MARYAMA

Page 06

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

  By 

Ummu Fadeela.

EPISODE 06.



.....Da hanzari na daga wayar na kara a kunnena hadi da fadin "hello"

Daga daya bangaren siyama tana murmushi tace "yau wace rana maryama ta tuna da ni, dan dariya nayi nace "haka zaki ce kenan? dariyan tayi itama tace "what's up babe? naji muryarki wani iri,ajiyan zuciya na sauke nace nothing much siyama,i really want to see you,"....hope all is fyn kina cikin damuwa ko"cewar ta, yake nayi nace all of the above yanzu dai kina ina, dan fasali taja kafun tace "ina boutique nawa," ohk ina zuwa nan da 30 minutes insha Allah.

Kiran da naji innarmu na kwalo min ne ya tsaida ni daga shirin da na fara na fita da sauri abun karin kumallo ta nuna min banyi musu ba na dauki plate mai dauke da dafaffiyar doya da kuli kuli ko arzikin mai bai samu ba sai kofin bakin shayi na juya, sosai hakan ya ba innar mu mamaki ganin yau ban turo baki ba amma sai bata ce komai ba... A daddafe na tura doyar rabin yanka daya kana sauran na tura shi kasan gado, gwara shayin shikam na shanye tas dan innarmu ta iya dafa bakin shayi irin na yan nijar, doguwar rigar material kalan milk na saka kana na dauko jilbab dina shima har kasa na zura na dan feffesa turare sama sama na fito ina tunanin karyar da zanyiwa innarmu kamun in fita, da sallama na shiga dakinta nadan durkusa nace "innarmu zan shiga wurin umaimah da akwai wani littafi da zamu duba tare da ita,"

Ba tare da tunanin komai ba tace "ki gaida mun da ummar ta su." da " to" na amsa ina jin dadin yadda ban samu matsala ba wurin fitar.Saidai ina sako kaina kofar gida idanun hamma jay ya shige cikin nawa tamkar dama jiran fitowa ta yake.wani irin faduwa gabana yayi amma sai na dake na shige gidansu umaimah badan raina ya so ba...Mintuna ishirin na kwashe a wurin umaimah da na same ta babu lafiya tana kwance ribb,amma duk da haka ummar su ta jibga mata uban wanke wanke wai sai ta wanke su tsabar rashin tsoron Allah, zan iya cewa tunda nake ban taba ganin azzalumar kishiyar uwa irin ummar su umaima ba,duk saurin da nake haka na tattare jilbab nawa na fara wanke kwanukan yayinda ummar ta ke ta banka min harara da fadin gwara da kika taimaka mata don ko uban ta ne yau bai isa ya hanata wanke wadanan kwanukan ba" ko kala bance ba don nasan halinta ba Allah a ranta, da sauri sauri na ke aikin don in samu in tafi.Haka na fito bayan na gama wanke wanken badan na soba sai dan kar in makara zuwa wurin siyama,koda na fito maimakon inbi kudu wanda zai kaini har boutique nata sai kawai nabi arewa duk don in gujewa hamma jabeer saidai banyi taku goma lafiyayyu ba call nashi ya shigo wayata, tsaki naja a raina nace ko kafi kuda naci bazan dau kiran nan ba,aiko kamar yaji abunda na fada ya ringa kira ba tsayawa wani na yankewa wani na shigowa keke napep na tsayar ba tare da nabi takan kiran da ya ke ta shigowa ba saida na zauna mai kyau na sanar da mai keken inda zai kaini kamun na daga kiran na kara a kunnena.

Wani irin ajiyan zuciyar da naji shi har cikin kwanyata hamma jabeer ya sauke, da breaking voice yace "damn it!baby ina kika yarda wayarki?".

Ina hararar wayar nace "sorry hamma jay wayar tana silent ne shiyasa ban ga kiranka ba".

"Ina kika tafi yanzu"

"Zan karbarwa umaimah magani a pharmacy ne yanzu bata jin dadi"

"Ohk ki kula min da kanki plsss kar wani ya gane min ke, ko inzo in rakaki"?

Na yi saurin fadin "a'a kayi aikinka ai babu ma nisa nan nan nefa, concentrate on your work plss ko so kake oga zubairu yayi fushi, yanzu zan dawo ma ai,"na fada da saurin da inda a gabanshi nake sai ya fahimci karya nake mishi tsabar yadda jikina ke rawa.

Jabeer ya shafa kanshi yana lumshe idanu murya kasa kasa yace "I love you pretty".

"Uhhmm" nace kana na katse kiran ina hararar wayar tamkar shi yai min laifi,...Lokacinda na iso na iske siyama tana tare da costumers suna siyan kaya, dan haka na ja gefe na samu plastic chair na zauna har ta sallamesu kafun ta juyo gare ni cikin fara'a ta kama hannuna zuwa wani dan corner dake cikin shagon mai dauke da kujeru guda biyu masu kyau sai center table a a tsakiyar kujerun bissmillah zauna ta fada tana wucewa jikin wani karamin fridge dake wurin, zama nayi ina karewa haduwar shagon siyama kallo,yanzu duk wannan uwar dukiyar nata ne babu mai kwace mata Ya Rabbi ka dubeni.

Maganarta ne ya katse min tunani na ba tare da nasan ta iso wurin ba,"hey girl,you look so worried and tensed me ya ke faruwa ne?.

Ta fada tana tsiyaya fanta mai sanyin gaske cikin glass cup wanda take raba ya cika har bayan cup din,turo min tayi gabana tare da wani bowl shima na glass mai dauke da crispies mai dan yawa a ciki, duk da yadda yawuna ya tsinke hakan bai hana ni kauda kai ba ina kallonta nace "nagode," na cigaba da fadin "siyama ina cikin damuwa matuka kinsan burina na son yin karatu mai zurfi alhmdullillah I passed my WAEC in flying colours,saidai kinsan iyayena are not financially enough dazasu iya daukan nauyin karatuna.

Rumtse idanu nayi ina jin ciwon abunda zan fada cikin zuciya ta, na daure naci gaba da fadin, "would you believe wai aure za'amin da hamma jay? hakan na nufin gaba daya mafarkina ya zama zero,siyama bazan boye maki ba,zamana ina ganin mahaifana cikin talauci ba karamin kona raina yake ba,haka kuma bazan amince in taso cikin talauci kuma inyi aure cikin talauci ba, can you imagine kwanakin baya baffanmu fom na tailoring school ya kawo min? plsss siyama i need help, i want you to help me da babbar sana'ar da zanyi inbar garin nan inje inyi karatu in zama successful woman abun kwatance."

Ajiyar zuciya siyama da tayi tagumi tana kallona pitiefully ta sauke sannan tace,"kwarai na tausaya maki maryama I feel your pain also, talauci babu kyau babe,..."Dan numfashi taja kafun ta cigaba da cewa,"Mutane da yawa kallon karuwa suke min, wacce take saidawa maza jikinta domin ta samu kudi,ganin wannan dan shagon da motar da nake hawa da gidan dana ginawa iyayena,saidai sam ba haka bane maryama."

Duk da ban yarda da maganarta ba amma hakan bai hanani gyada kai na ba alamar gamsuwa,...

Taci gaba da fadin, "akwai wani mai gidanmu wanda saurayi na ke aiki a karkashinsa nima ta dalilin saurayin nawa na saba dashi, yana aiki ne a yankin naija delta......Sai kuma ta matso kusa dani sosai ta min maganar a kunne sannan ta matsa baya tana dan murmushi da fadin aikin baida wani hatsari in kin amince yanzu zan kirashi nasan zai taimaka miki."

Without thinking twice na gyada mata kaina dan a wannan lokacin tamkar a cikin teku nake duk abunda aka mika min domin ya ceto ni kamawa zanyi koda ko wuka ce mai kaifin gaske.....Dariya tayi tace "that's my girl,just give me a moment bari inyi magana dashi".

Mikewa tayi tana taku daidai domin matsawa daga kusa dani, yayinda nabi bayanta da kallo cike da sha'awar hadaddun kayan dake jikinta,...Daga inda nake ina iya hango yadda bakinta yake motsawa tana magana cike da yanga,haka kawai na tsinci kaina da son jin me take fade cikin wayar saidai duk yadda naso hakan ya gagara domin kasa kasa take maganar,after like ten minutes ta katse wayar ta dawo kusa dani tana fara'a hannuna da suka sha jan kunshi ta kamo tace," You are a lucky girl maryama, munyi magana dashi yace zai shigo adamawa ran friday kuma sunday zai koma,so all what we have to do now shine muyi kokari ku hadu ran saturday kuma zai sauka ne a 10 STAR HOTEL a jimeta,yanzu bansan ya za'ayi kije jimeta daga nan ba? kina ganin za'a barki a gida?."

"Ba wannan maganar siyama,wa kike ganin zai barni in tafi jimeta a gida, ai saidai kawai in sati hanya inje ba tare da sanin kowa ba."

"Anyway, ki fito da wuri ranar asabar din sai ki biyo ta nan muga yadda za'ayi daga nan in baki contact nashi, and abu mai muhimmancin daya kamata in sanar miki shine,don't tell him your real age, idan ya tambayeki shekarun ki kice masa 23, ohk?.

"Meye ma'anar hakan?, na tambaye ta sounding confused...Just do as i say maryama" gyada mata kai nayi na tafi zuciyata na ta tsalle wani sashi na zuciyar na gargadina yayinda wani sashi yake karfafa mini guiwa.

Allah ya taimakeni lokacin da na dawo gida ban tarda hamma jay a waje ba a gida ma Innarmu tana bayi haka na shige kamar munafuka...Na kwashe yinin ranar ina tunanin yadda zan tafi yola ba tare da kowa ya sani ba a gida a bangare daya kuma na kagu asabar tayi domin ina ji a jikina mafarkina na rayuwa mai inganci ya kusa tabbata. "Shin zaki bijirewa iyayenki ne da kuma wanda ya sadaukar da rayuwarshi akanki saboda duniya ne maryama?anya kinyi tunani mai kyau kuwa? zuciyata ce ta tuna min hakan, rumtse idanu nayi da karfi hadi da matse pillown dake hannuna, ji nayi kaina na sarawa da karfi karfi...

Misalin bakwai na dare bayan nayi sallan isha na sake tambayar innarmu zuwa duba jikin umaima dan tana tsaye min a rai...Koda na shiga jikin nata da dan sauki saidai still tana kwance.

Kwance na sameta har lokacin tana fama da zazzabi, 

"to uwar iya yi me kuma ya kawo ki cikin daren nan?,muryar umma ya katse min hanzari daga kokarin zama da nake yi, na bude baki da niyyar bata amsa umaimah ta girgiza min kanta cike da tausayi saman fuskanta, tunda umaima ta taso take shan gallazawar kishiyar uwa sakamakon rasuwar mahaifiyarta ita kuma umma bata taba haihuwa ba don haka take zuba mulki a gidan son ranta ko baban umaima idan taga dama sashi aiki take yi kuma bai isa ya tanka ba.Sallamar da kanwar ta basira tayi ne yasa ta juyawa da fara'a suka shige daki da kanwar tata.

Kwafa nayi na zauna hadi da tagumi, abubuwa sun min yawa a yan kwanakinnan,.

Kallon tsaff umaimah ta min tace cikin muryar marasa lafiya, "pretty meke damunki? you look so dull." numfashi na sauke,banyi mamaki da umaimah ta fahimci akwai damuwa tattare dani ba,dan bama boyewa juna komai amma yau kam dole in boyewa umaimah sirrin dake raina don ko giyar wake nasha bazanyi gigin fadi mata decision dana dauka ba.

"Uhmmm ina jinki,karki ji shakkan fadi mani komai don na saba jin abubuwan mamaki kala kala a wurin ki maryama"cewar umaimah da ta kureni da idanu tana jiran jin abunda zan ce.

Yaken dole nayi nace "wai me kika gani ne? nifa ba abunda ke damuna, its just a mood swing, sai kuma halin da kike ciki da wannan uwar taki mai bakin halin tsiya, Allah dai ya kaimu ki yi aurenki ki huta da wannan rayuwar na kunci da takaici,kana gidan ubanka amma ka kasa rawar gaban hantsi" na fada ina dan dariyar da iya karshi saman lips nawa.

Umaimah tace "da dai bansanki bane saikice mood swing amma indai maryamar dana sani ne,then there most be something fishy, sannan halin da nake ciki kuma ai wannan ya riga da ya zama jiki maryama ni har abun ya daina damuna yanzu, nasan komai lokaci ne with time zata chanza insha Allah, ta fada da rauni cikin muryar ta...duk bama wannan ba,dazu karyar me kika bankawa hamma jay dan ya shigo,zaro ido nayi hadi da mikewa ina buga kirjin da bansan ma na aikata ba,cikin zaro ido nace" ya shigo umaimah?me kika ce masa to?."

"Relax mana yan mata, yace kince masa umma ta aike ki karbo min magani a pharmacy".

Da sauri nace "eheemm me kikace masa ke kuma"?

"Cemasa nayi karya ne ba wanda ya aike ki, kuma ma ai shima ya san umma dai bazata ce a siyo man magani ba".

Hannu na daura aka nace "shikenan kin kashe ni umaimah,yanzu idan hamma jay ya tutsiyeni da tambaya sai ya gano gaskiya, innalillahi wa'inna ilaihiraji'un nake ta maimaita wa....Nasiha sosai umaimah tamin kamar dai yadda ta saba kullum,zuwa yanzu kaina ya dade da yin haddar nasihohinta sai dai bana amfani dasu duk da cewa wataran ina ji a jikina cewar gaskiya take fadamin,shigowar innarmu ne yasata katse maganar da take yi, innarmu ta mata sannu da jiki sannan tace mu koma gida dare yayi,har nakai kofar fita umaimah ta kira sunana cikin sanyin murya, a natse na juyo muka hada idanu fuskata dauke da tashin hankali,tace "ban fadi masa komai ba".

Wani irin ajiyan zuciya na sauke na bi bayan innarmu da sauri....Kwanci tashi asarar mai rai yau gashi asabar tayi,kwana biyun nan na kwashe sune cike da zullumin abunda zai faru da yadda zanyi in tafi yola ba tare da kowa ya ankare ba,aikace aikacen dana saba nayi hamma jay kuwa na gefe sai faman daga karfen mota yake tamkar Allah ne ya aikoshi ya jike sharkaf da zufa...Dan satan kallon shi nayi ina mamakin yadda lafiyayyen jikinshi ke ta shekin daukan ido ga gargasa kwance gwanin sha'awa amma sabanin fuskarshi da yayi bakikkirin,kanne min ido daya yayi gami da dage gira bayan mun hada ido, kasa kasa yace "morning my pretty angel, ki kalleni yadda kike so am all yours"

Wani irin kunya ne ya lullubeni kenan hamma jay yasan ina kallonshi, hooo what a shame....Wanka nayi bayan na gama share sharen da na saba,na shigo daki na goge jikina da xani na musamman dana adana dan goge jiki bayan na fito daga wanka, lotion dina na jergens mai dadin kamshi na mulke ilahirin jikina dashi kana na shafa roll on a armpit dina na dauki body spray na vivelle da kuma bakhour na feshe jikiina dasu suma, take dakin ya bade da kamshi Na nufin gaban akwatuna na dake jere na bude daya ina tunanin kayan da zan saka,fitar na musamman ne don haka dole kayan da zan saka ya zama na musamman.

Karshe dai bayan na gama ruwan ido wasu riga da siket na atamfa na fitar mai kalan dark pink and brown touches na bude akwatin inners dina na dau pant bra da under wear su na fara sakawa sannan na saka atamfata da ta zauna min dasss tamkar a jikina aka dinka, gaban mirrow na na koma ni ba mai cika kwalliya bace a fuska,dan haka dan farar hoda na murza a hannuna na goge face nawa dashi sai chapette dana gogawa lips nawa nadan gyara eyebrow da eyelashes dina da mascara, nan na fito gwanin sha'awa turaren rasasi na fesawa jikina kana na ajiye kwalbar ina karewa kaina kallo jikin mirrow ba karamin kyau nayi ba...Wani tunani ne ya fado min cikin kaina yanzu duk abunda nayi amfani dashi kama daga sabulun wanka har zuwa sutara da kayan kwalliya da dangin perfumes dana shafa duk hamma jay ne ya siyamin fa, kai hatta wannan mirrown da nake ganin kaina a ciki shi ya buga min a wurin sana'arshi, "anya maryama"

Da sauri na kawar da tunanin ina barin wajen,jakar islamiyyata na sauke na cusa gogaggen gyale na pink colour a ciki kana na dau hijab din islamiyyata da ya kasance har kasa na zura a jikina na dauko nikab na daurawa fuskata flat shoe bakake na sanya na rataya jakata na fito kirjina na dukan tara tara.

Wani kallon da ya haddasa min kadawar yan hanji innarmu ta banka min, tace "ina kika nufa da wannan farar safiyar dan nasan dai lokacin islamiyyar taku baiyi ba, ko yau kuma sabon salo kika bullo dashi?"

Agogon dake daure tsintsiyar hannuna na duba,inna lillahi na furta a kasan makoshina, ashe bakwai ma yanzu ta cika,what i have done ni maryama?.

Amm...emm...In. Innarmu "rufe man baki cewar innarmu ganin sai kame kame nake yi"kin shige kin jira abun karin kumallo ko sai na make ki jai'ra kawai,nasan don ki gujewa dumamen tuwon ne yasaki shiryawa da wuri, to sai ki fadan gidan uban da zakije ki karya da asubahin nan,"

Nannauyan ajiyar zuciya na sauke ina barin wurin ganin inda innarmu ta dosa...A daddafe naci dumame yanka daya nasha koko inajin tamkar zanyi amai,amma don kar in makara yasa naci na fito ina dan kame kame nace da innarmu "zan wuce".

A tsanake ta dubeni tace "wai saurin na meye haka yau?."

Cikin saisaita nutsuwata nace "ina so in shiga wajen umaimah ne inga ya ta kwana da jiki, kuma kinsan zata rike ni innarmu gashi banson yin latti".

Bayan na fito ko kallon kofar gidan su umaima banyi ba, na sake nikab nawa na tsaida keke napep na shiga ban zame ko ina ba sai boutique na siyama, zaune na tarda ita tana jiran isowata, 

"Wow babe!you look just a pretty you are,cewar siyama lokacinda na zame nikab da hijab dake jikina, da hanzari na yafa gyale na wanda ya rufe min har kan mazaunaina,ina blushing nace "stop whining me abeg," dariya siyama tayi tace "serious kinyi kyau sosai,act classy acan maryama plsss koda shike bani da damuwa da wannan na sani"turaren bondage ta dauka ta kuma fesheni da shi sannan ta dau wani jaka samfurin gucci dake rataye jikin rack na jakankunan siyarwarta ta jefa turare da lipbalm sai chewing gum da kudi 5k a ciki ta rataya min a kafadata,tace manage with this".

With much suprise nake kallonta kafun inyi karfin halin cewa "amma banida kudin da zan biyaki wannan siyama".

'"Karki damu ba sayar miki nayi ba kyauta na baki"cewar ta.

Ita tamin rakiya har inda na hau mota kafin ta koma, kirjina ne keta tsalle lokacinda na gyara zama cikin motar, wannan shine first time da zan tafi wani gari ba tare da sanin iyayena ba, shin anya nayi daidai kuwa? anya ban kauce hanya ba? sai karfe sha biyu na rana muka iso yola wani napep na kuma tsayarwa na mika masa papern da siyama ta rubuta min address na bako na.

Bakin wani tangamemen hotel dan sahun ya tsaida ni, daga kai nayi naga an rubuta 10STAR hotel jikin wani allo, jikina ba kwari yayinda kafafuna ke rawa na nufi hanyar shiga hotel din,ya salam wannan shine karo na farko a tarihin rayuwata da ni maryama zan shiga hotel koda ko wani iri ne,duk inda nabi idanun mutane ne ke yawo akaina kamar sunga bakuwar hallita, da kyar na kai kaina reception na samu wuri na zauna ina sauke numfashi kamar wacce tayi gudun famfalaki.dama siyama ta fadi man cewa idan nazo in sanar da ita sai ta sanar dashi, hakan kuwa nayi na sanar mata isowata.

Daya daga cikin waitress dake wurin ne ta matso hadi da tambayata,"first time here ma'am?."

Daga mata kai nayi kafun nace "yes".

Tace "kina bukatar oda ne kodai jiran wani zakiyi"?

Nace mata "jira zanyi,amma ina bukatar ruwa mai dan sanyi".

Yess ma'am" cewarta kafun ta juya ta kawo min ruwan gora mai sanyi da kuma glass cup akan tray godiya na mata ta juya ta tafi, gyara zama nayi na tsiyaya ruwan kadan cikin cup dan am very thirsty,sipping ruwan na fara kadan kadan kamar bana so...,I waited patiently is not too long amma a wurina ji nake tamkar nayi awanni zaune wurin. kamar ance in daga idanu na na hango shi ya shigo wurin,wani irin bugawa zuciyata yayi take ruwan dake bakina ya kauce hanya ya nemi fita ta cikin hancina.......