MARYAMA

Page 11/12

by @ummufadeela01

💫 MARYAMA 💫 


         by

Ummu Fadeela.



Episode 11 / 12.



Shekara kwana, tun daga wannan lokaci Jabeer ya sanyawa ransa soyayyar Maryama da niyyar auren ta idan lokaci yayi. Duk wani abu da ya danganci Maryama a gidan shike yi, wankin kayan ta kuwa ya mayar dashi wajibin sa, tun tana da wattani Jabeer ya iya mata wanka, tun Innarmu na fada dan tsoron kar ya sheka mata ruwa a hanci har ta hakura, wata rana idan ya dauki Maryama shan nono ne kawai ke sa shi mikata ga Inna, kana duk wani abun da ya samu ko mai yawansa komai kankantarsa a kan Maryama yake karewa, idan a ka bashi kudin break na makaranta kuwa, gaba daya Maryama yake kwasowa su tarkacen sweets da chocolates, tun bata iya sha har ta koya.

                 **************
A hankali wani irin shakuwa ya shiga tsakaninsu, har ya kasance da Maryama ta ga Jabeer zata fara daga hannu alamar ya dauketa yana daukar ta ko zata ringa babbaka ma sa dariya, idan ta fara kuka kuwa ba wanda yake iya rarrashin ta sai j
Jabeer. Lokacin da ta fara koyan magana sunan shi ne abu na farko da ta fara fada Jay Jay Jay wannan sunan ya bishi har girma a wurin Maryama dan sosai sunan ke mashi dadi idan ta ambace shi da hakan.

Ranar da aka yaye ta kuwa kwana sukayi suna kuka tare da jabeer wai sai Innarmu ta tsammata nono kadan in yaso gobe a yi yayen, murmushi kawai Inna tayi ta juya abinta, haka Jabeer ya dauki Maryama zuwa dakinshi ya dinga lallashin ta. Aranar dai a kan wajansa ta kwana yanda suka ga rana haka suka ga dare.. As life goes on, abubuwa da ya wa sukan zo su shude wani ya kan wuce a manta dashi, yayin da wani ke wucewa da barin tambari a zuciya na har abada...hakan ce ta kasance a gidan su Maryama, yayin da take girma sirrin kyawun da Allah ya bata yana kara bayyana, tamkar ita ta hallici kanta.
(Fatabarakallahu Ahsanul Khaliqeen)

Time da ta kai shiga makaranta aka sanyata a nursery, kullum Jabeer ke dorata a kafadunshi ya kaita ya kuma dawor da ita,kowa kaunar maryama yake tun tana karamar ta,,irin yaran nanne da idan ka kalle su dole saika daga su.Kyawun fuskarta mai fusgar hankali da kuma yalwataccen gashin kanta da ya bayyana har saman goshinta shike kara fadada kaunar ta ga mutane,,jabeer ma yana ci gaba da karatunshi sannu a hankali,kana ya na bin baffanmu kasuwa inda suke sana'ar kayan miya, saidai kaso casa'in cikin dari na kudin da ya ke samu a kan maryama yake kashe su, kama daga kayan kwalam zuwa kan kayan kwalliya da kuma sutura,inna tayi fada akan ya dinga tara wa shima yayi abu mai amfani amma a banza, dan yana samun kudi zai siyowa maryama wani abun...

Rayuwa tana tafiya, soyyayar maryama a zuciyar jabeer tana kara yaduwa da kyawawan yabanya,kana alkawain baffa yana ta kara kusanto su, duk wani numfashi da jabeer zai shaka, yana shaka ne da zunzurutun kaunar ta da kuma taraddadin mai gobe zata haifar sakamakon farin jinin da ta ke dashi, ba ga yara ba baga samari ba kana har tsofaffi son ta suke,saidai duk wanda yazo baffanmu kance maryama dai an mata miji.Da wannan jabeer ke samun nutsuwa kadan amma duk da haka cike yake da fargaba,innarmu ta kara haihuwar yaya biyu bayan maryama, fatima da kuma salima...Maryama tayi fama da kidney diasease lokacin tana yar shekara tara domin har an cire rai ga rayuwar ta amma jabeer ya sadaukar da nashi kidney din guda a gare ta inda yake rayuwa da koda daya duk a dalilin ta...Daga time din da ta fara zama yan mata komai na cikar hallita ya bayyana a jikinta duk da kasancewar ta mai kananan shekaru, amma tana da kira irin na manyan mata da wani irin kwarjini da aji da Allah ya bata hakan yasa mutane da yawa suke kiranta maryama matar manya.

Ire iren wadannan maganganu sunyi tasiri matuka wajen jirkita tunani da zuciyar ta, tana son hamma jay irin so wanda kanwa take yiwa yayanta amma bata mishi so irin na aure a ganinta bai mallaki abubuwan da zai inganta rayuwar ta dashi ba sai dai bata taba nunawa ko a fuska ba, a gefe guda kuma ga zugar da mutane ke mata na cewa bata dace da talaka ba, ita din matar hutu ce.kana muradin ta na karatu mai zurfi shima yana kara taka rawa wurin gurbacewar tunaninta.

Jabeer yayi karatu har zuwa matakin jami'a ya karanci law, amma yanayin rayuwa ya hanashi tafiya ci gaba da karatu a school of law, wannan dinma da kyar da sudin goshi aka gama shi, duk kuwa da cewa ya fito da sakamako mai inganci amma samun aiki ya gagara kasancewar kasar tamu ta zama wa ka sani, wa ya sanka ne yanzu...Dama jabeer bai mai mataccen zuciya bane, yasan zafin nema, dan baffa yayi iya kokarin shi na ganin dan nashi bai zama cima zaune ba masu dogaro da kwalin boko, dan tun yana zuwa makaranta yake aiki tukuru wajen ganin ya share wa iyayen shi da kuma masiyiyar shi hawaye ta hanyar neman na halak karkashin oga zubairu mai gadaje, zuwa yanzu babu irin nau'in gado da kujeru da jabeer bai iya bugawa ba.saidai karancin jari yasa shi ci gaba da zama a karkashin ogansu.

Maryama tana da kawa daya ko muce aminiya wacce ita kadai ce ke fada mata gaskiya a duniya kuma ita kadai ce tasan sirrinta, umaimah kenan kullum cikin fada suke kuma basa batawa basa jimrar fushin junansu, suna yiwa juna soyayya na fisabilillah duk da bambancin halayya dake tsakanin su, umaima yarinya ce mai fara'ar gaske wacce ke shan musgunawar kishiyar uwa, dan mahaifiyarta ta rasu da jimawa inda rikon ta ya koma hannun ummar su matar babanta, ita ko tayi amfani da wannan damar tana gana mata azaba son ranta.Umaimah tana yawan nusar da ita akan rayuwa, sau tari tasan gaskiya umaimah ke fadi mata amma sai tayi biriss da maganar,tamkar ba da ita ake magana ba.....Rashin jin shawarar umaimah da kuma rudin shaidan ya kaita ga ziyarar shagon siyama tsohuwar kawar ta da iyayenta suka raba su da jimawa dan sanin bata samu tarbiya mai kyau ba, har kaddara ya kaita inda sadeeq yake shi kuma ya.....Wannan kenan.

           *******************

           CI GABAN LABARI.

************************-***************.

Har jabeer ya kama hanyar fita waje sai kuma ya dawo baya ya shige dakinshi,kada kai baffanmu yayi ya ce, "Allah ya kyauta".

Rigar jikinsa ya zame take farar fatar sa mai cike da gargasa da kuma murdewa irin na mai gymin wacce ko kadan bata yi kama da fuskar saba ta bayyana, kwanciya yayi ruf da ciki bisa katifar sa dake kwance bisa leda carpet da ta malale dakin, a hankali ya lumshe idanunsa yana sauke wani irin nimfashi mai nauyin gaske da zafi kana yana jin kanshi yana mashi wani irin kara gim gimm gimmm kamar ana buga karfe da karfe, ba abunda ke mishi yawo a kwakwalwa sai sautin muryar sadeeq inda yake fadin, "pretty naji dadin wunin yau tare da ke,."

Rumtse idanu da karfi ya kuma yi yana kokarin hana kanshi tunanin amma ya kasa, "why pretty? why?." shine abinda ya furta yana danne kanshi cikin katifar.

         ******************

Tunda ya sanar da siyama lallai ta fadi wa maryama ta kirashi yake zaune yana jiran tsammanin kiranta, wasa wasa har karfe goma shiru, goma da minti arba'in shiru,goya hannayen shi yayi a baya yana zagaye hotel room din kamar mai gadi,ya kasa tsaye balle zaune, dialing layin siyama ya kuma yi amma switch off, damn it! ya fada a harzuke kana yayi cilli da wayar kan gadon shi, saukar wayar yayi dai-dai da shivowar wani kira, a tamanin ya bi wayan saidai sabanin tunaninshi bai maryama bace kamar yadda yaya zato. Kara wayar yayi a kunne yayi magana na tsawon minti biyar kafun ya yanke kiran yana sauke numfashi, a na bukatar shi da gaggawa wurin aiki, and bayajin zai iya komawa ba tare da ya kara kallon fuskar maryama ba.

Mikewa yayi ya dauki wata yar karamar jaka ya dura abubuwan da yake da bukata kana ya zuge zip din ya ajiye gefen gado da alkawarin gobe zai je garinsu maryama ya ganta kafun time na tashin jirginsu yayi....

Kuyi manage da wannan ba yawa da babu dai gwara ba dadi.....Gobe idan Allah ya kaimu baza'a samu update ba dan ina da wasu uzurin da zan gabatar,...