Page 19/20
💫MARYAMA💫
By
Ummu Fadeela.
Episode19/20.
"Ince ko akwai abun da ke damun yaran nan Dijah? Duk na gan su sukuku sukuku kamar an jiƙa ƴaƴan kyanwa". Cewar daada ta na kallon innarmu, gefe da gefenta jabeer ne da maryama a zaune.ta ci gaba da faɗin, "duk ba irin ɗokin nan na aure a fuskokinsu ko kaɗan hala dai lafiya gashi ɗannan ya sanar dani auren haka bagatatan."
Kafun Innarmu ta ce wani abu, Hamma Jay ya riga ta faɗin, "ke dai faɗi gaskiya tsohuwa, ki ce kawai kishi ke ɗawainiya dake kinga wata zata ƙwace maki miji, to kwantar da hankalinki ko anyi auren ma bazan manta da ke ba ai da tsohuwar zuma ake magani" Ya ƙare da dariya saman fuskar shi. Dariya sauran ma suka yi.
Daada ta ce, "yo Allah na tuba ina abun da zanyi kishi anan, duk inda kaje nan zaka dawo ne ka same ni daram dam."
Jabeer ya na murmushi ya miƙe haɗi da zura hannu cikin aljihu ya ce "ni nasan zancen zai fito ai dama kawai yar tsohuwa ki ce kishi na kike" kafun daada ta ce wani abu ya kalli Maryama dake ta cika tana batsewa ya ce, "meet me outside pretty". Sai ya juya ya ce da daada yana zuwa yanzun nan, da kallo su dukka uku suka bishi har ya fice daga ɗakin Innar ɗakin Maryama ya shiga a zatonshi ba kowa saidai saɓanin tunaninshi ɗakin cike yake da mutanen da suka zo bikin da ga nijar tare da daada, ƙannen mamarshi biyu sai yayar innarmu da kannenta biyu sai daada, iya mutum shida ne suka zo daga nijar saboda yanayin hanya....tsugunnawa ya yi ya gaishe su ya juya a gurguje ya fice daga ɗakin...
"Ba jiranki ake ba ne?" cewar inna tana kallon Maryama wacce ke ƙara gyara zama jikin Daada, turo baki ta yi sannan ta miƙe ta fita, daada ta taɓe baki ta ce,"yaran zamani ba su san yadda ake riƙe miji ba ko kaɗan, amma Dijah me kika yiwa yar nan na gyara don ban ga wani alamar kin fara mata gyara ba, kamar dai ba ƴan nijar buzaye ba?"
Murmushi Inna ta yi ta ce, "gani na yi budurwa ce ai daada shi sa"
"Amma kin iya sa kai a uku Dijah, yaran yanzu da suka gama zubar da budurci a waje da tsalle tsalle da É—aga abu mai nauyi, yanzu ko Æ´an gyara mai sauki sauki baza ki mata ba, duk rawar kan da yaron nan yake yi da yaje yaga ba abin da yake tunani ba sai ki ga yanayi ya canza." ke dai ki ji tsoron Allah Dijah, amma ke da ba'ai miki gyaran ba ai da yanzu wani labarin ake".
Inna dai bata ce komai ba dan tasan halin daada na mita,...wata katuwar ghana must go daada ta janyo ta fara fitar da wasu itatuwa da dakan gari kulli kulli, ta ce, "to bude idanunki da kyau dijah, haka ta fara lissafa mata daga na tafasawa zuwa na jiƙawa da na sha da nono, ta ƙare da cewa "kuma ki tashi ki fara tun yanzu."
A bayan kitchen ɗin Inna na sameshi tsaye ya harɗe hannu a kirji, gaskiyar daada ne cewa hamma jay ya rame ya ƙara baƙi sosai, kafe shi na yi da ido,bansan sanda maganar ya fito ba sai ji nayi na ce, me ke damunka hamma jay, baka da lafiya ne?."
ÆŠan matsowa ya yi kaÉ—an ya rankwafo saitin kunnena har inajin sautin numfashinsa ga kamshin turarensa na oud essential da ya cika min hanci, ya ce, "ke ce damuwa ta Pretty,"....."ni kuma?" na faÉ—a innocently.
"Yes ke ce, amma na kusa warkewa in six days masu zuwa insha Allah", ya faÉ—a ya na É—an murmushi, " ko ba haka ba amaryata?."
Turo baki na yi gaba bance komai ba...jingina yayi da bangon kitchen É—in ya ce, me ne shirye shiryen ki, ganin yadda komai ya zo mana a kurarren lokaci?".
Da'ace zan iya, cemasa zanyi ni bana son auren, amma nasan furta wannan kalma daidai ya ke da É—aukewar numfashin hamma jabeer a yanzu. ...don haka sai na tsungunnar da kai kawai bance komai ba.
"Say something mana pretty."
"Ni bani da wani shiri" na faÉ—a ina jin wani irin zafi a raina,a tsarina big wedding na ke so a aure na,amma sai gashi ....
"No dole akwai plan É—in da kuke dashi ke da frnds naki pretty,ki daure ki sanar da ni,plsss wife."
"Da gaske babu fa,sai dai ko ka nemi Umaimah,. Ni zan koma ciki" ban jira ya ce wani abu ba na juya na koma cikin gida,...dafe saitin zuciyar sa jabeer dake jingine da bango yayi ya rufe idanunsa a hankali yana jin wani irin zogi a wajen,"sonki ya mini illa Maryama, da'ace nasan inda yake tabbas zan ciroshi ko zan samu nutsuwar zuciya, saidai kash shi so ba ya shawara kafun ya shiga haka kuma ba ya jin rarrashi bayan ya shiga sannan ba ya sanin kan wanda ya ke sauka, wannan shine soyayyata".
Kamar yadda daada ta umarci innarmu hakan ta yi, take ta haɗa wuta ta fara dafa tsumin yar nijar da daada ta kawo na sha da nono kuwa ta tura fati ta siyo mata nonon,....Da yammacin ranar aka fara bata tsumin kasancewar yana da daɗi tas Maryama ta shanye abinta ba tare da tasan minene ba, bayan kamar minti biyu Inna lami ƙanwar innarmu ta shigo da wani abu a kwano ta ce maza tuɓe kayan nan na jikinki zamu fara dirje maki jiki, bansan wani irin sakaci ne wannan adda dijah tayi ba, ace biki saura kwana shida amma ba'a fara gyara ki ba, wannan sam ba dabi'ar zuriyar mu bace ba can ta samo shi wallah,..."ganin ban motsa ba ne ya sata daka min wani tsawan da ya kaɗa min yan hanji don Inna lami ba sauƙi tana da zafin gaske,ko lokacin da muke zuwa nijar bana yadda in kwana gidan ta dan tsananinta.
"Kin ta shi ne ko sai na ma ke ki?" jiki na yana rawa na ta shi na tuɓe kayana sai dan zani da na ɗaura zuwa kirji, haɗin dilkar gargajiya ta fara ɗeba tana dirzar jikina dashi kamar zata canja mani fata.....sosai ta dirje ni sannan ta barni for one hour abun ya bushe ta zo ta kamani zuwa toilet wai zata min wanka, ni abin ma dariya ya bani shirgegiya dani wai za'a min wanka, amma ba yadda na iya don ina turjewa na tabbata ba karamin aikin Inna Lami bane ta min duka a wajen. Ruwan wankan ma na musamman ne, ga wani kamshi da ya ke tashi aciki kamar gonar turare, nan ta wanke ni tas da wani sabulu na musamman amma ban cire ɗan kampai ba, idan ka kalle ni a lokacin zaka rantse da Allah a inji aka sani aka canja min fata, hmmm wannan ma sau ɗaya kawai akayi. Wani mai shima na musamman ta bani mai ɗan karen kamshi da santsi na mulke jikina dashi, take skin ɗina ya ɗau wani irin glowing.. Ni da kaina na kasa daina kallon kai na a madubi. Nan ta fita ta barni tana ta sababin mu yaran zamani bamu san sirrin gyara ba sai iyayi da kauɗi...
UWAR GIDA KEMA KI GWADA WANNAN DILKAR ZAKI GODEMIN 👇
.Lalle
.Kurkur
.Jar dilka
.Madarar ruwa
.Man zaitun
.Kwai guda uku amma kwaiduwar
.Manja
.Lipton
.Nescafe
.Sandal powder
Ki samu ki zuba lallenki, ki juye kurkur akai, dama kin jiƙa jar dilkar ki da ruwan zafi idan ya kumburo sai ki juye akan lallen ki diga manja kaman table spoon ɗaya, shima lipton dama kin jiƙa guda ɗaya da ruwa dan kadan sai ki juye a cikin lallen, ki ɗauko kwaiduwar kwanki ki kada ki juye a kai, sai man zaitun kamar table spoon biyar, Nescafe table spoon daya Garin sandal table spoon biyu,sai madara ta ruwa idan lallen dayawa ne zaki juye duka idan kaɗan ne, sai ki sa rabin gwangwani, ki hada ki kwaba su sosai har sai sun hade jikin su, da tauri ake so kar yayi ruwa ko kadan, and ba'a samashi ruwa a kwabin iya haɗin kawai ya isa, idan kina so zaki iya ɗiga lemon tsami dan kashe karnin kwan sai ki samu container dinki mai murfi ki zuba ki rufe, duk sanda zaki yi amfani dashi sai ki ɗeba ki kara mashi ruwa ki dirje jikinki dashi idan ya bushe ki bambare ki shiga wanka, hmmmm uwar gida har ma da yan mata, idan ku kafara wannan kin huta da kashe kudinki wajen sayan man bleaching......
Daga baya zamu yi bayanin hadin mai da sabulu É—in.....
Da dare Inna lami ta kuma kawoman wata dafaffiyar kaza haÉ—e da itatuwa a cikinta wai in cinye ni kaÉ—ai, wayyo duniya ina sonki zan barki, duk da rashin taste da ke tattare da naman kazar haka na ringa figar ta ina mata cin huce takaici, ni Maryama na san indai nama ne to ko da ruwan batir aka dafa ta sai na ci, musamman a ce namar ta kaza ce. Ina cikin figar kazar da sometimes na kan manta da aure za'a min sai wani abu ya faru ko na ga yan biki nake tuna hakan, ko me yasa hakan?
Kamar daga sama na jiyo muryar Innarmu tana ta bambamin faÉ—a.
"Wato Jabeer ban isa in hanaka abu ba ko, da na ce ka bari ko daga baya kayi shi ne ka ƙi jin magana ta"? faɗa ta ke ta inda ta shiga bata nan ta ke fita ba.
Daada dake fitowa daga bayi har zaninta na ƙoƙarin faɗuwa ƙasa ta ce "kai wai wa ya ke mana jaraba da farar magaribar nan ne haka? Dan shiru tayi bayan an gama mata jawabin abin da ke faruwa.
Wani irin salati ta saka da ya sa gaba ɗaya jama'ar wajen kamewa ta ce, "amma ke dai Dijah ba tsoron Allah a ranki, wallahi kin cika sa kai a uku, ke ba'ayin lefen aka miki? na ce ba'a yin lefe aka miki tun duniya ba ta waye bama balle yanzu da aka waye. ah ah yau nake ganin jaraba ni Mero, ki fa fita a idona Dijah, yo Allah na tuba mazan nan na yanzu da ke yiwa aure rikon sakainar kashi sun sha bakar wahala sunyi lefen ma ya aka kaya balle an kai masu ƴa haka nan ziƙau uwa marar gata. To ki fitar da kan ki a harkar nan, Jabeer da Mairamu dai kece bare a tsakaninsu.".
Tsokar da ke baki na na tofar sakamakon maƙalewa da ya yi, na miƙe cikin sanɗa na leƙa tsakar gidan ta gefen labule, Hamma Jay da ke tsaye kanshi a ƙasa ya goya hannunsa a baya na ke hangowa, sai wasu akwatuna guda uku red colour masu kyau dake ajiye gefe.
"Ke Lami maza ɗauko mana tabarma mu baje kaya mu gani, ni ina can ina tausaya masa ashe ja'irin kuɗi gareshi" cewar Daada ta na janyo akwati guda, shimfiɗa babbar tabarma Inna Lami tayi duk mutanen dake wurin suka zazzauna suka fara buɗe boxes ɗin, fittt na fito tamkar wacce aka turo na tsaya a kan su ina zare ido da rashin sanin takamaiman abin da zanyi. Wani mugun hararar da Innarmu ta banka min ya sa ni juyawa ba shiri, Daada da ta ganni ta ce "Ina kuma zaki takwara? zo zauna ki ga kayan da aka miki mana gasu nan wallahi duk ba na yarwa a ciki, yo ba dole ya kashe kansa ya zaɓo miki kaya na gani na faɗa ba, tunda ya samu mata kamar ba hindiya" cewar ta lokacin da ta ke ɗaga kyawawan zannuwan dake cikin akwatin.
Ban gama jin abin da zata ce ba na faÉ—a É—aki wani kuka mai cin rai yana taho min.
Jabeer ya yi ƙoƙari wajen sayan kayan akwatin nan, la'akari da cewa tsakanin jiya da yau kawai ya siye su, kaf kudin da ya ke tarawa dan auren ya kashe akansu, a ganinsa idan da duka duniyar nan ya mallaka zai iya bawa Maryama matuƙar zata yi farin ciki. Kayane na gani na fada unique one ya zuba cikin akwati guda uku duk wani abin da ake bukata a lefen masu karamar karfi jabeer ya saka wa Maryama, sosai Innarmu taji daɗi dama tana faɗa ne ganin bai da shi kuma komai na gida ne.
Bayan an gama kallon kayan aka shigar dasu ɗakin baffanmu aka ajiye su, Daada kuwa ta fitar da nata guzurin da suka yo daga nijar, tabbas duk da rashin wadata da suke ciki yan uwan sun fitar da juna a kunya, ba karamar kudi suka tarawa jabeer ba, ita ko Maryama kayan kitchen sosai suka mata both dangin Innarmu da na mamar Jabeer da shike duk family ɗaya ne dama....ƙin karbar kudin Jay ya yi yace a bawa Innarmu, har saida inna ta nuna mashi bacin ranta sannan ya karba ya na ta godiya ga Allah da yake ta sauƙaƙa masa abubuwa.
Yan da naga rana haka naga dare banyi bacci ba tsabar tashin hankali, yanzu shike nan da gaske aure za'amin aure da hamma jay, shike nan mafarkina da burina ya tashi a banza kenan?...koda na tashi da safiya fuskata ta kumbura suntum, gashi gida ya fara daukar harami dan sai shirye shiryensu suke yi, ina kwance a ɗaki baifi minti biyar ba da fitar inna lami ta zo ta ƙara dirje min jiki da wannan haɗin nata na jaraba, na jiyo sallamar Umaimah labulen ta ɗaga ta shigo da fara'arta ta ce, "amarsu ta ango, amarya a gidan hamma jay," wuri ta samu ta zauna ko kallon inda ta ke banyi ba, ta ce, "pretty ki godewa Allah, yanzu Innarmu ta nuna min kayan lefenki, a gaskiya hamma jabeer yayi ƙoƙari matuka gaya, wayyo Allah na inama my yusuf ya min ko da rabin wannan ne, oh Ya Rabb, ta faɗa tana kwanciya saman gadona.
Dogon tsakin da na ja ne ya sa ta miƙewa da sauri, na ce, "yanzu Umaimah fisabilillahi wannan har lefene da mutum zaiyi alfahari da fatan samun kamarsa akwati uku fa for God sake, haba mana dan Allah, wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro mini
Wannan karon saukowa ta yi zuwa gabana cike da tausayawa kawar tata Umaimah ta kama hannun maryama duka biyu ta riƙe su gam, a ranta tana tunanin anya kan Maryama daidai yake kuwa? abun ya fara bata tsoro gaskiya.
Cikin sassauta murya tace, "Maryama ina ji maki tsoron ranar da zakiyi nadama marar amfani, ina ji miki tsoron ranar da zaki fara sharar kasuwa a maimakon ta masallaci, Maryama irin son da hamma jay ya ke maki zai iya mallaka miki komai kamar yadda ya mallaka miki wani sashi na jikinsa a baya, ki yi tunani mana pretty, yanzu da bai da shi ma yana fafutuka a kan ki duk don kiyi farin ciki, me kike tsamanni zai faru idan yayi arziki, karki manta kuma dare É—aya Allah kanyi bature, plssss Maryama kar ki zama butulu karki bar hamma jabeer da tabon da bazai warke ba a rayuwarsa ke yanzu a tunaninki arziki shine farin ciki? mutane nawa ke rayuwa da arziki amma ya kasa basu farin ciki? Wasu ga dukiyar amma ba Æ´aÆ´a, wasu ko ba bu lafiya kuma dukiyar ya kasa samar musu da lafiyar,..babbar arziki maryama shine lafiya, kina ji kina gani kina magana kina tafiya, ko ina ajikinki yana motsi, Maryama wasu da dukiyar amma sun rasa wannan,...kuka ne ya ci karfin Umaimah tilas tayi shiru, gaba É—aya jikin Maryama ya yi sanyi kalau hannu ta sa tana sharewa aminiyar tata hawaye,...É—an murmushi tayi tacigaba da cewa hamma jay ya tambaye ni me shirinmu wai ke kince babu abin da zaki yi, so mun yanke da ke cewa zamuyi walima kawai ya isa tunda ga halin da ake ciki...tsawon awa É—aya umaimah ta yi a gidanmu tana ta tsara min yadda abubuwa zasu kasance sannan ta tafi..
Yauma inna lami ce tamin wanka ba shakka ina dirjuwa dan sau biyu kawai aka min amma ni da kaina nasan na canja....bayan na fito wanka na fitar da wayar da siyama ta bani dama boyeta na keyi kullum, missed calls na sadeeq na gani kusan goma, kafun in kira shi kiran siyama ya shigo wayata...."Maryama me nake ji haka? da gaske aure za'a miki nan da five days?"
Fashewa na yi da kuka nace, "Wai siyama"
Wani irin ashar siyama ta lafta san nan tace
"Kuma kina zaune baki ce komai ba? gashi Sadeeq ya ƙirani har ya turo min ƙudin jamb naki wai yana ta kiranki tun jiya baki dauka", dafe kirji nayi nace, "da gaske siyama? yaushe ya turo? Kin san dama nace masa su Innarmu sun amince da maganar makarantar, yanzu yaushe zamu haɗu?" duka a hankali nake maganar dan kar in janyo hanklin mutane zuwa kaina.
Munyi magana ya kai na minti bakwai ni da siyama kafun muka ajiye waya, kwakwalwata ta fara nazarin maganganunta, anya zan iya abin da ta sani kuwa, anya?.
A bangaren Siyama kuma tana ajiye wayar wani irin tsalle ta yi tana dariya ta ce, yarinya bazan taɓa bari kiyi auren nan ba ki toshe min hanyan samu na sai na ɓamɓari rabo na, wayar ta ta ɗauka ta kara kallon alert na 100k da sadeeq ya turo mata wai ta bawa Maryama ta zana jamb. Hmmmm lallai boss ya shiga da yawa, yasin nima sai na ci rabona.
A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah cikin kwana huɗun da suka biyo baya abubuwa dayawa sun faru, jabeer ya gama gyaran gidanshi wanda ya fito sak na amarya, su innarmu sun gama haɗa kayan kitchen da na gado har anje anyi jere an kuma yi kayan fulawa irin su cincin da sauran su.wayar mu da sadeeq kuwa sai abinda ya qaru dan ma gidan a cike ya ke yanzu, umaima kuwa ta yi kokarin haɗa kan ƙawayen mu gaba daya, yayinda maganar da muka yi da siyama ya ke cigaba da yawo a kwnayata, hamma jay kuwa duk yadda ya so inje inga gida ƙi nayi thou kwana biyun nan ya shiga busy shima.yau alhamis akayi walima kamar yadda umaimah suka tsara abun ya tafi cikin tsari gwanin sha'awa, malamar da suka gayyato tayi wa'azi mai shiga zuciya sosai,saidai ko kaɗan banji ba, duk da cewa dan ni akayi amma hankali na ya tafi wata duniyar na tunanin maganganun siyama.
Karfe shida aka tashi walimar kowa ya kama gabanshi sai kuma gobe É—aurin aure, kawayen inmarmu da suka dawo gidanmu sai an gama biki kuwa suka hau gyaran gida da shirin abincin liyafar bayan É—aurin aure. bayan sallar isha na ji alamar ana kiran wayar da na ke ta boyewa cikin bra dina, dan haka na zari buta na shige bayi na buya siyama ce, dan haka da sauri na kama na kara a kunne na."Pretty baki manta ba ai ko? ina nan jiranki a kasan layi karki manta basai kin É—auki kaya ba kinji ai ko,cikin mutuwar jiki nace, "amma siyama bakya ganin..." katseni ta yida sauri ta hanyar fadin, "haba mana ba min gama wannan maganar ba? karki maida mu baya mana, duk fa ina wannan ne dan taimakonki."
"Shikenan zan yi ƙoƙari insha Allah."
Dare yayi misalin sha ɗaya da rabi lokacin kowa yayi bacci, masu girkin ɗaurin aure ma sun girka tukwane kowa ya shiga saboda yanayin sanyi da ake ciki, ɗakin mu ma cike yake da ƙawaye na waɗanda zasu kwana ciki har da umaimah, a hankali na buɗe idanuna kana na sauƙe kafata cikin sanɗa na fita daga ɗakin ba tare da making any sound ba, ba abin da na ɗauka kamar yadda siyama ta ce sai zumbulelen hijab dake jikina. A tsakar gidan na tsaya ina karewa ko ina kallo, hawayen da nake ta riƙewa suka silalo min saman fuskata da sauri na juya na nufi kofar fita zuciya ta tana bugun tara tara.
Akwai littafin MARYAMA complete doc 1k kachal book 1 ya kusa karewa book 2 na kudi ne tanks all