22
by @sadisakhna
______👑 *JODA* 👑_____
Na
*Sadi-sakhna*
Ƴar mutan Jama'are
THE TRIO OF TALES
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)
@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp
LITTAFI NA 1
👑*Warƙa ta (22)*👑
Da murna kana da fara'ah na nufi lungun dazai sadani da ɗakin karatun,sauri nakeyi amma gani nake kaman bazan isa ba,hakan yasa na ƙara da gudu . Hannu na saka a kunkumi ina ƙarewa wajen kallo cikeda zumudi,wata Jaka na zaro daga ƙasan rigata wacce dama da ita nazo wajen. Cikin hanzari nake duba littafan da nake buƙata,duk wani wanda yakeda alaƙa da abinda nakeso saida na ɗauka,bansamu wanda nazo dominsa ba sai a ƙarshen lokaci na samoshi a kan wata kanta,yayi ƙura sosai,ina hurewa na kalli sunan a rubuce. Malikush-shifa marubuci Abisinniyah gogeshi nayi cikeda kulawa nasaka a cikin jakar. A taƙaice na ɗauki litattafai sunyi goma a wajen,jan jakar nayi zuwa bakin taga na wurga,amma na cire wanda nazo dominsa saboda kada a ganeni. Hannuna na kaɗe ina murmushin samun nasara,daganan na juya kokawa inda Hammar yake zaune shiga malam,Fasihmu mu fita da sauri na ɗauki jakata a bayan wajen kafin wani ya kulada ita.
"Meyasa batada farashi ya shehun malami,dan Allah ka faɗamin ko nawane idan inada hali zan biya,nayi maka alƙawari bazan fansheta bane domin na cutar da ita,sai domin hakan nada alaƙa a cetar rayuwarta"
"Taya zan yarda dakai akan hakan,taya zan yarda bada ƙudurin dayazo kaima kazo ba. Joda baiwa ta ce,wacce na fansheta badan naji daɗi da ita ba,kokuma nayi amfani da ita ba tawani siga,sai domin rayuwarta ta inganta a wannan waje,harma itama ta amfanar da wani, kaine mutum na goma a wanda yasameni da cewar yana son mallakar joda,badan komai ba saidon yana son cin moriya daga baiwar da take da ita, Hatta wanda kukayi tsama dashi a yau yazomin da cewar yanason mallakarta,amma ko zama dashi ban amince dayi ba,saboda nasan ƙudurinsa na son mallakarta,hakan yasa a fusace yakoma masarauta domin tahowa da shirinsa. Bayan bai sani ba tun jiya mahaifiyarsa tayimin maganar tanason fansarta zata koma da ita cikin masarauta ta zama mai kulada lafiyarta,amma naƙi amince mata. Domin har yanzu ƙwaƙwalwarta na a matakin farko farko,tana buƙatar sake zurfin ilimi,kafin hakan ya kasance dole tana buƙatar wanda zasu nusar da ita akan hakan,kuma tana buƙatar inda baza'a ɗora mata ragamar nauyin bauta ba,hakan yasa Ɗan uwana yakarbi kulada ita da kuma koyar da ita mataki mataki. Bazan boye maka ba ku kanmu wannan Jami'a muna son mutane masu baiwa irinta,domin ta hakanne zamu samu ƙwararrun malamai kuma masu fikira,dan haka ka sanar dani sharaɗin ka na mallakarta naji ko zai iya kaiwa farashinta."
Numfasawa Hammar yayi kafin yace.
"Badan barazana na dawowar wannan yariman ba to iya waɗannan bayanannaka sun gamsar dani daga barin roƙon na fansheta daga hannun ka. Domin ko kaɗan banzo nan da mallakarta domin nasakata a cikin ikona ba,kokuma na rabata da nahiyarta ba,naso mallakarta ne saboda ta hakanne kaɗai zan dakatar dashi daga cimma ƙudurinsa akanta. Idan lokacin tafiyata yayi kuma tace zata bini bazan hanata,intace zata zauna nan ma bazan hanata ba,ƙarshe ma inaso na miƙa mata ƴanci,ta hakanne kaɗai zan saka mata da abinda tayimin na samamin magani da takeyi bayan na fidda tsammanin samu. Sannan nayi maka alƙawarin bazan cutar da ita ba, dan Allah ka lamuncemin mallakarta,idan tana a ƙarƙashin ikonka Sarkin wannan garin zai iya umartarka daka barmasa ita,ko itama mahaifiyarsa tunda tana sonta zata saka baki wajen ganin ta koma masarautar"
Numfasawa yayi bayan yaji bayanan Hammar,ƙur'anin dayake gefensa ya ɗauko,wanda da kansa ya rubutashi shekaru da suka wuce.
"Naji naka bayanan kuma bazan ce banyi na'am da zancenka ba,Dokarmu ce ta wannan makaranta bama saida bayinmu ko barinsu su fita Fasihmman wanda suke bangare na sanin ilimi,amma kuma barinta a hannuna kaman yanda kace a yanzu bazai ceceta ba,saboda abin ya haɗa da masu ƙarfin iko. Zan karya wannan doka saboda bawa wannan baiwa kariya,amma kasani dole sai kayimin rantsuwa da dukkan abinda ka faɗa gaskiya ne,na cewar baka fansheta domin ka cutar da ita,ta hakanne zan yarda cewar bakazo da kwatankwacin abinda shi yazo dashi ba"
Tun kafin ya rufe baki Hammar ya ɗora hannunsa akan alkur'ani kana yayi rantsuwar cewar baizo fansar Joda domin ya cutar da ita ba.
Wata takarda Ya ɗakko a gefensa ya rubuta sunan joda a jiki sannan yamiƙawa Hammar kan cewar ya danna zanen hatiminsa a jiki,wanda yake nuna yarjejeniyar ya sallama masa ita. Ganin Hammar ya tsaya yana kallonsa da mamaki yasa yaƙara mika masa takardar alamar ya karba.
"Amma ban biya kuɗinta ba,mai yasa zaka bani takardar shaidar mallakarta a yanzu?"
"Rantsuwar da kayi da littafin Allah na cewar zaka kulada ita bazaka cutar da ita ba shine Farashinta,idan ba wannan ba darajarta a matsayinta na mai ilimi ya wuce duk wani kuɗi dazan saka maka"
"Nagode da karba buƙatata dakayi kuma harka biyamin ita,duk da baya cikin dokokinku amma ka karya domin ka bani ita, nayi maka alƙwarin zan yi iya ƙoƙarina wajen ganin ban cutar da ita ba. Duk da cewar ka nunamin darajarta yafi na kuɗi saina kima amma zan saka a aiko da kilo goma na zinare,sannan za'a gina sansani na majalisi guda ɗari Insha'allahu"
"Mashaallah to mungode da wannan kyauta Allah yasaka maka da alkhairi yakuma tafiyar dakai akan hanyar daidai,Allah yakai lada ga iyayenka dakuma nahiyarku gabaki ɗaya"
"Ameen ya Allah nima nagode da karamcinka"
To wai wannan mai suke tattaunawa ne haka harna fito basu gamaba,hmmm to kodai zagowa yakeyi Baba guru ya koyar dashi da kansa saboda ya cinye gasar. In hakane kuwa to ai yana cuta kenan. Kodayake kowa tasa fitar yake dubawa ai. Fasih na kalla a gefe suna zuba hira shida wata hadima,dariya nayi da har bazan ƙarisa ba saikuma na nufesu,inason bashi sallahun cewar zan tafi kada dare yayi min.
"Assalam hirar masoya kukene,to ni zan tafi Fasih naga har yanzu basu gama ba kuma zanyi dare a hanyar komawa"
"To shikenan in yafito zan sanar dashi"
Yayi maganar yana sosa ƙeya,nidai murmushi kawai nayi nabar wajen.
*** *** ***
Ya mai girma mai martaba dagaske nakeyi maka idan har na samu wannan a matsayin ƙwarƙwarata bazan ƙara bibiyar kowacce baiwa ba,sannan abinda nake faɗamaka gaskiya ne,tana da kaifin basira dakuma baiwar warkar da cututtuka sosai,idan harta shigo cikin masarautar nan baƙaramin amfana za'a yi da baiwarta ba,lokacin da aka kai Asmah wajen ta jikinta a halin tsanani yake,amma tana dubata nan da nan tasamu bacci jikinta yafara samun lafiya. Sannan naji ance duk malaman cikin jami'ar da shekarunsu suka ja tana haɗamusu wani shayi da dare wanda yake kwantar musu da hankali ya ƙara musu lafiya,nutsuwa da kuma samun bacci mai nauyi lafiyayye,ka tambayi Sunkia Madina ma kaji idan baka amince da maganata ba Mai martaba"
Shuru mahaifinnasa yayi yana saurarensa cikeda nazarin maganganunsa,indai har ɗansa da ko matarsa baya darajawa ballantana ɗauka da muhimmanci zai zauce masa akan wannan baiwar to lallai akwai abinda yagani a gameda ita mai daraja. Idan kuma yasameta zaisa ya daina bibiyar bayi mata yana zubar masa da kima to hakan ai babban abun farincikine a garesu"
"Shikenan ka tashi kaje zanyi nazari,amma kafin sannan ka daina wani shashanci ka kulada matarka kasan batada lafiya kuma ka ciki. Idan masarautar su suka samu labarin abinda kakeyi mata zaka zubar mana da mutunci,sannan ka saka a ɗaukemu a ƙananun mutane"
"To shikenan Mai martaba nagode,dan Allah ka aikawa Guru da saƙon,da gaske nake zan kasance mai cika maganata"
"Shikenan kaje inada baƙin dazan gani yanzu"
Cikeda murna da zumuɗi yerima Kabeer yabar cikin fadar mahaifinnasa yashiga cikin gidan masarautar. Inda lambun shan iskar sa yake ya nufa,bayi suna ta aikin gyaran wani ƙwataccen ɗaki dayake wajen, ga dama gurin ya ƙawatu da kayan nishaɗi ƙananun dabbobi da kuma furanni masu daɗin ƙamshi. Leƙa ɗakin yayi yaga yanda aikin yake tafiya.
"Ku tabbatar komai yayi yanda yakamata"
"To ranka shi daɗe ai komai mai aminci muke sakawa yanda cin amarcinku zai zamo cikin nishaɗi da amarshi,lallai wannan baiwa ta taki sa'a,da alama tasamu gurbi mai girma a cikin ranka shugaba"
Wani hadiminsa na hannun daman sa ya faɗa,wanda dama shike kula da duk wata sharholiya dayake aiwatarwa.
"Tabbas hakane faɗi kasake nanata wannan batu,dan tashigo masarautar nan a matsayin mallakina nanne inda zan sauƙeta,sannan zan tsaya nazama na miji wajen ganin Asmah bata cutar da ita ba. Muyi rayuwarmu cikin nishaɗi"
Yakarisa maganar yana ɗauke da wani murmushi a kan fuskarsa.
Tun safe yake safa da marwa domin yaji ƙira daga wajen mahaifinnasa kan ya akayi bayan Masinjan da aka aikawa Shehu Al'azhar jiya da daddare yadawo. Kwana uku kenan bai koma wajen matarsa ba dake wajen magani,burinsa kawai shine samun abinda zuciyarsa ta ƙyalla ido tana so. Ganin Sarki bazai ƙirashi ba yasa kawai yayi ta maza ya nufi fadar. Akwai mutane ana yanke hukunci,hakan yasa saida yajira aka gama suka tafi kafin ya ƙarisa inda mahaifinnasa yake hakimce akan kujerar mulki.
"Ya akayi magajin Karaga?"
"Uhmm dama nazo mu gaisa ne naji ya yanayin jikinka"
"Naga ɗaxunnan kazo muka gaisa,kuma ni nace maka banajin daɗi ne,kawai jikine daya fara gajiya saboda yanayin shekaru da suka fara kamani,amma naji sauƙi sosai"
"Ayyah sannu dama yanzu kam sai a hankali,da wannan yarinyar ta iso fada aida ta dubaka"
Ɗan murmushi Sarkin yayi irinna manya,domin tun jiya ya ɗago menene ya damu ɗannasa ba,tunda yake shi ba mutum ne mai yawan zuwa inda yake ba,saidai idan yanada wata bukata a gareshi,hakan yasa ya ɗauko wata takarda wacce ɗan aike yakawo daga wajen Shehu Al'azhar ya miƙa masa.
Karba yayi da sauri cikin zumuɗi,domin duk a zatonsa takardar yarjejeniyar mallakar joda ne,domin dama su irin wannan wajen idan zasu sallamar maka da bawa to sai sunyi a rubuce,saboda doka ne koda mutum yakalla bawansu a wani wajen bai isa yace nasa bane, idan babu takardarsa a hannunsa,saboda sunada wani hatimi a jikin bayinsu wanda idan sun saidashi ma basa gogewa in har yanada ilimi,da wanann hatimin bawan zai iya amfani a kotun shari'a ya karbi kansa idan wani yace zai mallakeshi batareda takardarsa ba. Saboda ko a cikin bayi wanda suka tashi a wajen hidimar karatu daban suke tunda sunada ilimi,kuma zasu iya tayaka wasu abubuwan kaman su kasuwanci,magani da kuma rubutu ko karatu.
Amma ganin sabanin abinda yake tunani sai nan da nan fuskarsa ta sauya,baƙin ciki da furgici suka shiga.
"Baba mai wannan yake nufi,wanene wanda yakeda ƙarfin ikon da zai iya mallakar ta a faɗin wannan nahiyar da har bazaka iya karbarta daga hannunsa ba,waye shi waye ya isa Mai martaba"
"Mai matsayi irinnaka amma a nahiyar da take daidai da tamu koma nace tafi tamu,wannan shine zai iya mallakarta kuma bazaka iya ƙwatarta daga hannunsa ba saidai idan shi yaga dama yabaka da kansa. Kayi jinkiri yarigaka mallakarta,a yanzu haka takardar yarjejeniyar mallakarta yana hannunsa,dan haka ka manta da wannan yarinya ka nemi wata,domin baiwa batakai ta jawo mana yin faɗa da Wata nahiyar ba.
"To amma mai marta ba..........."
"Ya isa!!...... Idan na isa dakai to kada nasake jin maganar ta A masarsutar nan. In aure kake so ka samo kowacce ƴar sarki ka aura idan kana ganin Matarka tayi maka kaɗan ko bata gamsar dakai yanda yakamata. Amma wannan kam babu maganar ta ya wuce,baza'a zubarda jini dominta ba,sannan kuma matsayinta yayi kaɗan dazaka roƙeshi ya bar maka ita,bazan yadda da wannan zubda kima ba"
Babu yanda ya iya haka yafita daga cikin fadar da takardar dunƙule a cikin hannunsa,fuskarsa ɗauke da tsananin baƙinciki.
"Hmmm kaine ko,na tabbbata kaine,shiyasa har kasamu damar yimin gargaɗi,wato zaki ne kai ka lulluba fatar tunkiya ka buya a garken su,zan kuwa zaƙuloka na farauce Ka mu fafata,domin nima nan zakinne,kuma akan abin farautata bazan taba sararawa ba. Zamu ga wanda zai yi nasara tsakanin nida kai."
Sashen mahaifiyarsa ya nufa duk da yasan bata nan suna wajen magani, ko kaɗan baya sha'awar komai yarasa mai yake masa daɗi.
Zaleekah ya hango Tana tafe tana rangwaɗa tasha ado,Mahafiyarta Ƴar masar ce anan masarautar ta tashi. Kasancewar tana haske da kuma ƙira najan hankali yasa Yerima kabeer ya faɗa soyayyar ta tun farkon samartakarsa,babu irin baɗalar da basuyi ba da shi, har ƴanci yabata kan cewar zai aureta,amma iyayensa suka ƙi amincewa,maimakon haka sai aka karbo masa auren Gimbiya Asmah. Shima kuma a hankali Sai ta sane masa a rai yafita harkarta yakoma biye biyen mata bayi,ganin hakan yasa ta ɗora laifin dukka akan Asmah,saidai babu abinda zata iya mata,saboda iya ƴanci ne kawai da ita na cewar ita ba baiwa bace,amma batada matsayin dazata kara da ita ko kaɗan. Ta daɗe tana bibiyar malamai amma ko kaɗan yaƙi kallonta,kuma an tabbatar mata idan ba dawowa yayi gareta ba to bazata taba cin galaba akansa ba, saboda matarsa tayi masa katanga da ita.
Yanzu ma ganin shigarsa fadar sarkine yasa ta tsaya jiran fitowarsa,kamar kullum tasan bazai kulataba amma sai taga sabanin koda yaushe Ya kama hannunta yajawota jikinsa ya ƙanƙameta. Wani murmushin daɗi tayi kafin takai bakinta wajen kunnensa.
"Yerimana da alama kana cikin halin baƙinciki,sannan kanason mai kwantar maka da wannan bacin rai,to amma muna kan hanyar mutane"
"Ina ne yake kusada mu?"
"Uhmm sashenka da nisa danan,ballantana muje lambunka saidai sashen ummanka shi kuma......"
"Muje can ɗin"
Wani murmushin shu'umanci tayi kafin tajashi sashen Sunkia madina,tun a hanya tafara sumbatarsa tana zaro da harshe kaman wata macijiya.
Aminatou wacce ta fito daga ɗakin Sunkia Madina hannunta ɗauke da Sultan zata kaishi tayi masa wanka ta hangesu Zasu shiga wata turaka dake kallon na wanda tafito. Razana tayi tana kare fuskar yaron saboda kada ya kalli abinda yake faruwa,wani shu'umin kallo Zaleekah tayiwa Aminatou tana wani sake shishshige masa,yayinda shima kallonta yayi cikin halin ko in kula da yanayin data gansu,saima ɗan sake Zaleekah da yayi yace.
"Zamu shiga ciki,ku kama kanku banason hayaniya,sannan kishigomin da ruwan inibi ciki inada buƙatar sa bayan kin ajiye yaron"
Yana maganar yana kallonta,yana yawan kallonta a sashen saboda ita ke kulada Sultan ɗansa. To amma mai yasa ya kalli tanayi masa kama da Yarinyar daya gani a Al'azhar,kai inaga dan ya sakata a cikin ransa ne tafara yimasa gizo. Da haka ya basar da maganar suka shige ciki shida Zaleekah. Wanda take jinta tamkar sallah Yaudai burinta zai cika na mallakarsa a karo na biyu. Asmah kuwa saidai ta haɗiyi zuciya ta mutu.
Sadi-sakhna ce ✍🏼
Comment
Like
Share
Follow