Chapter 12
Zuhura ta gama shirinta tsaf, cikin doguwar riga ce ta atamfa mai launin ruwan madara, an yi mata ɗinkin zamani mai matuƙar kyau. Ta ɗaura ɗankwalin atamfar cikin tsari mai kyau da ya fito da kyakkyawar fuskarta, ta saka kwalliya a idonta, da man leɓe, ta yi kyau sosai. A gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta. Murmushi ta yi na jin daɗin yadda ta ga ta yi kyau. A hankali ta fito daga ɗakinta bayan ma'aikaciyar gidan ta sanar da ita cewar Alhaji ya ce ta je baƙonta ya iso. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin falon tana taku ɗai-ɗai. Ƙamshin turarenta ne ya daki hancinsa Sudais, cikin nutsuwa ya ɗago da kansa ya kalle ta na ɗan lokaci sannan ya amsa mata sallamar kafin ya mayar da hankalinsa ga danna wayarsa.
Zama ta yi tana ƙare masa kallo. A zahiri ma yafi kyau.
Cikin karairaya ta ce "Barka da yamma, ina fatan ka zo lafiya?".
Ba tare da ya ɗago da kansa ba ya ce "Yawwa barka dai, kina lafiya?". Cikin iyayi ta ce "Lafiya ƙalau Alhamdulillah. Ya gida ya su Momyna?".
"Alhamdulillah Mammy tana lafiya". Ya sake ba ta amsa. "Au Mammy ce? To a gaisar mini da ita sosai". Ya ce "Za ta ji". Shiru ne ya shiga tsakaninsu. Zuhura ta zuba masa ido tana nazarinsa, shi kuwa Sudais ci gaba da danne-dannensa ya yi, daga bisani ya ɗago da kansa ya kalle ta sannan ya ce "Ni zan wuce".
Zuhura ta ce "A'a da wuri haka? Na ga ma ko abincin da aka a jiye maka ba ka ci ba". Sudais ya ce "Na ƙoshi". Daga haka ya tashi yana ƙoƙarin barin falon. Zuhura ta ce "Amma haka za mu rabu ba tare da mun karɓi lambar juna ba?".
Tsayawa ya yi ya ce "Ba ni ta ki lambar". Zuhura ta ce "A'a ba ni taka dai". A gurguje ya karanto mata lambarsa sannan ya yi mata sallama ya fita, ba tare da ya tsaya sun yi sallama da Sardauna ba ya ja motarsa ya bar gidan.
Yana fita Zuhura ta ce "Kan bala'i yau naga wanda ya dama ni ya shanye a gurin jan aji, hmmm da sannu za ka shigo hannu. Duk wannan shan ƙamshi sai ka zo ka na ƴar murya a gurina".
Sudais kuwa yana fita kai tsaye gida ya nufa domin a mugun gajiye yake, dama daga gurin aiki ne ya wuce gidan saboda ya yi masa alƙawarin zai je. Yana isa gida ɗakinsa ya wuce ya watsa ruwa, sannan ya kwanta domin rage gajiyar da ya kwaso, haka kawai Zuhura ta faɗo masa a rai. A fili ya ce "Ba laifi yarinyar ta haɗu". Daga haka ya lumshe idonsa yana jin wani bacci na taso masa.
****
Ana gobe auren ƙawar su Ma'u Baba Saminu ya zo daga ƙauye duba jikin Abida da ya samu labarin ba ta da lafiya. Baba Saminu Yaya ne a gurin baban su Ma'u, sai dai shi a ƙauye yake da zama shi da sauran yan'uwansa, asalin su ƴan ƙauye Gwagwa ne, Baban su Ma'u ne ya zauna a birni tare da iyalinsa kafin Allah ya yi masa rasuwa. Dalilin ci rani da ya zo sai ya samu aikin gadi a wani gurin, hakan ne ya sa ya ɗakko iyalinsa ya dawo da su nan ya kama haya. A lokacin Aliyu na da shekaru goma sha biyar, kaɗan-kaɗan yana tara kuɗinsa har ya samu wani ƙaramin gida ya saya a nan. Bayan haihuwar Ma'u ne Allah ya yi masa rasuwa.
Sosai suka ji daɗin ganinsa, ya ga jikin Abida da sauƙi sosai. Sai dai kallo ɗaya ya yi wa Halima ya ce "Subhanallah! Ƴata ba ki da lafiya ne?". Kafin ta yi magana Inna ta ce "To gata nan dai, kullum sai rama take yi kuma an tambaye ta ta ce ba ta san abin da yake damunta ba". Ƙuri ya yi da ido yana kallonta, kafin ya sauke numfashi ya ce "Allah ya ba ki lafiya ƴata, Ubangiji ya tsare daga sharrin wannan ciwon".
Suka amsa da "Amin"
Baba Saminu ya ce "Yawwa dalilin zuwa shi ne, na farko dai na zo duba jikin yarinyar nan ne, sai kuma abu na biyu a kan batun taron da muke yi ne duk bayan shekara, kusan sati ɗaya da ya wuce manyan garin sun tsayar da ranar taron. Na yi ta ƙoƙarin nemanku a waya ban samu ba, kuma gashi lokaci na ƙaratowa, yanzu haka kwana biyu ya rage a yi taron. Kun san da cewar duk in da ɗan'uwa yake dole ne ya halacci taron, idan bai samu zuwa ba to ya tura ko da mutum ɗaya ne a cikin zuri'arsa. Shi ne na yo tattaki na zo da kaina domin in sanar daku, saboda haka ya kamata ku shirya ku je a yi daku, idan ma ba za ku samu zuwa duka ba to kai Aliyu sai ka shirya ka je".
Numfashi Inna ta sauke, ta ce "Ma sha Allah, kwanaki ba wuya yanzu shekara har ta zagayo? Shikenan ba damuwa Yaya, ina ga sai Gadanga ya shirya ya je". Ta yi maganar tana kallon Aliyu, ɓa ta fuska ya yi, saboda ba ya son zuwa taron nan, hayaniyar nan da ake yi da kaɗe-kaɗe ne baya so, gyaran murya ya yi ya ce "Inna a wannan karon sai dai a yi haƙuri saboda ba zan samu damar zuwa ba. Akwai wani babban uzuri da nake da shi a ranar, aikin ne zan samu kuma a ranar ne zanje na amsa tambayoyin da za a yi mini, saboda haka ina ga Baba sai a yi haƙuri a yi mana uzuri na wannan shekarar".
"Ba zai yiwu ba Aliyu, dole ne sai ɗayanku ya je an gudanar da bikin da shi kamar yadda aka saba, ko da Mustapha baya raye dole ne a ga zuri'arsa a gurin. Saboda haka na karɓi uzurinka, ga Asma'u nan sai ta shirya mu tafi tare, idan aka gama bikin washe gari sai ta dawo". Kasa musa masa suka yi. Duk da cewar da ya ambaci zai tafi da Ma'u sai da gaban Inna ya yi dukan uku-uku. Ma'u kuwa cewa ta yi "A'a Inna ni ba zan je ba, gobe ake bikin Hadiza, kuma ni ce ƙawar amary..." Kallon da Aliyu ne ya yi mata ya sa babu shiru ta yi gum da bakinta. Babu yadda ta iya, haka tana ji, tana gani, ƙarfe uku da rabi Baba Saminu ya yi musu sallama, tare da Ma'u suka tafi.
*****
Faruk na kwace a ɗakinsa Mammy ta shigo da sallama, tashi zaune ya yi ya ce "Mammyna ke ce da kanki? Ai da waya kika yi mini sai na je har ɗaki na same ki". Dariya ta yi tana faɗin "A'a na hutar da kai, ka ga tun ɗazu nake kiran wayar Yayanka ba ta shiga. Kira mini shi a wayarka ko Allah zai sa ta shiga".
Faruk ya ce "Ok to bari na kira shi" kiran wayar Sudais ya yi sai dai shima a kashe ya ji ta. Faruk ya ce "Mammy ba ta shiga".
Cikin damuwa Mammy ta ce "Sudais baya rufe wayarsa, Allah ya sa lafiya, yau tun safe ya fita ya ce mini zai je wani guri". Faruk ya ce "Ki kwantar da hankalinki Mammy in sha Allah yana nan lafiya, maybe matsalar network ne, amma bari in kira Yaya Hanif in ji ko suna tare".
"Yawwa Faruk kira shi".
Kiran wayar Hanif ya yi, nan take ya ɗaga yana faɗin "Hello Faruk kana lafiya? Ya Mammy da Zahra?". Faruk ya ce "Lafiya ƙalau Alhamdulillah Yaya, su Mammy na nan ƙalau, yanzu haka ma ita ta saka na kira ka ko kuna tare da Yaya Sudais ta kira wayarsa ne ba ta shiga". Hanif ya ce "Allah Sarki Mammy, ba ma tare da shi, ya je wani ƙauye ne da aka tura shi a gurin aikinsu. Ko ɗazu mun yi waya da shi, ya ce mini gashi nan a kan hanyar dawowa, ina tunanin matsalar network ne, amma babu wata matsala in sha Allah kafin magariba zai ƙaraso". Faruk ya ce "To shikenan mun gode sosai". Daga haka ya kashe wayar, Mammy ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah ya dawo da shi lafiya". Faruk ya amsa da "Amin" yana faɗin "Ashe dai Mammy na son ɗanta da yawa, ji yadda duk kika ɗaga hankalinki". Ya yi maganar yana dariya.
Ita ma dariyar ta yi ta ce "Eh mana ai dukanku ina sonku, ƙaunarku a jinana take".
"Allah ya bar mana ke Mammynmu" Mammy ta amsa da "Amin" tare da barin ɗakin.
****
"Abbi"
"Na'am Zuhuran Abbi" .
"Abbi ba ka tambaye ni ya muka yi da Adam ba".
Ya yi murmushi sannan ya ce "To tambayar me zan yi miki Zuhura? Ai na san halinki idan har ya yi miki ina zamana za ki same ni da zancen".
Rufe fuskarta ta yi tana dariya ta ce "Allah Abbi ya yi mini ina sonsa ni dai, sai dai ban sani ba ko shi ya ga na yi masa". Sardauna ya ce "Ai dama na san za ki so shi, saboda babu macen da za ga Adam ba ta ji ya burge ta ba. Yanzu aiki ya rage gare ki sai ki yi ƙoƙarin jawo ra'ayinsa a kanki, idan Allah ya nufa kun fahimci juna shikenan".
Zuhura ta ce "To shikenan Abbi ka yi mini addu'a, Allah ya sa ya so ni kamar yadda nake sonsa" . Ya ce "In sha Allah zan yi miki Zuhurata".
Ta mayar da dubanta ga Hajiya Bilki dake zaune tana kallonsu ta ce "Mamana kema ki yi mini addu'a kin ji". Hajiya Bilki ta yi dariya ta ce "Addu'a ai kullum cikin yi miki ita nake Zuhura, Allah ya tabbatar da alkhairi".
Ta amsa da "Amin" tana jin daɗin addu'ar da iyayen na ta suka yi mata.
*****
Bayan sallan isha, Aliyu na zaune tsakar gida yana ɓare wa Abida ayaba tana ci, Inna ta fito daga ɗakinta tana faɗin "Gadanga ko ka yi waya da Babanku Saminu ne? Tun ɗazu nake kiran wayarsa ba ta shiga, in ji ko sun isa lafiya".
Aliyu ya ce "Ni ma na yi ta kiran wayar ban same shi ba, ina ga ko babu caji ne a wayar, amma na san zuwa yanzu sun isa".
Jiki a sanyaye ta ce "To Allah ya sa". Ta yi maganar tana ƙoƙarin juyawa ta koma ɗaki sai ta ji kamar nishin mutum a cikin soron gidan.
"Gadanga kamar nishi nake ji a soro" ta yi maganar tana kallonsa, tashi Aliyu ya yi ba tare da ya ce ƙala ba ya nufi soron gidan, kasancewar dare ne ya sa shi haska fitilar wayarsa. Ma'u ya gani a kwance jikinta busu-busu da ƙasa, tana fitar da numfashi da ƙyar. Da sauri ya ce "Innalillahi wa inna ilaihim raji'un, ke lafiya? Me ya same ki? Ina Baban yake?".
Da ƙyar ta fizgo maganar ta ce "Baba sun kashe shi". Daga haka ta yi shiru, salati Aliyu ya yi yana faɗin "Asma'u ki yi mini magana, su waye suka kashe shi? Kuma a ina na?".
Amanarcool
***