aka bata domin ta sauÆ™a. 

 

Shiga nayi tareda samun can Æ™asa a gefe na durÆ™usa ina sunkuyar da kaina. 

 

Ina jin idanuwanta a kaina amma ban É—ago na kalleta ba,duk da cewar sunzo neman taimako wajena amma bazan manta matsayina a garesu ba na baiwa. 

 

"HaÆ™iÆ™a salon maganinki ya burgeni,kin cancanci yabaki da akayi min har hakan yasa na É—auko Æ™afafuna nazo gareki,da farko banyi tunanin abubuwan dakikeyi zasuyi ba,ni nakaina nayi mamakin wanda bashi da lafiya mai zai haÉ—ashi da tausa kuma,amma sai gashi cikin ikon Allah jikinta ya sake hankalinta ya kwanta kuma tasamu bacci. Saidai duk da haka ina so naji daga bakinki a wanne mataki take sannan shin ta warke ne idan ta tashi daga baccin kokuma akwai abinda za'a sake?" 

 

"Ahah ranki ya daÉ—e yanzu bacci jikinta yake buÆ™ata,ta hakanne zuciyarta zata saurara daga watsa jini da takeyi da Æ™arfi,idan hakan yacigaba rayuwarta zata shiga cikin hatsari Fasihmman da yakasance ba ita kadai bace. Dan haka zaifi kyau abarta tayi ta bacci harsai jikinta ya huta sosai, kafinnan akwai magunguna da zan haÉ—a,wanda idan ta tashi zata dunga amfani dashi,sannan a tabbatar an kula wajen kiyaye abinda zai sakata cikin bacin,hakan nada matuÆ™ar haÉ—ari shima" 

 

"Shikenan yarinya Insha'allahu za'a kiyaye,ni nan zan tsaya akan lamarin wajen ganin an kiyaye waÉ—annan sharuÉ—É—a harda ta haihu lafiya,mungode sosai yarinya Allah yaÆ™ara miki basira" 

 

"Ameen ranki ya daÉ—e" 

 

Daga haka nayi saurin barin É—akin,duk da tana kirki daga kallonta amma masu mulkin ne kwata kwata basuda tabbas,yanzu zaka gansu fari ana jimawa zasu rikiÉ—e zuwa baÆ™i. 

 

Wajen haÉ—a magungunan dana ambata zanyi na nufa,rasa mai ma zan haÉ—a mata nayi,saboda tunda na samu kaina cikin duniyar ilimin lafiya nake haÉ—uwa da abubuwan da ban taba haÉ—uwa dashi a baya ba,ko wani wanda yafini ilimi,na É—auki hakan a matsayin nima nawa Æ™alubalen na bangaren neman ilimi.  

  

Tun É—axu nake kai kawo a lugun na rasa da wanne zan fara,basirata ta Æ™are a sakata bacci danayi,to yanzu idan ta farka mai zanyi mata,mutanennan sun yarda dani yasa suka Æ™i neman kowa saini,duk masu maganin dake bangarennan sunyi shuru tareda zuba kunne suka ta inda zan kuskure suyi dariya da tofa albarkacin bakinsu,domin tun É—azu nakejin Æ™usÆ™us akan hakan. 

 

Iska naji ta bayan kunnena kamar Alamar wani ne ya huramin,kokuma akwai mutum a bayana,da sauri na zabura na waiwaiya. Wannan mutumin nagani na É—azu,yana min kallon Æ™urilla idonsa kaman zai faÉ—o,in banyi Æ™arya bama kaman gani nayi yana lashe baki. Sunkuyar dakai nayi ina ja da baya a hankali. Shima ganin hakan takowa yafarayi yana matsowa a hankali zuwa inda nake . Ban ankara ba saida naji gadon bayana ya mannu da bangon wajen tukunna. Tsoro ne da fargaba sukayiwa zuciyata dirar mikiya a lokaci guda. Yazamana Æ™irjina yana sama yana Æ™asa a duk lokacin da yaÆ™ara taku zuwa isowa inda nake manne da bango. A haka ban samu damar matsawa bayan razanin danayi har yamatso da jikina,har Æ™irjinsa yana gogar tudun nawa Æ™irjin,tsikar jikina ne naji ya zuba hakan yasani runtse,babu abinda nake buri a lokacin sai Æ™auracewa wannan baÆ™on lamarin danaji,to amma nasan yin hakan a matsayina na baiwa ga shi mai mulki abune mai matuÆ™ar hatsari amon muryasa naji ya doki dodon kunne na banyi zato ba. 

 

"Kyakyawa ina zaki gudu kijene,bayan nasan kin kula da kallon danake muki na cewar na Æ™yasa da wannan É—anyar surartaki,yanzu bazan yimiki komai ba iya kawai É—an rage zafi zanyi saboda kin matata tana kwance bana samun komai daga gareta......ina fatan zaki bini cikin masarauta na kawataki da kayan more rayuwa sannan na shayar dake daÉ—i,wannan bada maganin kwata kwata bai dace da kyakyawar budurwa irinki ba." 

 

Ƙarisa maganar yayi yana kaiwa hannu zai É—ora a Æ™irjina,ganin hakan bansan lokacin dana kai hannuna cikin zafin nama ina rike hannunnasa ba. Da mamaki ya É—ago ya kalleni domin bayyi tunanin zanyi hakan ba. Nima ganin ransa yafara baci da hanashi yin abinda yayi niyya yasa na fara jijjiga kai ina marairaice fuska. 

 

"Dan Allah kayi haÆ™uri ranka yadaÉ—e,ni banyi kama da irin wanda kake tunani ba,yanzu haka tsaka nake dayin tunanin mafita na matarka wacce batada lafiya,to na roÆ™eka dan Allah kabarni karka kademin hankali da wani abun daban." 

 

"Matata waye yace ki maida hankalinki gabaÉ—aya akan matata, kishinta na haukane da yayi yawa yakaita ga halinda take ciki,sannan da kuma Æ™aramar zuciya,dan haka karki wahalar da kanki akanta,dan ko kin sha wahala ta tashi tana sake kallon wani abun zata sake komawa,wataÆ™ila ajalinta ne a kusa a haka,kinga idan kika bani haÉ—in kai ma tunda ina sonki saina maidaki sarauniyar idan nazama sarki,bakisan nine magajin wannan babbar masarautar ba" 

 

Kallonsa nakeyi baki sake yanata zuba tamkar tababbe,anya kuwa kansa É—aya,matarsa da tsohon ciki na wannan halin amma yake waÉ—annan maganganun na ko in kula,kuma a hakan ni ya maidani gara kamar sauran bayin dayake samunsu da wannan kalamannasa sai na yarda dashi?.. 

 

Ko kuwa muka farayi dashi a dole sai ya tabani ganin maganganun nasa basuyi tasiri ba, ganin bazaici nasara ba yanda yakeso yasa yaja da baya a fusace tareda kifeni da mari,riÆ™e wajen nayi ina shashsheÆ™ar kuka,kunnuwana kuma suna cigaba dajin kalmomin Æ™asÆ™ancin dayake jifana dasu. 

 

Sake É—aga hannu yayi zai sake marina,tareda yin iÆ™irarin sai ya saka dogaransa sun horani,muryasa naji,abinda ban taba kawowa a kaina ba a lokacin. 

 

"Kada ka sake marinta,idan kuma ka Æ™ara sai kayi nadamar hakan ko kai waye" 

 

Shida baisan waye yayi maganar ba,da mamaki ya sauÆ™e hannunsa tareda waigawa yaga wanne shafaffe da mai ne a kaff faÉ—in Æ™asar nan yakeda Æ™warin gwiwar cemasa zayyi nadama. Duk da cewar yaga kayan jikin É—an sarkin amma hakan baisa ya janye maganar dayayi ba,saima takowa dayakeyi zuwa inda muke cikin izza,takama da kuma nuna zallar bacin rai a kan fuskarsa,idan nagani daidai ma harda wani abun daman a kwayar idonnasa wanda na gagara fassarashi. 

 



Version:1.0 StartHTML:0000000156 EndHTML:0000220352 StartFragment:0000000469 EndFragment:0000220344

 

Tunda yayi maganar idona yake kansa har ya iso inda muke É—in,mamaki yabani matuÆ™a ganin bai girgiza ba da ganin dawa yake magana,a lokacin wata a ayar tambayar tawa tasake dasuwa akansa nacewar shi ba bawa bane kamar yanda yake iÆ™irari,domin bayyi kama dasu ba kwata kwata. 

 

"Kasan ni waye da har kake Æ™iramin nadama idan banyi abinda kake so ba?" 

 

"Kai waye banda banzan namiji mai cin mutuncin mata,har kanaso a san kai waye daya wuce wanda ka nunawa kowa?" 

 

Cije baki Yerima Kabeer yayi,domin cin fuskar da Hammar yayi masa kuma yana sanye da kayan da ba É—an kowa ba,ba Æ™aramin cin zuciyarsa yayi ba. Haka shima a bangaren hammar É—in bacin raine Æ™arara a fuskarsa,wanda shi na rasa na menene,ince dai bana cin zarafin dayaga anayimin bane,ko ya manta matsayinmu ne daga ni harshi dazayyi wannan katsalandan É—in,koshi jarumin namijine amma ai matsayi yafi jarumta. Ganin hakane yasa naja hannunsa da sauri muka bar waje kafin dakarun da suka zo dasu su kulada me akeyi su nufo wajen,wanda nasan bazatayimana kyau ba sam. 

 

Jansa nakeyi baice komai ba har saida muka bar sansanin wajen muka nufi hanyar masauÆ™insa. Ganin muna tafe bance komai ba yasa ya fincike hannunsa yanamin kallo kaman zai haÉ—iye sama don baÆ™in ciki, mamaki abin yabani amma na haÉ—iye kana na fara magana cikin Æ™asa da murya. 

 

"Kasan kuwa abinda kayi,kasan matsayinsa kuwa,kasan waye ubansa a nahiyar nan zaka bashi umarni,kuma kace idan bayyi ba zayyi nadama. Nasan abinda yayimin bai kyauta ba,amma kar hakan yasa ka dunga manta banbancin matsayinmu da nasu, Fasihmman ma ni gwara kai baÆ™one mai tafiya,sannan kace ubangida yanaji dakai,tunda gashi har magani akeyi maka tamkar mai Æ´an ci,amma nifa ko a yau namutu babu wanda zai rasa komai,kokuma ya cutu akan hakan duk da inason kimata da darajata,amma banasaka a raina cewar zanyi iya kare hakan watarana idan wanda ya mallakeni ya nemi karbar hakan,mai Æ´anci ce take da yaÆ™inin kaiwa martabarta ga mijinta amma ba baiwar da gobe ma za'a iya sayar da ita ba Hammar. Yanzu wannan abun dakayi zaisa yaga tamkar soyayya muke ya tunzurashi ya saye ni ko ya karbeni a hannun wannan makarantar sannan yayi abinda yakeso,kuma yanada ikon yin hakan babu wanda ya isa ya hanashi, to kaga Yanzu bansan wacce irin chakwakiya ka ballo mana ba indai ba Allah ne yayi ikonsa ba. Domin irin waÉ—annan mutanen idan suka saka idonsu akan abinda zuciyarsu ke muradi to dole sai sun samu" 

 

Duk maganar danakeyi kafeni yayi da ido kawai,batareda ya furta ko kalma É—aya,ganin kaman yana fita hayyacinsa yasa na matsa kusada shi ina girgizashi cikeda damuwa. 

 

"Hammar Hammar dan Allah ahah,idan maganar ce bakaso nayi akan lamarin na daina,amma dan Allah karkajawowa kanka matsala a dalilin hakan" 

 

Sai a lokacin ya numfasa,har sannan wannan abun dayake tafasa a cikin idonsa bai  mutu ba. 

 

"Shi kenan wato dan saboda ke baiwa ce,kokuma matsayinmu ba É—aya dasu ba kina tsoro kada hukuntaki sai hakan yasa duk abinda suka buÆ™ata ki basu,koda kuwa hakan shine kaÉ—ai ke abinda kika mallaka yake naki? Kenan kema kinason hakan tunda kika tsaya batareda kin gudu ba yanayi miki yanda yaga dama. Kikace wai yanada Æ™arfin dazai mallakeki koh,kuma yayi abinda yaga dama. To shikenan ga wajennan yasamu hakan yayi yanda yakeso,kema kuma yabaki abinda kikeson." 

 

Sake baki nayi ina kallonsa har ya wuce fuu kaman zaki yabar wajen,binsa nayi da ido har ya shige É—akin ya bugo Æ™ofar katakon kafin na Æ™ifta,gabaÉ—aya gani nake tamkar a mafarki,dama haka yake bantaba kallonsa koda wasa yayi irin wannan fushin ba.  

 

"Ransa yabaci matuÆ™a tunda kikaga yagaza cewa komai,domin ko yaushe idan ransa yabaci haka yakeyi ya kulle kansa a É—aki,kokuma yayi ta karatu da bincike yaÆ™i bawa Æ™waÆ™walwarsa daman yin tunani akai. Tun da hantsi da muka dawo ya tarar bakyanan kuma takardu duk a warwatse hankalinsa ya tashi,domin bai san meyasa kika tafi ba har kika bar wajen haka,abinda baki saba yi ba. Hakan yasa yaÆ™i zama ya nutsu,ko abincin baici ba yana ta nemanki a duk inda yasan sai sameki,zuwansa wajenne ko nace da mukaje ya tarar dake wancan mutumin yasaka kansa a wuyan ki ke kuma kina tsaye,ransa ya baci matuÆ™a,da farko bazai yi magana ba domin yayi zaton da son ranki,amma ganin ya zabga miki mari yasa ys Æ™arisa wajen da sauri har yafaÉ—i abinda yafaÉ—a." 

 

Jikina ne yaÆ™ara yin sanyi, tunanin danake ciki na taimakon marar lafiyan can yasa na manta da zai nemeni,domin tare muke cin abin,duk da ba kwano É—aya ba amma yana gefe yana ci nima ina cin nawa,idan mungama anyi sallah mu tafi Lambu. Koda safe yakalli banzo da wuri ba sai yazo yaji ko lafiya.  

 

Hanyar Æ™ofar daya bugo É—in na nufa,abubuwa da dama dasuka faru tsakaninmu a É—an zaman da mukayi suna dawomin a raina. Tura Æ™ofar nayi a hankali naji shuru,hakan yasa na saka Æ™arfina na tura,wanda hakan yasa Æ™ofar ta wangale da Æ™arfi, yana zaune a gaban Æ™aramin teburin karatu,kaman yanda Fasih ya faÉ—amin.  Nakai daÆ™iÆ™a uku a tsaye ina kallonsa amma ko kaÉ—an bai É—ago ya kalleni ba,kamar baisan da wata halitta a wajen ba. Ganin da gaske bazai kulani ba yasa na fara takawa a hankali cikin sanyo jiki zuwa inda yake. Bayan na isa numfasawa nayi kafin na tsugunna a gabansa saitin fuskarmu yana tsayi guda,duk da haka bai É—aga ido ya kalleni ba,sai karatu dayake yi idonsa akan littafin,nasan ba komai yake karantawa ba,koma yana karatun bai zama lallai yagane mai yake ciki ba. 

 

"Hammar! Hammar dan Allah ka kalleni kayimin magana,fushinka yana saka zuciya ta yin nauyi,wlh ba abinda kake tunani bane,ko kaÉ—an taya zan amince da abinda yakemin,sanin kanka ne ba haka nake ba,kawai akwai fifikon matsayi a lamarin wanda babu yanda na iya a ciki" 

 

Har sannan bayyi magana ba,har na cire rai dazai kulani sai kuma naga ya É—ago idanuwansa ya zubemin,godiya ga Allah nayi ganin tafasar da sukeyi É—azu babu sun lafa. 

 

(Hammar) 

 

ÆŠaga ido nayi na kalli Æ™ananun labbanta wanda suke furta kowanne harafi na sunana daidai yanda ya dace,idan ba a cikin shauÆ™i nake ba da sainace ban taba sauraren wanda ya furta suna na daidai ba irinta,a lokacin data shigo É—akin zuciyata tafasa takeyi tamkar zata tsaga cikin Æ™irjina ta fito,amma sautin muryarta daya ambaci sunana yana dukan dodon kunnena na nemi duk wani yanayi danake ciki narasa. Tabbas abinda yafaru ba laifinta bane,amma bacin rai da abinda nakeji yahana na kalli hakan. Tunda na shigo kallon littafi kawai nake,amma zuciyata Æ™unshe take da tunanin neman mafita saboda kar wannan lamarin yasake faruwa,gani nake idan ya faru bazan iya jurewa ba. Bakomai ne yake rururi a cikin kunnena ba sai furucinta na karshe,wanda take cewa ita baiwa ce,zai iya siyanta sannan yayi yanda yaga dama da ita,saboda shi mai mulkine kuma mai iko. Idan hakan tafaru kenan dukkan wasu mafarkai datake Æ™okarin cimma sun rushe kenan, har yanzu ban yarda abinda nakeji a gameda ita so bane,gani nake tamkar tausayinta nakeji, sannan kasancewar ban saba kallon baiwa mai Æ™oÆ™arin cimma manufofi irinta ba da kuma É—auke da É—umbin baiwa sai hakan yafara burgeni nakejin tana bani sha'awa saboda yanda take tafiyar da lammuranta. Idan kuwa hakane bazan taba barin wancan sokon ya durÆ™ushe wannan jaririyar fulawar ba wacce take Æ™oÆ™arin wajen ganin tazama É—a wanda za'a ci kuma a amfana....... 

 

"Tunanin mai kakeyi ne Hammar lafiyanka tun É—azu ka Æ™uramin ido baka ko Æ™iftawa sosai,kodai ciwonne kai ka faÉ—amin baka jin daÉ—i ne?" 

 

Jijjiga mata kai nayi tareda sake mata guntun murmushi,gaba É—aya fuskartata dariya take bani,kuma yana min daÉ—in sosai idan naga damuwa Æ™arara a fuskarta na nuna kulawa akaina,sai ta dunga yin tamkar uwa taga É—anta a halin rashin lafiya. GabaÉ—aya Æ™yaÆ™yÆ™yawar zuciyarta bata dace data marar Æ´an ci ba,wacce za'a dunga cutarwa a kodayaushe,ta dacene da zama sarauniya kuma jagora ga É—umbin al'umma,to amma taya hakan zai yiwu,kaman kiyashi É—ayane yace zai É—aga damin kara,koda nafara saka sha'awar yiwuwar hakan nasan bazai taba yiwuwa ba,saidai in wani tsananin ikon Allahn. Hannunta na naji akan Æ™irjina da kuma wannan sanyin dayake kaimin ziyara a duk lokacin dana saka hannunta a Æ™irjina shi nasake ji wannan karon. Bansan lokacin dana lumshe ido ba inajin nutsuwa a cikin zuciyata.  

 

"Hammar wai lafiyanka kuwa,idan bakada lafiya dan Allah ka sanar dani kaji,wai tukunna ma ko maganinka ya Æ™are kai,idan yaÆ™are ka faÉ—amin,zuciyarka har yanzu da rauni a cikinta" 

 

BuÉ—e idona nayi tareda zare hannunta akan Æ™irjina,tunawa da nayi ita É—in ba baiwata bace dan haka bata Æ™arÆ™ashin ikon mallakata,idan ita a matsayin mai Jinya take tabani ni bai kamata nabari hakan yana faruwa ba tunda na san bana cikin halin ciwo a yanzun. 

 

"Ni lafiyata Æ™alau babu abinda yasameni,sannan ki daina wannan bada haÆ™urin haka ya wuce,amma karki sake bari hakan tasake faruwa,kiyi koÆ™arin wajen bin duk wata hanya da zaki ga baku haÉ—u ba,harsu gama abinda zasuyi su tafi" 

 

"ÆŠaga kai tayi tana share É—an guntun hawayen daya taru a idonta, lokaci É—aya kuma hankalin ya tafi kan littafin dayake gabana,uhmm wai wannan ina zata jene da neman sani,idan taga littafi kamar takalli gasasshiyar kaza. 

 

Can kuma kaman an tsikare ta ta É—ago ido takalleni,wannan kallon tayimin wanda nasaba ganinsa idan zata nemi wani abu a wajena ko kuma tanason nayi abinda banyi niyya ba. 

 

"Hammar, Yah hammarrrr!!" 

 

Juya ido nayi cikeda nuna tafaÉ—i kawai mai take so,murmushi tayi wanda yasaka gefen kumatunta lotsawa,kuma hakan yasa na kasa É—auke idona daga kai. 

 

"Uhm nace ba,dan Allah wani littafi nake nema,kuma yana sashen babban É—akin karatu,shine nake neman taimakonka dan Allah,yaÆ™unshi abinda yashafi ilimin jijiyoyin jikin É—an adam,to ina ganin baxan rasa samun abinda nake nema ba,kaga kaima zai maka amfani idan na samu" 

 

"Kedai faÉ—i kanki tsaye kice matar wancan mutumin daya gama ci miki mutunci zaki taimaka,ai naji labarin inda kika je nake ta nemanki. Wani lokaci saina kasa gane anya da akwai zuciya ma a Æ™irjinki,duk inda ba'a ganin darajarki kinfi shiga wajen da alama"  

 

Wani murmushi tayi wanda duk mai yinsa to yagaza samun kalmar dazayyi maka amfani da ita wajen faÉ—in bazaka gane halinda yake ciki ba. 

 

"Akwai zuciya a Æ™irjina Hammar,zuciyar da take jin zafin kasancewarta a ruwan rijiya maimakon na kogi,idan tana son cika muradinta kuwa na shiga ruwan kogi to ya zame mata tilas karta damu da duk wani yanka da Æ™arfen guga yakeyi mata,ko yaushe idan taga an zuro dole take kanta ta jure duk wani yanka,da haka har tayi Sa'ar samun mai É—agata ya fiddata" 

 

Hmmm joda badai magana ba,maimakon ta faÉ—amin dalilinta kai tsaye shine ta tsaya bani wani labarin guga da rijiya da kogi,wato dan dole na sarara mata,nasan idan nace ban gane ba tsaf gaba zata kawomin labarin kwaÉ—o da maciji ma. 

 

"Shikenan to naji zabiya mai iya magana,da daddare zanje wajen Shugaban makarantar zamuyi magana dashi,inyaso saiki bimu idan mukaje zan rokeshi alfarmar zaki shiga É—akin karatu,saiki duba abinda zaki duba kafin mu taho" 

 

Wani farinciki ne ya bayyana a fuskarta,lokaci É—aya kuwa tafara jijjiga kai tana dariya tareda jeromin godiya da neman Æ™arin lafiya,na saba hakan takeyi a duk lokacin danayi mata wani abun farinciki. Nasaba kallon mutane suna yimin godiya da nuna farinciki idan nayi musu abu,amma ban taba ganin wanda yayi godiyar domin Allah ba irinta. A haka ta cigaba dayin wasu abubuwan ina shagala da kallonta har lokaci yaja bansani ba. 

 

Tun kafin ayi sallahr isha na tsinkayo muryarta suna magana da Fasih,nasan bazai wuce tazo da wurine kar mu tafi babu ita, ban fita wajen ba ina nan zaune akan Buzu ina wuridi saidai É—ayan kunnena yana waje inda nake jiyo muryarta. Ni kaÉ—ai ina murmushi kamar tababbe,Joda akwai surutu,bakinta ko kaÉ—an baya gajiya idan ta zauna wajen yiwa mutum bayani abubuwan dayake jagaye dashi. Sannan bayaninnata akwai kama zuciya, saikaji tamkar wata Æ™ugiya akan harshenta ta kama ranka ka shagalta da jin bayaninnata. Nasan nima ba komai ne yakama raina gareta ba illah hakan. Tunda nake ban taba fita daga nahiyarmu da niyyar wani abu ba bayan yaÆ™i. Lokacin da labarin tafiyar ya riskeni ji nayi akam an jefamin wani Æ™aton dutse akan fuskata, Saboda É—auka da nake me zan gani wani waje wanda zai ja hankali na bayan wanda nake zagaye dashi nake kallo. Ni mutum ne da bai yarda da kowaba sai tsirarun mutane,ban taba sanin bayi wasu cikakkun mutane bane masu hankali ta har za'a samu wanda zai É—au hankalina a cikinsu. HaÆ™iÆ™a yanzu na yarda É—an adam yana sauyawa idan ya sanja waje. Domin gashi nagani a kan kaina,na tabbata idan aka nunawa Joda yanda nake a zahirin asalina bazata taba cewa mutum É—aya bane.  <…