Page 13 / 14💫MARYAMA💫 By. Ummu Fadeela Episode 13/14.
💫MARYAMA💫
By.
Ummu Fadeela
Episode 13/14.
Yan abubuwan bukata kadan ya hada cikin jakar ya ajiye gefe da niyyar washe gari zai je garin su Maryama before time na tashin jirginsu....Cikin nutsuwa da ya kasance dabi'arsa ya koma bakin gadonsa ya zauna ya dafe hannayensa duka biyu bisa gadon.
"Sadeeq me zai kai ka garin su yarinyar nan?".
Zuciyarsa ta tambayeshi. Shafa beard nashi zuwa kan gemunsa na yan gayu yayi, wani bangaren na zuciyar shi ta bashi amsa da. "Dan in san ya ta koma gida, tun da dan ni tazo garin nan".
"Dan kai ta zo, amma bukatar ta ne ya kawo ta, this is madness Sadeeq, actually madness. Is better ka farka daga nannauyan baccin nan da ya dauke ka lokaci daya".
Sashin zuciyarsa ta kara gargadinsa, kamar wadda aka mintsina ya mike tsaye ya goya hannayensa a baya ya ci gaba da zagayen dakin.
Shi kansa ya san abin da kwakwalwarsa ke ankarar da zuciyarsa gaskiya ne, amma why ita zuciyar ta ke ingiza shi ga son zuwa taga fuskar Maryama wacce a kallo daya ta yi haddar fuskar ta? ko me ya tuna?. Da sauri ya girgiza kai shi kadai yana murmushi a zahiri yace "She's too young".
Tayi karama da yawa, ina zan kaita?...Haka Sadeeq yai ta sambatu shi kadai ya saka ya warware har around 11pm Sannan ya kwanta ba tare da ya tsaida takamaiman abinda zai aiwatar ba...
Washe gari kiran waya ne ya farkar da Sadeeq daga bacci, inda mai kiran yake kara jaddada masa muhimmancin zuwan sa a kan lokaci dan wani Important meeting suke dashi, kana kasancewar sa a wajen yana da matukar amfani, don ya je ya ba da bayanan da ya zo ya tattara a nan Adamawa....Ba dan ya so ba haka ya tattara ya tafi sai dai jirgin su na tashi ya ji kamar ya yi tsuntsuwa ya sauko, yana jin kamar ya bar wani sashi mai girma na jikin shi a kasa shin wannan ce love at first sight? Sadeeq ya tambayi kansa.
**************************
Maryama....Tunda muka dawo asibiti babu wanda ya leko ni haka kuma babu wanda yace min sannu da jiki, Innarmu sai harkokinta take Yi, Baffanmu ko yana kasuwa, Hamma Jay da nake sa ran samun sassauci a gareshi, shima ko keyar sa ban gani ba... Haka na kasance a daki ni kadai tamkar mayya, ina zaune ina ta sakawa da kwancewa aka daga labulen dakin, Innarmu ta shigo fuskar ta daure babu alamun fara'a a tattare da ita. Kwanon abincin dake hannunta ta ajiye gefe ba tare da ta kalle ni ba ta ce, "Idan kinga dama ki ci, idan kin ga dama kuwa ki zubar duk yadda kika yi daidai ne, ta sa kai zata fice a dakin.
Bansan ya aka yi ba sai tsintan kaina nayi bakin kofa rike da bakin zanin Innarmu. Ina durkushe hawaye na shatata a idanu na na ce,
"Don girman Allah kiyi hakuri Innarmu, wllh Allah daya kenan bazan sake ba, dan Allah kiyi hakuri ki bawa Baffanmu hakuri bazan sake ba Innarmu ku daina fushi dani Don Allah".
Na fada ina kara fashewa da wani irin kuka mai ratsa zuciya.
Duk yadda Inna taso kwace zaninta daga rikon da maryama ta mata kasawa tayi sakamakon zuciya irin ta uwa. A hankali ta kamo kafadu na ta mikar da ni tsaye, rungume ta na yi na kuma fashewa da kuka, cikin kukan na ce, "Sorry Innarmu! I fail you, amma bazan sake ba sharrin shaidan ne Allah bazan sake ba na yi miki alkawari" baya na Innarmu ta ke shafawa cikin lallashi sannan ta tafi dani har bakin gado na ta ajiye ni gefe itama ta zauna ta zuba tagumi tana kallona sai ta sauke ajiyar zuciya da numfashi sama sama, hannayena duka biyu ta kamo ta rike su gam ta na fuskan tata ta ce.
"Maryama ita duniya a sannu ake binta, lallabata ake sai a samu rayuwa mai inganci, Maryama duniya idanunta a tsakar ka take, sau tari zata yunkoro ta dauki mutum sai ta daga shi sama sai ta ga ashe bashi ta ke son dauka ba, maimakon ta saukar da kai a hankali, a'a hajijiya zata yi da kai sannan ta wantsalo ka zuwa kasa kana ta dauki waninka idan bakayi sa'a ba sai ka karya wuyarka garin saukowa." dan jimmm Innarmu tayi sannan ta ci gaba da cewa, "Maryama kowa yana tafiya ne bisa tsarin kaddarar da Allah ya rubuta masa tun yana cikin mahaifiyar sa, kina da ilimi Alhmdllhi kin karanta hadisi na hudu cikin arba'unanawwawi, ka da ki bari kyale kyalen duniya su rude ki, ki zo kina nadama a lokacin da wuri ya kure maki, Maryama a matsayina na wacce ta haifeki ina tabbatar maki har abada bazaki taba samun miji mai kaunar ki da zuciya daya kamar Jabeer ba,.....Jabeer ya so ki tun baisan menene so ba, dan haka ki nutsu ki mayar da hankalin ki jikin ki, arziki bai taba zama dauwamammiyar jin dadi da farin ciki ba, kamar yadda talauci bai zama bakin ciki na har abada, ba amma ki sani cewa manzon Allah S A W ya hore mu da neman tsari da talauci mai tozartarwa, wasu ma arzikin su shi ne musabbabin shigar su fitinar duniya da ta kiyama, Allah ya ki ya shemu, wasu ko talaucin su shi ke masu tsani har zuwa gidan aljannah idan sun yi hakuri, sau tari abin da kake hange daga nesa ya na walkiya kamar gwal Maryama sai ka iso shi ne zaka fahimci ashe rana ne ya haske shi, amma zahirin bakin karfe ne."
Dan fasali Innarmu ta ja sannan ta kara duban fuskata da ya yi jage jage da hawaye da majina ta ce, "yanzu ki tashi ki je ki baiwa Hamman ki hakuri akwai aikin da na ke yi zan dawo ki ban dalilinki na abin da kika aikata"
Sake hannuna ta yi ta fice ba tare da ta bani damar cewa ko uffan ba.
Mikewa nayi don cika umarnin Inna, hijabi na saka jiki na ba kwari kana yayi tsami sakamakon dukan mutuwar da na ci wurin Innarmu, dakin shi na shiga ina ta sakawa da warwarewa.
Yana kwance sambal ba riga a jikinsa ya cusa kanshi cikin katifa ba ka ganin alamun numfashi tattare dashi, wani irin sauti kirjina ya bada dammmm, da sassarfa na iso gareshi ba tare da shirya wa hakan ba, durkushewa nayi bakin katifar nace "Hamma Jay, Hamma Jay, amma shiru ko motsi bai yi ba, hannu na sa na kama nashi hannun ina jijjigashi da ci gaba da kiran sunansa amma bai motsa ba,....Tun shigowar ta dakin yana ji kuma yasan ita ce, dan ita kadai ke shigo masa daki gaba gadi haka ba tare da sallama ba, mikewa nayi cikin tashin hankali dan zuwa kiran Innarmu ta zo ta ganshi ban yi aune ba naji ya janyo hannu na saura kadan in fada kansa ya yi azamar matsawa baya sosai na fada bisa katifar, cikin sakwan daya na mike da iya karfi na na juya baya ina turo baki, cikin gunguni na ce "Dama idanka biyu shine ka bani tsoro ko?"
Bansan ya taso ba sai maganar shi na ji a gefe na, "Uhmmm da ma za ki ji tsoron mutuwa ta ne pretty? Na dauka farin ciki za ki yi da hakan"
Ya fada ya na bayyana a gabana. Da sauri na sa hannuwa na duka biyu na rufe fuskta da su.
"Tambayarki na ke yi" na ma ke kafada na kara juya masa baya nace, "ni dai ka sa rigar ka tukunna"
"Why"? ya tambaye ni, kara turo baki nayi nace "ni dai Allah tsoro kake bani a haka,".
Shafa kai yayi yana dan karamin murmushi wanda rabonsa da yi kusan kwana biyu da yini kenan.
Bayan kamar second biyar yace "to bude idon haka tunda ni na zama abun tsoro" make kafada na kuma yi nace "ni dai kasa riga" na sa rigar ai Pretty bude idon ki gani mana"
Still ban bude ba nace "kace wallahi ka saka" sosai ta bashi dariya amma sai ya fuske yace, "eh nace".
Ta tsakanin yatsun hanuna na dan leko shi kadan dan tabbatar da ya sa rigar, dan tsakani da Allah jikin Hamma Jay yanda ya mummurde din nan yana bani tsoro.
Sosai dariya ke cinsa amma ya maze ganin da gaske ya saka rigar ne ya sani matsowa kusa dashi na durkusa a hankali nace "Hamma Jay kayi hakuri da abinda ya faru bazan sake ba insha Allah". wani abu ya ji ya soki zuciyarsa saida ya rumtse idanu da karfi, abubuwa da yawa suna dawo mishi cikin kwakwalwa.
"Ka ce wani abu mana plssss" na fada ganin ya yi shiru idanun sa a rufe.
Bude idanun yayi wanda dama tun shigowa ta suke rine cikin kwantar da murya yace, "Pretty kaunar ki ce JARABTATA kuma watakila shi zai zamo AJALI NA. amma idan hakan ta kasance ina farin ciki da cewa kin san ni ma'abocin son ki ne da nake fatan rayuwa da ke har gaba da abada wato a gidan aljannah. Shiru yayi yana sauke ajiyar zuciya da fitar da wani huci mai zafi da alama duk abinda zai furta yanzu yana mashi zafi cikin kirjinsa, yana kallo na yace "Maryama son da nake miki bazai barni in cutar dake ba, zan iya sadaukar da soyayyata matukar ke din zakiyi farin ciki, na zabi jinyar zuciyata duk da ina da yakinin bazai warke ba sai dai ya kaini kabari akan ke kiyi jinyar taki zuciyar. Abin da kike so shi ne farin cikina Maryama ina sonki har zuwa karshen numfashi na abinda ya faru shekaran jiya ya haska min wata hanya mai cike da duhu da kuma karangiya, nayi kokarin fahimtar da baffanmu amma yaki bani listening ears, shin Maryama zaki iya zama dani a matsayin miji ko akwai wanda zuciyar ki ke muradi? kar ki ji shakka na ki fada min zallar gaskiyar dake ranki koda ko in naji zanyi collapsing a nan ne ki fadan Preety,
Shin zaki iya aure na? Za ki iya zama da ni a matsayin mijinki?....