23
by @sadisakhna
______👑 *JODA* 👑_____
Na
*Sadi-sakhna*
Ƴar mutan Jama'are
THE TRIO OF TALES
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)
@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp
LITTAFI NA 1
👑*Warƙa ta (23)*👑
Yaune kwana na uku da kawowa marar lafiyan tawa,wacce nakejin sunan ta mata ga yerima mai jiran gado na masarautar Songhay. Gimbiya Asmah,a yau ɗinne kuma n janye duk wani abu danake saka mata wanda yake sakata bacci,dana kula cewar jikinta ya samu hutun da ake so. Kuma a yauɗinne na haɗo mata maganin dazata fara sha,wanda zai sake kwantarwa zuciyarta hankali kuma a yataimaka mata a ƙarishen watanninta na goyon ciki. Garin zobone yafi yawa a ciki sai citta saboda kumburin dana kula ƙafafunta sunyi.
A hankali ta fara buɗe idonta tana kallon ɗakin,dukkan mun ja da baya kuna jiran farkawarta daman tun ɗazu,ita kanta Surukarta sunki madina ta taho daga masauƙinta dana bata labafin yiwuwar tashin nata a yanzun.
Matsawa nayi inda take zan taimaka mata ta tashi,domin nasan tashin zayyi mata wuya Fasihmman gata ɗaukeda laluri kuma tayi kwana uku a kwance. Saurin fizge hannunta dana kama tayi tana bina da wani kallo mai cikeda ƙyama,Fasihmman ganin kayan danake sanye dashi na bayi. Matsawa nayi da baya a hankali cikin sanyin jiki,domin ko bata faɗaba kallonnata yabani amsar yanda ta ɗaukeni.
Yunƙuri ta sakeyi a karo nabiyu zata tashi amma takasa,nima kuma ban sake gigin ƙarisawa inda take ba,balle na taimaka mata. Sunkia madina ce ta ƙariso ta ɗagata ganin tagagara tashi. Waigawa take tana kallon ɗakin cikeda tunanin ina ne wajen,don har aka kawota bata cikin hayyacinta.
"Ummah ina ne nan ɗin,ina mukazo nan haka,wai mai yake faruwa ne"
"Kinga Asmah ki kwantar da hankali,bayan ƙokarin da akayi na kwanaki karki koma gidan jiya ki yi haƙuri"
"Ummah ina Aban sultan kinsan mai yayimin kuwa,kinsan mai ya faɗamin kuwa ummah"
Tayi maganar tana rushewa da kuka mai cin rai iya karfinta.
Shiga jikinta tayi tana jijjigata cikin sigar lallashi,saida tayi mai isarta kafin tafarayin shuru tana jan majina,sauran bayin dukka sun fita saini kaɗai kawai ɗauketa Ƙoƙon tsumin dan iyo mata a hannuna. Ganin ta lafa da kukan yasa na matsa a hankali ina miƙa mata ƙoƙon dayake hannuna. Wani kallon banza tayimin kafin ta kalli Sunkia Madina tace.
"Wai umma wannan ɗin wacce irin baiwa ce mai tsaurin ido,tana ganin kowa ya fita amma ita tana tsaye,sannan dana tashi harda wani kawo hannu zata ɗagani"
Numfasawa sunkia madina tayi,ita kanta nakulada fuskarta bataji daɗin abinda gimbiya Asmah ta faɗaba,Fasihmman ganin ƙoƙarin danayi akan ciwonnata,koyaushe ina tafe da wani sabon,duk abinda na karanta saida na zo na jarraba,wani yayi wani bayyiba da haka har Allah yadafa mana ta samu lafiya. Amma wannan kallon da kalaman sune tukwuicina na abinda nayi mata,tunda nasan koda wasa ba biyana za'a yi ba,inma kyautane saidai ayi wa su ummu hajar.
"Bakowa bace,amma itace tayi miki magani,wannan baiwar ce da aka bamu labarin tayi ƴar Ƙawata magani to shine da jikinki ya rikice muma muka kawoki wajenta,tayi ƙoƙari sosai kuwa tunda gashi har Allah yatashi kafaɗunki"
"Haba umma ki rasa wacce zaki bari ta taba jikina sai baiwa,nidai gaskiya ba'a min adalci,kawai danni ba ƴar nan bace babu nawa a kusadani sai a dunga yimin kallon tamkar ba jinin sarauta,muma ai babu wanda bashida labarin ƙarfin mulkinmu"
Nidai ja da baya nayi ina jinsu,ko kaɗan raina bai baciba,saboda idan irin wannan ne anshani na warke ina fuskantar irinsa daga mutane irinta da dama. Anyi mata magani ta samu kanta tana iƙirarin sarauta,to da sarautar tazo tayi mata aiki mana, shiyasa yanzu na daina saka ran aiki domin nakalli yabo daga garesu,sai domin zan cigaba dayi ina ƙwarewa,yanda zan zamemusu ciwon ɗuwawu da dole a zauna dani.
Tana cikin rikicin itakuma tana aikin lallashi da haka har na ajiye musu ƙoƙon maganin na fita basu sani ba.
Kai tsaye masauƙin su hammar na nufa,yau juma'a basuda ɗaukar karatu nasan zan sameshi yana nan,zan lallameshi ya rakani na maida litattafan dana sato a bangaren Baba guru.
Ban sameshi ba baya nan,fitowa nayi na dudduba hadarabar amma nan ma dagashi har Fasih babu alamar su,kama kunkumi nayi ina nazari,to ina zaije haka?.
Dabara ce ta faɗomin sai na nufi ƙofar mashigar wajen domin na tambayi dakarun da suke gadin ƙofa. Cikin sa'a kuwa na samu bayanin inda suke.
Mata basu fiye zuwa wajen ba,amma bawai haramun ne ba a garesu,hakan yasa na kore shakku na nufi wajen,duk da ba wannan ne zuwana karo na farko ba,na taba zuwa lokacin danayi basaja a matsayin Namiji,naje akayi min duka,tun sannan ban ƙara komawa ba, Idan na tuna ni kaɗai nayi ta dariya.
Tun daga nesa na hangoshi shida Shamaruz jarumin badakare wanda akeji dashi a Jami'ar saboda ƙarfin dantsensa da kuma yawan horon daya samu, dalilin dayasa kenan aka naɗashi shugaban dakarun da suke tsaron makarantar.
Fafatawa suke tuburan shida Hammar,kowannensu ya haɗa gumi amma babu alamar rusunawa a tattare dasu, abin mamaki yabani gameda zallar al'ajabi ganin yanda Hammar yake sarrafa takobi tamkar yasamu cokalin cin abinci,surar tsoƙar jikinsa wanda suke tamkar an zanasu suna motsawa cikin salo na ƙwarewa,baki na sake tun kafin na ƙarisa wajen ina kallonsa,wani abu da bansan ko menene ba naji yana farkawa daga cikin zuciya ta,wani irin shauƙi ya lullubeni.
A haka na shagala da kallon fafatawar har zuwa lokacin da Hammar yakai jarumin sadaukin ƙasa,wanda muke kallon tamkar babu wani a duniya da zai iya kadashi. Anya kuwa to Hammar mutum ne,ba aljani bane ba kuwa yayi basaja ya shigo jami'ar nan, ga kyau,ga ilimi Ga kuma jarumta duk shi kaɗai,matsayine dai kawai har yanzu ina cikin shakku ban gama tantancewa ba.
Dukka wajen kowa shewa yake yana cewa ya burgeshi,bandani da bakina ya mutu murus na kasa cewa komai,illa binsa da ido kawai danakeyi,narasa mai yake damuna gabaɗaya gabobina sun mutu,zuciyata cike take da shauƙi wanda ban gane kansa ba.
Ɗumi da kuma laushin fata baki naji akan nawa bakin wanda hakan yasa na razana kana kuma na dawo daga tunanin dana dulmiya. Saurin Ja nayi da baya ina kallon bakinnasa wanda ya yanzu mun samu tazara tsakani,saboda matsawa danayi,ji nai kaman an jona min walkiya a jikina. Wannan wanne irin yanayine haka?
"Me kike tunani haka,ko na burgeki da yawa ne da har hakan ya jefaki cikin tunanina"
Saurin jijjiga kaina nayi ina ƙoƙari zare hannuna daya riƙe,ya kulada hakan sai yasake matseshi a cikin nasa kyam, Kwana biyunnan tunda muka dawo daga wajen Baba guru na kula yana yawan riƙemin hannu,ko kuma taba wani sashe na jikina,bazance a cikin raina ina so ko banaso ba,amma dai hakan sai yazomin a baƙon yanayi kasancewar ban saba ba sam. Inaso nayi masa magana akan hakan amma gizon dayakemin yasa na kasa tunkararsa da Maganar, a lokacin dayake halin jinya idan ina tabashi da sunan inji yanayin jikinsa na kula bayaso sai ya dunga zamewa,amma yanzu shine da kansa yake jawo hannuna yasaka a ƙirjinsa,sannan idan mun haɗu to lallai sai yayi yanda yayi wani sashe na jikinmu ya haɗu. Abin yafara bani tsoro,nasan bai daceba amma tabbas zuciyata naso tafara sabawa dashi a tareda ni,wanda idan hakan ya tabbata to kuwa lallai akwai gagarumar matsala.
"Uhmm Hammar bai kamata muna kasancewa a haka ba domin mu......."
"Shhh basai kince komai ba Joda, idan har kin yarda dani,to ki yarda nafiki sanin abinda yake daidai da wanda ba daidai ba,har abada bazan taba yimiki abinda zai cutar dake ba,saidai idan na kasance daga cikin laluri na rashin sani"
Furucinsa lokaci guda suka samu damar ɗinkemin bakina daga faɗin wani abu,ganin Shurun danayi yasa yayi wani murmushi mai ƙayatarwa tareda kama hannuna a karo na biyu muka bar wajen. Nikuma nabishi a baya babu ko musu tamkar rakumi da akala.
Tafiya mukeyi babu mai cewa wani komai,lokaci zuwa lokaci nake kallon hannuna wanda ya riƙe ina karanto a'uxiyya a raina,gashi na gagara ce masa yasakeni,gaskiya inada raunin zuciya akan abinda nakeso,gwargwadon yadda zuciyata ke faɗawa a komar sonsa gwargwadon raunin da zuciyar tawa take kasancewa a ciki. Idan hakan yacigaba da faruwa anya bazan faɗa matsala ba kuwa. Har yanzu bansan koshi wanene ba,shin daidai yake da matsayina kokuwa jelar raƙumi ne shi dayayi nesa da ra'bar danake ciki. Ba'azo ma zancen shi ɗan wanne nahiya bane,domin yanayinsa da kuma ɗabi'arsa bayyimin kamada mutanen wannan nahiyar ba,idan kuwa hakanr inna bari zuciyata ta faɗa sonsa daga baya nazo na tarar da cewar ya bace batt a cikin duniyata ya zanyi kenan? Ko dai in...........
"Shin na burgeki ne a lokacin danake faɗa da har hakan yasa kika faɗa mafarkin tsaye Wanda har yanzu baki farka ba? idan kina sha'awar Koyon faɗa mai zai hana mu bar koyon alƙalami mu koma na takobin. Kinaso na fara koya miki"
"Ehh ......"
"To shikenan horo zai fara da misalin ƙarfe takwas na safe,kije gobe kizo da wuri karki makara"
Yanzun ma yana murmushi yaƙare maganar tareda kashe min ido guda ɗaya, zaro ido nayi ina kallon bayansa har ya juya ya fara tafiya. Meee? Wai cewa nace masa,yaushe ne gabobin jikina suka fara bijiremin suna karbar umarninsa ba tareda izinina ba. Kodai asiri yayimin kai Ni Joda.
Kafafuna babu ƙwari na kama hanyar sansaninmu,ina jin yanayin dana shiga har yanzu a cikin jinina,wanda ban taba jin irinsa ba tunda uwata ta haifeni,kama fatar bakina nayi na riƙe inda nasa bakin ya taba. Wani shokin naji zuut hakan yasa na saki ina jijjiga kai tareda mitstsika ido kodai bacci nayi kai tun ɗazun har yanzu ban farka ba.
(Hammar)
Kallon bayanta nakeyi tana tafiya,wani farincikine ya mamaye zuciyata,mallakarta danayi jinake tamkar an mallakamin duniya. Miye laifina,waye zai mallaki irin wannan abu mai daraja batareda yayi farinciki ba. Nazarinta da fikirarta ne suka fara janyoni izuwa gareta,amma kuma sai daga baya na lura cewar ashe surarta da kyan fuskarta ko kaɗan suma ba baya bane, ko kaɗan bana gajiya da kallon yanayinta idan tana cikin shauƙin so na,shiyasa nakeyin duk wani abu dazai sa nakalli wannan yanayin a cikin ƙwayar idonta. Amma nakula yin hakan danakeyi ba iya ga ita kaɗai yake shsfaba hadda ni. Domin a iya kwanaki ukunnan wani irin danƙon soyayyar ta ya mannewa zuciyata,ta yanda inna tashi da safe bana jina a sukuni idan ba nayi ido huɗu da ita ba,kunnuna sun saurari muryarta,sannan fata ta taji tata fatar a jikinta. Nima abinda nake tsoro shine kadda rayuwata ta zama saba da ita ta yanda rayuwa ba ita zayyimin matuƙar wuya kokuma ma ta gagara. A baya da bata a matsayin mallakina banajin hakan dangane da ita,amma yanxu abubuwan da zuciyata take bijiromin dasu wanda ban taba aikatawa ba akanta sunada matuƙar yawa. Saidai banason ko kaɗan hakan yakasance tsakani na da ita. Domin wannan baya daga cikin abubuwan da suka sakani mallakarta. Taba fatar bakina nayi,ni kaina nayi mamakin ganin kaiwa bakina danayi izuwa ga nata,a lokacin zuciyata ce ta rinjayi tunanina,bana kallon komai a gabana sai ƙananun labbanta masu ɗauke da zane mai kyau tamkar su suka zana kansu. Da ƙyar nima na boye nawa yanayin,nasan da tana cikin nutsuwar ta da tuni da fuskanci halin da nake ciki. Kasancewar nima shine karo na farko a rayuwata dana taba kaiwa bakina kan labban wata ƴa mace,mutane da dama gani suke kaman Ina fakewa a boye ana kaimin ƴan mata ganin bana kulasu a zahiri,Fasihmman da akasan jinin ƴan sarauta da ƙarfin mazantaka,sannan kuma da son mata. Saidai sabanin tunaninsu tunda nake babu wata mace dana taba jin irin wannan yanayin gareta kamar yanda nakeji akan wannan baiwar. Ni kaina mamakin kaina nakeyi,idan wani zaice min zan shigo uwa duniya na faɗa soyayyar baiwa bazan taba amincewa da furucinsa ba,sai gashi hakan ya faru dani,ji nake kamar mafarki nakeyi ba zahiri bane. Da waɗannan tunane tunanen nasamu bacci barawo ya ɗaukeni,wanda nasan itama dole sai tayi tunanin baƙon yanayin daya kasance a tareda mu.
Wani irin mungun razana nayi tareda tashi zaune,gumin dayake fuskata na fara sharewa Jin abu ya tashi tsaye a gabana yasa na kai hannu,sai kuma naji na taba wani abu mai damshi,da alama wani abu na fitar kenan. Ɗaga kaina nayi ina kallon ɗakin har yanzu duhune da alama ko sallar Asuba ba'a ƙiraba,Numfashin danake saukewa da ƙarfine yasa Fasih tashi zaune daga kan shimfiɗinsa wanda yayi a ƙasan gadona. Fitilar aci bal bal ɗin dake ɗakin ya kunna,Jan hasken ya gauraye Tsakanin mu nan take.
Ƙaremin kallo yayi,ganin bana riƙeda ƙirji yasa yagane cewar ba ciwon zuciyata bane ya tashi. Yana so ya tambayeni amma yana shakkar yin magana. Nima ganin halin dayake ciki kaman mai son magana amma kuma yagagara yi yasa nayi saurin ce masa.
"Karka damu ba ciwon ƙirjina bane,kawai nayi mafarkine wanda ya razanani amma babu komai"
"To barka tunda ba ciwo bane, mugun mafarki addu'a yakamata kayi ranka ya daɗe ba......"
"Waye yace maka mugun mafarki ne,mafarki ne wanda ban tabayinsa ba a rayuwata a sai yanzu, inajin labarin maza sunayinsa a lokacin da suka shiga shekarun mazantaka amma ni ban tabayi ba,sai yanzu yazomin hakanne yasakani cikin Yanayi mai wuyar fassaruwa"
"Yallabai inna fahimci maganar ka kanaso kace baka taba mafarki da wata mace ba sai a yau?"
Ɗaga masa kai nayi batareda nace komai ba,lokaci guda naga kalli tsagwaron mamaki akan fuskarsa.
"Hakan yana nufin baka tabajin wani abu dangane da wata mace ba a baya Kenan yallabai? "
"Hakane fasih babu wani abu daya taba tsirgamin a zuciyata dangane da wata ƴa mace,su da maza bana rabesu sosai. Wasu gani suke kaman ina kebewa da mata tunda bana kulasu a boye,amma ba haka bane,dama banajin komai dangane dasu ne shiyasa rayuwata ta ginu a iya karatu da yaƙi kawai"
Kallon tausayi nakalli yanamin,har ya buɗe baki zaicemin wani abu nayi saurin katseshi,ni bansan ma mai yasa na faɗa masa kodan banida wanda zan tattauna hakanne dashi?
Bazai ka faɗa ba dama nasan banida lafiya a lokacin,rashin sanin ta ina zan fara yasa na tattara lamarin na watsar,tunda bai tabani ta wata siga na cancanta ta namiji ba a bayyane yasa ban damu da hakan ba,saima na ɗaukeshi a matsayin babbar dama da zan maida hankali na iya ga abinda zai kaini ga matakin nasara."
"To amma yallabai ai ya kamata ka nemi magani,namiji kam babu iya tarawa da mace ai ba namiji bane Fasihmman da akeso ya zama sarki Mai haifar da zuri'ar da zasuyi mulki anan gaba, amma koba komai alhamdulillah tunda ka warke wanda yayi maka kuma Allah ya maidashi kansa.....ohh mutane yanzu ba imani, in ba haka ba mai ruwanka da Ma***kutar mutum in ba zalunci ba"
Shuru nayi ina jinsa yana sambatu,ganin bazayyi shuru ba yasa na tashi na bar masa ɗakin izuwa waje. Kallon sararin samaniya nake yanda taurari sukayi haske sosai tamkar zasu faɗo ƙasa,mafarkin danayi ne yake dawowamin daki daki,ni kaɗai nayi wani murmushi dana tuna yanda nake sarrafata a Lambun da muke yawan zaman. Yanayin yayi daɗi sosai daya zamto kuma mu kaɗaine a duniyar. Wannan mafarki yayi nutso cikin raina,banajin har kasa ta rufeni zan manta da wannan marfaki a cikin raina.
Sadi-sakhna ce ✍🏼
Comment
Like
Share
Follow