MARYAMA

Page 08

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

 

Na 

Ummu Fadeela

Episode 08.



"Maryamaaa!" Ya fada da karfin da ya janyo hankalin sauran mutanen zuwa kaina, tashi Baffanmu ya yi daga kishingiden da yake, Innarmu ma ta mike ta nufo inda nake yayin da Salima da Fatima suka zo suka rungume ni da gudu, tsananta rawa jikina yayi sakamakon kallon da Innarmu ta ke min kamar yau ta fara sani na, a hankali ta juya ba tare da tace min komai ba tana share hawayen da ya gangaro mata da bakin zani.

Salima tace "Antinmu ina kika je kika sa Innarmu tana ta kuka ita da anti uymaimah, gashi anje islamiyyarku bakya nan, Fatima tace "ehh anje islamiyyarku mu'allim yace bakije ba yau, shine Hamma Jabeer da Baffanmu suka yi ta yawo ba a ganki ba, kuma ana ta kiran wayarki yana shiga baki dauka, Salima ta kara amshe zancen da fadin "kuma Hamma Jabeer ya kara fita nemanki shi ne ya dawo da hijab naki da kuma nikab da jakar islamiyarki, sai kawai anti Umaimah ta fadawa Innarmu wani magana shine suka kama kuka dukkansu".

Wani irin zufa ne ya shiga karyo min cikin jikina, yayinda idanu na suka zazzaro waje kamar wacce ta hadiye kunama, damke yaran nayi sosai ina jin kamar zan bar duniyar ne, banyi aune ba naji tarwatsewan ledan dake hannuna, gaba daya abincin dake ciki yayi pieces a kasa yayinda bottle watern dake ciki yayi wani irin gangarawa ya tsaya dab da kafar Hamma Jay dake tsaye ya goya hannuwanshi a baya, duk tsiyarka bazaka karanci expression dake kan fuskar shi ba, goran yabi da kallo kana daga bisani ya dago kai yabi fried rice da kuma naman kazar da ya yi dai dai a kasa, sai kuma ya maida kallonshi kan fuskata zuwa jikina dake makyarkyata kamar an jika dan akuya kana jakar dana damke da iya karfina dan kar shima ya tarwatse.

Kamo Umaimah dake kuka Innarmu tayi cikin sanyin muryar da ban taba sanin ta da irin shi ba tace "Umaimah tashi kije gida hakanan kinga ai ta dawo ko? kuma lafiya kalau ta dawo ba abin da ya same ta, kinga harda abincin yan gayu sabbin iyayenta masu kudin suka sai mata, wanda mu bama bata ir.... Kasa karasawa tayi sakamakon rawar da muryarta ya fara, Umaimah dake rawar zazzabin da tashin hankalin batan Maryama ya tsananta mata shi tace "kiyi hakuri innarmu, kuskure ne kuma ba wanda baya kuskure, zata gyara Insha Allah, don Alla kiyi hakuri Innarmu".

Ta fada tana hada hannayenta wuri daya, juyawa tayi ta shige daki ta barsu a wurin, Baffanmu ma baice komai ba ya tashi ya shige dakinsa saidai da ka ganshi kasan yana cikin matsanancin damuwa.

Taku Umaimah tayi zuwa wurinta tace "why Maryama? why? meyasa kika aikata haka, kina ganin wannan shine rayuwar da zai fishsheki? meyasa meyasa? Ta fada da karfi tana hawaye, ba tare da na bata amsa ba itama ta juya ta fita daga gidan.

Hannu na daura aka zan zunduma ihu amma nayi saurin toshe baki na "Meyasa suka min shiru? Me yasa kowa yake shigewa daki ya barni,? Hamma Jabeer ne ya matso kusa damu har na fara jin dadin cewa zai min magana amma sabanin tunani na cewa yayi yana kallon Fatima "Fati samo tsintsiya ki kwashe wannan ki kai bola,"Ya nuna mata abincin da ya zube nan kasa kama hanyar dakinsa ya yi shima ya barni nan tsaye, da sassarfa nabi bayansa jikina na rawa nace "Ham..mm.ma j..ay plssss"

Wani irin juyowa yayi idanunshi sunyi jajur kamar garwashin wuta, na kuma gathering courage nace "Hamma Jay ba y....Wani irin dunkule hannu yayi da karfin gaske yace "bullshiiiiit".

Hannuwa biyu nasa na toshe kunnuwa ta kana na tsugunna da sauri ina jiran jin saukan duka dan na gama sadakarwa, amma sai naji ya kaiwa randar Innarmu na kasa wanda ke kusa damu bugu da kafarsa, take kuwa randar ta bule ruwan ciki ya fara zuba a kasa, cike da mazantaka ya juya ya shige dakinsa ya barni nan durkushe.

Da rarrafe na shiga dakinmu ina jin tamkar duniya ta juya min baya, tamkar kowa ya tsaneni, me yasa baza su duba burina ba, me yasa bazasu yi la'akari da abunda nake so ba, (niko nace anya kuwa maryama?.)

Ajiye jakar danake damke dashi tun dazun nayi ina bin hijab da nikab dina dake ajiye kan gado da kallo, waya dauko su daga shagon siyama? me ya faru? banida mai bani wannan amsar,zama nayi bakin gadon na zuba tagumi ina jin wani irin yunwa tana azalzalata gashi banyi sallan maghrib da isha'i ba.

Dago labulen dakin akayi innarmu ta shigo fuskar nan tata ba alamun annuri, wani irin juyi nayi sai ganina nayi tsaye karshen dakin ina zare idanu,calmly tace "dawo nan ki zauna" ta na nuna min inda na tashi,jiki na yana karkarwa nace "don girman Allah innarmu kiyi hakuri wllh b.."dawo nan ki zauna nace" ta fada wannan karon a dan fusace,

Ko motsi banyi daga inda nake ba sai mazari da jikina keyi yayinda zufa ya gama yimin wanka.

A fusace innarmu ta finciki jakar dana dawo dashi tana kokarin balle hannun jakar wanda ya kasance chains ne,hannu na daura akai na kurma ihun da yayi daidai da watsewar gaba daya kudin dake cikin jakar yayiwa innarmu wanka daga sama har kasa.

Bin kudin da ya watse daidai ya cika dakin tayi da kallo gabanta na faduwa sannan ta dago ta kalleni tace "maryama,karuwanci kika fara?"

Da sauri na durkusa kasa still holding my hand on my head nace "wllh innarmu bana karuwanci wallahi Allah kenan, shine ya samin cikin jakar".

Shi wa? inji ta.

Sai lokacin na tuna baran baramar da nayi na fara zare ido bance komai ba.

Fita a dakin innarmu tayi bayan kamar minti daya saigata ta dawo da wata zabgegiyar dorina mai baki biyu,tuni na saki fitsarin da na ke ta faman matsewa, without thinking twice tayo kaina gadan gadan ba abunda nake yi sai ihun neman agaji tun dorinar bai sauka jikina ba,sai dai duk ihun da nake ba wanda ya kawo min agajin.

Zabga min dorinar tayi a gadon bayana wani ihun na kuma yi da wannan karon nayi imanin cewa duk anguwar mu ba wanda baiji ba sakamakon wani azabar da ya ziyarci kwakwalwata,...duka na take yi duk inda ta samu bata ji bata gani a take na fita haiyacina ina kiran sunan baffanmu hamma jabeer suzo su taimakeni,.

Mikewa jay dake kwance rub da ciki yayi ya fito ya shiga dakin da gudu,wani irin sufa yayi ya kamo dorinar dake hannun innarmu ya rike gam kana yayi kneeling a wurin yana bata hakuri ganin yadda jikin maryama ya parpashe sai digan jini yake yi, a fusace tace "Ka sake bulalar nan ko sai na hadaku duka na zane lusari kawai".

Ba tare da ya sake ba yace "kiyi hakuri innarmu for the sake of Allah kiyi hakuri dan Allah kiyi hakuri" rokonta yake amma bakin shi rawa yake yi ga hawaye har ya cika idanunshi abunda innarmu bata taba gani ba".

Fisge bulalan tayi tace barni in kashe ta kafun ta kashe mu gaba daya ci gaba da labtar maryama da zuwa lokacin ko motsin kirki bata iya yi, kukan ma ta fara kasawa,ganin da gaske innarmu zata kashe ta ne yasa jabeer fadawa kan maryama dake kwance ranga ranga ya kankameta tsam a kirjinsa,yana fadin Ah ah ah innarmu bazata kara ba kiyi hakuri bazata kuma ba, idanunta ya rufe bata ganin gabanta sai zabgawa jabeer dake rungume da maryama dorinar take tana cewa "ka matsa ko in hada da kai".

Rike bulalar akayi ta baya innarmu ta juyo da sauri ganin wanda ya rike dorinar yasa ta durkushewa kan kafafunta tana tsiyayar da hawaye,calmly baffanmu yace "dijah duka would not be a solution to kangararrun yara saidai ma ya kara lalatasu,ki bar dukanta haka nan".daga haka ya fita ba tare da ya kara cewa komai ba,duk da azabar da na ke ciki hakan bai hana kalaman baffa dukan kirjina ba so yanzu na zama kangararriyar yarinya kenan, inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un.

Bin bayan baffa tayi zuwa dakinshi ta same shi zaune bakin gadonshi hannunshi daya dafe da goshinsa daya kuma yana rike da wayar dake kare kunnensa bayan dan lokaci kadan ya fara magana a wayar "barka da dare dada,ya mutan gidan da kowa,dama ina son sanar muku ne na yanke auren yaran nan zuwa sati biyu masu zuwa,sai a sanar ma sauran yan uwa. 

Daga haka ya yanke wayar ba tare da ya jira jin abunda dada zata fadi ba.wani irin sayi innarmu taji a bayyane ta furta "Alhamdulillah".

Karar da wayata tayi na shigowar kira ne ya sa hamma jabeer sassauta rikon da ya min kamar zai maida ni cikinsa duk da tsananin azabar da na ke ciki bai hana ni jin yadda zuciyar sa ke bugawa kamar zai balle ya fado kasa ba kana makwogoronsa sai hawa da sauka yake da sauri sauri...tashi yayi yana rike da hannuna ya ajiye ni bakin gado, sai a lokacin ya kula da kudaden dake watse tsakar dakin juyowa yayi zaiyi magana wayata ta kara daukan tsuwwa,daukar wayar dake yashe gefe yayi sakamakon faduwar dayayi lokacin da innarmu ta balla jakar.

"Sadeeq?" ya furta yana kallon screen na wayar, tabbas da ina da iko da na karbe wayata jin sunan daya ambata amma inda nake ko yatsata bazan iya motsawa ni kadai ba,Picking call din yayi ya kara a kunnenshi a hankali na lumshe idanu na ina jiran bomb din ta pashe,dan nasan yau kam ta kasance bakar rana a cikin rayuwata,...Daga daya bangaren sadeeq relaxing yayi kan makeken gadonshi dake dakin hotel din cikin low voice jin anyi picking call din yace,

 "Hii pretty, fatan kinje gida lafiya? nayi ta kiranki baki dauka ba duk kin tayar min da hankali hope all is fyn? naji dadin yinin yau tare dake matuka."

Jabeer baisan sanda wayar ta subuce daga hannunsa ta fadi kasa ba,bin wayar yayi ya durkushe bisa guiwarsa,kana ya dunkule hannunsa biyu ya naushi kasan carpet din,jan da idanunsa sukayi yana karuwa tamkar zaiyi tartsatsin wuta, jijiyon wuyansa suka fito rado rado, da karfi yace "Noo maryama,nooooooo don't do this to me,nooooooooo.Wani kiran ne ya kuma shigowa a harzuke ya daga wayar ya maka ta da bangon dakin take ta rabe biyu,yace "what the heck?"

Ficewa yayi daga dakin da sassarfa ba tare da ya juyo ba, gaba daya ahalin wannan gida yadda suka ga rana haka suka ga dare idan ka cire salima da fati, bacci kauracewa idanun jabeer sukayi yayinda yake jin ciwo a zuciyarsa don sautin bugunta ma ya sauya haka kuma yana yawan jin faduwar gaba cikin lokaci kadan zazzabi mai zafi ya rufe shi amma yayi ta karfin hali da jarumta, a bangaren maryama ma zazzabi mai zafin gaske ne ya lullube ta sai rawar sanyi takeyi daga inda take zaune, da kyar na iya kwanciya a gefe guda tsabar yadda jikina yayi tsami duk yadda naso lulluba kasawa nayi sai shivering nake yi.

*****

Washe gari da kyar jabeer ya fita sallar asubahi ana idarwa kuwa ya dawo ko azkar bai tsaya yi ba, duk kaunar shi ga daga karfe kuwa yau ko inda karfen yake bai gani ba ya shige daki ya kudundune a bargo...,kafun karfe bakwai jikin maryama ya rikice ba shiri aka kwasheta sai asibiti dan ba karamin tsanani jikinta yayi ba, tuni jabeer ya wartsake ganin abar kaunar sa tana halin mutuwa ko rayuwa.

Emergency aka karbe ta likitoci suka rufu a kanta don ceto rayuwar ta sakamakon daukewar da numfashinta yayi,saida suka kwashe akalla awanni uku a kanta kana daga bisani aka makala mata oxygen tube dan taimakawa numfashinta da kuma karin ruwa kana aka kaita female ward akayi admitting nata,.

*********.

Zare siririn farin gilashin dake makale saman fuskar sa likitan yayi yana kallon baffanmu da kuma hamma jabeer dake zaune gabanshi tsananin tashin hankali kwance saman fuskar su, dan goge zufar dake tsatstsafo mashi yayi sannan yace yana kallon baffa,

"Sakamakon binciken da muka gudanar,mun gano cewa patient namu tana fama ne da....."

Shiru yayi yana kallon su daya bayan daya, cikin kaguwa hamma jabeer da idanunsa suka yi jajawur kamar gautar da ya sha rana yace,

"Kamana bayani mana dacta ka tayar mana hankali fa"

Karkada kai likitan yayi sannan yace,"kuyi hakuri ba wata cuta da ta sauka duniyar nan face da maganinta, ita jinya jarabawace idan akayi hakuri aka ci jarabawar za'a samu result mai kyau, patient nawa dai tana fama ne da kidney diaseas, duka kodar ta biyu sun kamu da cutar dole tana bukatar dashen koda wadda ya zama wajibi a mata cikin lokaci kadan idan ba haka ba komai na iya kasancewa".

Wani irin zabura hamma jay yayi ya mike tsaye yana kallon likitan bakin shi na rawa yace,

"Dr. You mean...Maryama...Kana nufin..Maryama ta ce kidney dinta ya samu damuwa?...