Farautar Mutunci

Chapter 2

by @oumfatayat

*FARAUTAR MUTUNCI*

Marubuciya:
Na’ima Sulaiman Daƙayyawa (Oum Fataya)

Page: 2

Kallonsa ta yi kawai ta fashe da dariya.
“Haba Hubby, Allah ka zauna a cinyata ai karyewa zata yi, na ga alama fa rigima kawai kake ji yau ɗin nan don kaga Al’tab baya nan ko? Ya tafi gidan Ummi Weekends”.

Haɗe rai yayi ya sake langwaɓe kai, kana ya ce “Ina ga dai yau yinwa ce kawai ake so ta kashe ni”.

Kafin ya sake cewa wani abu Nurin ta fara sakko da kayan abincin da ta shirya musu, nan da nan ta gama jere komai cikin nustwa, Brown Spaghetti ce da Salad sai Mango juice da ta haɗa shi da kanta, zama ta yi kusa da shi kana ta janyo  shi kusa da ita, rungomo shi tayi a jikinta ta fara ba shi abincin a baki.

Sosai ya saki jiki yaci abinci, yana ci yana lumshe ido, tsabar santi ko ƙala ya kasa furtawa har ya ƙoshi. Gyara zama ya yi, ya ɗakko ta cilak ya ɗora ta a kan cinyarsa kana ya fara bata abincin,” bai fi loma goma tayi ba ta fara alamun za ta yi amai, don ta daɗe da ce masa ta ƙoshi amma ya ƙi yadda, sanin halin Nuri ne yasa shi rabuwa da ita, nan ya tayata suka kwashe kayan, ya kuma dage akan shi ne zai wanke duk wasu abunda suka yi amfani da shi.

Bayan sun gama ne suka dawo falo, a nan ta ɗakko wayarta ta fara karanta musu wani littafi na Sayyid legend mai suna Sartse nan Mahmoud, ya tausayawa Nana ya kuma yi Allah wadai da masu hali irin na Sardauna.

Kallonta ya yi sosai, kana ya riƙe hanunta ya ce “Nuri”. Sai kuma ya yi shiru kallon idanuwansa ta yi ganin ya ciciko da ƙwalla ne ya sa ta tashi zaune.

 “Wai don Allah Hubby mai yasa kwanan  nan sai ka kira suna na kuma naga kayi shiru, idan da wani abun da yake faruwa ne ka faɗa min, wallahi hankali na yana ƙara tashi sosai”.

Rungumota ya yi sosai a jikinsa, kana yace “Nifa duk abunda zai sa na ga hankalinki ya tashi ba naso ko kaɗan, amma a wasu lokutan zuciyata na kanji tana matuƙar tausayinki ke da Al’tab, sai na ga kamar a kwai wani abu da zai faru amma nima Nuri ban san mai nene ba”.


“ A duk lokacin da ka ji haka kana yawaita karanta innalillahi, wa’inna ilahi raju’un, kuma in sha Allahu babu abunda zai same mu Hubbyna”.

“Shi yasa fa kullum kike ƙara shiga raina, saboda a wajenki ne kawai nake ƙara samun nutsuwa da kwanciyar hankali, don kinsan halin Hajjo bata da aiki sai son a bata, ga rikicinta na yau da gobe da ta saba yi”.

Murmushi Nuri ta saki, “Tom Hubby ai duk abunda iyayenmu suka yi a kanmu daidai ne, babu wani abu da ya rage mana illah kawai mu rabu da su lafiya”.

Shiru ya yi kamar mai yin nazari, can kuma zumbur ya miƙe, maza ta shi kisa hijabi mu fita shopping.

Ba musu  ta nufi ɗaki ta sanyo ƙaton hijabinta har ƙasa, suka fita har zai ɗakko mota 

“Ko dai mu tafi a ƙafa Hubby ko?”Shagwaɓewa tayi ta sake cewa “Dan Allah Hubby tunda ba nisa sosai”.

Baice ko mai ba ya sa mukullin motar a al’jihu ya kamo hanunta suka fita, Dakiɗo mai gadi ya bisu da……

بقلم أم فتيات 👧👧👧  ✍🏼…..