ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

22

by @gureenjoh

Kowannensu idanu ya janye a take, Wayanshi ya cigaba da amsawa yayinda ta fitar da nata wayan ta shiga taɓawa dukda ita ba gwanar media ba ce amma zaman shirun ya ishe ta.


For over 30minutes babu wanda ya motsa cikinsu, ganin lokacin magrib yayi ya sa ya miƙe ya tafi ɓangaren masallaci yayi sallah ya sake dawowa same spot ya zauna, har aka yi isha saboda yanayin delayance na jiragenmu suna zaune kan aka fara announcement za su yi boarding, shi ya fara Miƙewa ya ja trolley ɗin shi yayi gaba, sai da ta bari ana final announcement ma kan ta miƙe kamar ba za ta tafi ba ta nufi wurin shigewa ɗin, duba ticket ɗinta aka yi ta wuce zuwa ciki a hankali take duba seat number ɗinta tana zuwa inda yake zaune ta ɗaga kai ta kalli number ɗin abin mamaki ita ce daga ciki jikin Window shi yana daga gefe kuma ya riga ya zauna.


Luggage ɗinta ta ɗora a sama tana jin bai ma isa ta ƙi zama saboda shi ba, dukda yadda take jin wani abu mai kama da nauyi da bata taɓa ji kan kowa ba.


"Excuse me pls!"


Faɗin haka da ta yi ya sa ya ɗaga kai ya kalleta suka haɗa ido sai ta nuna seat na gefenshi wurin zamanta, dole ta yi baya ya miƙe ya fita kan ta shiga shima ya zauna.


Har suka ɗaga babu mai magana, ta kwanta jikin kujerar tana kallon waje shi kuwa karatun alqur'ani yake yi chan ƙasa ƙasa amma muryar na shiga har cikin zuciyarta, tsikar jikinta ke tashi, ta rasa Meyasa take jin amsa kuwwar karatun har cikin kanta dukda ba lallai ma wani ya san yana yin ba amma fessss take ji, karatun ya saukar mata da wata natsuwa da bata san akwai shi a jininta ba, ko da aka kawo musu snacks ma ruwa ta karɓa kawai ta sha tana sake yin lufff shi kam babu abin da ya karɓa.


Sun sauƙa Abuja dare ya ɗan fara ga ruwa da ake ta tsulawa kamar da bakin ƙwarya, kusan kowa ya fita yana zaune bata motsa ba sai da ya miƙe ya ɗauki akwatinshi ya fice itama ta miƙe ta ɗauki nata ta fita.


A terminal ta tsaya tana kallon yadda ruwan ke zuba gashi babu wani taxi, kalle kalle take ɗan yi wannan ne karonta na biyu zuwa Abuja din kuma ba wai ta san yanayin garin ba ne dukda ko ɗarrrr babu uban da take tsoro ko shakka kawai bata san yadda za ta fara ba ne.


Wayanta ta kalla ta sake duba sunan hotel da Jagaban yayi mata booking akan anan za ta zauna har sai ya ce ta dawo.

Numfashi ta ɗan sauke Idanunta na yawo kan mutanen da ake ta ɗauka ta ɗan lashi lips kaɗan kan ta harɗe hannu tana tsaye kawai bata gama yanke hukunci ba.


A hankali ta ga wata black Mercedes ta yi parking gabanta sai matukin ya sauko yana rike da lema ya zo inda take cikin girmamawa ya ce 


"Madame ko za ki shiga mu rage miki hanya? Kin san nisan dake tsakanin nan da cikin gari kuma taxi sun ɗauke saboda ruwa"


Wani irin kallo ta mishi don bata yarda da shi ba, sai glass na motar ɓangaren da yake na baya yayi ƙasa  Idanunta suka sauka kan Shehi dake zaune a baya yatsina fuska ta yi.


"Dukda ban nemi taimakonku ba amma mu je!"


Da sauri ya ɗauki Luggage ɗinta ya sa a baya ta buɗe gaba ta shiga don bata jin za ta iya sake zama kusa da wanchan mutumin, haka ya ja ya fara tsula gudu a titin na Abuja a lokacin sheikh ya amsa waya yayi biyar zuwa shidda sai tsaki take ja don an cika mata kunne.


"Ina za mu ajiye ki ma?"


"Grand Cubana hotel, Jabi"

Ta faɗa kai tsaye.


"Wow! What a coincidence ai mu ma chan muka nufa"

Baki ta taɓe kaɗan shi kam sheikh bai ma san suna yi ba.


Har zuciyarsa kuma taimakon musulunci ne yayi mata don za ta zama stranded a inda take, hakan ya sa yayi wa drivern umurnin su rage mata hanya zuwa open place da za ta iya samun abin hawa, ganin ta fara fuskar rashin mutunci ya sa ya sauke glass din don ta tabbatar ba cutarta za su yi ba bare ma su cuceta su ce sun cuci wa? Ya ayyana a sadda drivern ke saka mata kayan da shigowarta kamshin ta da yayi ta hawa mishi kai gabadaya zaman flight din ya sake yi mishi sallama, Sam ba ya son kamshi mai ƙarfi irin nata shiyasa lattafas suka zama best perfumes dinshi kamshi ne masu sanyi da natsuwa dukda shima ya kan cika waje musamman na maza ɗin amma nata ya yi over a hancinshi.


Ko da take Faɗin hotel da za ta je bai yi mamaki ba, haka suka cigaba da tafiya shiru yana amsa call sa'i da lokaci har suka isa hotel ɗin, drivern ya sauƙa ya buɗe mishi ko kan ya gama sauƙa ta zagaya ta buɗe booth din ta fitar da akwatinta da kit ɗinta.


Har ta taka baya kaɗan kan ta ce 

"Thanks"


Ya kalleta kaɗan sai ya gyaɗa kai ta juya ta yi ciki, sunanta kawai ta basu suka bata key a daidai shi ma ya shigo ya faɗi sunanshi suka karbeshi zuwa cikin elevator, tuni an kaita corridor din da room ɗinta yake ta ƙagu kwarai ta ga ta kwanta ga shi yunwa take ji na bala'i don rabonta da abinci tun safe, tana shiga ɗakin ta tura Luggage ɗinta ta faɗi kan gadon rigingine Idanunta rufe. 


Bata san adadin lokutan da ta ɗauka ba kan ta miƙe ta fara zame kayan jikinta sai da ta cire tas kan ta nufi toilet tayi wanka, hotel room din ya mata kyau kwarai hotel ne mai matsakaicin tsada amma komai intact har da kayan bacci sabbi fill a Leda bayan towel da su tissue da ake tanadarwa duk wani sabon customer.


Ɗaure da towel din ta nufi akwatin ta janyo ta buɗe me za ta gani? Neat and clean jallabiyoyi ne Kala daban daban a jere ga su Ghutra da jubba har nan a shirye a kuma goge.


Baya ta koma ta zauna dabas fuskarta a kwaɓe!


"Garin ya muka yi exchanging akwati da wanchan mutumin?"

Ta faɗa a bayyane kan ta ja tsaki ta miƙe tsaye ta tafi ta dauki kayan baccinsun farare tass ta sa bai mata yawa ba riga da kuma wando ne free sai ta ɗaura dankwalinta a kanta.


"Allah ya sa bai buɗe min akwati ba don wallahi zan iya yi masa rashin mutunci akan akwatin nan abubuwan da ke ciki sun fi karfin karamin kanshi na wa'azi"

A bayyane take maganan cikin sauri.

Dankwalin kawai ta mayar ta ɗaura a kayan da ta cire ta zura lofas na hotel din farare ta ja akwatin ta fice daga ɗakin kai tsaye reception ta koma don bata san inda yayi ba ma a cikin hotel din.


"Sannu! Akwai wani da muka shigo tare mun yi exchanging Luggage can you please check his room number for me?"


Matar ta fahimci frustration dake muryar Diva ga gajiya don haka ta amsa mata da 

"OK ma lemme check"


Ta duba numbern ɗakin sai dai ba ta so ta yi gaggawar exposing customer sai ta shiga kiran landline na dakin amma bai ɗauka ba sai da Diva ta buga kan desk na gabanta.


"Malama jiranki nake kin bar ni tsaye wata tsiyar zan je in ɗauka dakin da sai kin sanar masa? Faɗamin numbern in je da kaina kafin ya buɗe min akwati!"


Ta ɗan firgita kan ta ce

"Sorry ma! It's room 409 block B"


Tana A ne, ginin kuma A na kallon B ne, wanda ke tsaye a corridor din A tsaf zai kalli wanda yake corridor din B, layin kowani block kuma da farkon number ya fara wato dakuna goma ne kowani floor har hawa biyar.


Lift da zai kaita ɓangaren ta hau ta danna 4 ta tsaya tana ɗan bubbuga ƙafa saboda sauri da take kar ya buɗe mata akwati.


Shi kuwa ta bangarenshi shima zama yayi ya ɗan huta saukinta ba wani sallah a kanshi, ya cire jubba da rawanin ya bar iya gashin kanshi mai spring asalin na Fulani amma da yake yana ɗan tarawa sai ya ba da wani style mai kyau, system dinshi ya ɗauko daga jakarta dake daban ya shiga dubawa ya fi awa zaune dukda yunwar da yake ji amma ba zai iya cin komai a lokacin ba sai ya ja waya yayi placing order na tea daga restaurant na hotel din.


Daga nan ya miƙe ya shiga toilet don aikin ba ya mishi yadda yake so sai ya fara da wanka kan ya fito ɗaure da towel a ƙugunshi ginannen jikinshi da bai murde dayawa ba tsaka tsaki na yalƙi, shi ma kayan baccin da suka ajiye sabbi ya saka sai ya nufi akwatin ya buɗe don duba files da yake so yayi amfani da su kan ya kwanta sannan kuma ya fesa turare.


Kasancewar girgida da akwatin yayi Sossai yana buɗewa da yake a kan gado ya ɗora sai ya ji abu ya faɗar masa a ƙafa, tsuguna wa yayi ya ɗauka yana mamakin menene wannan ɗin don bai tuna sa abu haka a jakanshi ba, Yana buɗe karamin envelope ɗin wani strong abu ya shige hancinshi da sauri ya yar yana ambaton 


"Subhanallah!"


Tari ya ɗan fara fuskarsa har ta sauya, idanu ya kai kan akwatin sai ya ga kwata kwata ma babu abin da ya haɗa shi da nashi daga ciki ta waje ne dai suke kama da nashi ɗin.


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un... La haula wala quwwata illah billah"

Abinda yake ta maimatawa kenan.


"Akwatin 'yar daba!"

Ya sake faɗa a zahiri don tabbas nata ne, hannu ya sa ya riƙe waist dinshi bai taɓa tunanin zai rike irin wannan abu ba a rayuwarsa. What sort of nonsense? Ya sake ayyanawa yanzu idan mistakenly wani abu ya faru jakarnan ya buɗe cikin mutane matsayin nashi ai ta gama zubar masa da ƙima nan duniya.


Bai ma gama sanin abin yi ba ya ji ana knocking da ƙarfi, ya kalli kofan kan ya nufi kofar ya buɗe tana tsaye dab har sun kusa cin karo yayi baya.


"Me ya sa za ka chanza min akwati? Me zan yi da akwatinka?"


Kallon ba ki da hankali yayi mata don ta gama raina masa wayo, da ma duk natsuwar da tayi dazu kaman ba ita ba na munafurci ne ya zaci ta fara sauyawa don ya zauna da ita for over 4hours a ranar bai ga tayi faɗa da kowa ba, amma ji abin da take ce mishi a kan kayan maye?


"Wannan tambayar daga bakina ya kamata a ji shi, me zan yi da kayan maye? Me zan yi da abin da Allah ya tsinewa? A'uzubillah! Wa'iyazubillah"


Wani abu ne ya daki zuciyarta ranta ya shiga tafasa, ɗan kirkin da take mishi tuni ya kau don ya zo inda ba za ta bari ba.


"Wa ya sani kila kana da abin yi da shi? Ai maye shi ya san makwancin maye idan baka sha ta ya ka san menene ciki...."


Ido cikin ido suke kallon juna don ji yayi kaman ya rufeta da duka, shi take kallo take gayawa wannan magana? Shi dai Irshad Omar Al-Noor? Wonderful! Ya ayyana a ranshi kan yayi magana ta ce 


"Malam ka dauƙo min akwatina ko ka ba ni hanya in ɗauki abata!"


Matsawa yayi don ba zai ma iya sake cewa komai ba tunda tace shima shaye shayen yake baya so ma wani ya ji su ko cikin baƙin taron su fito su ga yana magana da irin wannan, ciki ta shige ta ga akwatinta a buɗe tana mita tana rufewa har ta gama ta ja abin ta ta fice, nashi ya ja ya shigar ciki yana rufe kofar cikin adu'ar Allah kar ya sake kawo abin da zai haɗa su.


Yana shiga bai zauna ba Wayanshi ya shiga kira ya ɗaga ya duba Ammar ne sai yayi picking yana komawa ya zauna har da kishingiɗa.


"Ammar!"


"Ya na ji muryarka haka ko ka fara bacci ne na tasheka?"


Tsaki ya ja yana sake Miƙewa zaune wai shi za ta cewa yana shan wani abu! Duk yadda ya so yayi shiru ba ya jin zai iya abokin taya kuka yake nema, sai yace wa Ammar ɗin 


"Yau ni aka kalla tsakiyar ido aka ce ina shaye shaye."


Ammar yayi kasake...kan ya ce 

"Ban gane ba! Wa zai ganka ya furta hakan? Waye bai san fuskarka ba da zai iya jefanka da wannan maganan? Ko kwarjininka da kamalanka sun fi ƙarfin a yi musu irin wannan suɓutar bakin lallai ko ma waye ne da tsaurin ido yake"


Irshad ya sauke Numfashi 

"Mace ce!"

Sai da ya ɗan muskuta ya furta 

"Wannan 'yar daban!"


"Mace?"

Ammar ya maimaita da tsantsar mamaki, shi karan kanshi wani lokacin Irshad kan mishi kwarjini kai hatta iyayensu suna matukar jin nauyin shi a abubuwa dayawa saboda tarin baiwa da Allah yayi masa har mace ta faɗa mishi hakan a cikin ido? Lallai ko wacece bata da kunya kuma fitsararriya ce.


"Wace 'yar daba? Me ya haɗa ku haka?"


"Wannan da ta yi sharing hospital room da Daddah"


"Diva!!!"

Ammar Ya faɗa yana Miƙewa daga zaunen da yake mamakinshi na ƙara ninkuwa.