Page 10
💫MARYAMA💫
by
ummu fadeela
typing📲
EPISODE 10.
Yayi kasa da kai yace, "Baffanmu ina ganin..."
Dakatar dashi Baffa yayi ta hanyar daga mishi hannu cikin fada yace,
"Mu muka haife ku, ba ku kuka haife mu ba, dan haka wannan umarni ne nake baka ba shawara ba, kaje ka fara duk wani shiri da zaka yi nanda sati biyu za'a daura muku aure dan bazan zuba idanu ku bata min zumunci ba, na riga da na sanar ma daada ita kuma zata sanar da mutan nijar gaba daya, tashi ka bani waje mutumin kawai."
Tunda Baffa ya fara magana Jabeer yake jin kanshi kamar yana yawo a sararin samaniya, ya rasa farin ciki zaiyi ko akasin hakan,maryama ta riga da ta zama wani bangare na rayuwar shi,ta zama jinin dake gudana cikin jijiyoyin jikinsa rasata daidai yake da faduwar bangon da ya ke jingine da, amma abin da ta aikata jiya yasa ya fara tunanin an...
"Tashi ka bani wuri" muryar Baffa ya katse masa tunanin da yake yi.mikewa yayi har ya nufi hanyar fita sai kuma ya dawo ya shiga dakin shi,girgiza kai kawai baffa yayi tare da fadin "Allah ya kyauta."
TUSHEN LABARI....
Alhassan da Alhussain tagwaye ne kuma kyawawan buzaye yan asalin jamhuriyar Nijar cikin gundumar kancha, garin da jama'ar cikin ta suka yi kaurin suna wurin fita ci rani zuwa kasashe daban-daban cikin afirika,musamman Nigeria, Algeria, Senegal da kuma Libya.
Alhassan da alhussain sun taso ne cikin maraichi domin mahaifinsu mal.Amadou ya rasu tun suna yan shekara daya a duniya, sai mahaifiyar su maryamou wacce suke kira daada, sunsha gwagwarmayar rayuwa sosai dan mal. Amadou bai bar musu komai ba face gona guda daya da shima gadon sa yayi wajen mahaifinsa,... ganin wahala ya masu yawa ne yasa daada bin ayarin mata masu fita ci rani inda suka yada zango a kasar libiya, ba karamar wahala suka sha ba cikin sahara kafun su iso saidai basu wani jima a can ba suna bara gwamnatin libiya tasa aka kwaso su zuwa gida nijar, wannan kalubale yasa daada bata kara bin ayarin masu fita ci rani ba ta rungumi yayanta hadi da kama kananan sana'o'i da noma gonan su na gado,ba laifi tana samun na rufawa kai asiri da haka yan biyunta suka taso har suma suka fara fita neman na kai.
A lokacin da suka kai shekaru goma sha biyar ne suka nemi izinin daada dan fita ci rani! bata musa mu su ba tace, "kuje Allah ya bada sa'a" da wannan suka shigo nigeria inda kaddara ta hankado su zuwa adamawa suka fara neman na kai.Alhassan ya fara saida ruwan jarka, shiko Alhussain wankin takalma yake wani lokaci yana hadawa da yankan farce, ance mai nema yana tare da samu. cikin dan lokaci Allah ya sawa sana'ar tasu albarka, suna samun na rufawa kai asiri suna kuma turawa daada mahaifiyar su wani abu,idan damuna ta kankama ko sukan koma nijar ne suyi noma.
Da haka har suka zama samari sosai masu zafin nema ilai kuwa suna samu.daga baya suka fara sana'ar saida danyen kayan miya kasancewar inda suke kayan miya yana wucewa sosai,.
A wani zuwa da sukayi noma a nijar ne Allah ya hada jinin Alhussain da wata cousin dinshi ramatou suka fara soyayya mai cike da tsafta,nan daada ta rasa inda zata jefa kanta tsabar dadi da farin ciki, zaunar da su tayi ta nuna wa Alhassan ma ya zama wajibi ya fitar da mata a hada su duka rana daya tunda dan uwanshi ya samu, Baiyi gardama ba amma ya barwa daada zabi, a cewar shi ta zaba mashi duk wacce ta mata.
Sosai daada taji dadin wannan karramawa da dan nata yai mata,ta zabo mashi wata zukekiyar budurwa itama dai buzuwance dijah diyar wanta duk dai na gida dinne, da ya ke gaba daya talakawa ne kuma dangi daya ba,asamu sabanin fahimta ba,cikin lokaci kadan aka sha shagali angwaye suka tare da amaren su cikin dakuna falle daddaya da aka shafawa farar kasa a cikin gidansu, da alkawarin idan damuna ya kare zasu dawo nigeria da matayen su.
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah.bayan watanni uku da biki matar Alhussain ta fara laulayin ciki,a kayi rashin sa'a kuwa cikin yana bata wahala sosai dan ba abunda take iya yi sai kwanciya wannan dalilinne yasa da suka tashi dawowa nigeria daada tace a barta sai cikin yayi kwari saboda wahalan hanya.
Hakan ko akayi alhassan da matar shi dijah da kuma alhussain suka tattara suka dawo, nan gidan da suke hayan dai basu chanza wani ba,...a can nijar kuwa ramatou tayi fama da jinya har dai cikin yayi wata bakwai sannan ta dan fara gane kanta, yayin da dijah matar Alhassan kuma har zuwa lokacin ko ɓatan wata bata taba yi ba, kusan kullum sai daada tayi korafi har ma ƙorafin nata ya zame wa dijah jiki...
Lokacin da cikin ramatou ya kai wattani tara, wani dare ta fara nakuda mai matuƙar wahala wanda ya dauke ta awanni masu yawa har wayewar gari ana abu guda gaba daya ta fita a hayyacinta harta kai ta kawo ba ta gane wanda ke kanta, duk wata ungozoma dake wannan ƙauye tazo ta gwada dabararta amma haihuwa ya gagara ga kuma naƙuda na zuwar mata da wuta wuta, daga ƙarshe dai aka yanke shawarar kaita asibiti a garin da ke kusa da su kasancewar basu da asibiti a wancan lokacin.
Da taimakon Allah da dabarun likitoci ramatou ta haifo santalelen danta kyakyawan gaske jinin buzayen asali,kallo daya zaka mashi kaji ya shiga ranka.sai dai ko juyawa bata yi ta kalli wannan yaro ba Allah ya amshi ranta sakamakon jijjiga da ɓallewar jini da ta samu, drs din sunyi iya kokarin su amma sun kasa ceto ta dan kwana ya kare...ba karamin tashin hankli alhussain da dan uwanshi suka shiga ba yayinda labarin ya riske su hakanan suka dau hanyar nijar cike da tarin alhini mai tsayawa a zuciya,wani ikon ubangiji kuma shine suna akan hanya suka yi hatsari inda mutane da dama suka jikkata wasu kuwa suka rasa ransu, cikin wadanda suka rasu harda alhussain...Allahu Akbar.daada taga zallan tashin hankali lokacin da aka shimfide mata gawar Alhussain a gaban ta,tayi kuka har hawayen ta suka kafe.daga karshe ta fauwalawa mai duka, wanda yake bamu ba tare da yayi shawara damu ba, kana ya kan dauki abunsa duk lokacin da ya so ba tare da yayi shawara da mu ba.
Alhassan shima ya shiga dimuwa da tashin hankali mai yawa na rabuwa da wani sashi wanda suka rayu a mahaifa guda daya,amma haka ya daure ya nuna mazantaka ya rungumi dan da aka haifawa alhussain yayi masa huduba da suna JABEER.
Da ya ke duk dangi daya ne sai daada ta ce a bar mata jabeer ta rike shi hakan zai ke tuna mata da danta da kuma matar shi, da wannan rikon jabeer ya dawo hannun daada inda Allah ya rayashi da kunu da madarar shanu,...lokacin da ya kai shekaru uku a duniya ne alhassan ya roki daada ta biyoshi nigeria dama sun dade dayin plan da dan uwanshi kafun Allah ya dauki ranshi har sun sayi fili da niyyar gina mata,.Dukda kasa ya rufe idanun alhussain alhassan baiyi kasa a guiwa ba wurin cika masu wannan buri,inda ya ginawa daada dakuna biyu da sauran abun bukata a wannan fili da suka siya tare.
Daada batayi gardama ba ta biyoshi zuwa nigeria,a bangaren dijah matar alhassan kam shiru har lokacin ko batan wata bata taba yi ba,amma suna zaune lafiya da mijinta a cewar shi komai lokaci ne, daga wurin daada ne take samun yan matsaloli nan da can da baza'a rasa ba.
Lokacin da jabeer ya kai shiga matakin primary baffanmu baiyi kasa a guiwa ba ya sashi a wata makaranta ta gwamnati dama tuni ya dade da shiga karatu da islamiyya a lokacin ne kuma daada ta tayar wa baffanmu hankali zata koma nijar a cewar ta ta gaji da zama ba wurin zuwa ita ko ta bar danginta a cike a can anzo nan an yarda ita kamar marar galihu,wannan shine silar dawowar jabeer hannun alhassan ya ci gaba da karatu, kuma baffanmu da innarmu suka mishi riko na amana,riko irinna iyayen kwarai, duk da babun dake tattare da rayuwar su, jabeer bai taba kukan rashin mahaifa ba, daada kuma ta koma nijar saidai lokaci lokaci suje ko ita tazo,wannan kenan....
**********
A kwana a tashi asarar mai rai,jabeer yana da shekaru goma sha daya cibb a duniya ciki ya bayyana a jikin dijah,.
"Godiya ta tabbata ga Allah buwayi gagara misali mai kyautar da bata yankewa" .
Wannan shine kalmar da daada ta ambata cike da farin ciki lokacin da labarin cikin dijah ya risketa,.Duk yadda taso su koma nijar suyi rainon cikin a can ki alhassan yyi saboda gargadan hanya,ba don daada ta so ba ta hau hada itatuwa da ganyayyaki na wanka da na turarawa ta aikowa dijah tun daga nijar har nan a cewar ta maganin ido ne da bakin makiya tunda ta dade bata samu rabo ba.Farin cikin da alhassan da dijah suke ciki baya misaltuwa,hakama jabeer tunda ya fahimci innarshi nada ciki yake murna.
Cikin ya zowa dijah da laulayi dan haka kusan komai na aikin gidan jabeer ke yi...Saida dijah ta kwashe wata biyar sannan laulayin ya lafar mata.Haka suka ci gaba da renon cikinsu cike da kulawa da soyayya,..bayan cikin ya shiga wata tara, wataranar litinin da safiya,dijah ta tashi da nakuda Allah yasa jabeer na gidan bai riga da ya bi baffa kasuwa ba,ba bata lokaci ya gudu kasuwa ya yi kiran baffa nan suka dungumo gida hankali tashe, dan ba abunda alhassan yake tunawa sai mutuwar mahaifiyar jabeer da na dan uwansa alhussain,...A gaggauce suka tafi asibiti da ita cikin kasa da awa daya dijah ta santalo kyakkyawar diyar ta fara kal.
Kimtsa su ungozomar tayi kana ta tura su dakin hutu,. Tunda jabeer ya kyallara idanu yaga jaririyar nan yaki ba wa baffa ita, baffa yana dariya yace "jabeeru kodai yar gida za'ayi ne? tuwona maina ince wa daada ta fara shirin karban kishiya?.
Dariya dijah dake kwance tayi, a nashi bangaren shi kuwa hade rai yayi sannan yace, "Baffa nifa ba wani son daadan nan nake bafa dama, me zan yi da tsohuwa? kaga innarmu ta samo min amarya mai kyau ni ita nake SO, ya fada yana kure jaririyar dake hannunshi cikin tsumma da idanu...Wnn shine mafarin lamarin.
Murmushin manya baffa yayi yana kallon jabeer yace, "ni kuma nayi alkawarin aura maka wannan jaririya matukar ranmu yakai lokacin girman ku....😭(alkawari kaya ne baffa).
Ranar suna jaririya taci sunan daada wato MARYAMA, dijah ta sa mata alkunya Arwat amma daada ta fitittike idanu tace ba mai canza mata suna, Maryama nta za'a kira ta.
Jabeer dake rike da jaririyar suna zaune gefen Innarmu, ya shafa saman girar babyn dake ta baccin ta,a hankali ya furta,
MARYAMAAA...