KARFE DÜKKA KARFE NE

BABI NA SHA HUDU

by @maidambu41

KARFE DUKKA KARFE NE...!!!

{Zanen ƙaddarar Falilah}

BABI NA SHA HUDU

Ina godiya Aunty Nuratu da gyaran da kika min Ahmadi shine MIJIN Falilah na bakwai na gode sosai 😻🥰😍

🌸 Assalamu Alaikum Yan'uwa Mata.

Kowace mace tana son ta ga kitchen ɗinta cikin tsari da kyau, tare da kayan zamani masu inganci. Amma abin da kan hana mutane shi ne tara kuɗin saye lokaci guda.

Shin tara kuɗin saye ne ke miki wahala?

Ko kuma idan kin tara sai wasu buƙatu su sa ki kashe su?

Ki kwantar da hankalinki, domin MA KITCHEN ta zo da mafita.

Mun buɗe Adashen Kayan Kitchen domin ki mallaki kayan da kike buri cikin sauƙi, ba tare da wahalar tara kuɗi lokaci guda ba.

✨ Abubuwan da za ki samu:

✅ Kayan kitchen na zamani masu inganci.

✅ Farashi mai sauƙi.

✅ Adashe mai sauƙi da kwanciyar hankali.

✅ Ana kai kaya zuwa duk inda kike.

✅ Biyan kuɗi a hankali cikin sauƙi.

Za a fara nan ba da jimawa ba, In shaa Allah.

📞 WhatsApp/Call: ***

📲 Shiga WhatsApp Group ɗinmu domin samun cikakken bayani da fara rajista:

***

🌹 Arha ta fi bashi, adashe kuma ta fi bashi kwanciyar hankali. Ki yi rajista tun da wuri, ki mallaki kitchen ɗin mafarkinki cikin sauƙi.

MA KITCHEN – Muna tare da ke har ki cika kitchen ɗinki da kayan da kike buri. 💚

Ashe nayi kewa gida haka ban sani ba sai da  nayi barci har da makara sannan na gane inda nake ba, kai karshe Sai day Hajja Mama ta tashe ni, nayi wanka da alwala, sannan na gabatar da sallah asuba da ya kwace min na jima ina addu'a zaman lafiya a rayuwata da Ahmadi. Wayata Na duba Na ba Kiran Ya Nafi'ua kamar zai kashe min battery din wayata, ina dauka ya sauke ajiyar  zuciya ya ce min. "Mrs Lamido ina ba matsala ko?" Murmushi nayi ina daukar goran ruwa na kai bakina na ce mishi. "Babu sai na albarkanka kawai nake jira." Na fada ina blushing, "Allah ya miki albarka, ya baki zaman lafiya yasa karshen wahalar kenan!"

"Amin Daddy."

"Hmm!" Ya ce min, "Na gode sosai" na ce mishi ina kashe wayar, sannan na je parlour na karya, ina gamawa na fito anan nake Jin labarin wai an fasa kai ni yola kayana kawai zaa kai, mu wuce Abuja, haka naji ba dadi kayana aka wuce da shi mu kuma bayan laasar mika wuce abuja har da Ya Nafi'u wanda ina yawan ganin dan yanayın damuwa a tare da shi,karshe na ce mishi. "Daddy lafiya dai ko?"  "Ba kome Falilah!" Kusan yadda nake hango damuwa a fuskanshi yasa naji bana daukin auren.

     Amma haka na share yayuna mata da suka rakoni aka wuce gidan da ahmadi ya gaya musu , sannan mun samu Ya Nafi'u ya saka kome ashe abin da ya tsayar da shi Kenan, idanuna sai da ya cika da kwalla, haka na yi ta kallon gidan cike da farın çıkı Musamman part dina,  can gefen part dina na Matar Ahmadi ce Mariya Maman Basma da Bassam. Muna jin hayaniyar mutane amma basu zo inda muke ba haka muma bamu je ba, har bayan isha yayuna suka wuce gidan Ya Nafi'u da nasihar nayi hakuri.

    A kaidar aure dole wurina zai zo, amma tunda ya shigo gidan ake tafka rigima kwana suka yi aka abu daya yau kuma ga Inda Allah ya kawo ni, haka na kwana kamar mayya washe gari da asuban farı sai ga shi ban nuna mishi na damu ba amma kuma shi na ga yadda ya damu, har sai da na ce mishi ba kome fa, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya, tun daga ranar abubuwa suke faruwa, wani lokaci yayi fushi wani lokaci ya kasa barcı, haka muka yi ta rayuwa ta wurinsa ban da matsala sai ta wurin matarshi rashin mutunci kuwa sai da na gaji na fara biye mata, domin ta ishe shi, ganin shima bata kyale shi ba na Yankewa kaina hukukcim kin daukar çıkı saboda fitinar Mariah da mahaifiyarshi.

      Tunda aka yi auren bamu je Yola ba sai sallah,  a zuwana na sha wulakanci, wani abin da ya kwantar min da hankali yan uwansa mata, alkhairin da nake musu yasa suka gane ni bani da matsala,  sai ita kai ba sai Mama ta ce na musu asiri ba, haka nayi ta hakuri da yanayin har muka gama Hutu muka dawo, itama Mariah da muka dawo ta kara bude mana huta, wani abinda yasa na yiwa Mariah uzuri jahila ce, bata da ilimin addini balle na zamanı, kun ga ai sai duaa.

   Sai da na kwashe wata goma  cib na gane ba zan iya rabuwa da Ahmadi ba, shima ba zai iya rabuwa da ni ba, sannan na dakatar da maganin da nake sha na Hana daukar ciki na kwantar da hankalina domin yana gaya min yana son haihuwa dağa gare ni,  har na koma ga Allah ba zan daina kaunar Ahmadi ba, ina son Ahmadina, ina kaunar Ahmadina, ranar da na gaya mishi ina da ciki a ranar na ga yadda take rawan jiki, kai ko a tv ya ga abu ya mishi sai na sayo ya kawo mana, kada ku yi tsammanin Iya ni ce aa har da Mariah da mahaifiyarshi.

        Ban sake Jin ina son zama da shi ba, sai da Mariah ta bashi zabi ita ko ni? Ya ce mata sau dubu ni zai zaba domin rashina ya saka ya aureta, budar bakinta ta ce mishi. "Karuwa dai wacce aka Fas'a aurenta saboda tayı abin kunya, " a ranar na gane mai hakuri bai iya fushi ba, sake ta yayi ta Kama hanyar yola ni kuma ya mana visa muka bar kasar, ashe wani course ne na wata biyu da rabi suka tura shi, a kasar Holland, anan nayi fama da laulayina, har ya gama abinda ya kawo shi muka dawo gida, muna dawowa bane wannan

Alamarin ya faru. Mariah ta kashe min mijina dük da kwanansa ya kare, nima kashe ni tayı da raina, a duk lokacin da na tuna da Ahmadi sai nayiwa Mariya Allah ya isa domin ta katse min Jin dadin rayuwata."

   Na fada Nina fashewa da kuka, Mubarak ya saka kai ya fita yana ji a ransa, falilah ba saarshi  bace, har abada tayı mishi nisa amma kuma

Akwa wani abin da ya kasa fahimta. Haka ta wuce sallah. Bayan ya ıdar zai koma çıkın asibitin ya hango Ya Man da sauri ya isa wurinshi. "Ya Man?"

   Tsayawa Ya Man yayı yana murmushi, "tambayar ka nake son yi." "Ina jinka Nurse Mubarak."

"Ya Man kai ka haifi Nafi'u?" Kura mishi ido yayi kafin ya ce mishi. "Dan abokina ne da yazo karatu tun yana Yaro ya rasa iyayensa, me yasa ka tambaye ni?" Mubarak kamar zai

Yi kuka ya ce mishi. "Saboda naji a jikina ba jini ne ya hada Ya Nafi'u da Falilah ba, soyayya ce da Allah yake daurawa bawansa, a yanzu na gane dalilin da yasa yake kaf-kaf da Falilah saboda a koda yaushe dai iya samunta, Ya Man ka bashi Falilah Ya Nafi'u shine zai iya rayuwa da ita ba tare da tayı kuka ba. A yanzu na gane haka "

    "Bani da ilimin kaddara amma idan sun dace da juna har kaddara ta basu damar haka idan kuma ta hada ta da wani lafiya lau." Ya Man ya gaya mishi yana barın wurin.

      Bayan an gama min koma aka shiga da ni aiki, da misalin karfe goma na dare aka fito da ni, tare da Yarana biyu mace da namiji, babu Wanda ya kawo biyu zaa ciro min, domin cikinsu bai muna haka ba, a lokacin da aka yi aikin Ya Nafi'u' yana asibitin ana ciro babyn aka mika mishi, shi ya musu huduba, aka saka Ahmad Ahmadi Lamido, macen kuwa Fatimah ya saka mata, sunan Hajja Mamah, lokacin da aka fito da ni yana tsaye a gefena. "Sannu kin ji." Gyada mishi kai nayi Sannan aka wuce da ni dakin hutu, a nan na ga su Hajja Mama da Aunty Sadiyah, a hankali na cigaba da barci.

——-