14
Chapter 14
Washe gari.
Nazli ce zaune a baranda tana wasa da maficin hannunta lokaci zuwa lokaci ta ke ɗaga kai tana kallon mai Koko da ke shiryawa a ɗaki da alamu fita za ta yi, kamar ba za ta yi magana ba amma sai ta kasa hakuri ta ɗago ta kalli ta a karo na ba adadi ta ce. "Mmm ...mai Ko––– Sai kuma ta dakata, sam sai ta ji nauyin ƙiran ta da mai Koko kamar yadda kowa ke ƙiran ta sunan ya yi mata nauyi a baki, girman ta da darajarta da ƙima a gurin ta ya fi ƙarfin ta ƙira ta da wannan sunan. Domin yanzu matsayin uwa take a gurin ta bayan tarin alkairan ta a gare ta ta fi ƙarfin haka a wajen ta, idan wasu za su iya ƙiran ta da hakan ita ba za ta iya ba.
Ta sunne kai ƙasa cikin raɗa ta ce. "Ammie fita za ki yi." Ba mai Koko ba har ita sai da ta ji bambarakwa da sunan da ta ƙirawo ta da shi, nevertheless shi ne sunan da ya kwanta mata da kuma jin ya dace ta ƙira ta da shi don yanzu a matsyin Mama take a wurin ta. Mai Koko da ke gyara zaman hijabinta tana shirin fita ya sa ta tsaya cak da abin da take, daga cikin madubin dakin da ke kallon ƙofa wanda hakan ya bata damar kallon ta.
Sosai sunan ya dake ta, tunda ta ke ba wanda ya taɓa ƙiran ta da sunan kowa da mai Koko ya san ta daga yara har manya da sunan suke ƙiran ta, Allah kuma bai bata haihuwa ba bare ta samu wanda zai ƙira ta da sunan Mama sai gashi yau an samu wanda ya ƙira ta da sunan mahaifiya. Idanunta ne suka ciko da kwalla ta yi saurin saka hannu ta goge cikin dai daita muryarta ta ce. "Eh 'yar nan kasuwa zan tafi na samu mana kayan gida da kayan kasuwa, zama haka nan bashi da daɗi gwara da daɗi ba daɗi dai kana samun dan sisi da kabon ka ya fi zaman banza nan."
Nazli ta gyada mata kai cikin fahimta. "To na biki mu tafi tare?" Ta tambaya. "A'a ki yi zaman ki ke da lafiyar ma bata ishe ki ba ina ke Ina zuwa kasuwa, ki bari idan kin samu kawarin jiki kin warware sai ki bini tun da kullum muke hanyar zuwa kasuwar wataran ma da kanki za ki na je mana kasuwa kina yo mana cafane."
Ta faɗa hakan daidai sanda ta fito ta buɗe purse ɗinta ta cire naira ɗari ta miƙa ma Nazli. "Ga wannan ki riƙe a hannunki ko za ki ga wani abun ran ki ya biya.ki siya." Hannu biyu Nazli ta sa ta amshi kuɗin tare da yin godiya tana mamakin yanzu wannan sai ya siya wani abun? ta kada kai cikin mamakin da bai gama sakin ta ba tunda ta tako ta shigo anguwar duk motsi sai ta ga abin da ke ƙara bata mamaki cikin wannan sabuwar rayuwa.
"To ni na tafi sai na dawo ba zan daɗe ba da na gama siyayyan abin da ya kaini zan dawo, ki kular mana da gida sai na dawo." "To Ammie a dawo lafiya." Ta miƙe ta raka ta har ƙaramar ƙofar su kana ta koma ciki.
~~~~~~
Mai Koko na fita ta tsaya gaisawa da matan gida, ta kalli Maman Sadiq da ke suyan awara ta ce. "Maman Sadiq idan an gama suya a saka mana muma a ba yara su kai." Ta amsa da to hankalin ta na kan suya. Amarya da ke wanki a ƙasan rijiya ta ce. " Baba ina baƙuwar ta mu ce ko tana ciki?" "Ehh." Ta amsa a taƙaice cikin rashin son jan maganar. "Mai Koko kasuwa za a tafi kenan?" Cewar Maman Khadija da ke na ta baranda tana daura kayan miya. "Ehh zama haka ai ba zai yu ba gwara a koma sana'a." "Ki ce gobe da akwai Koko." "In sha Allah." Cewar mai Koko tare da mikawa Maman Sadiq kuɗin awarar ta ta juya ta fita.
Maman Sadiq na gama suya ta zuba na mai Koko cikin plate ta rufe ta aje a gefe saboda lokacin yara basa nan suna makaranta, bayan ta gama tana shirin kai awarar da kanta yar tallan ta ta zo. Hakan ya sa ta bata ta kai ma Nazli kamar yadda Mai Koko ta buƙata.
=========
Nazli na kwance a ɗaki tana abin da ta saba wato tunani ta ji sallama a waje, tashi ta yi ta fita inda ta samu yarinyar tsaye a tsakar gidan. "Gashi wai na kawo." okay kawai ta ce ta ƙarbi awarar ta koma ciki ta a je a gefe, da yunwa ya kama ta fito kitchen ta zuba jollof din macaroni da Ammie ta dafa kafin tafiyar ta ta zauna ta ci ta wanke kwanon ta maida kitchen ta a je.
Tana zaune ta ji sallamar Ammie na shigowa, da saurin ta ta miƙe ta ƙarbi kayan hannunta tana mata sannu da zuwa, Ammie ta nemi wuri ta zauna cikin sauke haki saboda ba laifi ta kwaso rana ga gajiya. Nazli ta mika mata ruwa mai sanyi daga randa ta sha kana ta kawo mata abinci. Sai da Ammie ta huta ta ci abinci ta yi sallah kafin ta soma buɗe kayan da ta shigo da ta su, kayan masurufe ne da ya danganci Wake da su gero kayan ƙamshi. Sai kuma kayan miya na su na gida.
======
Sai da dare ya yi suna cikin cin abinci ta tuno da awarar ɗazu da a ka kawo, tashi ta yi ta ɗauko ta kawowa Ammie da ke kallon ta da mamaki a fuskarta. "To ai dan ke na sa a kawo miki shi ne baki ci ba?" Ammie ta tambaya, ita dai Nazli bata yi magana ba ta nemi wuri ta zauna ta koma cin tuwon ta. Ammie ta girgiza kai kawai tare da tura mata awarar gaban ta da fadin. "To na ki ne ni bana cin awara." Da kamar Nazli ta ce wani abu sai ta yi shiru ta jawo plate ta samo cin awarar ding da ta yi sanyi hakan bai sa bata mata daɗe ba a baki musamman da kasance da yajin ta.
"Nan gaba idan irin haka ta faru ba sai kin jira ni ba idan ma ba za ki iya cinyewa ba sai ki ɗibi iya wanda zai miki ki bar saura, ya fi da ki bar abu haka an kawo abu maimakon ki ci ki ka matsalar gefe kin zuba masa ido hakan sam bai yi ba. Na fada miki ki ɗauka nan gidan ku ne karki ji kunya ko shayin komai dan ban dauke ki bare ba sai kallon 'ya da nake miki, dan ma wannan ba abun da zai ɓace da wuri bane da sai dai a yi hasarar sa a banza ba a ci ba."
"To Ammie ki yi haƙuri zan gyara." Ta faɗa a sanyaye cikin ƙoƙarin ta na hana kwallar da ta cika mata ido ta hana su zubowa, tunowa da yanzu fa bata da kowa sai Ammie.
~~~~~
Washe gari da asuba bayan sun yi sallah Nazli ta koma bacci, Ammie kuwa bata koma bacci ba ta tashi ta soma shirye shiryen gabatar da sana'ar ta. Da wake ta fara inda ta ciƙa ta wanke kana ta koma ta hura wutar icce ta ɗaura babbar tukunya da ruwa a ciki kana ta fita kai nikan wake.
Minti ashirin ta dawo lokacin ruwan har ya tafasa nan ta haɗa kunun Koko cikin babban bokitin kafilas kafin ta ɗaura man tuya a wuta ta soma shirin tuyar ƙosai. Lokacin gari har ya gama wayewa nan jama'a suka soma rubbing shigowa a na biɗar koko da kosai.
Nazli ba ita ta farka daga bacci ba sai tara saura, lokacin rana ta fito Ammie kuwa na ciniki cikin zafi zafi Nazli ta fito tana miƙa. Turus ta yi ta tsaya tana kallon Ammie da ke sallamar jama'a, ita shap ta manta da yau Ammie za ta koma sana'a ai da ko aike ta taya ta da shi amma ta tsaya can tana baccin hasara ita ma bata tashe ta ba. Ganin tsayuwar ba za ta fidda ta ba ya sa ta koma ciki ta ɗaura kallafi ta fito ta wanke fuskarta kana ta nufi Ammie tana gaishe ta, murmshi Ammie ta yi ta ɗago ta dube ta da faɗin. "Kin tashi kenan." "Ehh Ammie sannu da aiki." Ta faɗa cikin ɗan jin kunya, hankalin Ammie na kan juya kosai ta amsa da. "shiga kitchen ki ɗauko plate da cup zo ki zuba je ki karya" to shi ne abin da ta faɗa ta miƙe ta nufi kitchen domin ɗauko cup.
Ta zuba iya cinta ta koma ɗaki, a hankali take ci tana yaba ƙosan da kunun dan daɗe. Nadiya ce ta faɗo mata a rai ta tuna yadda take matukar son kosai yana daga cikin abincin da take matukar so, za ta iya cewa ita ta koya mata cin kosai da ma wasu cimar. Ko ya take yanzu? Tana gidansu ne ko ta koma wurin Mamanta, sanin cewa basu jituwa da Neesah dama dai ita ke tare mata idan Neesah ke mata wasu abubuwan yanzu da bata nan kuma bata san ya take copying da bata na.
Jin mood ɗinta na neman ɓaci ya sa ta saurin kawar da tunanin su ta maida hankali ga abincin da ke gabanta, tana gamawa ta kai plate kitchen kana ta koma tattara ɗaki ta share ta fito kitchen ta haɗa wanke wanke ta yi kana ta fito wajen Ammie tana ganin yadda ta ke tafiyar da abun komai yadda take jefa ƙosan da yadda take sallamar mutane.
======
Wasa wasa Nazli ta yi wata biyu a gidan, tun tana ɗare–ɗare har ta saki jiki tana harkokin ta kamar yar gidan. Ta saba da jama'ar gidan ma sosai idan bata komai ta kan fitowa waje a na hira da ita, sannu sannu har ƴan anguwa ɗai–ɗaiku sun santa masu shigowa gidan, tsakanin ta da Ammie kuwa shaƙuwa mai ƙarfi ce ta shiga tsakanin su idan ka gansu yadda ka san 'ya da uwa haka suke, well haka kowa ya ɗauka da kowa ya tambaya sai ta ce yar Yayan ta ne da ke ƙasar Ghana mijinta ya rasu shi ya sa ta zo wurin ta da zama.
Ba abin da ta nema ta rasa idan dai bai ƙarfin ba Ammie na ƙoƙarin yi mata shi duk da ita dai bata buɗan baki ta ce tana son abu ba sai dai Ammie ce take ganin dacewar abu ta yi mata, Ammie ta yi wa dallali ta samar mata gwanjo da za ta samu na canzawa kana ta siya mata sabbin atampopi har kala hudu ta bada a ka mata ɗikunan zamani ta haɗa mata hijabai da mayafi biyu, sosai Ammie ke kokari a kanta yadda ka san yar cikin ta haka take mata komai tsakani da Allah, don ba ƙaramin jin daɗin zama da Nazli take ba kuma yanzu tana jin komai ta samu dan ita ne yadda ita ma take bata da kowa to haka ta riƙe Nazli na ta.
Cikin ƙanƙanin lokaci rayuwar Nazli ta canza ta tashi daga wancan Nazli yar gata da gayu ƙwalisa ta koma Nazlin Ammie kamar yadda kowa ke ƙiran ta. wannan gayu da izza da ƙasaita na nan bai je ko ina ba, sai da ta dishe da yar rama wacce bata rabo da tunani da ta saka a gaba.
Bangaren sana'ar su kuwa yanzu tare suke Ammie na tuya ita kuma na sallamar jama'a, sosai ta maida hankali kan rayuwarta ta yanzu tana kuma dukkan mai wuya na cire damuwa da tunani a ranta sai dai wani lokacin ita kanta bata sanin lokacin yin su.
A yanzu damuwarta ɗaya ce zaman ta a haka nan babu karatu zaune haka take kurum komai sai dai Ammie ta mata, gaba ɗaya nauyin ta da ɗawainiyyar na kan Ammie da ita ma ba wani ƙarfin ne da ita ba, bata jin daɗin haka ta so a ce tana wani abu ko dan ragewa Ammie wani abun. Duk da tana taimakawa wurin sana'ar kokon su amma tana son yin wani ko kaɗan ne tana supporting da wani abu a cikin gida.
Sai dai duk yadda ta yi tunani bata san mafita ba, ita bata gama karatu ba sai next year a ke sa ran za ta yi graduating balle a yi maganar samun aiki, kuma a yadda take nan babu wasu takardun makaranta wa ma zai bata aiki kuma koda za ta samu wani irin aike za ta samu duk da bata tunanin za'a samu ɗin.
Amma abun na damunta sosai, da shi take kwana take tashi hankalinta kuma ba zo kan fara sana'a ba kawai aiki shi ne ta saka a rai kuma take tunanin idan an yi dace ta samu position mai kyau to zasu samu sauƙin rayuwa.