MARYAMA

Page 01

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫
BY
Ummu Fadeela
Typing... 📲
EPISODE 01
Bismillahi Rahmani-Raheem. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin sammai da ƙassai. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga shugaba, jagaba Annabi Muhammad (S.A.W), da iyalan gidansa da sahabbansa baki ɗaya.
KHALEEFA BIN ZAYED AL NAHYAN STREET, ABU DHABI CITY (UAE).
Katafariyar unguwa ce da ke cikin babban birnin HaÉ—aÉ—É—iyar Daular Larabawa wanda aka fi sani da Abu Dhabi. Unguwa ce mai É—auke da rukunin gidaje masu kama da aljannar duniya...
Lumshe kyawawan fararen idanuna na yi. Na daÉ—e ina jin yadda ake yabon kyawun zubin halittar idanuna; mutane da dama idan sun tashi yabon kyan halitta ta, sukan kira ni da "mai idon madara" tsabar irin hasken da kyawun da Allah ya ba ni. Amma a halin da nake ciki yanzu, sabanin kasancewar su launin madara, idanun sun yi jajur kai kace attaruhu aka É—aka aka watsa a cikinsu, ko kuma na kwana uku ina kuka ba tare da tsagaitawa ba. Sai dai ba ko É—aya daga ciki; tsabar tashin hankalin da nake ciki ne ya haddasa mini canzawar launin idon.
A hankali na juya na kuma kallon shi, zuciyata na bugawa da ƙarfi da ƙarfi, yayin da nauyin da kaina ya yi ya haddasa mini ganin dishi-dishi... Yana durƙushe gaban gadon da nake zaune ya ba ni baya, yana ta daddaure hodar iblis (C0C@!NE) cikin wasu ƙananan ledojin nylon. Cikin sauri-sauri yake aikin, wanda duk bayan daƙiƙa ɗaya sai ya ɗaga kai ya kalli ƙofa.
Runtse idanuna na kuma yi, zuciyata na tsananta bugu yayin da nake tuna cewa wai ni ce zan haɗiye gaba ɗaya wannan hodar iblis ɗin a cikin cikina, in yi safararta zuwa Nigeria. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, na furta cikin raina, kana na bi dogayen ƙafafuna farare sol da kallo. Ɗaure suke cikin sarƙoƙi (chains) sakamakon yunkurin guduwar da na yi, hakan ya sa suka ɗaure ni. Zuwa yanzu na tabbatar roƙo da magiya ba za su yi mini amfani ba.
"You have to be brave," zuciyata ta faɗa mini. Tabbas dabara ce kawai zan yi da taimakon Ubangiji in bar wurin nan; idan ba haka ba, rayuwata ta ƙare. Safarar cocaine ba ƙaramin haɗari (risky) ba ne ga rayuwata. Cikina ne ya hautsine gami da ba da sautin kululululu sakamakon tunawa da na yi wai haɗiyar waɗannan ledodin zan yi a cikina. Duk da ya sanar da ni hanyoyin da za a bi a fitar da su idan mun isa Nigeria, hakan bai rage ko da ƙaso ɗaya cikin ɗari na irin tsoratar da na yi ba.
A hankali na fara bin ɗakin da kallo ko zan dace. Aiko idanuna suka sauka kan bedside lamp dake kusa da ni, ga kuma wani tangaran mai ɗauke da furen rose duk a wuri ɗaya. Cikin dabara na kai hannuna duk biyun na ɗauki lamp ɗin da kuma furen (flower vase) ɗin... Ya duƙufa sai aiki yake a gaggauce, hakan ya sa bai maida hankali kaina ba.
Runtse idanu na yi ina tabbatar wa kaina abin da zan aikata shi ne daidai. Bai yi aune ba ya ji saukar tangaran a ƙeyarsa, ji kake garammm! Cikin azama ya juyo jin abin da bai yi tsammani ba (unexpected). Yana juyowa na kuma rota masa bedside lamp ɗin a daidai gurin. Take ya yi baya-baya, ya ƙwala wani irin ihun kiran sunana: "MARYAMAAAA!" Ya faɗi ƙasa, jini ya fara malala a wurin.
Da gaggawa na fara ƙoƙarin kwance sarƙoƙin da ya ɗaure mini a ƙafata. Sai a lokacin na kula da cewa tunda ya faɗi bai ƙara motsi ba, ga jini dake tsartuwa ta ƙeyarsa, baki, har da hanci. Zuciyata ce ta kuma bugawa da ƙarfi. Ɗan matsawa na yi kusa da shi, a hankali na ce, "ABDALLAH?" Amma shiru, ko motsi bai yi ba. Na ɗaga hannunshi ina sakewa, hannun ya dawo matacce.
Mikewa na yi ina ja da baya-baya yayin da wani irin jiri ke kwasata. "Ya mutu!" na furta da ƙarfi. A lokaci ɗaya kuma wani irin ƙarrawa ya yi ruri cikin ƙwakwalwata: na kashe shi! Idan aka kama ni shikenan, ba mai ƙara jin labarina a duniyar nan...
Ba tare da wani dogon tunani ba, na janyo bedside drawer, na cire fasfo (passport) nawa da kuma credit card, sai wayoyina guda biyu da kuma tablet tawa. Cikin sauri-sauri na kuma zuge wata doguwar drowar mai ɗauke da kayayyakina jere reras; ba tare da na bi ta kansu ba, na janyo wata 'yar akwati na buɗe. American dollars ne shimfiɗe ɗauri-ɗauri. Duk ƙaunata ga kuɗi, duk irin wuyar da na sha da irin haɗarurrukan da na shiga wurin tara su, amma na kasa ɗaukarsu. Tabbas wani tashin hankalin ya fi gaban wani.
Ɗauri biyu kawai na ɗauka, na sa su tare da wayoyina da na riga na sa su a flight mode. Na yafa gyalen baƙar abayana cikin hanzari, kana na bi gefen Abdallah na fice daga ɗakin.
"Act smart Maryama, this is Dubai, not Abuja, Nigeria," zuciyata ke ba ni shawara. Sai dai duk yadda na so bin shawarar zuciyata, na kasa; jikina sai rawa yake, yayin da launin idanuna ke ƙara sauyawa saboda tsananin tashin hankali. Cikin sa'a na fita daga gidan ba tare da mai gadi ya tuhume ni ba, sanin matsayina da ya yi a gun mai gidan. Taksi (cab) na tsayar na shige, haɗe da ce masa: "Airport."
Ina daidaita zamana cikin taksin, wani irin kuka mai masifun ƙarfi ya taho mini, amma haka na dinga dannewa, wanda ya haddasa mini rawar jiki haɗi da takurewar fuska.
ABU DHABI INTERNATIONAL AIRPORT, UAE.
"I need a ticket to Nigeria," na faÉ—a muryata na rawa.
ÆŠago kai mutumin ya yi yana kallona jin yanayin muryata, sannan ya mayar da kanshi yace, "Your passport, ma'am."
Ciro ɗan ƙaramin fasfo ɗina na yi jikina na rawa, na miƙa mishi. Ya karɓa ya ɗan dudduba, kana ya miko min yace, "Okay, give me a moment to check, ma'am."
Ya maida hankali kan kwamfutar dake gabansa, ya É—an yi danne-danne na É—an lokaci, kana ya É—ago yace, "The earliest flight is Emirates Airlines, but the economy is full. Would you like to opt for business class? Ko kuma in yi scheduling naki zuwa gobe?"
"Gobe?" na maimaita. A'a, babu yadda za a yi in kai gobe a ƙasar nan, wannan ba mai yiwuwa ba ne. Cikin roƙo na ce, "Please sir, ka ƙara duba mini economy ɗin, maybe a dace."
Kafin ya ba ni amsa, kamar ance in juya, na hango su suna ta baza ido cikin filin jirgin (airport ɗin). Sun kai su biyar; ƙatti ne sosai marasa kyan gani, idan sun damƙe ka sai dai uwarka ta haifi wani ba dai kai ba. Yara (boys) na Abdallah ne, mun kwashe lokaci sosai muna aiki tare da su.
Zaro ido na yi yayin da wani irin gumi ya ƙaryo mini har yana ɗiga a ƙasa. Jikina na rawa na zaro credit card nawa na miƙa masa na ce, "A ba ni business class ɗin."
Kallona ya yi da mamaki ganin yadda nake ta jan mayafina don ya rufe mini fuska, yayin da nake jin rawar da ƙafafuna ke yi tana gab da kayar da ni ƙasa... Kaina a sunkuye nake tafiya bayan na gama da batun tikiti. Mutumin ya sanar da ni na je na duba information panel domin sanin ainihin lokacin da zamu tashi da kuma lambar kujerata (seat no).
Ɗan ɗago kai na yi kaɗan na kalli gefen da na hango su ɗazu. Aiko ƙaraf muka haɗa ido da John, wanda shi ne babban yaron Abdallah. Muna haɗa ido naga ya tunkaro inda nake. Na san ba zai yi gigin da za a kama shi ba ganin a airport muke, hakan ya sa nima na ɗan saita nutsuwata, amma can cikin zuciyata saura ƙadan ta shige cikin cikina. Tafiya nake amma gaba ɗaya hankalina yana kansu, ganin bina suke bil-haqqi.
Ba tare da tunani na biyu ba, na ƙwasa a guje. Domin duk ƙoƙarina na ganin ban yi gudu ba, kasawa na yi, ga uban gumin da ya gama mini wanka. Gudu na dinga yi irin na ceton rai. Cikin ikon Allah ban haɗu da jami'an tsaro (security) ba...
Ƙaraf na ji na buƙi wani abu mai ƙauri kuma mai laushi, kana mai sanyayyen ƙamshi. A lokaci ɗaya kuma wani irin zafi ya ziyarci hannuna haɗe da watsewar wasu takardu a ƙasa. Jikina na mazari na sunkuya da sauri-sauri na shiga tattare takardun da suka zube a ƙasa. Cikin daƙiƙa ɗaya na miƙe, na kamo tafin hannunshi ba tare da na ɗaga kai na ganshi ba, na damƙa mishi takardun haɗi da furta: "Sorry, sorry, it is not intentional." Ban yarda na haɗa ido da shi ba, na ci gaba da gudu na.
Juyawa ya yi yana kallona da madaukakin mamaki kafin ya bi tsadadden kwat (suit) nashi da na ɓata masa da kofin shayi (coffee) dake hannunsa... Wani ɗan lungu na bi, na ga wani babban jikin juji (dustbin). Ba tare da dogon tunani ba na shige cikin dustbin ɗin mai cike da tarkacen datti, ina sauke numfashi da zare idanu kamar ɓera cikin bokitin gari, tare da addu'ar Allah ya tseratar da ni.
Wani lokaci can baya
GOMBI L.G.A, ADAMAWA STATE.
Wasu kyawawan 'yan mata ne su biyu sanye da kakin makaranta (uniform); riga da wando da kuma hijabi. Wandon kore mai duhu (dark green), yayin da riga da hijab ɗin ya kasance farare tas. Ƙafafunsu sanye cikin takalman sawu-ciki baƙaƙe ƙirar Toms. Hannunsu riƙe da wasu dogayen takardu waɗanda suka fi kama da takardar jarabawa (question paper).
Fuskar É—ayar cike take da murmushi da annuri, yayin da É—ayar kuma duk tsiyarka ba za ka fahimci yanayin da ke saman fuskarta ba. Tafiya suke cike da nutsuwa irin ta 'yan matan da suka san kansu, yayin da mai fara'ar take É—an magana kaÉ—an-kaÉ—an, É—ayar kuma amsarta ba ta wuce "Uhum" ko "Um-um".
A haka suke ƙetara hanyar da suka shigo, kasancewar wurin kasuwa ce sosai irin dai kasuwar bakin hanyar nan; babu abun da zaka nema a wurin na siyarwa ka rasa. Saboda haka, wurin cike yake da jama'a ana ta harka. Wasu cikin shaguna, wasu kuwa tebura suka kakkafa, wasu kuma tantuna (tampol). Don haka ko da yaushe wurin cike yake. Mutanen unguwar ba su da kewa ko kaɗan. Unguwar KASUWAN BUTU ke nan dake garin Gombi na jihar Adamawa.
Tsallake kwaltar da ta raba kasuwar da kuma cikin unguwar suka yi, suna ci gaba da tafiya suna ratsa gidajen dake cikin unguwar, waɗanda galibinsu tsofaffin gidaje ne irin na masu ƙaramin ƙarfi... Ɗan taɓa ta mai maganar ta yi, ta ce, "Pretty, kinga mutumin ki tunda ga wurin fulani masu sayar da nonon can nake hango shi ya kafe ki da idanu, sai murmushi yake zabgawa kamar mai tallan Closeup. Ni tsorona ma kar ya yanke hannunshi da zarton nan mu shiga uku," ta faɗa cikin sigar zolaya.
Wacce aka kira da Pretty ta ƙara ɗaure fuska tamau kamar ba ta san me dariya ba. Cikin muryarta mai daɗin sauraro ta ce, "Kinga UMAIMAH, raba ni da jarabarki. Ba na son tashin hankali da tsakar ranar nan. Ki bar ni in ji da abun da ke damuna, please..."
Hakan kuwa ya yi daidai da isowarsu kusa da wani wuri da ake aikin ƙera gado da kujeru da dai sauran kayan katako. Wani saurayi ne tsaye riƙe da zarto, yana ƙoƙarin tsaga katako. Ƙakkaƙfa ne sosai, a ƙalla zai yi shekara 27 zuwa 28 a duniya. Kallon fari zaka ɗauka shi ɗin baƙi ne, amma a zahiri fari ne sol; tsabar tsayuwa cikin rana ne ya ƙodar da shi. Dogo ne mai kiran mazantaka, sai dai kallo ɗaya zaka masa ka fahimci talauci ya samu lasisi a jikinsa. Duban wacce aka ambata da Pretty kawai yake yi ba tare da ƙiftawa ba (without blinking), yana ɗan murmushi kaɗan-kaɗan, wanda zahiri daga can cikin zuciyarshi murmushin ke fitowa.
ÆŠan rusunawa Umaimah ta yi ta ce, "Barka da aiki, HAMMA JABEER."
Murmushinsa ya kuma faÉ—aÉ—a, yana kallon cikin idanun Pretty, ya ce, "Barkanku dai. Ya jarabawar? Hope dai bai ba gimbiyata wahala ba?"
Ko uffan ba ta ce ba. Sai Umaimah ce ta kuma cewa, "Alhamdulillah, final exam ya yi daɗi Hamma Jabeer. Sai ku taya mu da addu'a kawai." Kafin ta ƙarasa maganar, ta hango Pretty ta yi nisa, da ɗan sassarfa ta bi bayanta.
Murmushi Jabeer ya yi ya ce, "My drama queen."
Umaimah ta ce, "Wani irin busasshen walakanci ne wannan Maryama? Ya zaki yi tafiyarki ki barshi ko gaisuwa ba kiyi mishi ba, bayan kinsan domin ki yake tsaye a wannan uban ranar? Haba mana Maryama, at least you should show some concern mana."
Tsaki Maryama (Pretty) ta ja, amma ba ta ce komai ba.
Umaimah ta kuma cewa, "Wannan dai ba halin ƙwarai ba ne wallahi, ki gyara. Gidanshi zaki je a matsayin mata. Ko ba ma wannan ba, yayanki ne jini ɗaya, ai ba wasa ba. Maybe ma yanzu haka gadon aurenki yake ta fafutukar ƙerawa, amma ko sannu kin gaza ce masa."
Ɗum! Ɗum! Ɗum! Ƙirjin Maryama ya ba da sauti jin furucin Umaimah na ƙarshe: "Maybe ma gadon aurenki yake fafutukar ƙerawa." Ta ƙara maimata maganar a zuciyarta.
Da sauri ta ce, "Impossible! Ni na fi ƙarfin a mere ƙafinta ya ƙera mini gadon aurena. Kamar ni?" ta faɗa tana nuna kanta. "Impossible wallahi!"
Buɗe baki Umaimah ta yi da nufin yin magana, Maryama ta yi saurin katse ta ta hanyar ɗago dara-daran idanunta ta zuba mata haɗi da fadin, "Look Umaimah, dan girman Allah ki ƙyale ni in samu sauƙi. Rayuwata daban, taki daban. Don kina matsayin aminiyata ba shi zai sa rayuwarmu ta zama ɗaya ba. You know me, and you know all my dreams and my desires, so leave me alone, please."
Ta juya haÉ—i da shigewa É—an tsurkukin gidansu wanda ya fi kowane lalacewa a unguwar. Girgiza kai Umaimah ta yi, kana ita ma ta shiga gidansu wanda yake katanga É—aya da na su Maryama.
Wani irin takaici ne ya turnuƙe zuciyarta lokacin da ta shiga cikin ɗan matsakaicin gidan na su, sakamakon arba da ta yi da wani ƙatoton bokiti cike taf da ruwan da aka wanke ƙalwar yin daddawa, ga ƙudaje sai yawo suke yi a kai. Gefe guda kuma, innarta ce ke ta faman kirɓa ƙalwa a wani ƙatoton turmi.
Yamiɗa fuska ta yi ta ce, "Kai Innarmu! Yanzu ba zaki daina wannan abun ba? Duk gida ya cika da ƙauri ta ko'ina. Ni shi yasa fa ba na son kawo ƙawayena gidan nan, don kada su raina ni."
Dakawa Inna ta yi mata ta ce, "Ungo naki Maryama! Ja'ira da idanu kamar É—an farin alade. Wannan shi ne sallama ko haka aka koya miki?"
Turo baki ta yi ta ce, "Kai Innarmu! Don kawai na faÉ—i gaskiya? Duk sana'ar duniyar nan ki rasa wadda zaki yi sai daddawa? Allah, duk sanda na yi kuÉ—i zaki huta da wannan wahalar."
Tana fadin haka, ta ɗaga labulen ɗakinsu ta shige ciki tana kunkuni... Dafe kumatu Inna ta yi, sannan ta ce, "Allahu ya shirya mini ke, Maryama." Kana ta ci gaba da kirɓa daddawarta.