MARYAMA

Page 05

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

  By 



               (Ummu Fadeela).



EPISODE 05.

.....Cikin nutsuwa jabeer yace "duk yadda kuka tsara shine daidai ranka shi dade mu namu bin umarni ne idan kunce ayi yanzu sai nafi kowa farin ciki da hakan ...,zaro idanu tayi tana jin gabanta na tsananta bugu,jabeer ne yaci gaba da fadin "amma tunda kunce ra'ayinmu kuke son ji to nidai a bangare na dama ina planing ta zana jarabawar neman gurbin shiga jami'a by then na samu aiki watakila abubuwa zasufi yi mana sauki,amma wannan tunanina ne baffanmu,idan tayi jarabawar gaba kadan za'a fara deban sabbin dalibai kunga sai ta jona kawai koda tana dakinta.duk maganan da yake kanshi yana kasa bai yadda sun hada idanu da kowa ba, ba karamin kokari yayi ba kafun yayi wannan jawabin Allah ya sani yana son auren cikin lokaci kadan kodon fargabar da ya ke ciki na barazanar rasata da yake yawan fado mashi a rai,amma dole ne ya cikawa maryama burinta koda ko shi zai take nashi burin, Wannan shine hakikanin soyayya.ka take naka kaso abunda wanda kake so ya so.

Tunda maryama take bata taba sanin wani abu wai shi relieve ba sai yanzu,wani irin ajiyan zuciya ta sauke wanda yasa gaba dayansu dagowa suka ganta,...Dan daburcewa tayi ta fara kame kamen fadin "eh baffanmu kaga yanzu an fara saida fom din jamb kawai sai..." shiru tayi sakamakon wani kallon da innarmu ta aika mata.

Dan gyara zama yayi yana kallon su both yace, "cikin ku wa ya tsara wannan maganar?....ba tare da ya jira sun bashi amsa ba yaci gaba da fadin "sannu mongo park mai kankat kenan a boko,nace sannu mongo park mai kashin ABCD,kai da kayi digiri din me ya tsinana maka?cikin fada baffa yake tambayar jabeer da ya tsunkui da kai kasa,ba magana nake bane jabeeru,nace amfanin me digirin da kayi ya maka kaida kake namiji ma balle ita mace, ina ce duk wuyan da kasha da kudin da aka kona akan digiri din karshe filo kayi da sakamakon da ka samu ba aikin yi,aiki a kasar nan sai dan wane da wane sai yayan masu hannu da kumbar susa,dan talaka saidai yayi kallo ko ya rike sana'ar da ya sauwaka.

"Ayi hakuri baffanmu" cewar jabeer yana shafa sumar kanshi.

Sassauta murya baffa yayi yace "jabeeru karatun diya mace yana da kyau bance bashi da amfani ba amma ana sara ana duba bakin gatari, maryama ta samu ilimi iya abunda ya sauwaqa na matakin sakandire ta sauke alqur'ani yanzu tana haddanshi da na wasu litattafai,dama ana son mace tayi ilimi ne dan a samu al'umma masu aminci tunda uwa itace matakin tarbiya na farko, ina da tabbacin uwata bazata bani kunya ba a wannan bangare, nasan tunaninka shine inda zaka ajiyeta da kuma sauran abubuwan al'ada,mun rigada mun yanke shawara da innarku gidan da yake kasan layi na dada can zaku zauna farar kasa da penti kawai za'a samu a goga,tunda akwai komai ciki da bayi da madafa madafar ne kawai yake bukatan gyara, tunda dada ta koma nijar sai ku zauna ciki har muga abunda Allah zaiyi zuwa gaba,batun lefe kuma ko zuwa gaban bazai hana ka mata ba idan Allah ya hore maka," innarmu da tunda suka fara maganar bata ce komai ba tace "oh oh Allah ita maryaman ce maku tayi bata da kayan sawa ne?".
Baffa yace "ah ah amma al'ada ce ai dole zai mata", wani irin hautsinawa cikina yayi da gudu na mike kafun in iso kwararo na fara kela amai kamar yan hanjina zasu fito,innarmu ne ta tashi zuwa kaina da fadin sannu,kinci abincin nan dayawa ko maryama? daga can kuwa ba karamin jarumta jabeer yayi ba wurin hana kanshi tashi ganin idon baffa amma jikinshi har rawa yake yi, baffanmu dake lure dashi yana mamakin irin son da jabeer yake wa maryama tamkar dai labarin laila da majnoon,yana iya sadaukar da komai domin farin cikinta,kamar dai yadda ya sadaukar da.....

Katsewa tunaninshi yayi sakamakon "Subhanallah" da innarmu ta ambata tana kokarin rike maryama dake shirin faduwa kasa,a tamanin jabeer ya nufe su baisan ya akayi ba sai ganin shi yayi rike da maryama wacce jiri ke kwasarta sakamakon aman da tayi mai yawan gaske,ruwa innarmu ta kawo domin wanke mata baki jabeer ya amshi ruwan hadi da tsugunar da ita kasa a hankali ya fara zuba mata ruwan tana kurkure bakinta da wanke fuska,gaba daya maryama ta galabaita kamar mai jinya gyara wurin da ta bata innarmu ta fara shikuma ya kama ta da nufin shigar da ita daki, "sannu uwata Allah ya kiyaye gaba" cewar baffanmu daga kai kawai ta iya yi su salma ma sannu suka mata duk tabisu da daga kai haka jabeer ya kaita har cikin daki kan gado rike da hannunta ba tare da ya yi la'akari da idanun da iyayen nasu suka bisu dashi ba.

 
Kwantar da ita yayi saman gadon calmly yace "bazaki canza kaya ba?naga wadannan sun baci, gyada mishi kai kawai tayi bata ce uffan ba, hakan yasa ya bude mazubin kayanta ya fitar da wankakken bedsheet ya rufa mata har kan kirjinta, cikin nutsuwa yace "sleep tight pretty,don't stress your self with thinking, anything will be alright, okay? ya kare da daga mata gira daya, jin batace komai ba kuma yasan zaiyi wuya tace din yasa shi juyawa don fita karsu baffa suga ya dade a dakin, jin lallausan hannunta mai kama da garin fulawa yayi cikin nasa, rumtse idanu jabeer yayi kafun ya juyo a hankali yana kallonta da gajiyayyun idanunshi,.

Cikin marayan murya mai cike da alamu na rashi maryama tace "do something hamma jay. Plsss na rokeka kar ka bari su baffanmu su hanani yin jamb dinnan kaga idan nayi missing yanzu sai next year, and i don't want t....Shhhhht ya katseta ta hanyar sa dan yatsanshi a saman lebenshi ya kafe ta da ido wanda ya tilasta mata janye nata idanun domin wasu irin bama bamai take hangowa cikin nashi idon wanda anytime zasu iya tarwatsewa,yace cikin sanyin murya "you don't worry pretty zaki jana jamb Insha Allah zanyi kokari ganin nayi convincying baffanmu idan ya amince nasan innarmu ma zata amince,kedai keep praying idan Alkhairi ne Allah ya tabbatar idan kuma sabanin haka ne Allah ya musanya mana da mafi alkhairi"

Turo baki tayi gaba tace "kai hamma jay, ka taba ganin inda neman ilimi ya zama ba alkhairi ba, nidai alkhairi ne Allah, yadda take maganan ba karamin yamutsa jinin jikin jabeer take yi ba, da shakakkiyar murya yace "da gaske pretty ba komai mutum kanso ba a rayuwa ya zame masa alkhairi,....Shigowar innarmu dauke da ruwa da magani ne ya katse masa maganar da ya fara.

Tace "to bawan mace saika bamu wuri haka nan, ni naga yadda za'ayi auren ai kana nuna mata rawar kafa tun yanzu ba dole ta rena ka ba ta ringa wahalar da kai, murmushi yayi yana shafa sumar shi as usual kana simi simi ya fice a dakin, juyowa innarmu tayi tana banka mata harara ganin yadda ta turo baki gaba tace "kin tashi kinsha maganin ko yaya?.....Misalin karfe sha biyu dare ya tsala amma barci ya kauracewa idanun jabeer dake kwance rungume da filo, hakama maryama dake ta faman juyi saman gadonta tunanin duniya ya isheta na yadda zata raba kanta da auren jabeer ba tare da ta bata ran iyayensu ba da shi kanshi jay din don yana da wani matsayi na musamman a zuciyarta amma bangaren yan uwantaka na jini ba soyayyan aure ba, a gefe guda kuma zuciyarta na batan shawaran gobe da safe ta kira kawarta siyama ta tabbata zata taimaka mata. Da wannan tunanin ta tsaida matsaya.

Lumshe idanu yayi ya kuma budewa cikin mutuwar jiki ya janyo wayarshi gallery dinshi ya shiga ya fiddo wani hotonshi da maryama wanda suka dauka a asibiti lokacin bata da lafiya tana zaune kan gadon hospital din fuskarta tayi fayau kamar ba jini a ciki, bakinta ya bushe sosai shikuma yana gafenta ta kwantar da kanta a kafadunshi, ya dade yana kallon hoton yana saka abubuwa dayawa a ranshi kafun ya rufe ya nufi messages ya fara rubuta mata kamar haka, 

"This is for you my life."

Yadda kunne yaji haka zuciya ke aunawa.
Inda raina da rabo na zaki yi ganewa.
Nida ke sirrin juna zamu yi boyewa.
Ra'ayina kece kikka zamanto tawa.
Ki kula min da kaina ma'ajin sirrina.
Hakan shine zai sanyaya ruhina.
Wa'adina yazo indai bakya sona.
Tunda naji wadansu akanki suke zagina.
Kinga tauna sam ba'ayi saida hakora.
Kiyi kirana gefenki nazo na sarara.
Ko a dan aiki daukeni na kore kura.
Nifa ba komai kanki koda anmin kyara.
Ni kawai sonki nake dan zuciya ta harbu.
Da'ace zakiyi shagawaba ni zan miki bambu.
Fadamar sanyi kika so na hada miki lambu.
Kanki zan iya dambe koda hannu ba kambu.
Tausaya min agaza min kada kiyi min bore.
Na aiko sakonnin so karda ki share.
Na rasa ki masoyiyata a dole na zare.
Shi dafin so naki da wuya taya zan jure.
Kalmomin da kike min nake yin hadda.
A kwakwalwata na aje su zamar mini shaida.
Bani in baka sone ba ya yin tsada.
Nai sabo dake sonki zuciya ya huda.
Ki tuna ni dake kowa tare ya ganmu.
Hanta da jini tilas sai an barmu.
Nayi kuka kwakwalwa sonki yake damu.
Nazarina aure naki a taya zan samu.
Babu laifi dan ni ke dai nayiwa kishi.
Ko kallon ki naga wani yanai sai na tsaneshi.
So ya danne ni a sa'in da kyar zanai nishi.
Kinji sakona ina fatan zaki karbeshi.
mKarki bari ya zamanna inayin kuka.
Ni masoyine kanki kamar zan hauka.
Ki gina min sharuddai naki kawai na dauka.
Tunda kaunarki nake babu dare ba rana.
Ajikina na ke jin kina saurarena.
Abar kaunata kin tsaurata alwashina.
Mafakar ruhi kaunarki tana ta gudana kanki ni na zaqu daure ki zamo gatana.
Ina fatan wataran ki kirani habeebi.
Zanji dadi mai sona ko bayan raina.
Koda ace a duniya ba numfashina.
Da kin tuna wanda kike so ya zamo ni daina.
Lyrics by hameesu breaker.

Lokacin da sakon ya shigo wayar maryama tana kwance sai faman juyi da kulla wasikar jaki take yi ita kadai, janyo wayar tayi cike da kasala,ganin sunan hamma jay yasata bude sakon...Maryama ta karanta content din yafi sau goma ta karanta ta sake yayinda take jin kanta kamar tana yawo cikin gajimare tsabar yadda kalaman suka shiga har cikin zuciyarta, ayyanawa take a ranta wannan kalaman daga bakin attajirin mai kudi ya fito ma'ana dream husband dinta wayyo dadi kan dadi kenan dan turo baki tayi gaba duka ita kadai tunowa da hamma jay ne ya turo mata ba wannan mai kudin ba, rungume wayar tayi a kirjinta ta sake fadawa duniyar tunanin da ta saba, da haka bacci ya kwasheta, a bangaren jabeer ma yayi ta jiran ganin ko zata mishi reply amma shiru har dare ya raba haka ya saduda ya rungumi pillow yayi baccin wahala.   

Washegari da ya kasance alhamis maryama ta gama aikace aikacenta da ta saba dan ma yanzu aikin ya ragu mata tun randa hamma jabeer yayi magana su fatima suke wanke wanke da diban ruwa, itako yawanci daga sharar tsakar gida da gyaran dakuna wataran da wanke bayi shikenan aikinta.dakin su ta nufa da sauri dan ta riga da ta gama yanke hukunci jiya da dare jiran wayewar gari kawai take yi ta aiwatar,wayar ta ta janyo mai kyawun gaske kirar samsung wanda hamma jay ya siya mata koshi wayar dake hannunshi bata kai girman nata ba,contact ta shiga ta fara laluben lambar siyama.

Siyama kawata ce amma ba sosai ba dan ta girme ni da akalla shekaru shida zuwa bakwai, farin jinin mutane da nake dashi ne ya hadani da ita saidai ko kadan innarmu da hamma jay basason alakata da ita a cewarsu idonta ya bude da yawa kuma gidan su ba gidan mutunci ne ba,wannan ne yasa na dan fara jan baya da ita,siyama tana yawan fada min idan ina neman taimakonta akan komai kar inyi shakka in tambayeta kawai,ba laifi tana da budaddun idanu kam dan yanzu haka ma babban shago take dashi na saida suturu irin na mata kala kala mutane da dama ganin karuwa suke mata dimin kowa yasan iyayenta talakawa ne gashi ita kuma tana juya miliyoyin kudi cikin lokaci kadan....Ajiyar zuciya na sauke lokacin da na iso kan lambarta ina tunanin anya abunda zan aikata daidai ne kuwa? da sauri na kauda tunanin daga raina na danna mata kira na kara a kunne na,...Muryar matar nan ta mtn ce ke sanar dani bani da kati a wayata,wani dogon tsaki naja da zan kama matar nan ta mtn Allah ne kadai yasan abunda zan mata,kwata kwata na manta banida da kati, to dama wa garen da zai samin kati duk wanda yazo da dan maikon shi sai baffanmu yace anmin miji shikuma mijin da ake hankoron anmin din sai yayi leburanci an sammishi before ya zo ya sanmin, kaico na! ni maryama.

Bani da zabi fache in turawa siyama 'please call me,'hakan kuwa nayi in the hopes that she will respond, tagumi nayi ina jiran kiranta patiently, it was only a few minutes,but it was the longest waiting in my life,wani irin zabura nayi lokacin da naji karar wayata alamar kira yana shigowa....