16
Chapter 16
Gida ne babba dake ɗauke da madaidaicin parking lot da aƙalla zai ɗauke motoci biyu zuwa uku, ko ina na gida shinfiɗe ya ke da interlock a ƙasa, ba laifi an ƙawata gidan daga wajensa har ciki iya gwargwadon masu hali.
Yaron gidan mai baiwa flowers ruwa shi ya masu iso ciki kana ya wuce sama don sanar da Hajiya, kai tsaya Nazli ta nufi kujera za ta zauna Turai ta ja hannunta da sauri cikin ƙasa da murya ta ce. "Kai me haka kike shirin yi ba ki san basa son ana zama masu kan kujeru ba?" To ba kowa ke da wannan girman da zai zauna a kansu." Mamaki fal fuskar Nazli ta yi mata wani duba na bata gane ba? "Su fa masu gidan nan basa son a na zama masu kan kujeru haka nan duk zuwa na a ƙasa na ke zama, yanzu sai ki sa a kore mu aikin ma ki rasa shi baki ɗaya." Turai ta ƙare maganar tare da neman waje a ƙasan carpet ta zauna ba tare da ta bi ta kan Nazli da ta yi kasaƙe tana jin ikon Allah, to idan ba'a zauna kan kujeru ba kan me za'a zauna? To me ma anfanin su idan ba za'a zauna a kansu ba ai ko dan decoration a ka jera sai an zauna.
Ta girgiza kai cikin mamakin halan mutanen gidan ta nemi wuri ta zauna a ƙasan carpet ita ma suna zaman jiran fitowar masu gidan. sun fi minti 20 a palon amma shiru kake ji ba wanda ya fito ya ce da su ku ci kanku. Tun Nazli na ɗaga kai tana kallon agogo har ta soma gajiya da wannan zama, ta ja tsaki ta tare da miƙa ƙafafunta jin yadda suka riƙe saboda zaman da ta yi. "Anya akwai mutane a gidan kuwa?" Shiru tun ɗazu babu wanda ya kawo labarin mu." Ta yi maganar cikin haushin barinsu su ƙadai haka kamar waɗanɗa ba su da galihu, ai ko ba komai ɓakon ka annabin ka amma gaba ɗaya an share su kamar ba'a san da zuwan su ba.
Turai za ta yi magana kenan suka ji motsin saukowa, cikin ƙasa ƙasa da murya ta ce. "Kin ga ma ta fito."
Dai dai lokacin da Hajiya Binta ta ƙarasa sauƙowa cikin taku ɗai–ɗai ta shiga palon da izza da taƙama ta zauna kan kujera cikin harɗe ƙafafu ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.
Sama–sama take ma amsa gaisuwar su sai wani yatsine–yatsine take da fuska kamar wanda ta ga kashi, Turai ta gyara zama tare da nuna Nazli ta ce. "Hajiya dama ƴar aikin da kika nema ce an samu na kawo ta ki ganta idan ta yi dai–dai ra'ayinki." Sai a lokacin Hajiya Binta ta kai duban ta kan Nazli daga sama har ƙasa ta ke ƙare mata kallo, duk da a cikin hijabi take hakan bai hana ta ganin diri da tsantsan kyawun halittar ta ba, take kuwa zuciyarta ta motsa cikin ɗaure fuska ta ce. "Turai ki ke ko wa?" In ce ƴar aiki na ce ki nemo min ba wacce za ta zo ta kwace min miji ba, ke yanzu da hankalin ki da tunanin ki za ki kawo min wannan zangaɗeɗiyar yarinya da sunan me aiki?" To ni tsohuwa na ke so ba yarinya kamar ta ba." Ta faɗa hakan ne cikin wurga ma Nazli kallo, cikin razana da kalamanta Nazli ta ɗago ai kuwa carab idanunta ba su faɗa a ko ina ba sai na cikin Hajiya Binta da ke cikin ƙare mata kallo da kyau zuciyarta na ƙin amincewa da yarinyar, ko ita da ta ke mace sai da ta ƙyasa da kyawunta bare kuma namiji haka kawai ta je ta ɗauko ruwan dafa kanta yarinya ƙarama ta zo ta ƙwace mata miji da sunan aikatau.
"Afuwan Hajiya amma tsohuwar bata samu ba duba da yadda kika matso da yar aikin ya sa na kawo ita wannan ɗin kafin a samu wacce tai daidai ra'ayinki, in sha Allah ita ma wannan ba za ki kuka da ita ba yarinya ce mai hankali da nutsuwa ga ta da son aiki kamar me, in Allah ya yarda sai kin ji daɗin zama da ita, maganar kwacen miji ma bata taso ba abun da ya kawo shi za ta yi ta koma."
Ɗan jim ta yi kamar me nazari kana ta ce. "Zan ɗauke ta aiki amma da sharaɗi, sharaɗina a nan shi ne ba za ta na zuwa min haka kai tasya ba, duk sanda mijina zai kasance yana gari to dole ne ta saka hijab da kuma niƙab, kai ban so ko kusa na ganta a inda yake duk inda ta gansa to ta kau da kai gefe kar ta sake ta bari ya ganta har ya samu damar ganin fuskarta. Idan ta kiyaye wannan to zamu zauna lafiya akasin haka kuma ba zai mana daɗi ba." "Ai kar ki damu Hajiya ba ma za ta kai ga haka ba in sha Allah za ki same ta da bin dukkan dokokin da kika gindaya ba za ta tsallake ko ɗaya a ciki." Hajiya Binta ta kaɗa kai cikin gamsuwa da kalaman Turai ta ce. "Sai kuma abu na gaba, bana son wasa da aiki, ki faɗa mata dole ne ta maida hankali kan aikin ta bana son shiririta da ƙazanta please a dinga tsabtace jiki kafin a zo." Iya ƙuluwa dai Nazli ta ƙulu ta cika ta yi fam jin renen hankalin da ta zo da shi, nufin ta wari suke ko me? Saboda baƙin ciki da takaicin wulaƙacin matar ko amsa bata yi sai Turai ta ce. "Ai kar ki damu in dai maganar tsabta ce kam ba ki da matsala ita ɗin ma akwai tsabta bata son datti ko kaɗan." Hajiya Binta ta taɓe baki da faɗin. "Ya sunan ta?" "Nazli." Nazli ta amsa ta a taƙaice. "Nice name."
––––––––
Tun da suka bar gidan Hajiya Nazli ke tunani tunani ita dai a gaskiya ta ji aikin ma ya fita a ranta bata san me ya sa Turai ta amsa mata ba ma amma da ra'ayin kanta ne da ba za ta ƙarbi aikin, amma gudun watsa mata ƙasa ido ya sa ta ƙarbi aikin ko dan yadda ta ga ta tsaya mata har ta samu aikin ya sa kawai ta haƙura ta barshi kan Allah ya sa hakan shi ya fi Alkairi, za ta riƙe aikin ta tattale sa har zuwa ranar da Allah zai kawo mata wanda ya ya fi shi.
Koda ta isa gida bata nunawa Ammie wata alamar komai ba illa samun aikin da ta yi, Ammie ta ji dadi sosai tare binta da add'uar fatan alkairi bayan nasiyoyi da jan kunne da ta yi mata kan aiki a ƙarƙashin wasu. A yadda suka tsara daga gobe za ta fara zuwa aikin da safe da ta gama ayyukan ta za ta koma sai dai idan da wani abu, aikin ta iya kitchen ne girki da kuma wanke wanke a wata kuma za'a biya ta dubu 20 wanda a ciki ta cire dubu biyar da za ta ba Turai da ta nema mata aikin. Duk da ba ta farin ciki da aikin hakan bai hana ta zumuɗin zuwan gobe ta fara zuwa aikin ba.
=======
Washe gari tun asuba da ta tashi bata koma bacci ba, bayan taimakawa Ammie ta karya ta shiga wanka. Sharp sharp ta shirya tsaf cikin dogon hijabin da ya kai mata har ƙasa, lokacin har tara saura cikin sauri ta gama shiryawa ta fita Ammie ta bata kuɗin napep ta fita.
Minti 20 ya kaita gidan, ta samu har lokacin ma ba su tashi a bacci ba. Dama already tun jiya Hajiya ta nuna mata ko ina na gidan daga kan store har kitchen da inda komai ke adane sai da ta nuna mata, tunani ta soma na me za ta dafa masu na breakfast don Hajiya ta ce tana son komai ready kafin ta tashi a bacci kuma yara na zuwa school, dan ma yau weekend babu zuwa makaranta.
Ƙarshe doya da egg source ta yanke shawarar haɗa masu tunda Hajiya bata ba ta memu ɗin me za'a dafa ba, sharp sharp kuwa ta jawo doya ta soma ferewa nan da nan ta kama aiki kan ka ce me har ta gama ta haɗa ruwan shayi da ya ji kayan ƙamshi, ta jera komai kan dinning ta koma kitchen ta tsaftace ko ina ta haɗa wanke–wanke ta yi mopping kana ta koma palon ta yi zaman fitowarsu.
Tana zaune har 10:28 Abla da Araf suka fito daga ɗaki, yara ne kyawawa. Abla ita ce babba ƴar shekara goma sai Araf ɗan 7 years. Straight dinning suka nufa suka zauna ba tare da sun yi mata kallo na biyu ba suka watsar, jikin Nazli ne ya yi sanyi da ko in kula da suka nuna mata amma hakan bai hana ta tashi ta bi bayan su ba. Buɗe coolers Abla ta yi cikin yatsine fuska ta ce. "Iyiwww! What's this?" "Yam and egg source." Nazli ta bata amsa, tana cikin ƙoƙarin serving na ta Abla ta tura plate ɗin da