MARYAMA

Page 17/18

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

     By

Ummu Fadeela


 *Episode 17/18*




Iyayena da na ke yiwa kallon talakawa sune masu taimakon mijin da zan aura da kuɗin aurena?." Ya Rabb save me". na fada a hankali.

Da bin bango na koma ɗaki na faɗa saman gado wasu hawaye da ban san daga ina ba suka fara shatata saman fuskata,...ina cikin rera kuka wayar da na ɓoye cikin bra di na ya fara vibrate, sanin wanda ke kirana na yi saurin goge hawayena na yi picking call din."Hiii pretty," Sadeeq dake kwance cikin luntsumemiyar kujera ta alfarma dake cikin kayataccen falonshi ya faɗa. Duk sanda ya ƙira ni da pyretty sai zuciya ta ta buga gabana ya dinga faɗuwa, duk yadda na yi ƙoƙarin saisaita murya ta dan kar ya fahimci wani abu amma sai da ya gane, ɗan jim yayi bayan na gaishe shi.

"What happened Pretty"?

"Babu komai" na faɗa murya ƙasa ƙasa,

"No don't lie to me, ga shi na ji muryar ki kina kuka then ki ce min ba komai.

"Da gaske babu komai faaaa" na faɗa cike da shagwaba ina turo ba ki gaba.

Ta ke Sadeeq ya ɗauke wuta sakamakon wani irin yarrr da ya ji a jikinsa, da sauri ya ce,"ohk to shikenan....munyi hira dashi na lokaci mai tsawo, har saida naji su Salima sun nufo ɗakin sannan na mishi sallama ba don na so ba na kashe wayar.

Riƙe kafafun Inna ya yi wasu hawaye masu tsananin zafi suka gangaro mishi a ido guda ɗaya. Shafa kansa Inna ta hau yi cikin lallashi ta ce, "Ba kuka zaka yi ba Jabeer, Allah zaka godewa da ya bar maka mu a raye, na san abin da kake ji cikin ranka baya misaltuwa amma haka zaka daure...idan muna dashi ko da duniyar nan ce zamu iya mallaka maka kamar yadda mukayi imanin kaima zaka iya mallaka mana duk wani abin da ka ke taƙama dashi a rayuwa, yanzu ka tashi ka nemo mai gyara sai ku ke ku duba abin da za'a fara a gidan, hanzarta ka tashi mana angon Maryama, kuka ba na angwaye bane fa kar ka yadda ka zamo ragon maza masu kuka akan shirme." ta faɗa cike da zolaya. Dago kansa ya yi yana ɗan murmushi kaɗan, "yauwa ko kaifa, yanzu ka yi kama da ango" cewar inna cikin salon karfafa gwuiwa.

"Na gode Innarmu Allah ya ƙara girma, ban san da wanne irin kalma zanyi amfani wajen gode maku ba Allah ya......" 

"Ya isa haka, ta shi kaje ku fara abun da ya kamata" cewar Inna ganin Jabeer zai fara dogon jawabi.

Kamar yadda Inna ta ba da shawara hakan akayi ya samo masu gyara suka duba aiyukan daza'ayi haɗi da yin estimend,....aiyukan sun haɗa da ɓamɓare zinc dake saman ɗakunan da yin sabon roofing, sai hade ɗakuna biyun su zama room and parlor, kana a sa ceiling kasanvewar babu, za'ayi tailing parlor da dogon varendar dake gaban ɗakunan,sai germain floor da za suyi a tsakar gida da toilet kana a buga kanta a cikin kitchen, daga karshe a yi paint....(Mai karatu ya ka hango gidan gimbiya maryama?)....😍....

Sosai hamma Jay ya fitar da kuɗi dan a yi aikin yadda ya ke so kuma akan lokaci,. bai cika tarkacen abokai ba, amma jama'a abokan hulɗar yau da kullum sun shirya meeting na auren, kuɗin da ya daɗe yana tarawa ya fitar shima don haɗawa Maryama lefe na bajinta.

Sosai ake shirin wannan aure, a ɓangaren amarya kuwa kamar wacce aka cirewa ruhi haka ta zama bata uhm bata umum sai ido.

Umaima Innarmu ta ƙira a ranar ta bata cimgam da minti dan rabawa ƙawayen su. A ranar da ya rage kwanaki shida ɗaurin aure Daada da tawagar ta suka iso daga nijar, da gudu Maryama ta je ta rungume Daada ta fashe da kuka. Sake baki daada tayi ta ce. 

"Aniyar ki ta biki takwara, ya zaki zo ki tarbe ni da kuka da farar daren nan bayan uwar doguwar tafiyar da nasha, shima angon na ganshi ya ƙare tas kamar mayu sunyi guzuri da shi, anya lafiya kuwa"? bance mata komai ba sai ƙara rungumeta da nayi na ci gaba da kuka na.