MARYAMA

Page 02

by @ummufadeela01






💫MARYAMA💫

By

Ummu Fadeela

EPISODE 02

Dukkansu suna zaune a ɗan madaidaicin tsakar gidan bayan sallar Isha'i, shimfiɗe kan babban tabarma kamar yadda suka saba. Baffanmu, Innarmu, sai Maryama da kuma kannenta, Fatima mai shekara goma sha biyu, sai Salima mai shekara tara. Kana daga gefe, Hamma Jabeer shi ma yana zaune a bakin ƙofar ɗakinsa. Ya yi wanka ya sauya kayan aikinsa na dazu zuwa wasu black jeans da black shirt mai gajeren hannu wanda ya bayyana hasken fatarsa. Hakan ya sa ya yi kyau ba kamar dazun ba.

Kowa ya sa abincinsa na dare a gabansa yana aikawa cikinsa hakkinsa, amma banda Maryama, wacce ta kafe kwanon gabanta da ido. Ko kiftawa ba ta yi ba, kuma ta kasa kai ko loma ɗaya zuwa bakinta. Tukekken tuwon masara ne fari sol wanda ya samu tuki irin na ƙwararriyar hannu, ya yi sumul-sumul gwanin sha'awa, sai miyar kuka wacce ta sha attarugu da daddawa, sai kamshin man shanu yake tashi.

Duk abin da take, Innarmu tana ganinta, amma ba abin da ta ce mata. Sai ma girgiza kai da ta yi ta ci gaba da cin abincinta. Lokaci-lokaci Hamma Jabeer kan ɗago kai ya kalleta, ganin sai yamutsa fuska take yi. Ya san abin da ke damunta, hakan ya sa ya ɗauki wayarsa ya tura mata ɗan gajeren saƙo.

Ƙarar shigowar message a wayarta ce ta sa ta dawo hayyacinta, ta ɗauki wayar da sauri tana dubawa. Tun wayewar gari sai a lokacin Maryama ta yi murmushi bayan ta gama karanta content ɗin. Cikin dabara ta ɗaga kai suka haɗa ido da shi. Ya ɗage gira yana kanne mata ido. A hankali ta janyo marfin da ke kusa da ita tana ƙoƙarin rufe kwanon tuwon Baffa da ya gama cin nasa. Yana kuskure baki da butar da ke kusa da shi, ya kalleta gami da faɗin,

"Uwata, har kin gama cin naki abincin ne?"

Da sauri ta ce, "Eh, Baffanmu."

"Ya yi kyau," cewar Baffa. "To, ya jarabawar taku? Yau kuka gama ko?"

Sunkuyar da kai Maryama ta yi ta ce, "Eh, Baffanmu, yau muka gama."

Ya ce, "To, Allah Ya ba da sa'ar samun sakamako mai kyau."

Duk suka amsa da, "Ameen."

Gyara zama Baffa ya yi ya ce, "Dama da akwai wani fom da na saya miki jiya. Kafin zuwa safiya, ki yi ƙoƙari ki cike shi. Fom ne na koyon ɗinki, shagon M. BELLO FASHION DESIGNER suka fara siyarwa."

Dum-dum, ƙirjinta ya ba da sauti. A ranta tana maimaitawa, koyon ɗinki kuma? Amma don kada ta saɓawa Baffanta, cikin sanyin murya ta ce,

"Na gode, Baffanmu. Allah Ya ƙara girma."

Ya ce, "Ba komai, Uwata. Sai ki maida hankali."

Kana ya juya yana kallon Hamma Jabeer, wanda ya miƙe yana ɗan shafa sumar kansa zuwa yalwataccen sajensa.

Ya ce, "Ya naga ka tashi, Jabeeru?"

Yana ɗan murmushi ya ce, "Nan bakin hanya zan je amso saƙo. Ba da daɗewa zan dawo."

Baffa ya ce, "Ku riƙa kula dai. Kun san yadda duniya ta lalace. Ba abar mai kuɗi ba, ba abar talaka ba."

Jabeer ya ce, "In shaa Allah." Baffa, ya juya ya fita.
Hira suke yi sama-sama kasancewar akwai farin wata tarwai. Bayan wani lokaci kaÉ—an Baffa ya É—aura alwala ya shige É—aya daga cikin É—akuna huÉ—un da ke gidan.

Wani irin ajiyar zuciya Maryama ta sauke tana Allah-Allah Innarmu ma ta tashi. Ganin ba ta da niyyar tashi, lokacin ne ya sa Maryama miƙewa ta fara tattara tsakar gidan nasu da bai wani cika da tarkace ba, da kuma kwanukan da suka ci abinci. Bayan ta gama, ta zo ta ciccibi Salima, wacce ta yi barci a wurin, ta kai ta bayi ta yi fitsari, sannan ta shigar da ita ɗakin da yake mallakinsu ita da kannenta. Ta zo ta ɗaga Fatima ma ta shigar da ita.

Sai a sannan Inna ta miƙe tana ɗan hamma ta ce,

"Ban san me ya tsaida Hammanku a waje ba har yanzu bai shigo gida ba. Shi ya sa ba na son fitansa da dare sam. Hankalina baya kwanciya."

Tsagal Maryama ta yi ta ce,

"Innarmu, bari in leka shi. Yanzu haka ma bai yi nisa ba. Kin san baya wuce ƙofar gida in ba ya kama dole ba."

Inna ta ce,

"Ki hanzarta to, amma kar ki wuce ƙofar gidan. Ke ma kin san Baffanku zai yi faɗa."

Da sassarfa ta figi mayafinta ta yi hanyar waje. Ɗan dakatawa ya yi daga ƙoƙarin shigowa gidan jin footsteps, kuma ya san ita ce. Sai da ta kusa isowa ya fito da sauri gami da faɗin,

"Kamata!"

Tsabar irin tsoratar da ta yi, maimakon ta koma baya sai kawai ta sa kai da niyyar fita waje a guje. Hakan ya sa suka yi karo da Jabeer, wanda ya bayyana a gabanta yana murmushi.

Dafe goshinta ta yi tana faÉ—in,

"Ouchhhh... Allah, Hamma Jay, ka tsoratani."

Cikin shagwabar da ba ta san ma tana yi ba, wanda kusan yanayin halittarta ne hakan.

Jabeer, da ya ji wani abu na masa yawo a tsakar kai har zuwa kan yatsunsa, ya yi ƙarfin hali ya kwaikwayi muryarta yana faɗin,

"Kai dai, Pretty'n Hamma Jay, kar ki zama raguwa mana."

Kamar ya ƙara mata magana, sai ta fara dire ƙafafuwa a ƙasa tana kukan shagwaɓa wai ya buge ta da kansa mai kamar kwakwa. Tuni ta ƙara kunna masa wani yanayi. Jabeer ya daɗe da sanin ba shi da control when it comes to Maryama.

Wayarsa ya ciro daga aljihun jeans ɗinsa yana haska fuskarta, duk da cewa akwai hasken farin wata. Shagala ya yi da kallon fuskarta mai cike da kyau, da idanuwanta masu haske, da hawaye suka jiƙe gashin idanunta. Daga nan ya ɗaga kallonsa zuwa goshinta inda take ta murzawa, yana duban gashin da ya kwanta a gefen goshinta da kuma girarta masu kyau. A hankali ya gangaro zuwa Kan siririn hancinta tamkar an zana da fensir, Har zuwa Kan pink lips nata that looks sexiest, da gefen kumatunta da Duk sadda tayi murmushi suke lotsawa. Maryama is just a definition of beauty.

Kama hannunta da ke kan goshinta ya yi yana kallon wurin. Ba shakka kuwa ta ji ciwo, sai dai bai kai wanda za ta yi ƙara har haka ba. Wurin ya ɗan yi ja kaɗan kasancewarta fara. Ya fara goga mata wurin a hankali, ita kuma ta saki masa jiki kamar mage.

A ɓangaren Jabeer kuwa, jin yanayinsa ya fara sauyawa ne ya sa ya yi saurin sakin goshinta. Ya ɗauki ledar da ya shigo da ita ya miƙa mata cikin shakakkiyar murya ya ce,

"Maryama, shiga gida, dare ya yi sosai."

Karɓar ledar ta yi, dama abin da take jira kenan. Ta juya ba tare da ta yi masa godiya ba. Taku biyu ta yi, sai ta ji ya kira sunanta a hankali kamar mai yin rada.

"Maryama..."

Cak! Ta tsaya. Taku É—aya ya yi ya iso kusa da ita har suna jin numfashin junansu. Ya lumshe idanu, sannan ya É—an matsa baya kaÉ—an yana kallon cikin idonta ya ce,

"I love you, Maryama. I love you with all my heart. Please don't betray me no matter how the situation goes. Don Allah ki so ni ko da kaso ɗaya cikin ɗarin son da nake miki. Na roƙe ki, Maryama, ina miki son da idan kika guje ni zan iya rasa raina."

Ko uffan ba ta ce ba. Sai dai ta ci gaba da murza ledar da ke hannunta. Shi ma ya san ba za ta ce komai ba, domin wannan halinta shi ne ke ƙara ba shi tsoro. Yana ganin kamar wata rana zai rasata, duk da cewa ita ɗin tasa ce, lokaci kawai ake jira ta kammala sakandare, ga shi kuma ta kusa kammalawa.

Cikin sanyin murya, ba tare da ya yi tsammanin za ta ce wani abu ba, ya ji ta ce,

"Hamma Jabeer, zan shiga gida. Dare ya yi."

Murmushin ƙarfin hali ya yi ya ce,

"To, ba za mu ci tare ba? Tunda ba ki son tuwon Innarmu."

Ta ware masa kyawawan idanunta ta ce,

"Kai, Hamma Jay! Taya za mu ci tare kuma?"

Ya ware ido shi ma ya ce,

"Ta haka mana, Pretty'n Hamma Jay."

Da sauri ta juya ta ƙarasa shiga gidan. Jabeer kuma ya cusa hannunsa cikin aljihun wandonsa yana binta da kallo cike da lallausan murmushi.

Baje ledar Maryama ta yi a tsakar É—akinsu tana addu'ar kar su Fatima su tashi. Hollandia yoghurt ne mai É—an karen sanyi, sai ledar cake guda biyu da wani kunshi wanda ko ba ta kunce ba ta san kaza ce a ciki. Da murmushi take bin rabin kazar da ke cikin takarda, an yayyanka an barbade shi da yaji.

Ta lumshe idanu sannan ta buÉ—e tana jinjina irin kulawar da Hamma Jabeer ke ba ta. Ko da ba ta furta ba, daga yanayinta yake fahimtar abin da take so da kuma halin da take ciki. Yanzu haka ma, watakila duk kuÉ—in aikin da ya samu yau gaba É—aya ya kashe mata su a nan. Domin shi ma ba wai gidansu ba ne, idan sun yi aiki ne ake ba su wani abu.

Ita dai ba ta jin komai na soyayyar aure a zuciyarta kan Jabeer, amma tana tsananin ƙaunar irin kulawar da yake ba ta da kuma irin sadaukarwar da ya yi a kanta. Babu wani mahaluki da ya taɓa yi mata kwatankwacin sadaukarwar da Hamma Jay ya yi. Sai dai, kash! Ba irinsa take burin aura ba. Duk da iyaye sun haɗa su, tana jin lokaci ya kusa da za su wargaza shirin da suka yi.

Kofi ta ɗauko ta tsiyaye yoghurt ɗin ta kurɓa tana jin sanyinsa na ratsa maƙoshinta. Kana ta ɗauki tsokar kaza ta fara ci cikin ƙwarewa da murnar irin ta wanda aka daɗe ba a haɗu ba. Ta ci fiye da rabin kazar, sannan ta ci cake ɗaya. Hollandiar kuwa ta sha fiye da rabi. Wani irin gyatsa ta yi tana jin komai ya mata daidai. Hakan ya sa ta daure sauran ta ture su gefe, a cewarta da safe za ta ba su Salima.

Sai muryarsa ta dawo mata a rai.

"Ba za mu ci tare ba?"

Ta turo baki gaba, sai kuma ta miƙe ta zura dogon hijab har ƙasa. Ta ɗauki sauran naman da cake ɗin tare da yoghurt ɗin, sannan ta fita tana taku a hankali don kada ta janyo hankalin Inna da Baffa.

Ta je jikin ɗakinsa. Cikin sa'a tana tura ƙofar sai ta buɗe. Ba tare da sallama ba, don kada ta janyo hankalinsu, ta sa kai cikin ɗakin. Still tana riƙe da ledar a hannunta; ita ba ta fita ba, ita ba ta shiga ba, kuma ta kasa ɗaga idanunta ta ganshi tun bayan kallon farko da ta yi masa da halin da ta ganshi a ciki...