13
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_
*Na*
*AISHA ALTO*
*JAMILA UMAR(Janafty)
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.
*BABI NA GOMA SHA UKU*
Gyaɗa kansa yayi hawaye masu zafi da raɗaɗi na zuba daga cikin idanunsa ya duƙar da kai ƙasa yace "Tabbas nine nayi mata ciki...cikin jikin Mufeeda nawa ne bana wani ba..." Yana faɗa ya sake rushewa da wani irin kuka mai taɓa zuciya da ban tausayi. Itama Mufeeda ƙara sautin kukanta tayi da ƙarfi zuciyarta cike da tausayin Daddy ta tsura masa ido tana ji a ranta dama wannan ranar bata zo musu ba.
Gaba ɗaya falon salati suka ɗauka kowa faɗi yake "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...." Yayinda ita ko Farida ta ƙara gigicewa ta ruɗe da jin kalaman da Tahir yake faɗa, lokaci ɗaya komai ya tsaya mata cak, sai aikin nunashi take da yatsa tana girgiza kai ta kasa magana, kafin ta koma da baya ta faɗa saman kujera daɓas ta zauna a ruɗe tana faɗin "A'a Abban Basma don Allah kar kace haka...wannan nasan ba gaskiya kake faɗa ba...nasan ba halinka bane a ko'ina kuma zan iya yin shaidarka akan haka...kuma nasan kowa ma zai yi shaidarka indai akan haka ne, nasan ko akan wata bazaka taɓa iya aikata haka ba, balle akan Mufeeda 'yar damuka raina muka ɗauketa tamkar 'yar da muka haifa da cikinmu...plz Abban Basma karka sakamu cikin wani yanayi plz kace ƙarya ne abinda ka faɗa ba gaskiya bane...don Allah kace ƙarya ne Abban Basma.." Ta faɗa tana ji a zuciyarta dama a tasheta ace mafarki take ba gaskiya bane abinda kunnuwanta suke jiye mata ba.
Yana kallonta da idanuwansa da suka rine sukayi jajir suna tsiyayar ruwan hawaye yace "Tabbas Farida abinda na faɗa gaskiya ne, kunnuwanki sun jiye miki dai-dai...cikin dake jikin Mufeeda nawa ne...nine na yiwa Mufeeda ciki..cikina ne...amma a bisa ƙaddara data faɗa min ba'a son raina ba..." Salati duka falon suka ƙara ɗauka, kafin Inna Fulera ta fashe da kuka mai sauti ta miƙe ta cakumi Mufeeda ta fizgota ta rufeta da duka baji ba gani tana yi tana kuka take faɗin "Kin cuceni kin cuci kanki Mufeeda, kin wulaƙanta rayuwarki kin tozarta kanki...Allah ya isa tsakanina dake..ki rasa sakayyar da zakiyi min sai ta abun kunya...kina marainiya kin zubarwa kanki kima da mutunci...Allah ya gani iya tarbiyya na baki ita dai-dai gwargwado ban san kuma meya shiga kanki ba har kika iya watsar da mutuncinki a titi ba..." Ta faɗa tana ƙara shurinta da ƙafa tana kuka, Mufeeda ma kukan take tana jujjuya kanta amma ta kasa tashi ta ƙwaci kanta, da sauri Tahir ya matso ganin Inna Fulera ta ɗaga ƙafa zata taka cikin Mufeeda tana faɗin gwara na kasheki da inci gaba da ganinki ina jin baƙin cikinki a raina, da hanzari ya riƙeta yana girgiza kai a hankali yace "Laifina ne Inna, ita da niyyar taimakona tazo, dukkanmu bada niyya mukayi ba...ƙaddara ce ta afka mana..." A fusace Farida ta miƙe tana faɗin "Babu ruwan ƙaddara Malam, dama can kana da niyyar aikatawa shine zaka fake da ƙaddara..." Ta faɗa tana fashewa da kukan takaici da baƙin ciki tana faɗin "Amma Tahir ka cuce ni ka cuci zuri'arka ka wulaƙantamu, yanzu da wani irin idanu kakeso a kalli 'ya'yanka? Ka ɓata mana sunan zuri'a, ka haikewa 'yar da take ɗaukarka a matsayin uba...tirr da kai da irin halinka, wallahi bazan iya ci gaba da zama da kai ba, ni ba fasiƙa bace don haka bazan zauna da fasiƙi ba...sai dai ka zauna da ita da shegen cikinku..." Ta faɗa tana ƙara fashewa da kukan baƙin ciki da takaici tana kallon Mufeeda dake kukan itama tana ji kamar ta tashi ta shaƙeta har sai taga bata numfashi.
Wani murmushin dayafi kuka ciwo Tahir yayi yana kallon Goggo yace "Komai da ya faru bada son raina bane kawai na ɗauki hakan ne a matsayin ƙaddarata kuma na karɓeta hannu biyu, Allah ya bani ikon cin jarabawata... Nan take ya shiga bada labarin duk abubuwan da suka faru, kafin yana kuka ya ɗago yana faɗin "Duk da wannan abun daya faru dani ba kowa bane sanadin shigata wannan halin sai Farida dake Goggo, domin ke kika hanani na sanarwa Baba Hakimi wannan matsalar dake faruwa dani kuma kika hanani maganar ƙara aure, alhalin baki taɓa tambayata dalilin da yasa na nace inaso na ƙara auren ba, sai dai a kullum idan naje miki da maganar irin abubuwan da Farida take yi min sai kice inyi haƙuri zaki mata magana, zata gyara, baki taɓa nuna damuwarki akan halin da nake ciki ko ki tambayeni abinda yake faruwa ba, sai dai dana fara sai ki katseni kice bakyason ayi abunda zumunci zai lalace...Goggo ni ɗanki ne amma baki taɓa damuwa da matsalata ba, domin baki taɓa bani damar nuna miki damuwata ba, sai dai ma kiyi ƙoƙarin hanani faɗawa mahaifina halin da nake ciki, to yau ga abinda kika jawo min nan..." Ya faɗa tare da juyawa yana kallon Farida data daskare a zaune ta kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi hawaye sai zubowa suke a idanunta, Girgiza kansa kawai yayi yana faɗin "Kuka ai yanzu kika fara yinshi Farida, domin tun asali abunda na dinga gujewa faruwarsa kenan a tsakanina dake...Nayi haƙuri har na kai maƙura amma Farida baki canza halinki ba, nayi ƙoƙarin gyaraki amma baki gyaru ba...kin ɗauke ni tamkar ba mijinki ba, baki maidani a bakin komai ba, baki san ki sauke hakkina dake kanki ba, baki san ki kula da 'ya'yan da Allah ya baki ba...sai dai kullum kina yawon bin gidan bikin ƙawaye, baki san ki tambayeni fita ba, sai dai duk lokacin da kikaso kiyi fitarki kuma ki dawo duk lokacin da kika so ba abunda ya dameki, na nuna miki nima fa mai lafiya ne ba dutse bane kuma dole ne in nemi hakkina a gurinki, amma yawon zuwa gurin biki ya hana ki zauna ki kula dani da 'ya'yanki...kullum baki nan baki nan, kuma kinsan ban ajiye wacce zata kula dani bayan ke ba, tunda ke kaɗai gareni baki damu da wane irin hali zan shiga ba, kedai kawai abunda ya shafeki kuma ya dameki shi kikeyi, 'ya'yan da kika haifa kin barwa masu raino baki damu da tarbiyyarsu ba, baki damu da halin da zasu shiga ba, kedai kawai ki tafi biki..sai kibar gidanki da mijinki da 'ya'yanki babu abunda ya dameki, babu ruwanki da duk irin halin da zamu shiga, Saboda Haka Dukkan abunda ya Faru Tsakanina da Mufeeda Keda Goggo kuna da Alhaki akai..."
Ya faɗa yana Matse Ƙwallah, gaba ɗaya Falon ya Ɗauki Shuru banda Kukan Mufeeda dana Farida sai Inna Fulera sai na Goggo Abu Dake Tashi ƙasa ƙasa, wani mugun kallo Baba Hakimi ke Jifan Goggo Abu Dashi Lokaci Ɗaya Zuciyarsa na Lulluɓewa da Ɓacin Rai kukan Tahir Tamkar Saukar Dalma ne Cikin Ranshi Cikin Tsawa yace "Kukan me kike Zainabu...? Ai bai kamata kiyi Kuka ba Tashi zakiyi ki Taka Rawa kiyi Murna Kin Yi Sanadiyar Lalata Rayuwar Ɗanki Wanda Kika Haifa da Cikinki. Tir Dake Abu Wallahi Yawonki Da Girmanki Amatsayinki na Uwa bai amfaneki da Komai ba sai Sakarci Yanzu ace Ɗanki yazo ya Sameki da Irin Wannan maganar ki kasa gayamin Abun baƙin ciki kuma kin Hanashi ya Sanar dani..? Ke Har Kin isa ki gyara Abunda Allah bai gyara ba Wato kin Hanashi ƙara Aure Amma baki Taɓa Tunanin ina zai kai Lalurarsa ba kanki kaɗai kika sani Sai Wani Dalilinki mara Tushe Ballantana Makama, Wallahi Tallahi ina so ki Sani Duk Zunubin dake Kan Tahir Akan laifin Zina Dake da Farida za'a Rabawa Domin kune kuke da alhakin Duka Abunda ya Faru..Babu Abunda Zance miki sai godiya kin kuma kyauta.." Ya ƙarashe Faɗa yana Share ƙaramar kwallarsa Data Zubo mai Cikin Tashin Hankali.
Su Basma da Bassam da Muda da Laila Dake laɓe A koridon Ɗakin Basma Kuwa kuka Suke Ka Shirɓan na Tausayin Kukan da Daddynsu yake Duk Abunda aka faɗa kaf Acikin kunnuwansu Lokaci Ɗaya Sukaji Sun Tsane Farida da Komai nata ganin Itace Silan Shigan Daddynsu Wani Hali Hartana Sanyashi kuka dama ba Tun yanzu ba Rashin Kula Dasu da batayi yana Tsaye Acikin Ransu kuma Suna jin Haushin hakan gashi Dalilin Sakacinta Ta saka Daddynsu Cikin wani Hali, Basma Da Laila Suka haɗa kai Suna kuka yayinda Muda da Bassam Suma Suka Ɗora kai Agwiwa suma Suna ta kukan Tausayin Daddynsu.
Goggo Abu ko Kuka Take ba Bakin magana Maganganun Hakimi Sun Shigeta Sosai Tahir Kaɗai Take kallo Tana Jin Ta zama Sakaryar Uwa Mara Damuwa da damuwar ɗanta Data Haifa da Cikinta Innaro ko Tana gefe Itama tana Sharan Ƙwallah Tausayin Tahir na Jarabawar da Allah ya masa, Domin Wanna Jarabawa ce Domin Ajaraba Imaninsa Abba ko Wani Kallo yake Wurgama Farida Dake Jikin Umma Tana Kuka Ita kanta Umma Kukan Take Sharewa Lokaci Ɗaya Tana Faɗin "Muma muna da laifi ba Goggo Abu da Farida bane keda alhaki Akan Wannan Abun ba Harda mu kanmu iyayen Farida bamu Taɓa Lura da Irin Ƙararta da Tahir yake kawo mana ba, ko yazo ya Faɗama bama Nuna mata batayi Dai dai ba sai ma Mu kama lallashinta Cikin Soyayya musamman ni dana kasance Uwa agareta Wacce Nafi kusanci da Ita, Gatan da Muka Nunawa Farida Shiya Sangarta ta bata iya zama Gidan Mijinta ta bashi Dukkan kulawa, Muma muna da Laifi Muna Dashi muma.." Ta ƙarashe Faɗa Tana Sharɓan Kuka.
Abba yace "Haƙiƙa maganarki gaskiya ne Aliya muna da laifi Wajen Rashin Nuna ma Farida Muhimmancin Mijinta Hakika bamu kyauta ba..kuma bamu kyautama Tahir ba Domin Yayi Haƙuri da Ita Tun bayan Auresu, Dukkanmu bamu Taru mu Duba Halin da Tahir zai Shiga ba..Duka laifin namu Ne sai dai muyi fatan Allah ya ya yafe mana Gaba ɗaya..." Baba Hakimi ya amsa da Ameen Ishaq na gefen Tahir yana Ɗagoshi Amma yaƙi ɗago kansa Saboda Hawayensa Sun kasa Daina zubo mata Baba Hakimi ya Kalli Inna Fulera yana Faɗin "Fulera ki Daina Ma Mufeeda mugun baki kinji da Kunnenki Duka ba laifinsu bane, Ki saka mata albarka ki kuma kalleta kice kin yafe mata Babu kyau bawa ya Nuna Butulci ga Allah lokacin Daya Jarabceka da Wata Jarabawa Godiya zaki ma Allah, kar in sake jin kin aibata 'yarki.." Ya faɗa cikin Sanyin Murya gyaɗa kai Inna Fulera Tayi tana Kuka Lokaci Ɗaya Jikinta yayi sanyi Ta kalli Mufeeda Dake Durƙushe Tana Kuka Lokaci Ɗaya tace "Na..yafe miki Mufeeda...Allah ya bamu ikon Cin Jarabawarsa Haƙiƙa na Shaida ke yarinya ce mai Tarbiya Hakama Alhaji na yarda da Ƙaddara ne ta Faɗa muku Domin Dattakonsa Data iyayensa Shike Riƙe damu Har yanzu... Amma Ina Roƙon ku don Allah kada ku Zubar da Cikin ku barma Mufeeda Shi ƙila Wata rana Shi zaiji kanta ko kuma ƙila Shi kaɗai ne ƙwanta a nan Duniya.." Farida dake Jikin Umma ta ɗago Tana Faɗin "Wallahi sai yabi Rariya Uban Wa zata Haifa ma Shege..? Ba anan gidan ba Wallahi sai an Zubar Dashi..."
Ta faɗa Cikin ƙaraji Da Kuka Abba ne ya mata Daƙuwa yana Faɗin "Kinci Ubanki, Farida In na Sake jin bakinki Anan Wajen Wallahi sai naci Mutumcinki mutuniyar Banza da Wofi.." Ya faɗa yana Hararanta Umma dai ƙwallah Take Sharewa Duk Jikinta yayi Sanyi Su Goggo Abu kuwa An Shiga ƙwaryar Nadama.
Baba Hakimi ne yace "Dama waya ce miki za'a Zubar..? Haba kamar ba masu Hankali ba kenan bamu yarda da Ƙaddara ba, taya zamu aikata Wani Zunubin kan Wani Zunubin kuma..? Mufeeda zata Cigaba da Rainan Cikinta kuma ta Haifeshi da Ikon Allah Acikin gidan nan Saboda Lura, Ɗanbatta ƙauye ne In Muka Tafi da Ita labarin zai yi Tambari Gwara abarta anan Ɗin Harta Haihu muga Abunda Allah zaiyi..."
Zabura Farida Tayi Tana Faɗin "Awani gidan..? Wallahi ba a nan gidan ba..? Bata isa ta haifamin Ɗan Shege a gida ba.." Tahir Dake Duƙe ya Ɗago da Jajayen idanuwansa yace "Toh sai dai ke ki bar gidan, Amma Babu fashi kamar Yadda Hakimi yace Mufeeda zata Haihu anan gidan Insha Allahu..." Ya faɗa yana mata wani kallon Tsana Baba Hakimi ya saki Murmushin Takaici Amma ƙasan Ransa yaji Daɗin Amsan da Tahir yabama Farida.
Kuka ta ƙara sakawa kafin tace "Haka kace..? Toh Wallahi sai dai na bar gidan ni ban zauna ba...Bazan zauna gida Ɗaya da karuwarka wacce kama Ciki ba.." Umma ce ta Make mata baki Tana Faɗin "Rufema mutane baki Mara Kunya Gaban iyayenshi kike gaya mai magana Haka Irin Tarbiyar da muka baki kenan..?"
Ta faɗa Tana kallonta Cikin ɓacin Rai Durƙushewa Farida Tayi Tana Cigaba da Gunjin kuka, Abba yace "Saurareni Da kyau Farida kinga matuƙar naji labarin kinbar gidan Mijinki Wallahi sai na Saɓa miki Sakarya mara Hankali Wacce iliminta da shekarunta basu amfana mata komai ba..Wallahi in baki Shiga Taitayinki ba Naji labarin kinyi ma Tahir ko ita yarinyar Wani Abu sai nazo Har gida nan gaban 'ya'yanki na barki Kwance ja'ira kawai.." Ya faɗa Cikin Fushi da Sauri Farida Ta Miƙe ta Haura sama Tana Gunjin kuka gaba ɗaya Aka bita da kallo kafin Baba Hakimi ya kaɗa kai yana Faɗin "Ayyah Ibrahim ga Wacce Girmanta da Shekarunta basu mata amfanin komai ba nan Zainabu..ai ko banza ta Haifi Farida Tsakani ga Allah bata Fita Hankali ba..?" Ya faɗa Cike da Takaici Goggo Abu Dake kuka ta Buɗe baki zatayi magana Baba Hakimi ya ɗaga mata hannu yana Faɗin "Karma ki ɓata bakinki...Yanzu Maganarki banda ɓata min rai Babu Abunda Zatayi Gwara ma ki rufe bakinki zai fi alheri agaremu Gabaki Ɗaya.." Goggo Abu Tayi ƙasa Dakai Hawaye na Zubar mata tace "Attahiru ka yafemin...Mufeeda kema ki yafemin.." Daga Haka ta miƙe ta Fita Zuwa Haraban Gidan Tana Kuka.
Baba Hakimi ne yace "Fulera kama Ɗiyarki ku Shiga Ciki ki ƙara lallashinta kinji itama ba laifinta bane.." Jiki ba ƙwari Inna ta Miƙe ta Kama Mufeeda Da ƙyar Dake kuka Suka Nufi Ɗakinta Iya Dake gefe sai Lokacin itama ta Miƙe tana Sharan Ƙwallah na Tausayin Waɗannan Ahalin Innaro Ta miƙe Ta Bita tana Faɗin "Kai ni Ɗakinki Iya na kama Ruwa nayi sallah.." Da Toh Iya ta karɓa kafin su Nufi Ɗakinta Kowa Zuciyarsa ba Daɗi.
Umma ma Miƙewa Tayi tana Faɗin "Bari naga Farida.." Kai Abba ya gyaɗa mata kafin Ta Haura sama tabar Baba Hakimi da Abba da Tahir da Ishaq Suna ƙara Jajanta lamarin.
Umma Kwance Taga Farida na Kuka, gefenta ta Zauna Tana Faɗin "Farida...Bai kamata kiyi kuka ba kamata yayi ki zauna kima kanki karatun ta Natsu ki gyara Kuskuranki, ki kama Allah ki kuma Roƙi gafaran Mijinki ki Rungumi 'ya'yanki kinga Abunda ya Faru..? Izina ne gareki da Kuma mata masu irin Halinki Daga ƙarshe ina Ja miki kunne da ki Natsu In ba Haka ba Wallahi Dagani Har Abbanki zamu Ɗauki mummanan mataki Akanki.."
Daga Haka ta miƙe ta Fice Daga Ɗakin Tana Fitowa su Baba Hakimi na Miƙewa, nan Suka ce kowa ya Fito zasu Wuce Inna Fulera Data kai Mufeeda Ɗaki ta saka Gefen Hijabinta tana Share mata ƙwallah Mufeeda na kallon Inna Fulera Take Fadin "Inna ki yafemin...Ba laifina bane.." Murmushi Inna Fulera ta mata kafin tace "Na yafe miki 'Yata..Allah yayi miki albarka ya kuma Saukeki lafiya.." Jin Haka yasa Mufeeda Ta Rungume Inna Fulera Suka Fashe da Kuka Lokaci Ɗaya, Iya Data leƙo kiran Inna Fulera itama sai dai taji ƙwallar Sun kawo mata, muryan Iya ce ta saka suka saki juna Nan take sanar da ita ta Fito zasu Koma.
Kumatun Mufeeda ta Shafa kafim tace "Ki kula da kanki kinji ko Mufeeda..? Allah na Tare Dake..." Daga Haka ta saki Hannunta ta Fice Daga Ɗakin Tana Sharan ƙwallah kan gado Mufeeda ta zame tana kuka mai Cin Rai tana jin kamar Bazata ƙara ganin Innar ta ta ba kenan.
A waje Suka samu Goggo Abu bayan Dukkansu Sun Fito Innaro ce kaɗai ta samu yin Sallah Sauran Baba Hakimi yace in Sun Isa gida kowa sai yayi..Abinci kuwa Da Iya Ta jera ba Wanda ya kalleshi Motar Su Abba da Umma ce Ta fara Fita Daga gidan sai ta Baba Hakimi Wanda Garzali zai Maidasu bayan Baba Hakimi yaja Tahir gefe ya ƙara mai Nasiha sosai ya kuma Nusar dashi ya barma Allah komai Da Haka Suka rabu Bayan Motar Ta Fice Daga Haraban Gidan
Ishaq ma bai koma gidan ba, Daga nan Sukayi sallama da Tahir ya Shiga Motarshi ya Fice Daga gidan Bayan shima ya ƙara bama Tahir ɗin baki sosai...Ya Daɗe Tsaye yana Sauke Tagwayen Ajiyar Zuciya Lokaci Ɗaya yana Goge Siririyar ƙwallar data Siraro mai ya Juya ya tunkari Cikin Falon gidan.
Nanny(me reno) Free book ne amma ga waɗanda ba za su iya jira ba akwai completed documemt 1k ne ku tura ta wannan acct ɗin 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK ko tuntuɓar waɗannam lambobin ***
***.
*Janafty*
*Aisha Alto..*