15
PAGE 15
Yau ta kama asabar, bayan gama ayyukan gida da a yanzu suka zame mata ruwan jiki, domin kuwa tun da ta zo Ammie bata san wani abu wanki ko wanke wanke hatta girki ita ke yin komai na cikin gidan. Sosai Ammie ke jin daɗin zama da ita haka zalika ita ma tana matuƙar jin daɗin zaman gidan dan Ammie bata rage ta da komai ba, shi ya sa ita ma take iya kacin ƙoƙarin ta dan ganin ta taimaka ta ko wace hanya ce ba don za ta iya biyan abin da tai mata ba sai don son ganin ta kyautata mata da kuma hushe ta da ƙanunun ayyuka, da farko dai tana ɗan shan wahalan aikin don abu ne da bata saba da shi ba tun tasowar ta masu aiki ke yi masu komai bata san aikin wahala komai ta nema take a ke samar mata shi koda kuwa babu shi a lokacin to Daddy sai ya sa an nemo an kawo ma shalelensa wannan duk cikin ƙaunar da ya ke mata.
Zuwa yanzu ta manta da rayuwata ta baya ta rumgume ƙaddarar ta da hannu biyu tana rayuwarta kamar dama a cikin ta ta taso, wani bin ma har ta kan manta kanta, ita kanta tana mamakin yadda ta amshi wannan rayuwar cikin sauki har ta saba da ita.
Kasancewar Ammie bata nan ta je barkan ƴar Harira ƙawarta da a ka kawo gida haihuwa, sai ya zamana Nazli ita kaɗai cikin gidan dan ta ƙi bin Ammie a cewar ta tana ayyuka ba za ta iya zuwa ba wani lokacin ta je kawai, dalilin Ammie na barin ta a gida kenan ta fita.
Bayan gama ayyukan gida ganin zaman kaɗaici ya yi mata yawa ya sa ta zura hijabi ta fito waje tsakar gidan, gwara ta ɗan fito ta zauna cikin mutane da zama ita ɗayan nan haka in ta zauna ma ba abin da za ta tsinana facce ta faɗa tunani tunanin da zai saka ta cikin damuwa ya tuna mata baya, ita kuma a yanzu abu na karshe da take so kenan a yanzu bata son dukkan wani abu da zai tuna mata baya ta riga da ta naɗe rayuwar Nazli Mukhtar Maraya bata kuma son komai da zai danganta ta da haka, gujewa hakan ya sa take shiga jama'a duk da ita ba ma'abociyar magana ba ce amma hakan na rage mata ƙunci sosai.
=======
Gidan shiru yaran duk sun tafi islamiyya sai ya kasance gidan ya yi tsit kowa na cikin ɗakinsa, kai tsaye ɓangaren Amarya ta nufa don sunfi sabo da ita duba da rashin tazarar shekaru da ke tsakanin su.
Sallama ta yi ta tsaya tana jiran a bata izinin shiga idon ta faɗa kan takalmin mijinta a waje, da sauri ta janye jiki cikin sanɗa ta juya za ta koma kenan muryar Amarya ta katse mata hanzari, fitowa Amarya ta yi tana amsa sallama.
Dalilin da ya sa ta tsaya kenan suka gaisa kana ta juya ta za koma Amarya ta tsaida da ita da faɗin. "Ki shigo mana ya kika juya kuma, ba fera kika zo mu yi?" Ɗan murmushin yaƙe ta sakar mata cikin kunyar shigo masu haka da ta yi ta ce.
"A'a nan ma ya isa ai mun gaisa na zo anjima hira, ki je ki ji da mai girma Oga yanzu dai." Fahimtar ina ta dusa ne ya sa amarya tuntsure da dariya ta nuna takalmin mijinta Nura. "Ba fa ya nan, wannan tun na jiya ne da ya shigo da su ban ɗaga ba." Kallon ban yarda ba Nazli ta bita da shi ta ce.
"Hmmm! Ni dai kin ga tafiyata nan ina da aiki da ban gama ba gobe na zo hirar." "Wai baki yarda bane?" Allah baya nan tun safe ya fita shi ai bai zama har warhaka bai fita kasuwa ba, shigo dan Allah bana son wasa." Jin haka Nazli ta sauke ajiyar zuciya suka shiga. "Wai da nufin ki da yana nan ba za ki shiga ba kenan?" Kai tsaye ta ce. "To me zai kawo ni ma tun farko idan na san yana nan?" Yanzun ma tsautsayi ya sa kika ganni ke da kullum sai dai a zo wajen ki baki shigowa wurin mu." "Afuwan ƴar Ammie, dama yana cikin raina yau in na gama ayyukana zan leƙo in anjima sai kika riga ni shigowa, amma idan magana ta gaskiya ake ai ko jiya na zo." Yar harar wasa Nazli ta yi mata. "Wan can zuwan kanki ne ai koko kika zo siya ba don ni kika zo ba, ni kam zuwan ƙarshe kenan kika sake ganin ƙafafuna a ɗakin ki to haihuwa kika yi." Murmushi Amarya ta yi ta gurgiza. "Allah ya shirye ki Nazli, amma ba sai ta kaimu ga haka ba daga yanzu za ki na gani na cikin sashen ku akai–akai har sai Ammie ta gaji da ganin fuskata ta kore ni." "Da kin yi abun kai." Cewar Nazli, ɗan ƙarewa falon kallo ta yi ganin ko ina a harkitse kaya ne ta ko ina kamar wanda a ka sauke wa dilar gwanjo. "Wannan fa, hala kin soma dilar gwanjo ba mu sani ba?" "Ina wa ya faɗa miki, nan fa dukkan kayan wardrobe ne jiya cikin neman abu na birkice ko ina shi ne yanzu na fidda komai ina nannaɗe su na maida su ciki." "Ai ya yi miki kyau." Daga haka ta sauko daga kan kujera ta soma taya ta naɗe kayan suna jerawa.
Can dai Nazli ta ɗago ta kalli Amarya ta ce. "Yau dai ban ga ƴar ɗakin ki ba?" ta tamabaya. "Wa! Mardeeyah?" Ta tafi aiki sai anjuma za ki ganta ta shigo." Da mamaki ta ce "aiki?" Dama tana zuwa aiki ne?" "Ehh aikatau ba, duk sati ta ke zuwa tana masu goge goge wata in ya ƙare kuma a sallame ta." Ɗan shiru Nazli ta yi tana tunani, da kamar ta yi magana amma sai ta kama bakinta ta yi shiru gudun kar Amarya ta yi tunanin wani abu ya sa kawai ta riƙe dumbin tambayoyin ta suka maida hankali kan wata hirar ta daban.
=======
Wunin ranar ta yi sa ne da sake–sake tana tunani ƙarshe ta yanke shawarar da zaman banza nan da take da za ta samu koda aikin aikatau ɗin nan ne zai rage mata wani raɗaɗin, tunda sana'ar da take sa ran yi bata samu ba kuma a yadda take ɗin nan yanzu ko ta samu sana'ar ina kuɗin jarin? tunda ta buga ta raya bata samu abin da ranta yake so sai ta gwada nan idan Allah ya sa ta samu kuɗi sun fara shigowa sai ta yi tunanin kalar sana'ar da za ta kama, don a yanzu dai kam ta gaji da zaman gunki da take gwara ta miƙe tsaye ta nema ita kamar sauran mutane tana yiwa kanta ta ragewa Ammie ɗawainiya koda na kanta kaɗai. Amma zama hannu rabbana haka ba zai yu ba, haka dai ta yi ta sake–sake har Ammie ta dawo.
Kwana biyu da maganar amma har yanzu abun bai bar zuciyarta ba, tunani kawai take na yadda za ta tunkari Ammie da maganar, tana tsoro da ta raddadin yadda za ta amshi maganar tsronta ɗaya Ammie kar ta yi mata gurguwar fahimta ta kalli abun da wani fuska. Bayan sake–sake da tunanin zuci ta yanke shawarar kawai ta faɗa mata riƙe abun a zuciya ba zai solving ɗin komai ba gwara ta fito su yi magana in ya so ta ganar da ita ta nuna mata muhimmancin aikin a wurin su baki ɗaya.
Dan haka cikin wani dare bayan sun yi sallar isha'i suna cikin cin abincin, duk minti sai ta ɗago ta kalli Ammie da ke cin tuwon ta cikin kwanciyar hankali tana lumshe idanu cikin jin dadin tuwon akasin Nazli da zuciyarta sai faman bugun tara tara take. Sai ta buɗe baki za ta yi magana sai kuma ta yi shiru ta ji ta kasa magana kamar wacce a ka ɗaurewa baki, lura da abin da take ne ya sa Ammie kallon ta amma bata ce komai ba ta bari in ta yi tsami ta ji, domin tun ba yau ba take lura da take taken ta da akwai abin da ke damunta amma ta kasa fitowa ta yi magana, ba sau ɗaya ba sau biyu ta ke ƙoƙarin tambayar ta ta ji me damuwarta amma sai ta hani kanta ta da yin hakan zuba mata ido ta yi ta ga iya gudun ruwan ta za ta fito ta yi magana ne ko kuwa za ta bar tsoron da ta gani a idanunta zai ci galaba kan haka.
Har suka zo kwanciya Nazli ta kasa magana sai rakuɓe–rakuɓe take tsaf Ammie na lura da abin da take amma sai ta kawar da kai ta yi kamar ba ta san komai ba, don bata son tursasa mata magana ta fi son don kanta duk lokacin da ta ji ya dace ta yi magana sai su yi.
Nazli ganin Ammie na shirin kwanciya ya sa ta ari jarumta da dakewa ta ce. "Ammie dama akwai maganar da nake son mu yi kuma ina bukatar shawarar ki cikin lamarin." "To Nazli ina jin ki faɗi me ya faru?" Ammie ta faɗa haka cikin tattaro dukkan hankalin ta gare ta tana fuskantar ta. A hankali Nazli ta matso gaba cikin sanyi jiki da sanyin murya ta ce. "Ammie dama kan zama na a haka bana komai ne kullum ina zaune wuri daya." ta dan dakata da maganar ta zubawa Ammie ido don nazartar ta ta ƙaramin hasken fitilar ɗakin da ke kunne take hango fuskarta, sai dai bata ga wata alama ko reaction da zai karya mata guiwa hakan sai ya ɗan sanyaya mata zuciya da jin lallai Ammie bata za ta yi mata bahagon fahimta ba.
jin ta yi shiru ya sa Ammie faɗin. "Cigaba mana ya kika yi shiru ina sauraran ki." Gyara zama ta yi kana ta daura da. "to shi ne abun na ɗan damuna ina son nima na fara wani abu da zai dinga ɗauke mini hankali, ko ba komai na dinga taimakawa da wani abun daɗin daɗawa ma zai rage min yawan tunani tunani, amma kafin haka ina bukatar yardar ki da Kuma shawarar ki a matsyinki ta babba kuma Uwa a gare ni wacce ta fini sanin daidai da rashinsa kuma na ki shi ne daidai."
Tunda ta soma magana Ammie ta yi shiru ta zuba mata ido tana sauraron ta har ta idda ayah, kana ta sauke ajiyar zuciya cikin hankali datako da nutsuwa irin na ta gyara zama daga cikin shangen na ta ta ce.
"Gaskiya kin yi zurfin tunani kuma na yi mutuƙar jin daɗi samu na da kika yi da maganar, da kika nema izini da kuma shawara maimakon ki yi gaban ki, hakan ya kuma sake tabbatar min da hankalinki. Na kuma gode da girma da darajar da kika nuna min a matsayina na uwar riƙon ki, a haƙiƙanin gaskiya kin yi tunani me kyau na kuma jin jina miki duba da ƙarancin shekarun ki har kika iya irin wannan tunanin dan ba kowa bane zai yi irin wannan tunanin."
"Ni ba zan hana ki sana'a ba don sana'a tana da matuƙar anfani musamman ga ƴa mace kuma ko ba komai kema kya yiwa kanki wasu abubuwan ki tallafi kanki don duk wanda ya riƙe sana'a da hannu biyu kuma da zuciya daya to in sha Allah ba zai taɓe ba sai ya ga alkairinta a gaba." Ta dakata ta numfasa kana ta ɗaura da.
"yanzu wacce sana'a kike sha'awar farawa?" Murmshi farin ciki Nazli ta sake cikin jin dadi da kuma ƙarfin guiwar da ta samu cikin kalaman Ammie ta ce. "A'a gaskiya tukun dai ban sani ba a yanzu, amma da wai ni hankali na ya fi karkata kan aiki koda aikatau ne na fara da shi kafin nan gaba na san sana'ar da zan kama." "Anya?" Za ki iya da aikin nan kuwa ba gwara ki samu wata sana'ar ki kama amma aikatau din nan sai na ke ganin wahalar taa za ta yi yawa yin aiki ƙarƙashin mutum ba abu ne mai sauƙi ba, amma idan kina ganin shi din ne hankalin ki ya fi kwanciya da ba damuwa Allah ya bada sa'a. Zan yi wa Turai magana don na ga ita kam tana cikin harkar har mutane take samarwa da aikin, zan mata magana in ya so ta nema miki aikin kema." "To Ammie na gode hakan ya yi."
======
Washe gari kamar yadda Ammie ta ce ɗin ta yi tattaki ta je gidan Turai ta same ta da maganar a samarwa da Nazli aiki, inda ita kuma tai mata alƙawarin in sha Allah da an samu aikin za ta tuntuɓe su. Zuwan ta da kawana biyu da yammacin talata suna zaune cikin yar barandan su Ammie na haɗa masu kwaɗon zogale Turai ta yi sallama. Bayan sun gaisa take sanar da su aiki fa ya samu, wata hamshakiyar hajiya ce tana da buƙatar mai aiki amma kuma ƙaramar yarinya ko tsohuwa take da bukatar. Sai dai za su tafi ta ganta idan ta ga ta yi mata walillahil hamdu, idan kuma ta ce a'a sai a jira na gaba. Haka dai Ammie ta bada goyon bayanta ba don ta so ba dan haka kawai take jin miss feeling a kan lamarin amma sai ta kawar da abun da take ji ta bisu da add'ua.
Ɓangaren Nazli kuwa ta yi farin ciki da aikin ko ba komai ita ma za ta fara earning kudi ta taimaki kanta ta rage wani radadin, duk da a ƙasan ranta tana jin wani yanaye, wai ita Nazlin Daddy da aikin aikatau?" Lallai rayuwa juyi juyi ko a mafarki a ka faɗa mata ga inda za ta wayi gari ta ganta cikin rayuwar nan to za ta ƙaryarta amma sai ga zahiri ba wasa ko mafarki ba za ta je wani gida domin yin aikatau. Ganin za ta komai ruwa ya sa ta saurin kawar da tunanin.
Washe gari da safe kuwa sai ga Turai za ta kaita ta ga wurin, ta shirya tsaf cikin jar atamfa riga da skirt da suka dan kamata, ɗinkin ya fito da zallan shape dinta, hips dinta sun sake bajewa cikin skirt ɗin, kayan ba ƙaramin yi mata kyau suka yi ba, bata yi wani kwalliya ba kawai ta haɗa dogon gashin ta ta daure kana ta tusa cikin hula ta ta dɗura hijab mai hannu da ya kai mata iya guiwa, ma sha Allah ɓakin hijabin ya sake fito da farar fatar ta tudun gashin kanta kuwa idan baka sani ba sai ka dauka acuci maza ta saka saboda yadda ta yi parking gashin cikin hula cib ya zauna, dressing ne very simple amma sai ka ga irin kyauwun da ta yi.
Tasbihi Ammie ta soma a zuciyarta tana sake yabon kyauwun da yar tata ke da shi, ganin ta dauke purse tana shirin fita ya sa ta fadin. "to shafa kwalli mana haka za ki fita fuska fayau ba powder bare kwalli?" Cikin sanyinta ta koma ɗakin ta yi abin da Ammie ta ce kana ta fita suka yi mata sallam suka fita, yayin da ta bisu da add'uar samun nasara.
A hanya dai haka Turai ke ja mata kunne kan Hajiyar ta yi mata bayanin dukkan abin da Hajiyar ke so da Wanda bata so, ta yi mata bayani da kuma kalan mutanen gidan. A nan ne ma take sake sanin ashe mijin Hajiyar ma soja ne da ke riƙe da babban muƙami. Har suka isa Turai bata bar yi mata gargadi ba.