Page 15 / 16
đź’«MARYAMAđź’«
By
Ummu Fadeela.
Typing📲
Episode 15/16.
Kafin Maryama da ta yi mutuwar zaune a wajen ta samu zarafin furta wani abu aka bude labulen dakin, duk dagowa suka yi suna kallon bakin kofar, Salima ce ta shigo da sallama ta tsugunna ta ce "Anty Maryama kinyi ba'ki wai kizo in ji Innarmu". Wani irin sanyi na ji ya ratsa daga tsakar kaina har kan babbar yatsar kafata. Amma sai na daure na ce.
"Ba'ki kuma?" na tambaya cike da madaukakin mamaki, gyada kai ta yi ta ce "ehh wai kawar ki ce tazo duba ki da jiki. Da sauri na mike ina jin farin ciki na mafitar da Allah ya bani don gujewa amsa wannan tambaya ta Hamma Jay mai cike da sarƙaƙiya. Lumshe idanunsa ya yi sakamakon sarawar da kansa ke yi, ya so ta ce wani abu, ya so ta amsa mashi wadannan tambayoyin, amma hakan bai samu ba.
Koda na fito wata ƴar dattijuwar mata na gani zaune a tabarma ita da Innarmu suna gaisawa, gefenta wata ƴarinya ce da bazata haura shekaru na ba. Lallausan murmushi ƴarinyar ta sakar min lokacin da muka hada ido da ita tana ƙoƙarin miƙewa ta ce, "Ah Masha Allah, hajiya kin warke ashe?" ya jikin naki to?".
Kafun ince wani abu, dattijuwar matar ta katse min hanzari tare da hararar budurwar ta na fadin, "To uwar zuba kya bari ta isar dake É—aki tukunna ai, ba ki tare ta da surutu ba," ba don na so ba na gaida matar kana ina kallon budurwar da ke ta kallona tana murmushi na ce mata, "sannunku da zuwa mu isa ciki".
Ko da yaushe dakinmu tsab ya ke shi ya sa bana shakkan shigar da mutum ciki, dan dofanuwa ta yi bakin gado na tana ci gaba da murmushi ta ce, "ya karfin jiki kuma?".
"Alhamdulillah" na amsa ma ta kana na ci gaba da faɗin "sai dai ban gane ku ba, ko dai ɓatan kai ku ka yi ne?".
"Ko É—aya," cewar ta.
"Sunana Laurat kuma Siyama ce ta aiko ni wajenki, É—an waige waige ta fara kamar munafuka sannan ta gyara zamanta da kyau ta ce, "Ana ta kiran wayarki a rufe me ya ke faruwa?" Tunda ta ambaci Siyama na ji gaba É—aya miyau din baki na sun kafe, da kyar na tattaro jarumta da niyyan magana wayar ta ta É—auki tsuwwa.
"Yauwa ƴar halak" cewarta tana ƙoƙarin miƙo min wayar haɗi da faɗin "Ga shi kuyi magana da ita"...Jikina ne ya tsananta rawa har wayar tana faɗuwa ƙasa, amma na yi azamar tarota na kara a kunne na.
"Ina kika jefa wayar ki ne haka Pretty?".
Tambayar Siyama ta doki kunne na,..Cikin in ina na ce, "Siyama abubuwa da yawa sun faru, har na kwanta a hospital ma, wayata kuwa Hamma Jay ya fasata, siyama ya aka yi yasan na je wajenki? ya akayi hijab da jakata suka dawo gida kafin in dawo?".
Nan siyama ta bawa Maryama labarin yadda Jabeer da Baffanmu suka je shop nata har bala'in da Hamma jay ya yi mata. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama bata labarin sannan ta ce, "duk ba ma wannan ba, Sadeeq ya ce lallai lallai ki kirashi yanzun nan. Wai Maryama me ki ka yiwa bawan Allahn nan haka ne gaba daya ya fita a hayyacinsa?" Siyama ta fada cikin zolaya.
"Me zan mashi ni ko? kin san sanadiyyar kiran da yai min ne hamma Jay ya fasa min wayata?. yanzu bani da wayar da zan kira shi da, plssss Siyama ki bashi hakuri dan Allah."
Ba wannan maganar, yanda ya dau zafin nan ban isa in tunkareshi da wannan zance ba....Abin da za'ayi yanzu zan sanar da laurat ta baki karamar wayar ta dake hannunta zan miki sending na contact nashi sai ki ƙirashi yanzu nan, yanzu nan faa," ta ƙara maimaitawa dan in tabbatar. da "to" na amsa nima a raina na ƙagu in yi magana dashi. haka ko akayi Laurat ta bani ƙaramar wayar dake hannunta bayan ta sa ta a silent mode suka mana sallama ita da wannan matar da suke ta hira da Innarmu tamkar sun san juna.
Bayan kamar minti biyu sai ga massage na Siyama da layin Sadeeq. kallo daya na yiwa lambar na haddace shi, take na loda cikin wayar na fara tunanin yadda zanyi in ƙirashi ba tare da an kama ni ba,.....
ABiNDA YA FARU.
Tunda Sadeeq ya iso porthacourt ya ka sa samun nutsuwar zuciya da ta gangar jiki, da kyar ya iya presenting Data ɗin da ya zo ya tattara a wajen meeting din na su, ya koma gida ya kwanta, duk yadda ya so daina tunanin ta kasawa yayi, ya yi trying layin Siyama ya fi sau curin masaki amma switch off ake sanar mishi. Wata idea ce ta fado mishi na ƙiran saurayin ita Siyamar wato Huzaifa wanda ta dalilinshi ne suka haɗu da ita,...cikin nasara kuwa ya same shi, ta ke ya bashi umarnin ya je ya hada shi da Siyama. Huzaifa bai bata lokaci ba wajen cika umarnin uban gidan nashi, ko da ya kai mata wayar ma still maganar daya ce wato ta je ta hada shi da Maryama. Huzaifa ne ya kawo musu shawarar nemo wa Maryama kawa ta karya taje gidan tunda shi ko ita Siyamar ba bu wanda zai iya tunkarar gidan, bayan yan binciken da suka gudanar na sirri suka gano ai maryamar ma bata da lafiya har ta kwanta a asibiti wannan ne ya karawa tafiyar tasu armashi har suka nemo da uwar karya suka hada laurat da shi wacce itama biyan ta kudi suka yi kuma a kayi sa'a suka gama mission din nasu sucessfully....Wannan kenan.
Ina zaune sai tunanin yadda zan kira shi nake yi, daya barin na zuciyata kuwa cike ta ke fal da tunanin hamma jay da kuma tambayar da yai man da zu....Haske wayar dake hannuna ta yi kasancewar ta na silent, sai da zuciya ta ta kusan shigewa cikin cikina sakamakon arba da na yi da lambobin Sadeeq suna yawo bisa allon wayar, duk da zuciya ta tana rawa da tsoron kar wani ya shigo ya kamani, haka na kama call din ba tare da na jira ya katse ba.
"Ohh Damn It! Pretty ina kika shige ne haka?".
Abunda Sadeeq ya fara fada kenan lokacin da ya ji an dau kiran, lumshe idanu nayi amma bance komai ba sai numfashi na da ke tseren gudu.
"Assalamu Alaiki". Are you there baby?" ya kuma fada jin an kama kiran amma ba'ace komai ba.
"Barka da warhaka ranka ya dade" na fada cikin sanyin murya dan kar Innarmu ta jiyo ni. Maimakon ya amsa sai tambayar da ya jefo min. "Lafiyar ki kuwa?"
"Hmmmmm" na bashi amsa. Gami da fadin, "ina wuni, ya ka koma ?"
"Alhmdllh na koma lafiya qalau Maryama, sai kewar ki da ya addabeni kamar zanyi karamar hauka. Na kasa sukuni tun isowa ta har saida na nemo wanda zai hada ni da ke a waya sannan na fara dawowa normal."
Dafe kirji na yi hadi da zaro idanu waje na ce, "kewata ku ma?".
"Kwarai kuwa kewar ki Maryama. At first na dauka abun wasa ne, sai daga baya na fahimci kinmin kamu irin na kazar kuku".
"Ban fahimta ba," na fada cike da rudani....Da ma banson ki fahimta tun yanzu sai zuwa gaba by then kin kara girma". Gaba daya maganganunsa sun daure min kai amma haka na hakura ba don na fahimci komai ba sai don yadda na ke jin dadin hira dashi, duk sanda yayi magana sai inji wani abu ya na tasowa tun daga tafin kafata har zuwa cikin cikina, sannan gaba na ya na faduwa ban san dalili ba, mun dau tsawon lokaci muna magana dashi kafin ya yanke wayar, da sauri na cusa wayar cikin rigata jin footsteps.
Tun daga wannan lokaci kullum sai munyi waya da shi a kalla sau hudu a rana luckily ba wanda ya ankara cewa da waya a hannuna, dan kullum a silent ta ke, cikin sati daya munyi wani irin shakuwa da Sadeeq na ban mamakin da idan lokacin da ya saba kirana ya wuce bai kira ni ba na kanji tamkar bani da lafiya, Sadeeq mutum ne mai barkwanci da iya kalamai masu taushi da sanyaya rai wannan ya taka rawa matuka ga ya wajen kara dankon shakuwar mu da shi.
A bangaren Hamma Jay kuwa, tun ranar da ya min waccan tambayar bamu sake zama dashi ba har tsawon one week din, Iyaka ta da shi hange daga nesa shima ba kullum ba, dan kwannan nan ya zama tamkar mace kullum yana kwance a daki ba ya fita aikin shi ma ya daina zuwa, ko daga karfen da ya mayar tamkar ibada shima ya daina yanzu,sai wani rama da ya ke yi a tsaye tamkar mai jinya. ...Saidai abunda ba wanda ya sani tabbas Jabeer jinya ya ke yi a tsaye wani irin ciwon kai da ciwon kirji ya ke fama dashi these days musamman ya fi tasar masa cikin dare tamkar zai mutu...
Yau saura sati daya lokacin da Baffanmu ya dibar na bikin Maryama da Jabeer ya cika, saidai ba bu abunda ango ko amaryar suka fara na shirin biki, a yau ne kuma daada za ta zo daga nijar.
Daga labulen dakin Jabeer baffa ya yi ya leka kanshi ciki,cike da karfin hali jabeer ya mike daga kwancen da ya ke ya ce, "Sannu da shigowa Baffanmu".
"Yauwa Jabeeru, biyo ni daki akwai abunda za mu tattauna" cewar baffa yana sakin labulen da barin wajen.
Da sallama ya shigo dakin sanye da jallabiya fara kal ya samu gefe ya zauna gaisawa suka kara yi da baffa sannan yayi gyaran murya ya ce, "Jabeeru lokaci ya na kara matsowa banji kayi wani motsi ba har yanzu, ko akwai wani damuwa ne?"
Girgiza kai ya yi yace, " ba bu wani damuwa Allah ya nuna mana lokacin".
Dan jimm baffa ya yi sannan ya fara yi mashi nasiha mai ratsa jiki yawanci a kan hakuri da rayuwa ne. Sosai Jabeer ya ji dadin nasihar da baffa ya yi mashi har ya dan sake, ko da dai ciwon da ya ke ji a zuciyar shi ya tabbata ya na bukatar ganin likita.
Wasu damin kudi yan dubu dubu da suka gaji da rayuwa kamar kana kamawa za su tsage baffa ya fitar da ga cikin wani akwatin karfe, yana kallon Jabeer ya ce, "ungo wannan ka ka ra kayi wani abun da shi, nasan basu da yawa amma ka yi hakuri ba bu ce ta sa hakan Jabeer, na san da dan uwa na yana raye ba karamar farin ciki zai shiga ba a irin wannan lokacin," ya fada cike da alhini.
Ta ke idanun Jabeer suka kada jajur, ya yi karfin halin cewa, "ka bar wannan a wajenka baffa,ni ne ya kamata in baka ba wai kai ka bani ba".
"Ka rena abunda na maka ko Jabeer?"
"A'a ranka ya dade a yi min afuwa ba nufi na kenan ba, ganin abubuwa za su ma ka yawa ne shiya sa ka a yi hakuri" cewar Jabeer.
Baffa ya ce, "matukar ba raina wa ka yi ba yi maza ka amsa "
Hannu biyu jay ya sa ya amshi kudin ga mi da fadin, "Allah ya kara girma baffanmu".
Koda ya fito dakin baffa, da sallama ya shiga dakin Inna, tana zaune bakin gado da wani banki na katako a kusa da ita ta bude sai aikin shirya kudi take yi yan dubu dubu da dari biyar biyar masu yawan gaske, da alama an dade ana tara su....Da hannu ta mishi alamar ya matso kusa da ita, ba bu musu a tsakaninsu dan haka ya karasa shigowa ya zauna a bakin gadon ta kasa.Kusan minti goma suna a haka kafun Inna ta gama shirya kudin inda ta raba su gida biyu ta dago ta na kallon shi da dan murmushi fuskar ta ta ce, "ango ya aka yi ne".
Lallausan murmushi ya yi shima ya na shafa gashin kanshi ya ce, "Ba bu komai Innarmu," kudin da ke hannun shi ya ajiye kusa da ita ya ce, "Baffa ya bani su yanzu wai in yi wani abin dasu,sai dai Inna kamar......"
"Shiiit" inna ta fada tana sa dan ya tsanta a saman bakinta. Shirun ya yi kuwa, inna tace, "Ka rena abinda ya baka ko?".
Da sauri ya dago yace, "wllh ba haka bane innarmu kawai ganin shima abubuwa za su mashi yawa ta bangarenshi ne ga shi ba bu mai taimako, ni da ya kamata in taimake ku din kuma b....Ka sa karasa maganar ya yi sakamakon harbawa da kirjinsa ke yi.
Sassauta murya inna ta yi, sarai ta fahimci abunda ke damun dan nata, din haka itama nasihar ta shiga yi ma shi har saida ta ga ya saki jikinshi tukunna, kudin da ya ajiye ta dauka ta duba su, naira dubu dari uku ne cifff, mika masa su ta yi,kana ta kuma daukan kaso daya cikin wanda ta shirya ta ce, "Ga wannan ta bangare na, na dade ina tarasu domin lokaci irin ta yanzu, ga shi Allah ya kawo mu, ka hada da na wurin baffanku ka nemi ma'aikata ku je kuga gyaran da za kuyi wa gidan naku, sai batun lefe kuma kar ka damu kanka, dama ba addini ba ne, idan mun fita sayan kayan kitchen zan duba mata yan zannuwa ko guda uku ta samu na fitar bikin.. A yi ta hakuri da rayuwa dai wata rana sai labari,Allah ya rufa mana asiri ya yi maku albarka, ya kuma albarkaci auren naku".
Duk yanda Jabeer ya so daurewa kasa wa ya yi baisan sanda ya kama kafafun inna ya durkushe a kansu ba,wasu hawaye masu zafi suka gangaro ma shi a ido daya.
Dafe bango Maryama dake tsaye bakin kofat inna ta yi, da ma ta zo shiga ne ta ji suna magana hakan ya sa ta tsaya. "Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un." ta ke ta maimaitawa a ranta, ba dai ita za'ayi wa aure nan da sati daya ba, iyayenta da ta ke ganin talakawa sune masu taimakon mijin da za ta aura?.......