Chapter 3
by @oumfatayat
*FARAUTAR MUTUNCI*
Na’ima Daƙayyawa (Oum Fatayat)
SAHAFI NA UKU
Dakiɗo mai gadi ne ya bisu da addu’ar Allah ya tsare.
Sasanyar iskar da take busowa ne, ya ƙarawa Nuri shauƙi, tafiya take tamkar barewar da ta ke cikin alƙaryar dajin da yake cike da furanni. Ko ina na layin nasu yayi tsit, da sauri Mahmud ya mata ni sa, sai kawai ya juyo yake tafiya da baya da baya ya fuskance ta.
“Ɗagwas, ɗas, cacas, tako mana ‘yan matana , Sarauniyata abar ƙauna ta, inye mu ganta” shi ne abun da Mahmud ɗin yake faɗa yana tafiya da baya-baya yana kallon yadda take taku.
Can kuma sai ya tsaya cak ya nustu sosai, ya tafi wata duniyar, wadda har ta ƙaraso inda ya take bai luraba.
Hura masa iska tayi a fuskarsa, kana ya yi ajiyar wani taƙaitaccen nun fashi a hankali.
“Yane my guy,Tunanin fa?”.
“Gaskiya Nuri na fasa fitar nan”.
Zaro ido ta yi wanda suke kama da watan da ke tsakiyar samaniyan da take baƙaƙirin.
“Ni wallahi ina so muje fa” Bubbuga ƙafa ta fara yi a tsaye ds sauri ya zo ya rungumota, hakan ne ya sa ta tsaya cak.
“A’a Nuri muje kawai, kuma mai yasa za ki fara buga ƙafa idan wani yazo ya ganki a haka ai bazan yafewa kaina ba, ni fa abunda yasa gani nayi kin ƙara wani kyau, wallahi ga shi yadda kike tafiya tamkar ɗawisu, bana so kowa ya gane min ke a haka”.
“To, tunda ba muyi nisa ba mu koma mu ɗakko motar, idan muka je muka siyo Ice cream sai mu dawo, ko Hubby”. Ta ƙarasa maganar tana kallon idon Mahmud ɗin.
“E, to mu koma kawai ɗin, hankalina zai fi kwanciya”.
Riƙe mata hannu yayi ƙam-ƙam tamkar dai wanda za a ƙwace masa ita, langwaɓo kanta tai a kan kafaɗarsa ya kama ƙugunta da ɗaya hanun nan suka koma gidan, suna tafiya suna tattauna lamarin da ya shafi rayiwarsu.
Motar suka shiga kana suka fita, tuƙi yake cikin nutsuwa, suna cikin tafiya ne ya shafo gefen kumatunta, kana ya ce “One” Murmushi ta yi don ya tuno mata sunan da yake faɗa mata a lokacin da tana ‘yan matanci, idan ya ce mata One ita kuma sai ta ce masa Only.
“Kinsan menene” girgiza kai ta yi batare da tayi magana ba. “So nake ki samo min ƙawa nima, don na gaji da haɗinkan da kuke min ke da Al’tab yawwa”.
Tuntsirewa tayi da dariya sosai, tana nuna shi da ɗan yatsa, da yaga bata da niyyar ta daina dariyar ne, ya tsaya da tuƙin, ya gangara bakin titi, bata an karaba sai jin ya haɗe bakinsa da nata.
Bai sake taba har sai da ya gamsu. kallonta ya yi da kyau “Nuri ba wasa nake ba so nake ki sake haihuwa, don haka muje a cire miki tsarin iyalin nan, kinga Al’tab shekararsa 7 da ‘yan watanni, kafin ki sake haihuwa sai ya zama ɗan sheka 8 da ɗoriya”.
Mirmushi ta yi kana ta ce “Only da ma ai kai ne ka ce na huta, ka sanni da son na yi ta haihuwa ai, abunda yasa nake dariya gani nayi yau na ga alama tun safe da rigima ka tashi, in sha Allahu gobe sai na je a sibita a cire, hakan ya yi?”.
Cikin farim ciki ya cigaba da tuƙin 24 hours Store and more suka ƙarsa nan ya fita ya musu siyaya, suka kama hanya sai gida, suna shiga cilak ya ɗauƙe ta tare da kayan gaba ɗaya, bai tsaya a ko ina ba sai Ɗakinsa a hankali ya fara rage mata kayan da yake jikinta ya ɗauke ta ya shiga banɗaki , wanka suka yi kana suka fito cikin bege da ƙaunar juna.
Bugun ƙofar da ake yiwa falon na su ne, yasa Mahmud yin shiru na wasu 'yan lokuta jin yadda bugun ke ƙaruwa ne yasa shi buɗe ƙofat, tundaga ƙafafuwanta ya gane ita ce.
Haba dama yasan duk duniyar nan ba wanda zai masa haka a wannan lokacin, sai ranki yadaɗe binki dole Haj…..
بقلم أم فتيات 👧👧👧✍🏼…..