MARYAMAFree

ArewaPen original

General fictionFreeCompleted

MARYAMA

  • 1views
  • 64chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

About the author

Writer ✍️ | Storyteller 📖 Creating stories that touch hearts. ❤️

More from @ummufadeela01

Sample · Page 01

💫MARYAMA💫BYUmmu FadeelaTyping... 📲EPISODE 01Bismillahi Rahmani-Raheem. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin sammai da ƙassai. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga shugaba, jagaba Annabi Muhammad (S.A.W), da iyalan gidansa da sahabbansa baki ɗaya.KHALEEFA BIN ZAYED AL NAHYAN STREET, ABU DHABI CITY (UAE).Katafariyar unguwa ce da ke cikin babban birnin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wanda aka fi sani da Abu Dhabi. Unguwa ce mai ɗauke da rukunin gidaje masu kama da aljannar duniya...Lumshe kyawawan fararen idanuna na yi. Na daɗe ina jin yadda ake yabon kyawun zubin halittar idanuna; mutane da dama idan sun tashi yabon kyan halitta ta, sukan kira ni da "mai idon madara" tsabar irin hasken da kyawun da Allah ya ba ni. Amma a halin da nake ciki yanzu, sabanin kasancewar su launin madara, idanun sun yi jajur kai kace attaruhu aka ɗaka aka watsa a cikinsu, ko kuma na kwana uku ina kuka ba tare da tsagaitawa ba. Sai dai ba ko ɗaya daga ciki; tsabar tashin hankalin da nake ciki ne ya haddasa mini canzawar launin idon.A hankali na juya na kuma kallon shi, zuciyata na bugawa da ƙarfi da ƙarfi, yayin da nauyin da kaina ya yi ya haddasa mini ganin dishi-dishi... Yana durƙushe gaban gadon da nake zaune ya ba ni baya, yana ta daddaure hodar iblis (C0C@!NE) cikin wasu ƙananan ledojin nylon. Cikin sauri-sauri yake aikin, wanda duk bayan daƙiƙa ɗaya sai ya ɗaga kai ya kalli ƙofa.Runtse idanuna na kuma yi, zuciyata na tsananta bugu yayin da nake tuna cewa wai ni ce zan haɗiye gaba ɗaya wannan hodar iblis ɗin a cikin cikina, in yi safararta zuwa Nigeria. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, na furta cikin raina, kana na bi dogayen ƙafafuna farare sol da kallo. Ɗaure suke cikin sarƙoƙi (chains) sakamakon yunkurin guduwar da na yi, hakan ya sa suka ɗaure ni. Zuwa yanzu na tabbatar roƙo da magiya ba za su yi mini amfani ba."You have to be brave," zuciyata ta faɗa mini. Tabbas dabara ce kawai zan yi da taimakon Ubangiji in bar wurin nan; idan ba haka ba, rayuwata ta ƙare. Safarar cocaine ba ƙaramin haɗari (risky) ba ne ga rayuwata. Cikina ne ya hautsine gami da ba da sautin kululululu sakamakon tunawa da na yi wai haɗiyar waɗannan ledodin zan yi a cikina. Duk da ya sanar da ni hanyoyin da za a bi a fitar da su idan mun isa Nigeria, hakan bai rage ko da ƙaso ɗaya cikin ɗari na irin tsoratar da na yi ba.A hankali na fara bin ɗakin da kallo ko zan dace. Aiko idanuna suka sauka kan bedside lamp dake kusa da ni, ga kuma wani tangaran mai ɗauke da furen rose duk a wuri ɗaya. Cikin dabara na kai hannuna duk biyun na ɗauki lamp ɗin da kuma furen (flower vase) ɗin... Ya duƙufa sai aiki yake a gaggauce, hakan ya sa bai maida hankali kaina ba.Runtse idanu na yi ina tabbatar wa kaina abin da zan aikata shi ne daidai. Bai yi aune ba ya ji saukar tangaran a ƙeyarsa, ji kake g...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters64
premium1
12

Page 13 / 14💫MARYAMA💫 By. Ummu Fadeela Episode 13/14.

Free sample
Updated 3 months agoAvailable now
53

Page 66

Premium
Updated 2 days agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play