12
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_
*Na*
*AISHA ALTO*
*JAMILA UMAR(Janafty)*
*HIJABS CORNER BY JANAFTY*
*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design, muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*
*BABI NA GOMA SHA BIYU*
Da mamaki Likitan ke binsu da kallo, Tun ma Ba Mufeeda ba Wacce Taji Zuciyarta da Jikinta Sun Tsinke Gaba ɗaya, Hannunta Bisa kai Hawaye na Zubo mata Take Faɗin "Na Shiga uku Likita Ni keda Ciki...? Wani Haushi ya kama Farida mai Haɗe da tsantsar baƙin ciki, Cikin Zafin Nama Ta Saka Hannu Ta Kwaɓe mata baki Sai da Jini ya Fito Cikin Taruwan Hawaye tace "Eh Ciki don Ubanki Ai ba ƙarya yayi miki ba, Dama munga Alamu, Son Tabbatarwa ne, kuma yanzu Mun Tabbatar, kin Cucemu Mufeeda Kuma kema kin Cuci kanki..." Ta faɗa Hawayenta Suna Zubowa Lokaci Ɗaya Ta Miƙe Kafin Ta Sanya Hannu Tana Ɗauke Hawayenta Take Faɗin "Mun Gode Dr..." Daga Haka ta Finciki Hannun Mufeeda Dake Kuka Suka Fice Daga Office D'in Kamar Walkiya, Da Ido Likitan ya bisu Abun ya matuƙar Ɗaure mai kai yaran da basu Fita Taya Wannan Abun Zai Kasance.
Suna Fitowa Iya Ta Miƙe ko bata Tambaya ba ganin Yadda Idanuwan Farida Suka kaɗa Sukayi Jajir, ga Mufeeda na Kuka Wurjanjan Ta samu Amsarta Shiyasa bata Tsaya Tambaya ba Sai ma bin bayan Farida Datayi Wacce Ta Saki Hannun Mufeeda Tayi gaba Zuciyarta na Ta fasa da Fargaban Wani bayani Zatama goggo Abu..? Mezatace da Mahaifiyar Mufeeda..? Uwa uba Kuma Tahir Wanda Amanar Mufeeda Ya Damƙashi Ahannunta ya kuma ce Ta Kula da Ita Tamkar yadda Zata Kula dasu Basma..? Abunda yafi Ɗaure mata kai da bata mamaki Wayayi ma Mufeeda Ciki..? Yarinyar da babu Inda Take Zuwa Daga Makaranta sai makaranta kuma Makarantan ma Akaisu Adawo Dasu..? Kai Wannan Al'amari Akwai Ɗaure kai.
Ko Acikin Adaidaita Mufeeda Keta Gunjin Kuka Farida da Iya Kuwa Suka mata banza Kowa na Saka Abubuwan Mamaki Acikin Zuciyarsa Ita Farida Baƙin Ciki ne da Kuma Kunyar Wani bayani Zatama Su Goggo Abu Akan Wannan Baƙin Labarin, ita kuma Mufeeda Kuka take Wanda Ta rasa Dalilinshi Sai Da Akace Tana da Ciki Ta Tuna Malamin Islamiyansu ya sanar Dasu Duk macen Data Fara Jinin Al'ada Akayi Abunda Tahir Daddy yayi Da Ita To Zata iya Samun Ciki, ƙananun Shekarunta bai bata Damar Fahimtar Cewa Akwai Rana mai kama Data yau ba, Kuka Take na Baƙin ciki Bakinta bazai iya Taɓa Furta Wanda ya Aikata haka gareta ba Domin Tayi Alkawarin Ko Za'a Kasheta sai ta Rufama Daddy Asiri Domin Shima ya Rufa mata Asiri Lokacin Da bata da Kowa.
Ita ko iya Cikin Ranta Salati kawai Take, Tana Kuma Hasashe da Tunanin Waye yayi ma Mufeeda Ciki, ita bata ma kai da Nisa ba Tunani Take ko Garzali ne..? Ko maigadi ne..? Domin Iya saninta Gidan Tahir gida ne na Tsaro da Tsantsar Tarbiya, Amma Kuma Taya Hakan Ta kasance..? A iya saninta bata san Mufeeda da Wani Halin banza ba, bata da Saurayi ko Wata Ƙawar Banza Wanda Zai Nuna Alamun Hakan Zai iya Faruwa..? Kai Wannan Abu da Ban Mamaki yake.
Suna gab da Isowa gida Wayar Farida ta fara ƙara Tana Dubawa Taga Tahir ne sai taƙi Ɗaga Kiran Don bata da Abunda Zata iya Sanar Dashi Adaidai Wannan Lokacin Zuciyarta bata da Ƙwarin Gwiwa, suna Dawowa gidan Suka Iske Su Basma Sun Dawo Daga Islamiya Nan Suke Shaidama Farida Daddy ya Dawo Megadi ke sanar Dasu Sun Tafi Asibiti Shine yayi Ta Kiranta bata Ɗaga ba Sun Tafi masallaci Shida Muda da Bassam, Farida batayi magana ba Illah Hayewa Sama Datayi, Ranta Duk ba Daɗi Itama Iya Ɗakinta ta Shiga Tana Sauke Naila Data Farka Mufeeda ko Tana Kuka ta Nufi Ɗakinta Laila da Basma Suka bita Suna Tambayanta Ko lafiya Da ƙyar Ta Iya Cemusu batajin Daɗi ne, Basma tace "Oh dama ke Momy Taje kaiwa Asibiti? Sannu Allah ya baki lafiya" Nan Laila Itama ta mata Sannu Daga nan Suka Fice Daga Ɗakin Suna masu Tausaya mata ganin Kukan Datake Su Azatonsu Ko Ciwon nata yayi Zafi Shiyasa Take Kuka.
Farida ko Da ƙyar ta iya Shiga Toilet ɗinta ta Ɗauro Alwala tazo ta kabarta sallar Magriba ta Idar Kenan Tana Zaune Ta Ƙurama Saitin Makeken Gadonta Ido zuciyarta ba Daɗi Kamar mai Nazarin Wani Abu Amma Azahirin Gaskiya Tunanin Mafita Takeyi, Bata ji Shigowar Tahir ba sai da Taji Tattausan Hannunshi Akan Fuskarta yana Shafa Kumatunta Firgigit ta Dawo Cikin hayyacinta, Ta Ɗago Tana kallonshi Shima kallonta yake Cikin Mamaki yace "Lafiya..? Meyake Faruwa Ki kai nisan Tunani Haka.? Waye ba lafiya mun Dawo Kuna Asibiti..?"
Miyau Farida Ta Haɗiye mai Ɗaci Kafin Ta Tattaro Murmushin Yaƙe Tace "Amh..Umh...ba komai..." Ta faɗa Muryanta na Rawa Kamar zata Fashe da Kuka Tana Tunanin In Tahir yaji labari Ita Zai Ɗorama laifi yace Duk da Laifinta bata Son Zaman Gida Balle ta Fahimci Wani Hali yaran Ke Ciki.
Wani kallo ya mata kafin yace "Ban gane ba komai ba Farida? kinga idonki kuwa..? Kuka kikayi ko menene..? Kuma baki bani Amsa ba Waye ba lafiya Kuka Tafi ganin Likita..?" Ajiyar Zuciya Ta Sauke Kafin Ta Yunƙura Ta Miƙe Tana Zame Hannunta dake Cikin na Tahir Hijabin Jikinta ta Cire Tana Ƙoƙarin Isa gaban Makeken Wardrope Ɗinta Take Faɗin "Mufeeda ce take Fama da Zazzaɓi Tun Jiya Shine mukaje da Ita Taga Likita."
Lokacin da Farida Ta Ambaci Mufeeda sai da gaban Tahir ya faɗi, Haka yake Fama Da Faɗuwar Gaba Kwanan nan Duk Sanda Zaiga Mufeeda Ko Kuma yaji Muryanta ko Wani ya Ambaci Sunanta, Toh Hakan sai ya faru yanzu ma Tunaninsa bai taɓa bashi Ciki Mufeeda ke dashi ba Shiyace yace "Tun Jiya kuma..? Shine sai yau zata ganin Likita..?" Ya faɗa Cike da Nuna Kulawa, Farida na Maida Hijabinta Cikin Durowarta Tace "Kasanta da Nuƙu Nuƙu bata Sanar ma Kowa ba Nima Ɗazu ne Iya ke Sanar Dani Ko Islamiya ta kasa Zuwa.."
Numfashi ya Sauke kafin yace "Naji yanzu me Likitan yace..? Ya jikin Nata..?" Kamar tayi Ihu Da Tambayoyin Tahir Amma Sai ta kanne Cikin Sanyin Murya tace "Taji Sauƙi Zazzaɓi ne ya Dubata ya bata magunguna.." Kai Tsaye yace mata "Wani Dr Kuka gani..?" Gabanta na Faɗi bata juyo ba Saboda Kada ya Fahimci Halin Datake Ciki Tace "Dr Salis ne..." Miƙewa yayi yana Faɗin "Ok yayi kyau Zan kirasa Zamu yi magana." Ya faɗa yana Ƙoƙarin Ficewa Daga Ɗakin.
Zuciyar Farida na Lugude Ta Waigo Da Sauri bakinta na Rawa Tace "A'ah...Ka..karka kirashi Bafa Komai Abban Basma Zazzaɓi ne Kuma ya bata magaunguna." Ta faɗa Zufa na Ketomata Saboda bata Shirya Tahir yaji maganar nan kai Tsaye ba, Tsam yayi yana Binta da Kallo Cikin Mamakinta yace "Shikenan.." Ya faɗa yana ƙara Karantar Yanayinta, ganin Haka yasa Ta saki Dariyan yaƙe Kamar Wata Sakarya bai ƙara magana ba Ya sakai ya fice yana Girgiza kai,Tana ganin ya Rufo mata Ƙofa ta Saki Ajiyar Zuciya haɗe da Sauke Numfashi Lokaci Ɗaya.
Bayan Fitarshi Falon Ƙasa ya sauko yaso ya Shiga Ɗakin Mufeeda, Yaga Jikinta Amma Sai ya samu Wayar Ishaq akan yana Haraban Gidanshi ya Fito Su Tattauna nan ya fice Suna magana kan Wasu Sabbin Motoci ne da zasu zo Daga Kwatono gobe Sun Ɗauki Lokaci mai Tsawo kafin Su Rabu Wanda yayi Ya Shiga Su gaisa da Farida Amma yaƙi yace Dare yayi Dole ya Ƙyaleshi Suka Rabu Akan Sai gobe in Sun Haɗu A office, koda ya Shigo Falon ba Kowa Su Basma da Bassam Har Sunyi Dinner ɗinsu Sun Shige Ɗakunansu, Kan Teburin ya Nufa yaja Kujera ya Zauna yana Murmushi Shi kaɗai ganin Tuwon Shinkafa miyar Kuɓewa Ce Ɗanya Yana Son Abincin Sosai bai Damu da Cin Abincin dasu Basma Sukayi ba Tunda Shi ya Saka Dokar Daga yanzu Adaina Jiransa Sai yazo Kana Ayi Dinner, nan ya Zauna yaci Tuwon Sosai bayan ya gama ganin Dare Yayi sai ya Haƙura da Shiga Wajen Mufeeda ya barshi Sai da Safe, alokacin Kuma Daya Shiga Zai Isketa ne Tana Kuka.
Farida Kuwa Lokacin da Tahir ya Fita ta Daɗe Zaune Tana Tunanin Mafita, kafin Ta Janyo Waya Ta Kira Goggo Abu bayan Goggo Abu Ta Ɗauka Sun gaisa Kawai sai Farida ta Fashe Mata Da Kuka Nan Hankalin Goggo Abu ya Tashi nan da nan Ta Shiga Tambayanta A ruɗe Akan Abunda ke Faruwa, cikin Kuka Farida ke Zayyanama Goggo Abu komai game da Abunda Likita yace na Mufeeda Nada ciki, Wani Razana Goggo Abu Tayi Tana Kan Gadonta ne sai da ta Wuntsulo Ƙasa Saboda Razana da Maganar Farida Innalillahi Kawai Take Maimatawa kafin Ta samu Zarafin Magana Farida ta kwaso Rantsuwan basu san Wanda ya Aikatama Mufeedan Haka ba, Goggo Abu na Share Zufa tace "Farida Ita Mufeeda bata Faɗi Wanda ya yi mata Cikin ba? Na shiga Uku ni Zainabu Abu Mezan cema Uwar yarinyar nan..? Ta faɗa Tana Sharɓe Kwallah.
Farida tace "Ban Tambayeta ba Goggo Na shiga Ruɗani bana So Tahir ya Fahimci komai goggo laifina Zai gani.." Goggo Abu Tace "Wannan ba Hujja bane Farida Ya zama Dole Tahir ya sani, Babu yadda zamuyi Farida Dole maganar nan Zata Shiga Kunnan Waɗanda ya kamata, yanzu zan Shiga Wajen Hakimi mu Tattauna gobe in Allah ya Kawomu zan ma Tahir Waya ya Turo Direbansa ya Ɗauko mu Nida Hakimi da Ita Fulera ɗin sai Asan Abun yi..." Farida ta saka Kuka Tana Faɗin "Wayyo Goggo nasan Laifina za'a gani Amma ko Shegiyar yarinyar nan Ta Cucemu.." Goggo Abu Tace "Ba kaɗan ba Farida bar Kuka Gobe in Allah ya kaimu zatayi bayani Don Ubanta.." Daga Haka Suka Rabu bayan Goggo Ta Jaddada mata Gobe Suna Tafe.
Daga nan Zuciyarta taƙi NaTsuwa, Sai kawai ta Latso Nombar Umma Kano Ta Ɗauka Kenan Kafin Tayi magana Farida ta Sanya mata kuka Hankalinta Tashe Take Tambayanta lafiya...? Farida ta Buɗe baki Zatayi mgana sai Wayarta ta Ɗauke Ɗif ba Chaji Taji Haushi Sosai taso ta sanarma Umma Halin Da'ake Ciki, Da hanzari ta tashi ta Jona Chaji sai ta Sha'afa bata Kunna Wayar ba Ita Kuma Umma Daga chan ɓangaren Tayi Ta Neman Farida bata samu ba, Ta maida Akalan Kiranta kan Tahir Shima kamar Haɗin baki bata Sameshi ba Ashe ya sanya Wayarsa A Fligt mode bai sani ba, Hankalinta a tashe ta samu Abba Tana gaya mai Shima Ya shiga Ruɗu Amma sai ya lallashi Umma da cewa Gobe in Allah ya yarda sai Su Tafi Kadunan Tare Shima Dama Zai je Saboda Zuwan Sabbin Motocin nan, Da Haka Umma ta Ɗan Saki Amma Ranta ba Daɗi Jin Kukan Farida Tana Fatan Allah yasa Lafiya.
Shiko Tahir Daga nan Ɗakin Farida ya Nufa, Farida na Zaune gefen Gado Sanye da kayan Barci masu Taushi Tana Jin Motsin Tahir ta Sulale Bisa Gado Taja Bargo Ta Rufe Jikinta Lokaci Ɗaya Tana Kulle Idanuwanta, yana Shigowa ya Ƙaraso bakin gadon yana Kallonta ganin kamar Tana barci ne sai bai Tasheta ba Illah Ranƙwafawa Dayayi ya Sumbaci Goshinta Kafin ya ƙara gyara mata Blanket d'in Wutar Ɗakin ya Rage ya Kunna mata Dum light, Kafin ya Fice Daga Ɗakin ya Rufo mata Ƙofa ya Nufi Bedroom ɗinsa, yana Fita ta Buɗe Ido tana Sauke Numfashi kafin Taji Kwalla Ta Cika mata Ido, Farida Nadama ta Shigeta Alokacin da Komai ya Riga ya gama Kwaɓe mata.
********
Washegari Tun Safe Tahir ya Fita Office, Saboda Bakin Da zasu zo yau ɗin Kuma Sunyi Waya da Abba Tun jiya Dama yasan Da Zuwanshi Bai Dade Da Isa Company ba Wayar Goggo Abu Ta Iskeshi Inda Tace ya Turo musu Direba Zasu Zo Ita da Hakimi da Fulera Mahaifiyar Mufeeda Abun ya bama Tahir mamaki Sosai ya Shiga Tambayan Goggo Abu Wani Abu ya Faru ne...? Amma Sai tace Kar ya Damu In Suka Zo Zaiji Komai, Abun ya bashi mamaki barin Ma Datace Harda Hakimi, wanda Hakimi baya Zuwa Kaduna sai da Ƙwaƙƙwaran Dalili Mai karfi Amma Ko Ɗaya Zuciyarsa da Tunaninsa basu kawo masa Wani Abu mara Daɗi ya Faru ba, Ya mafi karkata Alaƙan Zuwan nasu ƙila ko Farida ce Takai Ƙararshi Toh Amma Ai yanzu basu da Wata Matsala, Haka dai ya gama Duk Tunaninsa Bai Hango Dalili ba Duk da gabansa na Faɗi bai Ɗauki Abun Nada Nasaba da Haka ba.
Ita ko Goggo Abu Tun Adaren Jiya Ta Isa Turakar Hakimi ta Zayyana mai komai Salati da Sallallami Hakimi ya Shigayi Cikin Ruɗani da Tashin Hankali Sun Daɗe Suna Jajanta lamarin, har Innaro Tazo ta Samessu Itama Taji Ɗimuwa Dataji Wannan Lamarin Daya Faru Haka Suka Zauna Jugum Jugum Abun Duniya ya Ishesu, Hakimi Shi ya yanke Hukunci Kada Asanar da Fulera Abunda Ke Faruwa sai Sun Isa Kaduna Allah barshi Sai Lokacin Taji Komai, Da haka Suka Rabu Innaro Ta Koma Shashenta Ta Kwanta Cike da Mamakin Faruwar Wannan Al'amarin Hakimi da Goggo Abu Kuwa basu Runtsa ba Suna zullumi da Tunanin Yadda Mutane zasu Ɗora musu Laifin Duk Abunda ya Faru.
Garzali ya bama Umarnin ya tafi Ɗanbatta ya ɗauko su Goggo, Ya koma Office Kenan Sai ga Abba ya iso, nan yake Shaida ma Tahir Cewa Tare da Umma Suke sun ajiyeta Gidanshi Abun sai ya Ƙara Ɗaurema Tahir kai barin ma Da Abba ya Shiga Tambayanshi Duk Gidan Lafiya ba Abunda ya Faru..? Yace mai ba komai, jin Haka sai suka Watsar da Zencen Suka Cigaba da Tattauna Batun Motocin nasu da zasu iso yanzu ba da Daɗewa ba.
Umma kuwa Tana Isowa Farida na Cikin Ɗakinta bayan Su Basma Sun gama mata Oyoyo Suka gaisa da Iya, Ta Haura sama Wajen Farida Wacce Ke Kwance Tana Tunanin Mafita, Sai kawai Taji Sallamar Umma Lokaci Ɗaya Tana Kiranta Zumbur Ta Miƙe Ta Isa gareta ta Rungumeta Lokaci Ɗaya Ta Fashe da Kuka Umma Ta Fara Lallashinta Ta hanyar Bubbuga Bayanta Sai da Farida Tayi Kuka mai Isarta kana Ta Sanar da Umma Abunda Ke Faruwa.
Ƙirji Umma Ta kama Tana Salati Lokaci Ɗaya Idanuwanta Duk A Bude Tana Tsaye ne Sai Da Ta Zauna Hannunta Duka biyu Bisa kai Tana Tambayan Farida garin ya Haka ta Faru..? Farida na Kuka Take Faɗin bata sani ba Wallahi...? Nan Take Shaida mata Abunda goggo Abu Tace Suna Tafe Yau Tagumi Umma Ta Buga Ta fara ma Farida Faɗan Rashin Kula da Sakaci Metake Tunani in Itama Basma Ta faɗa irin Wannan Halin..? Tunda Da Mufeedan Da Basma duk Tare Suke Ita dai Farida Kuka Kawai Take Tana Jin Kunyar yadda Duka kowa zai Bata laifi Amma Maganar Gaskiya Mufeeda Ta Cuceta Wallahi.
Wajen 12pm na Rana Su Hakimi Suka Iso gidan Tahir Farida Ta karɓesu Hannu bibbiyu Amma Da Faɗuwar Gaba Nan Suka Iske Umma, basu yadda Sun Tada maganar ba saboda Inna Fulera Wacce Tana Zuwa 'yarta ta Fara Nema,Wacce ke Ɗaki Dunƙule Tana Kuka Lokacin Data Ci karo da Fuskar Inna Fulera sai Rauni da Kunya Suka Zomata ta ƙanƙame Innar ta ta Tana Kuka Ganin Haka sai Jikin Inna Yayi Sanyi ta Zaunar Da Ita gefen Gado Tana Tambayanta Lafiya meya ke Faruwa..?" Don Goggo Abu bata mata Wani bayani ba, ta dai ce Ta Shirya Suzo Kaduna Jin Haka Yasa Jikin Mufeeda ya fara Rawa Kamar Mazari Idonta ya fara Zubar da Kwalla, Tana Tunanin Ya Zatayi in Aka Turketa sai Ta faɗi Wanda yayi mata Cikin..? Uwa uba ga Innarta Wani Hali Zata Shiga Intaji labari..? Ƙanƙameta Innar Tayi Ita Kuma Mufeeda tana Faɗin "Inna Kiyafemin Ba Laifina bane, Jin Haka sai gaban Innar ya faɗi Ta fara Tunanin Allah yasa Ba Wani Laifi Mufeeda ta Aikata Musu mara Daɗi ba, Gashi Kuma Mufeedan Taƙi magana sam balle Taji Abunda ya Faru.
Motocin Sunzo ba Daɗewa sai ga Kiran Goggo Abu Tace maza maza Tahir yazo gida yanzu nan, Sun Iso sai Lokacin ya ƙara jin Mutuwar Jiki Sosai da Faɗuwar Gaba, jin Haka yasa Abba Shima Direba ya Wuce Dashi Shi Kuma Ishaq ya Ɗaukosa Zuwa gida Suna Tafe Suna Fatan Allah yasa Lafiya.
Lokacin da Suka iso gidan Ishaq yaso ya koma Company Sai Tahir ya Matsa mai ya Shiga Ya gaisa dasu Hakimi Suna Dumfaran Falon Suka Fara Jin Shessheƙan Kuka da Koke koke Da Hanzari Tahir ya Fara Shiga Falon Ishaq na Binsa Abaya Idanuwansa Sukayi Tozali da Mufeeda, Wacce ke Durƙushe Tsakiyar Falon Tana Gunjin Kuka ga Inna Fulera gefenta Itama Tana Kukan ga Farida Zaune A ƙasa Kusa da Goggo Abu sai Hakimi dake Zaune kan Ɗaya Daga Cikin Kujerun Falon Shida Abba, Sai iya Dake Zaune chan gefe Kowa ka kallah Fuskarsa ba Annuri.
Lokaci Ɗaya gaban Tahir ya yanke ya Faɗi Yaji Jiri na Neman Kadashi, sai da Ishaq dake bayansa ya Riƙonsa, Idanuwansa Sun Fito Waje yake bin Kowa da Kallo Kafin ya maida kallonsa kan Farida Cikin Sarkewar murya ya Furta.." Fa...Farida...Meya Ke Faruwa...?" Ya faɗa suna ƙarasowa Cikin Falon, Jin muryansa yasa Duka Ido ya koma kanshi Cikin Damuwa goggo Abu Tace "Yauwa Attahiru Dama kai muke Jira kazo ka Tambayi Mufeeda Wanda yayi mata Cikin Jikinta Tunda Dukkanmu Taƙi Sanar damu komai..."
Ba Tahir kaɗai ba Hatta Ishaq Sai da Yaji Wani Abu ya Tsirga mai Daga Kwakwalwarsa, Shiko Tahir Kwalalo Ido yayi kamar Idonshi zai Fito Waje, Mufeeda Data Ɗago Kanta Tana Kuka Idanuwanta Suka Kumbura Suka Haɗa Ido da Tahir Wanda Jikinsa Ke Rawa Zuciyarsa na Gudu Naman Jikinsa na Cida Zufa na Keto mai Cikin Wani yanayi ya Saluɓe Hannunsa ana Ishaq ya Sulale A ƙasa yana Maimata kalmar "Innalillahi Wa'inna Ilaihirraju'un"un..." Sai ga Hawaye Suna Fitowa Daga Cikin Kwarmin Idanuwansa.
Ba Wanda yayi mamakin Halin Da Tahir ya Shiga Sanin Halinsa Mai Ƙoƙarin Kyautatama Kowa, Inna Fulera tana Kuka Take Faɗin "Mufeeda Meyasa Kika min Haka..? Zuciyata ta kasa yarda da Wannan maganar ki ƙaryata ko kuma ki sanar damu Wanda Kika bama kanki yayi miki ciki.." Ta faɗa Tana Kuka Girgiza kai Mufeeda Ta Hauyi Tana Kuka Take Faɗin "Kiyi Haƙuri Inna Ba Laifina bane, Amma bazan iya Faɗar Wanda yamin Wannan Cikin ba Ko zaku Kasheni.." Ta faɗa tana kallon Tahir Wanda Ya Ɗago yana kallonta, Jin Haka yasa Inna Fulera ta Taso da Hanzari ta Isa ga Mufeeda ta Fara Dukanta ta Ko'ina Tana Faɗin "Allah ya isa Tsakanina Dake Mufeeda zan ko kasheki kowa ya Huta da Na Dinga Kallonki kina sakani Baƙin ciki da Takaichi..."
Kuka Mufeeda Keyi Inna Fulera nayi Tana dukanta Farida ma Kukan Take Kafin Wani yayi magana Tahir ya Miƙe ya isa Ga Inna Fulera ya Duƙa agabanta bayan ya Shiga Tsakaninta da Mufeeda ya kalleta yana Zubar da Hawaye, Bakinsa na Rawa zai Fara Magana Ishaq yace "Don Allah Tahir kar kace Komai na Roƙeka..." Tahir ya Runtse ido kafin yace "Kabarni na Faɗa Ishaq Gwara Kunyar Duniya Data Kiyama..." Ya faɗa Hawaye na Kwararo mai.
Gaba ɗaya Falon kallo ya Koma kan Tahir Cike da Mamaki, barin ma Farida wacce Kukan Tahir ya fara Tsorata ta, Babu Zato kawai Sukaji Tahir na Faɗin "Bazata Taɓa Faɗa muku Wanda yayi mata...don Ba kowa bane Face Ni...ni...na mata Cikin Jikinta...." Ya faɗa yana Rushewa da Kuka Numfashisa na Sama Sama, Gaba ɗaya Falon Kowa ya Kwalolo Ido, Matan Gaba ɗaya Suka Miƙe Farida Wacce Ta Ɗora Hannu Akai ta Zaro Ido Tana Faɗin "What....? Kace kai kayi mata Cikin...?"
Nanny(me reno) Free book ne amma ga waɗanda ba za su iya jira ba akwai completed documemt 1k ne ku tura ta wannan acct ɗin 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK ko tuntuɓar waɗannam lambobin ***
***.
*Aisha Alto...*
*Janafty*