MARYAMA

Page 09

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

                   By
         Ummu fadeela.



Episode 09.


Janyo shi baffa yayi zuwa kan kujerar da ya tashi, shima cikin rudanin yace,

"Jabeeru kwantar da hankalinka mana ya mana karin bayani".

Likitan yace," ku kwantar da hankalin ku baba, matukar aka mata dashe cikin gaggawa zata tashi lafiya kalau kamar ma bata taba ciwo ba, da ace daya ne ya samu damuwa zamu iya cire shi, a bar mata daya domin dan adam yana iya rayuwa da koda guda tamkar kowa amma duka biyu sun tabu so dole yanzu muna bukatar cire su duka cikin gaggawa a dasa mata wani, hakan kuma zai faru ne ta hanyar samun wani ko wata da zai sadaukar mata da kodar shi guda daya,karku manta kuma muna bukatar shine cikin gaggawa dan tana cikin hadari matuka."

Rike kai baffa yayi da hannu biyu sakamakon wani irin sarawa da kan nashi yayi,cikin nutsuwa irin ta dattijai masu mutunci yace,

"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma ajjirni fi musibati wa akhlifni khairan minha,ya rabbi ka dubi baiwar ka".

"Ni zan bata nawa kodar".

Da sauri baffa ya dago kai ya kalli inda maganar ta fito,jabeer ne zaune idanunshi sun kada jajir jijiyar kanshi sai harbawa take yi dil,dil,dil.

"Kwarai kuwa zan bata,zamu raba nawa kodar da ita baffanmu" Jabeer ya kuma fada yana kallon baffa da ya tsare shi da idanu.

Gyaran murya likitan yayi yace,

"Baba kuna bukatar yin shawara a tsanake irin na family, amma karku dauki lokaci mai tsawo"

Fitowa sukayi daga ofishin suka durfafi inda innarmu da daada ke zaune dukkansu sun rabka uban tagumi,daada ne ta fara ganinsu dan haka ta mike har tana tuntube tace, 

"Ya ake ciki? Me dactan yace game da jikin takwarata? duk kunmin shiru kuna kallona,cewar daada ganin baffanmu da jabeer sun sadda kai kasa.

"Wai ba magana nake bane kuka min shiru,wato ga sabuwar yar iska ko,...Shiru tayi tana kallonsu sai kuma ta daura hannu aka ta rusa ihu tana fadin mun shiga uku Alhassan kodai mutuwa takwara tayi.? inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un,cikin tashin hankali ta kuma fadin,"wai ba magana nake yi bane?.

Da kyar baffa yayi karfin halin cewa,"kiyi hakuri daada, bata mutu ba amma......Nan ya kwashe duk yadda sukayi da likitan ya fadi mata, a rikice innarmu da tunda suka fara maganar take binsu da ido kawai ta mike duk yadda taso yin magana ta kasa sai rawar da jikinta keyi da bakinta tana nuna hanyar ward din da maryama ke kwance da hannu.

"Saidai jabeer yace zai bada nashi daya a sanya mata" cewar baffa da ya ci gaba da magana.

Sassauta wa daga kukan da take risga kamar babu gobe daada tayi,baki galala take kallon baffa kafun tace,

"Ban fahimta ba,me jabeeru zai bayar alhassan?.

Baffa yace, "cewa yayi shi zai bada tasa kodar guda daya a dasa mata".

"Karku maida ni sakarai shashasha mana, ina sam ba wannan maganar, so kuke in rasa jikokin nawa duka biyu lokaci guda? ko baku da hankali ne ne kam banda labari, jabeeru shi kadai Allah ya mallakawa abokin tagwaicinka alhussain kafun Allah ya dauki abunsa kuma shidinma dana ke gani inji dadi a raina saiku salwantar min dashi? ina sam ba Allah a ranka,ni na taba ganin inda aka cire kayan cikin mutum kuma ace ya rayu? ah ah wllh tunda uwata ta haifeni ban taba gani ko ji ba sai yau" Daada ta fada tana fyace majina da bakin zaninta dake kokarin faduwa.

"Ko da ace bazan rayu ba matukar maryama zata tashi nizan sadaukar da tawa rayuwar domin ceto tata,zan iya bada rayuwa ta dominta daada".cewar jabeer da kallo daya zaka masa ka fahimci alamun fitar haiyaci a tattare dashi.

Baki galala daada ke kallonsa cike da madaukakin mamaki, yayinda innarmu da kafafunta suka rasa garkuwar su nan take tayi baya baya kana tayi zaman dirshan a wurin, saidai kafun daada ta samu zarafin cewa wani abu suka hango wata nurse ta fito daga dakin da aka kwantar da maryama a guje ta nufi ofishin dr. 

"Your attention dr." Cewar nurse din bayan ta shiga office din...A dari da tamanin su daada suka bi bayan likitan da kuma nurse din ganin sun shige dakin da maryama ke kwance.

Juyi take ta faman yi hadi da murkususu akan gadon rike da gefen cikinta tana fadin, 

"Wayyo innarmu zan mutu, baffanmu cikina, hamma jay!mutuwa zanyi wayyo cikina,"...duk inda imaninka yake idan kaga yadda maryama take yi sai ka zubar mata hawaye a lokacin.

Yan dube dube dactan yayi sannan ya dago ya dubi su baffa yace, "lallai ana bukatar yi mata aikin cikin gaggawa".

Ya juya da niyyar barin dakin, daada ta kamo hannun farar labcoat nashi gami da fadin, "ah ah naga ikon Allah, dannan ba kai ne zaka shuka mata kodar ba?ai baka ga ta tafiya ba,gadai dan uwanta yace shi zai bada tasa a yanke a shuka mata,in gaya maka da uban shi da uban ta ciki daya suka zauna mahaifa daya suka fito dashi duniya, to ai kaga dan ya taimaka ya bata nashi ba laifi yayi ba ahto, zuciyar uban garesa, gashi shi kadai Allah yaba uban har ya bar duniya bai samu wani ba, sai kuma ta fashe da kuka cikin kuka take fadin Allah sarki sukuma haka tasu kaddarar tazo na rayuwa da koda daya daya,tana kallon jabeer tace maza jabeeru jeka a ciro a zo a shuka mata kaga dai halin da take ciki,kai kuma ubangiji ne kadai yasan da me zai saka maka wllh dan kayi shahadar da ba ko wanne mahaluki ne zai yi ba, yanda dai zumunci yayi karanci a zamanin nan yan uwa duk sun zama yan banza kamar ana ganin hanjin juna"

Murmushi likitan yayi yace, mama ba shuka wa ake fada ba,dashe zaki ce".

"A haap kaji zancen kawai"cewar daada, yo me marabar dambe da fada yaro?"

Jabeer da yake jin wani irin farin ciki ya matso likitan yace, dr muje a duba abunda ya kamata dan kamar muna kara wasting time ne a nan". Hakane muje a maka gwaje gwajen da ya kamata."

**********

Hamma jay zan mutu wayyo hamma jay cikina, karka tafi karka tafii karka tafiii,shine kawai abinda maryama ke maimaitawa tana ta faman murkususu ta jike jagab da zufa.

Jabeer dake zaune a kan farar kujerar robar dake gaban gadon da ta ke kwance baisan sanda bacci ya kwashe shi ba sakamakon baccin da bai samu ba daren jiya, kamar a mafarki kamar a gaske yake jin sautin muryar maryama cike da galabaita tana kiran sunanshi da fadin zata mutu karya tafi.Da sauri ya bude idanunshi da suka rine saboda dan baccin da yayi da kuma tashin hankalin da ya ke ciki suka haddasa masa,Tashinsa yayi daidai da wani irin kara da maryama ta saki kana ta mike zaune daga kwancen da take tana fadin hamma jayyy.

Babu shiri ya kamota ganin yadda ta rude, ya sassauta murya yace, "pretty gani nan kusa dake mi ne ne?.

Murya can kasan makoshi tace, "hamma jay zan sha ruwa."

Da azama ya cika ta ya nufi inda bag na pure water yake cikin kayan da ya koma gida ya taho dasu hospital din,.

Binshi nayi da idanu mafarkin da nayi yana dawo min sabo,...shekara tara kenan cifff yanzu da hamma jay ya sadaukar da kodar shi guda a gare ni sakamakon rashin lafiyar da nayi fama dashi lokacin ina yar shekara tara a duniya inda likita ya tabbatar da kidney dina duka biyu sun harbu da cuta dole sai an cire min an min dashen wata,.

A lokacin ba abunda bai faru ba,amma daga karshe anyi aikin cikin nasara,ma'ana yanzu koda daya hamma jay keda shi ta sila ta,saidai sam moment din yaki gogewa daga kwakwalwata,its always fresh as new saidai idan ban kwanta ba sai nayi mafarkin abunda ya faru a baya.

Ruwar da yake kokarin bani a baki ne ya dawar dani daga duniyar tunanin da na fada, hannunshi daya yasa ya tallabi keya ta daya hannun kuma ya sa min ruwa a bakina dashi,banyi musu ba na amsa na sha kadan gami da janye kaina gefe.

"Ki kara kadan" ya fada da shakakkiyar muryarsa da ya sani dagowa muka hada ido,he look so worried and tensed amma hakan bai hana shi sakar min murmushi ba ya na kokarin gyara min kwanciyata sannan ya koma kan kujerar da ya tashi ya kuma lumshe madaidaitan idanunshi cike da tarin damuwar da ke kwance saman fuskar sa.

 Kure shi da kallo nayi gami da tilastawa kwakwalwata son nemo min hujja da dalilin da ya sa zuciyata bata son auren hamma jay,saidai duk iya nazari na na kasa fahimtar komai,jabeer saurayine son kowa kin wanda ya rasa, bawai iya kasancewar sa cikakken namiji ba,yana dauke da wani baiwar da ba kowanne namiji ke dashi ba,gashi dan gayu duk da talaucin da ya masa tarnaki hakan bazai hana ka fahimtar cewa jabeer ya iya gayu ba da son kamshi.

Shafa gefen cikina na yi bangaren da kidney dina yake, take sadeeq ya fado min a rai, wani irin murmushi ne ya kubce min,jay ya fishi kyau da kuma kuruciya,amma shi kuma yafi h.Jay dukiya that's what I want,turo baki nayi gaba cikin kunkuni nace 
"To me ya sa shi h.Jay din bazai nemi kudin ba ya tara su kamar na sadeeq mai kyautar dubu dari daga haduwar farko?".
(Hmmmm,maryama kowa yana rayuwa ne akan tubalin kaddararshi.)

Kallon shi na kuma yi still idanun shi a rufe yayi matashin da kan kujerar da ya ke a kai,cikin murya kasa kasa da banyi zaton zai ji ba nace,

         "Hamma jay!".

Ga mamakina dagowa yayi ya daura min jajayen idanunshi mai tattare da rudani cikin nawa idanun,...Daburcewa nayi na fara inda inda da kyar na iya cewa "hamma jay, abunda ya faru jiya b.....Hannu ya daga min cikin tsananin fushin da bai kasance dabi'ar shi ba yace,

"Plsss maryama not here, you're sick I don't want....Sai kuma yayi shiru ya kara maida kanshi yayi relaxing hadi da rufe idanunshi yana jin zuciyar shi na mishi zafi, baison tuna abunda ya faru jiya, he could'nt believe prettyn shi ce taje wurin wani kato har wani gari,its hurt.It really hurt him to the extent da ko tunawa yayi sai kirjinshi ya harba.

Binshi na yi da kallo,wannan ba hamma jay din da na sani bane ba,wannan is something else dake tattare da fushi da kuma damuwa mai tsanani saidai duk da fushin da ya ke dani hakan bai hanashi zama dani a asibiti ba yana bani kulawa,

"Is this what pure love means?"

Bude baki na kuma yi nace, "innarmu bata zo ba ko?.Har muryata ta fara rawa.

Ba tare da ya dago ba ya daura yatsarshi manuniya saman labbanshi gami da furta, 

            "Shshsht".

          **********************

Cike da dumbin mamaki sadeeq yabi wayar tashi da kallo bayan ya sauke daga kunnenshi,kamar muryar namiji yaji yana magana,sake kiranta yayi yana fara ringing ya katse ya kuma kira wannan karon a kashe yaji wayar sakamakon rotsa wayar da jabeer yayi a jikin bango.

Juya akalar kiran yayi zuwa ga siyama, bugu daya ta dauka tamkar dai wacce take jiran kiranshi dama da hanzari tace,

"Hello yallabai" ba tare da ta jira amsawar shi ba ta ci gaba da magana muryar ta cike da tashin hankali, "ina fatan dai maryama ta dawo? dan yau naga tashin hanakali a rayuwa ta badon Allah ya takaita ba da yau a hannun yan sanda zan kwana".

Yamutsa fuska sadeeq yayi yana shafa gefen fuskarshi yace, 

"I don't get you lady".

Tace, "dazu bayan sallan azahar kwatsam yayanta yazo shagona wai ana neman maryama ba'a ganta ba, kuma anje islamiyyarsu duk bata nan,ina kokarin cewa bata zo wurina ba kawai yaga jakan islamiyyarta a wurin shine fa ya tayar man da hankali wai sai na fito da ita kai baka ga haukan da yayi a wurin ba da kyar na gudu."

Mikewa daga kwancen da yake sadeeq yayi yana ci gaba da yamutsa fuska kamar mai magana da abun kyama cikin dan fada fada yace,

"Mi ki ke nufi ne? dama iyayenta basu san ta fito bane?."

Sai a lokacin siyama ta ankare da baram baramar da tayi amma sai ta waske tace,

"No, yallabai, kawai dai dan uwan nata ne baisan bata nan ba amma iyayenta sun sani."

Duk da bai amince da maganar ta ba amma sai ya basar cike da bada umarni yace,

"Ohk go check her now, ta bar wurina tun da dadewa and make sure kin hada ni da ita a waya da zaran kin iso".

Jiki na rawa siyama ta amsa da "to yallabai".Sannan ta yi tagumi tana kokarin auna maganganun sadeeq,koma dai menene bazata iya zuwa gidan su maryama yanzu ba dan abunda jabeer yayi a shagon ta dazu daidai yake da abunda mayunwacin zaki zai aikata idan ya hadu da dabbar dawa....Kiran layin maryama ta yi saidai switch off matar mtn take ta maimaita mata, daga karshe shawaran da zuciyar ta ke bata tabi, inda ta bada tazaran mintuna talatin sannan ta kira sadeeq.

Yana zaune tsakiyar gadon shi dake hotel room din ya tisa wayar shi gaba yana kallo amma a zahiri ba kallon wayar yake ba yayi nisa cikin tunanin da yake, murmushi yayi mai dan fadi har hakoranshi suka bayyana sakamakon tunawa da kukan da maryama ta sakar mishi dazu cike da yarinta, "Yarinya ce" ya fada yana kara fadada murmushinsa,sai kuma ya shafi gefen fuskar sa kana ya dan bugi kanshi da karfi a zahiri yace,

"Why are you care sadeeq?" still shi kadai ya kuma cewa, "Yes why am I even worried?".

"Musamman dan kai tazo",wani sashe dake zuciyar shi ya sanar dashi, kiran siyama ne ya katse masa zancen zucin da yake yi, bai jira yayi bugu biyu ba ya daga da hanzari ya kara a kunnenshi,murya kasa kasa kamar sabuwar munafuka tace,

"Yallabai naje gidan nasu yanzu kuma na samu ta dawo, wani irin ajiyar zuciya sadeeq ya sauke da yasa siyama matsar da wayar daga kunnenta ba shiri,

"Hang the phone to her" 

Shine abunda taji ya fada, da sauri ta mayar da wayar kunnenta tace,

"Yallabai akwai matsala bazai yiwu tayi magana yanzu ba dan yayan nata ya kasa ya tsare yanzu ma makewayi na shiga".

"Ohk ki sanar mata lallai lallai ta kira ni anjuma"

"Insha Allah sir, ta fada tana sauke numfashi bayan ya katse wayar shi...Tunanin yadda za'ai tayi reaching maryama take amma ta rasa mafita Dan ba wanda ta sani a anguwar tasu sai wannan kawar maryama mai idanu zubin na munafukai umaimah.

              *************

A ranar aka sallamo maryama daga asibiti dan jikinta da sauki dama zazzabi ne da dukar da innarmu ta mata ya haddasa mata,har aka sallameta innarmu bata zo ba hamma jay kuma bai kara mata magana ba duk da bai matsa daga kusa da ita ba har ruwan da aka daura mata ya kare. Adaidaita ya tare masu suka koma gida amma ko ci kanki innarmu bata ce mata ba, sai ma hararar hamma jay da take yi da fadin ka juri wulakanci ai".

Bayan da baffanmu ya dawo kasuwa ne yayi kiran jabeer ya sanar dashi ya fara shiri nan da sati biyu za'a daura auren shi da maryama,..

Tsunkuyar da kai jabeer yayi yana jin zafi cikin zuciyar shi yayinda wani daci ke biyo makwogoranshi zuwa kan harshen shi yace, baffanmu ina gan.....