Page 07
💫MARYAMA💫
By
Ummu fadeela.
Episode 07.
......Walking slowly ya nufo inda nake ba tare da ya daina kallona ba, da sauri na tsugunnar da kaina kasa ina kokarin saisaita nutsuwata da yake shirin kubce min yayinda kirjina ke bugun tara tara, Siyama bata ce min haka yake ba na dauka zanganshi katon gaske bakikkirin mai katon ciki tunda tace mai gidan sarayinta ne, sai dai sabanin tunanina,...Babba ne akalla zai kai shekaru talatin da biyar ko ma fiye da hakan, shi ba baki ba kuma baza'a ce masa fari ba, dogo ne kadan amma hamma Jay ya fishi tsayi da kuma fadi kodon hamma Jay yana daga karafuna ne? Sanye yake cikin wasu tsadaddun suit black colour kallon farko idan ka mishi zaka fahimci arziki ya zauna a jikinsa kyakkyawan sajensa zuwa kan dan karamin gemunsa na gayu ya taimaka wurin fitar da kyawun bakar fuskarsa....lokacinda ya matso gab da ni zuciyata ce ta nemi shigewa cikin cikina hannunshi duka biyu ya daura saman teburin dake gabana ya dan rankwafo kadan yana leka fuskata kamar mai son gano wani abu..,da kallo few mutanen dake reception din suka bimu.
Cikin low voice yace "Maryama right?!". Ya yi tambayar yana dage gira.
Dago kaina nayi karaf idanuna suka shiga cikin nashi da hanzari na janye nawa idanun na mayar dasu kasa ina jijjiga masa kai kamar kadangaruwa.
Dariyar shi mai kyau yayi yace "ai ni legend ne wurin guessing abu" hannunshi daya ya miko min yana kokarin zama yace "I am Sadeeq.
Matse nawa hannayen nayi a tsakanin cinyoyina ba tare da na dago kaiba nace "nice name"....Thank you yace yana maida hannunshi ganin banda niyyan bashi nawa hannun, zama yayi a kujerar dake fuskantar tawa ya daura hannayenshi bisa kumatunsa yana min kallon kurilla,murya kasa kasa yace "wani ya taba fada miki cewa you're beautifull?".
Gabana ne ya fadi dan ba wanda ya fado man a rai a lokacin sai hamma jay, kusan kullum sai yace min " ke kyakkyawa ce maryama".
Kawar da kaina nayi daga kallon da yake min kamar sabon maye nace "i heard that for a million times".
Jinjina kai yayi yace "add with mine,you're very very beautifull". Na gode na fada jikina yana yin sanyin da ban san dalili ba.
"Anyway,siyama ta fadamin dalilin zuwanki, but you look younger than i expect, shekarunki nawa? ya tambayeni,siyama tace min kar in fada mishi ainihin shekaruna but me amfanin karyar shekarun? me hakan zai kare ni dashi? cikin rawan harshe nace mishi 17 almost 18.
"You are young,too young.Kinsan dalilin zuwanki nan? sam wannan business din bai dace dake ba kinyi kankanta sosai, bazan iya dealing da childinesh and drama da zaki min ba while working "
Wani irin bugawa kirjina da gabana sukayi lokaci guda, take wasu hawaye masu zafin gaske suka cika man idanu suna kokarin saukowa, da dabara na maida su ina jin duniyar tana juyamin tamkar ina cikin gajimare.
Waitress Sadeeq ya yafito ba tare da ya kula da halin da na shiga ba,da hanzari ta taho hadi da ajiye mishi menun dake hannunta, kallon menu din yayi for few second kana yace "table water for me, and fried rice with pepper chicken and soft drink for bakuwata.
Juyawa tayi tana fadin "yes sir".
"Banajin yunwa" na fada cikin muryar da ya bayyana halin da zuciyata ke ciki.
Kallona yayi kadan yace "duk wanda yazo wuri domin ni ki tabbata baya tafiya haka ba tare da yaci wani abu daga gareni ba, hope you get it pretty?."
Wani irin dagowa nayi jin sunan daya kirani da "pretty"oh Ya Rabb.Save me." na fada domin sak ya koma min hamma jabeer.
Bayan kamar minti biyar saiga ta ta dawo dauke da wani dogon tray tazo ta ajiye a gabanmu plate mai dauke da hadadden fried rice da yaji vegetables ta ajiye gabana sai wasu bowls guda biyu daya cowslow ne ciki dayan kuma pepper chicken ne da kallo daya na mishi na ji ya tono min yunwata na kusan shekara daya spoons ta ajiye bisa wani dan kyalle mai daukar hankali,sai drink din ta jere hadi da bottle water sai tissuen dake tsakiyar teburin da ta gyarawa zama, tana murmushi tace min "enjoy your meal ma'am ta juya ta bar wurin.
Tsiyaya ruwan da ta ajiye masa yayi yakai baki ba tare da ya daina kallona ba yace "kici abinci ki koma gida zan sanar da siyama cewa you are too young for me,bazaki iya aikin nan ba".
Hawayen da nake ta kokarin boyewa ne suka samu nasarar gangarowa bisa kumatuna, duk sanda yace nayi karama nakanji tamkar guduma ya buga min a kahon zuciya ta,shikenan dama shine last hope dina to shima na rasa shi, ban ankara ba ashe kuka nake yi sosai yayinda sadeeq kuwa yayi tagumi yana kallon ikon Allah. A ranshi yace "you see,wannan shine abunda nake gudu dama tayi karama sosai gashi nan yanzu daga magana dai harta fara min kuka."
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "yanzu me na kuka?kodai so kike ki tara min jama'a?"
Goge fuskata nayi cikin sheshshekar kuka nace "nothing sir, ina kuka ne dan na rasa damata,."
"Wani irin dama kenan?".
Ya tambayeni sounding so pissed off.cikin nutsuwa na fara bashi labarin yadda na gama candy na da sakamako mai kyau, kana na daura da labarin burina na son ci gaba da karatu zuwa matakin jami'a...Ina goge hawaye na nace "sir sai dai iyayena basu da karfin daukan nauyin karatu na zuwa gaba,dan haka suka fara shirin aurar dani ga dan uwana shiyasa na yiwa siyama hirar ita kuma tace akwai wadda ta sani da zai taimakamin da haka ne ta hada ni da kai, gashi kaikuma kace bazan iya business din ba so dole inyi kuka, dama kai ne last hope dina yanzu idan na koma aure za'ai min and thats the end of my hobbie,my dream,my passion,my ambition. And the end of me also".na fada ina fashewa da kukan da ya kara janyo hankalin mutane zuwa kanmu.
Tunda na fara magana yake kallona with much interest a labarin da nake bashi, saida na kai karshe sannan ya dau hankerchief ya goge goshinsa duk da ba zufa yayi ba,bude baki yayi cikin maturity yace "Sad, very sad, na tausaya miki matuka,amma yanzu gogen hawayen haka nan crying moody gal"
Cike da zolaya ya fadi hakan yana mika man hankin dake gabanshi,amsa nayi na goge fuskata.
Dan fasali yaja sannan yace "a matsayin yata ko kanwata zan taimake ki, for now kije kiyi magana da parents dinki duk yadda kuka yi you let me know ni kuma i will help you daga kan naira daya har zuwa million goma matukar zakiyi karatu ki amfani al'umma,shi karatun ya mace ai yana canza al'umma ne domin itace tarbiya matakin farko, so kije ku tattauna saiki sanar dani duk yadda kuka yi."
Wani irin farin ciki nake ji marar misaltuwa, ji nake kamar in tashi inyi ta tsalle a wurin tsabar farin ciki,ina kuka ina dariya duk ni kadai "cikin zumudi da tatin farin ciki nace "na gode sir, Allah ya sa farin ciki a rayuwar ka kwatankwacin yadda kasa ni a ciki,na gode Allah ya kara budi mai albarka".
Sadeeq dai ya tallabi chin nashi sai kallonta yake, da alama kallon yarinyar yana bashi nishadi don ta iya drama sosai, murmushi yayi yace "ba godiya a tsakaninmu dukda cewa yau na fara ganinki, ina respecting mace mai son yin ilimi a kowanne bangare na rayuwa,and don't call me sir again, call me sadeeq ohk?
Jinjina kai nayi nace "thank you sir, aww sorry am ehhhm..Yayaaa."
Dariya yayi yace "das you, yanzu kici abinci sai ki koma gida kar dare yayi, now bari inje masjid don azahar yayi, har ya mike sai kuma ya juyo ya kalleni yace "ko inzo muci tare"?
Da hanzari na kalleshi dan yanayin maganganunshi suna min yanayi da na hamma jabeer, dariya ya kuma yi wanda na fahimci shi ma'abocin dariya ne , yace "Iam just kidding pretty".
Tafiya yayi ya barni da sakakken baki, tsabar excitement kasa shan ko da ruwa nayi a wurin dukda yadda raina ya biya da abincin dake zube gabana... A haka ya dawo ya same ni ina ta kulla wa da kwancewa na yadda wannan al'amari zai kasance ba tare da iyayena sun gane ba.
Duk yadda yaso inci wani abu ki nayi daga karshe dai waitress din yasa tamin takeaway na abincin.ta mika min badon na so ba na amsa nace "na gode".k
Ya amshi wayata yasaka nomba dinshi yayi saving sannan yayi dialing zuwa wayarshi yayi saving tawa,yana kallona yace "idan kin iso gida we will talk,.Jakata na dauka da kuma fancy ledan da aka samin takeaway a ciki nace 'most grateful sir, ahh sorry yayaa".
Murmushi yayi yace "nice meetig you maryama hannu ya miko min wai muyi musabaha na noke kafada ina turo baki" a daidai lokacin kuma wayata tayi kara, da sauri na fitar daga jaka naga hamma jabeer ke kira gabana ne ya fadi ganin karfe uku saura minti biyar, inna lillahi na furta gami da sa wayar a silent, karfe uku ai lokacin tashi islamiyya yayi gaba daya na sha'afa gashi ko sallan azahar banyi ba, ganin mood dina ya sauya sadeeq yace "yaya dai ko daga gida ake kiranki?"
Nace "eh, sunga na dade ne bari inzo in wuce".
Jakata ya kama ya cusa min wani abu a ciki yace "take care sai na jiki a waya".
Tsunkuyar da kai nayi inajin bugun kirjina yana sauya wa,...har na kai bakin get na fita daga hotel din ban daina jin idanunshi a kaina ba, hakan yasa na juyo ilai kuwa yana tsaye ya kafe ni da ido, murmushi ya min bayan mun hada ido ya daga min yatsunshi guda biyu yana karkada su,murmushin na mayar masa na fita da sauri, saida na tabbatar na bar area din sannan na bude jakata dan ganin abunda ya jefa man a ciki, ,...Zaro ido nayi gami da dafe kirji na shiga uku ni maryama note na yan dubu dubu na gani a ciki, "dubu dari" na fada ina kara fiddo idanu na waje, da sauri na tare keke napep jikina yana karkarwa na shige nace ya kaini tasha,ya zanyi da kudi har dubu dari? nasan tawa ta kare idan innarmu ta kamani da kudin nan, ya zanyi dasu yanzu? siyama ce ta fado man a rai dan haka na danyi ajiyar zuciyar samun relief, wayata na kuma dubawa naga miss call na hamma jay kusan goma, "dan wahala" na furta a bayyane har mai napep din ya juyo yana kallona...A park din nayi sallar zuhr da asr kafun motar dana shiga ta cika muka dauki hanya ina ta addu'ar Allah yasa mu iso kafun a tashi islamiyya.
Munyi nisa a tafiya amma gani nake kamar dreban baya sauri yayinda agogon hannuna ya nuna min karfe hudu da rabi, saura mintuna talatin a tashi a islamiya... inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un, gaba daya mutanen cikin motar suka furta ciki kuwa harda ni,lokacinda tayar motar mu tayi wani irin kara dukkan mu mun rude Allah ya taimaka motar ta tsaya cak ba tare da ta fadi ba,cikin hanzari muka fito daga motar kowa yana gode wa Allah daya takaita mana bamu fadi ba.
Tayar ta pashe cewar direba, na duba gaba na duba baya gabas da yamma kudu da arewa ba alamar gari muna tsakiyar jejin Allah, na shiga tara yanzu kam dan yafi uku ga wani uban yunwan da nake ji kuma na kasa cin abincin daje hannuna kamar wacce aka hanata, kiran hamma jabeer ne ke ta rige rigen shigowa wayata shima n kasa dauka dan kar ya gane akan hanya nake, muna ta tsaye har karfe biyar ya cika mai motar mu bai dawo daga gari na gaba da ya jr neman mai gyaran taya ba, kamar hadin baki kuwa duk motar da ya zo wucewa a cike yake da pasinjoji.
Zuwa lokacin tashin hankalin da na ke ciki baya misaltuwa, idanuna sunyi jawur har wani zazzabi nake ji yana neman rufeni, sai bayan wasu minti talatin din direban ya dawo yana ta bamu hakuri akan dadewar da yayi, nan suka hau gyaran da ya kara kaimu wasu minti talatin din wanda yayi daidai da karfe shida da minti uku.
Duruwa mukayi a motar bayan ya tashi muka miki hanya, kiran umaimah ne ya shigo, jikina yana rawa nake kallon kiran amma na kasa dauka, wani kiran ya kuma shigowa wannan karon daga innarmu still na kasa dagawa sai hamma jabeer again sai kuma innarmu wani da layin baffanmu sai kuma layin umaimah, Inna lillahi, shikenan yau tawa ta kare ni maryama Alla ka dubeni, shine kawai abunda nake maimaitawa a raina har muka iso gombi wurin karfe bakwai na dare a lokacin an fito sallar isha shagon siyama na nufa bayan mun sauka ina jin kafafuna kamar zasu kada ni,still nayi a wajen na daura hannu aka ganin shagon a rufe, wayata na daga na shiga neman layinta unfortunately a rufe," kin kashe ni siyama" na fada hawaye na gangarowa bisa face dina yanzu ya zanyi in koma gida da gyale da jakar nan da kuma wannan uban kudin? bayan ansan da hijab na fito har da nikab da kuma jakar islamiyya.,ganin ina kara bata lokaci yasa jiki na rawa na tsaida wani napep din na shiga, a kofar gidanmu ya sauke ni na shigo hawaye yana bin fuskata yayinda karkarwar da jikina keyi ya tsananta, da kyar na sa kai tsakar gidanmu, ina tattare siket nawa gami da damke jakar dake hannuna kamar kace kyet in zura da gudu.
Da hamma jabeer muka fara hada ido, sai safa da marwa yake a tsakr gida hannayeshi goye a bayanshi,duk da dare ne hakan bai hanani ganin yadda fuskar shi ta sauya kamanni ba idnaunshi sunyi jawur, daga gefe kuma innarmu ce zaune tayi tagumi sai su salima da fatima jaune suma sunyi jugum jugum,kana baffanmu yana kishingide bisa tabarma sai umaimah da ta hada kai da guiwa tana sheshshsekar kuka.
Cikin wani irin takun da ya sa cikin juyawa hamma jabeer ya nufo ni gami da fadin "pretty" da karfin da ya janyo hankalin sauran mutanen gaba daya suka mike tsaye har baffanmu dake kishingide....