Page 04
💫MARYAMA💫
By
Ummu Fadeela.
EPISODE 04.
....Hankali a tashe ya shigo gidan bai zarce ko ina ba sai dakinta,zuwa lokacin ciwon da ta keji ya karu sai birgima take yi a kan gadon tana rike da cikinta tana kiran wayyo innarmu wayyo baffanmu,baisan yadda akayi ba sai ganinshi yayi bakin gadon rike da hannunta.
Jin hannun mutum cikin nata yasa ta rike wa gam tana sakin wani marayan kuka. murya cike da damuwa yana jin kamar ya maida ciwon jikinsa yace "maryama!ciwon cikin ne?gyada mishi kai tayi tana kara murkususu akan gadon,rumtse idanu yayi gaba daya basirar sa ya gudu ya rasa me zai mata. Wani irin yunkura tayi da karfi ta mike zata fita waje saidai kafun takai wajen nan tsakar dakin ta durkushe ta dinga kwarara amai tamkar zata amayar da yan hanjinta,jabeer da ya rasa abunyi shima durkuson yayi gefenta pitiefully yake mata sannu.
Mikewa tayi tana jin jiri na kwasarta ta koma kan gadon ta kwanta, gaba daya jikinta ya baci da aman da tayi.lamo tayi kan gadon tana sauke numfashi a hanakali domin aman da tayi yasa taji saukin kartawar da mararta ke mata.
Shafa gashin kansa yayi yana lumshe ido kafun ya mike ya fita waje, ruwa ya deba a bocket hadi da janyo tsummar da innarmu ke goge goge ya dawo dakin....Tas jabeer ya kwashe aman da tayi kana ya goge wurin da ruwa da omo,dan matsowa yayi kusa da ita yace "pretty, tashi ki canja kayan nan kar sanyi ya kama ki kinga sun baci gaba daya."
Ko uffan bata ce ba sakamakon sabon ciwon cikin da ya taso mata, haka maryama take fama da wannan jarababben ciwon ciki da marar duk sanda lokacin period nata yayi sai kowa ya sani, ga amai ga ciwon cinyoyi ga gudawa duk ita kadai kuma every month sai tayi hakan.
Jin bata motsa ba yasa jabeer kamota yana fadin "pretty ki tashi ki sauya kaya sai ki sha magani ki kwanta kinji?."
Bata musa masa ba ta tashi tana jin duniyar na juya mata,bin shafaffen cikinta dake cikin vest yayi da kallo wanda aman da tayi ya taimaka wurin kara lafewar vest din a jikinta, ga kuma wani sabon lamarin dake jikin vest din, bin jikinta tayi da kallo ganin yanda ya kureta da ido, da sauri ta juya mishi baya tana turo baki gaba ganin gaba daya farar vest nata ya baci da jini, arba tayi da bedsheet dake saman gadon wanda gaba daya shima yayi staining da jinin thats mean bayanta ma ya baci kenan,wani irin juyi ta kuma yi ta durkushe a wurin tana takurewa wuri daya gami da fadin Hamma j. Banaso
Murmushinsa mai kyau yayi yana shafa kanshi wanda ya zamo dabiar sa yace, baki son me prettyn hamma j."?
Ko motsi batayi ba hakan yasa qya fita a dakin, kitchen ya shiga dan yadda ta bacin nan tana bukatan wanka,cikin sa'a kuwa ya samu ruwan zafi akan wuta ba tare da wani tunani ba ya dauko bocket ya juye ruwan ya fito ya sirka saida ya tabbatar yayi daidai kafun ya shigar mata bayi,lokacinda ya dawo dakin maryama tana kokarin cire wandonta tuni ta cire vest din dama,wani irin ihu tayi gami da dirkusawa a wurin,cikin shagwababbiyar muryar da ya saukewa jabeer kasala tace.
"Ni banaso kuma ka fita a nan" dariya ta basa ganin yadda ta takure amma baiyi ba yace "ohk zan fita, kiyi sauri ga ruwan ,zafi a toilet kije kiyi wanka kar ya huce."...Da zani daure sai babban hijab da ta zura ta fito dauke da kwandon wanka zata wuce bayin,jabeer yayi kasa da murya yace "kindau PAD naki? ko ya kare in kawo miki wani."
Da kamar baza tace komai ba, sai kuma ta rufe fuskarta da hijab din jikinta tace "ya kare".
Baice komai ba ya wuce dakinsa bayan kamar minti biyu ya fito rike da ledan always ya mika mata, karba tayi ta wuce toilet din shikuma ya shige dakinta,...Kallon kayan dake kan gadon yayi nadan wani lokaci kamar mai nazarin su a hankali ya lumshe kyawawan idanunshi kana yasa hannu a kanshi yana shafa lallausan gashinsa, bude idanun yayi ya kwashi kayan da bedsheet din ya fita dasu waje, wurin da suke wanke kaya ya ajiye su kafun ya dauko bokitai da omo nan ya dara wanke kayan jinin maryama....Tas ya wanke su ya shanya ya koma dakin ya shimfida mata wani zanin gado ya fita. Lokacin da ta fito wanka da mamaki ta tsaya tana kallon kayan dake shanye bisa igiya, ba yau hamma j. Ya fara yi mata dauraya ba, amma na yau din yafi bata mamaki,...Haka ta shiga daki ta kimtsa jikinta ta hau gado ta kwanta domin kwanciyar take bukata a lokacin.
Jabeer da ya kasa komawa wurin aikinsa sakamakon halin da ta ke ciki ya shiga dakin yafi sau a kirga amma ganin ta samu bacci ya dauke ta sai bai tayar da ita ba,jin shirun yayi yawa yasa ogansa kiran wayarsa don ya bar aikin da ya fara a walakance,...Daga karshe dai innarmu jabeer ya kira awaya ya sanar mata maryama ba lafiya.
"Me ya ke damunta."?, Cewar innarmu,kame kame ya fara kafun yayi gathering courage yace "ciwon cikinta ne ya motsa mata," dan jim tayi sannan tace "to Allah ya sauwake ganinan tahowa gidan yanzu".
Saida innarmu ta dawo jabeer ya koma wurin aiki wanda ko kadan hankalinsa baya kai, ya karkata ga tunanin halin da ta ke ciki.
Tsawon kwanaki biyar maryama ta kwashe tana fama da cramps before ta ci gaba da harkokinta zuwa islamiyya da kuma koyon dinkin da baffa ya samar mata wanda ko kadan hankalin jabeer bai kwanta da zuwanta shagon ba ganin duk shagon maza ne, a bangaren maryama ma bata son zuwa amma dan karta bata ran baffanta yasa ta fara zuwa da niyyar idan result nasu na SSCE ya fito zata dena zuwa...
-----------------------------------------------
Tafe suke cikin murna,yan mata ne kusan su biyar ko wacce ka gani baki har kunne tsabar farin ciki fitowar su daga cafe kenan inda suka yi browsing result nasu na kammala sakandire,duk murnan da sukeyi ya kamata ace maryama ta fisu dan duk tafisu samun sakamako mai kyau, inda ta samu 7credit da 2 distinction a both waec and neco dinta,wannan ba karamar nasara bace saidai ga maryama ba alamun annuri saman face. nata kwata kwata ma bata tare dasu hankalinta ya karkata ga wani tunani na daban.
Tun ina karama na taso da wani buri a rayuwata, burin yin karatu mai zurfin gaske da zamowa hamshakiyar mace wacce za'ake kwatance da ita,sannan in auri miji hadadde mai ilimi mai arziki wanda zai mallaka min duk abunda na bukata,kana ina da burin rayuwa da mijin da zan aura a manyan biranen duniya,duk sanda naga mace a cikin mota tana tukawa nakan ji inama ace nice,wani lokacin har hawaye nake zubarwa amma nakan lallashi kaina da ba kaina tabbacin idan na girma zan mallaki duk wadannan.
As I grew older,the likelihood of my dreams becoming true,kasancewar zallar madarar kyau dake bayyana a gareni irin na buzayen asali,duk ta inda nabi sai mutane sun tanka akan hallita ta yaayinda wasu da dama ke kirana da maryama matar manya,ga wani irin farin jini da Allah ya bani baga maza kawai ba hatta mata jinsi na kaunata suke yi manya da yara,wannan ne ya kara min karasashi wurin neman cikar burina, domin a gani na duk wani mutum mai kyau to ya mallaki makaman samun abunda yake muradi a rayuwarshi.
Saidai iyayena sun katse min hanzari tun ban fara nisa ba,inda suka shirya hadani aure da tilon dan uwana ba tare da sun nemi jin ra'ayi na ba,...Wannan sakamakon jarabawar ssce dake hannuna yanzu shine chance dina na cikar buri a yanzu,idan iyayena da suka kasance talakawa tibisss da abincin da za'aci ma sai an nema wataran ma rasawa ake,idan sun amince na ci gaba da karatu zuwa matakin jami'a xanfi kowa farin ciki,idan ko sabanin hakan na samu lallai zan kare rayuwata cikin dauwamammiyar kunci marar gushewa.
Ni maryama ina cikin shekara ta goma sha bakwai ne a yanzu,saidai idan ba baby face nawa ka karewa kallo ba,zaka dauka nidin cikakkiyar budurwa mai shekaru ashirin da biyu ne domin irin kirar da Allah ya min na dirarriyar mace, ina da tsawo da murjejjen jiki,bani da kiba amma ina da cikakkun kirji masu daukan hankali a kallon farko kana inada wadatattun mazaunai da kuma shimfidaddiyar hips,wanda ke bayyana asirin shafaffen cikina,skin nawa fari ne kal irin na matan indiya,yayinda fuskata ta kasance oval shape mai dauke da dara daran idanu masu haske da kuma yalwar lashes masu tsawo saman su kuwa eyebrow ne da yake so thick bakikkirin,daga saman goshina akwai kwantattun gashi wanda zai tabbatar maka inada arzikin gashi a cikin kaina, hancina dogo ne sosai ta bakin hamma j. kamar ni na zana wa kaina,kana bakina zagayayye ne mai dauke da pink lips masu sheki koda bansa musu lip gloss ba,ta ciki kuwa suna dauke da set white teeth a jere reras gwanin sha'awa yayinda a tsakiyar guda biyu na gaba dake sama akwai dan tsaga siriri wanda yake kawata murmushi na, a duk sanda bakina ya motsa kuwa gefe da gefen kumatuna sukan loba ciki abun so masha Allah......"Wai tunanin me kike yi haka ne?, gasu safeena suna miki sallama amma har suka shiga gida baki tanka musu ba,kodai yauma kin hau jirgin takardar ne ya lula dake wata nahiyar maryama?."cewar umaima da ke karkadawa mata papers din dake hannunta a saman fuskanta ganin tayi nisa cikin tunanin da take har sauran yan mata ukun suka shige gida bata ma sani ba.
Dago dara daran idanunta tayi that look very restless ta zuba su kan umaima cikin sanyin muryar ta tace." kinyi magana ne umaima?".
Cike da tausayawa rayuwar da ta daurawa kanta umaima ta kalli aminiyar tata tace "cewa nayi gasu feena suna maki sai anjuma baki tanka su ba,yanzu haka sai su zaci girman kai kike nuna masu maryama,plsss kina rage yawan tunani kinsan yawan tunani is not good for health barin ma wannan tunanin rayuwar da ke kika daurawa kanki wllh ki canja maryama if not zaki sha wahala a nan gaba."
Fuska a cunkushe ta kalli umaimah cikin sanyin voice nata tace "I regret telling you what's in ma heart umaimah,idan baki bani kwarin guiwa ba bai kamata ki dinga discouraging dina ba haba mana for God Sake ke baki da aiki kullum saidai ki bata min rai ? ni ban isa inyi tunani yadda rayuwata zata kasance ba, inace ke kullum sai kinyi planing yadda zakuyi rayuwa da yusuf,ki barni dan Allah this is my life dole inyi yadda nakeso dashi" bata jira jin abunda zata fada ba ta shige gida ta bar umaima da baki agape...
Kamar kullum yauma a tsakar gidan aka shimfida tabarma din cin abincin dare, yau da fara'a maryama ta ke cin abincinta domin favourite nata a ka dafa,white rice da stew da yaji nama zuku zuku hamma jabeer ne ya sai musu shinkafar da nama don anbiya ogansu kudin wasu funitures da suka yi shikuma ya rabawa ma'aikatan hakkinsu,ganin hakane yasa shi masu cefanen abinci, innarmu tasa baffa ya kawo kayan miya da ganyen salad aka zuba girki tamkar ranar salla.yayinda hamma j. Yake jin wani irin dadi a zuciyar shi ganin masoyiyar tashi tana cin abincin happily.
Bayan an gama fatima ta tattara wurin,baffanmu ya kishingida cikin dan hiran da suke yi ya tambayi maryama "uwata ya maganan sakamakon naku? ina fatan dai yayi kyawu ko?"
Mikewa tayi fara'a fal fuskarta tace "eh baffanmu yayi kyau sosai bari in kawo maka dama ina jira ka gama abunda kake ne".
Daki ta shige hamma j. ya bita da ido, ba jimawa ta fito dauke da takardun ta durkusa cike da ladabi ta mika masa.
Karba yayi yana dariya yace "uwata ni me na sani anan, banda dai fararen takardu da na gani, maza jabeeru zoka duba min, ya fada yana kallon hamma j."
Duk dariya sukayi banda jabeer da ya taso daga inda yake zaune, salima dake tattare da yarinta tace baffanmu lokacinda kuke zuwa makaranta ku ba malamai ne?" dariya yayi yace "salima ta baffanku bai yi boko ba,kune dai kika dace kuna bokon yanzu,dakuwa innarmu ta mata tace "banason banzan tambayoyin nan marasa kan gado salima,".
Still laughing baffanmu yace "kayya dijah barta tayi tambayarta mana ai tambaya yana bude kwakwalwar yaro kuma yana nuna yaro mai kaifin basira ne".
Karbar takardar jabeer yayi ya dudduba kafun yace "baffanmu sakamakon yayi kyau, ina ganin ba wanda ya samu result irin nata a shekarar nan".
"Madallah" cewar shi "amma anya jabeeru baka karawa sakamakon armashi ba kuwa, ya fada cikin barkwanci. nan ma duk dariya suka yi banda maryama da ta sha murr, gyara zama baffanmu yayi kafun ya koma serious yana kallonsu dukansu, yace "to alhamdulillah, wannan lokacin muke jira dama dukkanmu gashi ubangiji ya nuna mana uwata ta kare sakandire yanzu menene shirinku akan maganar aure?,domin a namu bangaren nida mahaifiyar ku dama mutanen nijar mun gama namu shirin lokaci kawai dama muke jira".
Yana kallon jabeer da ya sunkuyar da kai kasa kana maryama ma tana durkushe gabanshi kamar wacce ke neman gafara saidai sabanin jabeer da kanshi ke kasa, ita ta kafe jabeer dinne da manyan idanunta kirjinta na tsalle kamar zai fito waje yayinda jikinta ke dan rawa kadan kadan tana jiran jin me zai fada....