Halimatus’sadiya (sakayya)

2

by @102565813543784586917

Bismillahir rahamanir Rahim_________


9:45pm

“Ammi! Ammi! Ammi!


Muryar yarinya yar shekara 8 da ke kiran mahaifiyarta daga waje har ta karaso ciki.


Ammi da ke parlour zaune saman carpet din parlour ita da Fatima mai shekara 4 ta na tayata homework ta dubai ta tare da tambayarta.


“Siyama lafiya ki ke kwala min kira tin daga waje?


Siyama ta zauna bisa carpet din ta na Hucin gudu ta ce “Abi ya ce mu shirya za mu fita, Ammi a dauko min kaya.”


Ammi ta ce “Ba kayan da za ki chanza.”


Siyama ta mike tare da cewa “Allah ni dai sai na chanza.” Ta wuce ciki.


Fatima da ke kwance saman carpet ta na wasa da pencil Ammi ta ce mata “Oya stand up let continue.”


Ta ce: “A’a sai mun dawo.”


Ammi ta ce: “Ki na so aunty ta duke ki, maza tashi kiyi.”


Kafar ta ta dora daya bisa daya ta ce: “Ammi da mun dawo zanyi.”


Fatima ba ta tashi ba har sai da Ammi ta ce za ta bata sweet sannan ta tashi suka cigaba da assignment.


Siyama dakin su ta shiga ta budai wardrobes din ta ta zubdo kayan ta duka sannan ta dauko olive gown. Ta aje bisa gadon ta sannan ta budai chest of drawer nan ma ta fiddo duka headband da hulunan da ke ciki ta na neman headband din ta ba ta gan shi ba. Ta koma wurin gadon su. 


Gado biyu na yare ke jera a dakin kowan ne da side drawer. A dayan gado nan ma wata yarinya ce kwance ta na bacci sai dai ta dara siyama da shekara 5.


Siyama ta fara jijigata ta nace mata ta tashi. Bata ta shi ba har sai da ta ji Abi zai fita da su da sauri ta tashi zaune.

Siyama ta ce “Yaaya ina ki ka aje min headband di na?


Qawwama ta ce "Ki du ba." Ta na karasa maganar idanuwanta suka fada kan kayan da siyama ta zubdo ta fara mata fada;


“Siyama wai ke miyasa ba ki abu cikin nitsuwa ji yan da ki ka zubda kayanki dazu na gama gyara dakin.”


Siyama bata damu ba ita dai ta headband din ta ta ke"Ni dai ina headband di na?


Qawwama ta ce: “Ya na bisa kai na zo ki dauka, mtssww.”


Ta mike za ta shiga toilet dan ta wanke fuskar ta Ammi ta shigo. Ta na shigowa qawwama ta ce: “Ammi ni nagaji ko 30 minute ba a yi ba da na gyara dakin nan wannan yarinyar ta zo ta zubar da kayan ta.”


Ammi ta dubi siyama fuskar ta ba yabo ba fallasa jira kawai take a fadi magana ta maida. Ammi ta ce: “Siyam wai miyasa ba ki jin Magana?


Ta ce: “Ammi headband di na fah na ke nema.”


Ammi ta ce: ‘Ba ki iya neman shi cikin nitsuwa ke ko mi sai kin yi na rishin hankali. Maza ki maida kayanki ki gyara dakin.”


Ta dubi qawwama ta ce mata “Za ku fita da Abi ki nemo kaya masu kauri ki sa wa Fatima.”


Qawwama ta amsa mata da toh ta shige toilet.


Ammi ta cewa siyama da ta gyara dakin. Ta wu ce. Ta na fita siyama ta cigaba da neman headband din ba yanda ta iya ta hukura da kayan ta dauko English skirt and blouse ta sa. Ko da qawwama ta fito ta mata Magana ta yi banza ta kyale ta. 


Qawwma ta kyale ta ta shirya kanta da Fatima. Ta na gamawa ta dauki wayar ta ta kira Abi.


Abi na majalissa ya ga kiran ta ya daga. Yana dagawa ta ce; “Abi mun shirya.”


Abi ya ce: “I’m coming be ready.”

Ta ce: “We are.”

Ya ce: “Okay I will be there.” Ya yanke kiran ya mike yayiwa abonkan sa sallama ya shiga mota ya koma gida.


Suna jin horn din sa da zumudi kowannan su ya bar dakin. Ko da suka fito ba su iske Ammi ba Fatima da Siyama suka wuce, Qawwama kuma ta koma ta shiga dakin Ammi ta re da yin sallama. Ammi ta amsa ta.

Ta ce: “Ammi we are leaving.”


Ammi ta ce: “Sai kun dawo take care of your sisters.”


Qawwama ta ce; “Okay, Ammi mi zan tawo maki da shi? 

Ammi ta yi siririn murmishi tare da ce wa “Ko mi ma.”


Qawwama ta ce: “Ok bari na je kar mu makara.” Ta juya ta fita.


Ta na fita waje ta ga siyama a gaban mota ta zagaya wurin Abi. Abi ya sauke Window din ya ce shiga mu je.


Ta tsaya a wurin bata da niyar shiga ta ce: “Abi ka ce wa yarinyar nan ta koma baya.”


Murmishi yayi ya kalli Siyama da ta daure fuska ya ce: “Mamana ko ma baya ki bar wa Yaaya gaba.”


Siyama ta ce "but Abi.. shike nan. " 


Abi ya ce "Good girl." Ta koma baya ba tare da ta fita ba Qawwama ta zagaya ta budai ta shiga.


Yayi wa mai gadi horn ya budai gate din suka fita… 


ALBAIK 

A nan Abi yayi parking motar shi, suka fito bayan sun fito ya dauki Fatima, a dayan hannun siyama ke rike da yatsun shi. Su ka shiga ciki suka zauna a table of 4. Waitress din wurin ta kawo mashi menu  ya mika wa Qawwma ta zabi abin da ta ke so sannan ta mikawa siyama  ita ma ta zaba sai ya tambayi Fatima  mi ta ke so. 


Bayan wasu Mintina waitress ta kawo masu abin da suka yi order. Su ka ci su ka sha. Sun gama za su fita Qawwma ta tuna da mahaifiyarta ta ce:"Abi zan siyawa Ammi meatpie.


Ya ce:"Ok dare, ki samai mu a reception. Suka wuce ita ma ta je ta siyo meatpie biyu Abi ya biya duka kudin sannan  suka wuce gida.


11:05pm

Suna dawo siyama da fatima suka wuce daki, Qawwma kuma ta wuce kitchen  ta sa 2 meatpie din a fridge sannan ta koma dakin su. Abi ma ya wuce na shi.


Suka chanza kaya zuwa na bacci. 

Siyama na kwance bisa gadon ta ta na playing video game Qawwma ma tana kwance bisa nata gadon tare da waya a hannun ta na kallon reals sai Fatima dake bacci a gefan ta. Ammi ta shigo.


Qawwma ta tashi zaune tare da cewa “Ammi I think you have slept."


Ta karaso kusa da su ta tsaya a taskanin gadon siyama da Qawwma ta ce: “A’a ban kwanta ba.” 

Ta ida maganar ta na duban siyama dake kwance bisa gadon ta ta na playing game da ipad din ta, ta ce “Siyama a bar wa gobe kashe ipad din nan ki kwanta.”


Kallon Ammi ta yi tare da turo baki ta ce “Ammi ba fah najin bacci.”


Ammi ta ce “Eh kashe ta 11 ba ku kwanta ba sai gobe a Dinga fama dake wurin tashi.”


Ta zunburo baki ta kashe ipad din ta aje ta sannan ta ja blanket ta rufe duka jikin ta.


“Ammi your meatpie is in fridge.” In ji Qawwma.


“Thanks but sai da safe zan ci.”


Sanyin da dakin ya dauka hakan ya sa Ammi ta kalli ACn dakin da ke kunne ta ce "Qawwma miyasa ba ku ji? 


Ta sauke idon ta bisa qawwma da ta aje wayar ta tana azamar kawncya. “Ga AC ga fanka sai sanyi ya maku illa."


Ta ida maganar tare da daukar remote din ACn ta kashe ta ta na cewa “Akwai sanyin damana ba zafi a ke ba.” ta wuce har ta kai kofar dakin ta ce da su “don’t forget to pray.”


Qawwma ta amsa mata “Okay Ammi good night.”


Ammi na fita siyama ta jawo ipad din ta ta cigaba da game din ta ko da Qawwma ta mata Magana ta ce mata ban Ruwan ta. Qawwma ta masu addu'a ta kwanta ta kayale ta.


Ammi ta na barin dakin ta shiga dakin Abi ta yi sallama ya amsa.

Zaune yake kan sofa ya na duba wasu files idon sa na kan su ya tambaye ta “where are the kids?


Ta amsa shi sun yi bacci

“Good.” Ya fadi ba tare da ya dago ya kalle ta ba.


Ta zauna a gefan sa ta na kallon sa ta ce “Habibi ba ka tunanin fita da yaran nan da dare zai shafi makarantar su also su mata ne bai kamata ka saba masu da fitar dare ba ga kuma mutanaen unguwa.”


Hannu ya sa ya dagatar da ita ya dago ya kalle ta ya ce “They are young, let them enjoy their life daga wannan stage din ba za su kara samun time da za su yi enjoing time din su ba.”


Ta ce : “Duk da haka at least sau biyu a sati, but almost every day sai ku fita.”


Files din da ke hannun shi ya ajje ya dubmbe ta tare da ce wa “:Look habbiti don’t upset me, a bar su su ji dadin su. I want to spend a lot of my time with my kids da sun daga ni ma na tsufa shike nan fah, ahh ki ma dai na wannan maganar. I need time to laugh and play with my kids. Yan unguwa nobody have the right to question me. So dan Allah mu ma bar maganar nan.


Ganin bai da niyar saurarn ta ta mike tare da ce mashi sai da safe.


Ya ce "Okay, good night and tight sleep."


Ta fita ba tare da ta ba shi amsa ba ya cigaba da masifar shi “a kyale ni na ji dadi na shakata da yarana, uban su na da kudi sai abar su ji dadi. Haba duk an bi an saman ido. Mtssww ko ina Ruwan mutane da rayuwar sai shegan sa ido.


Washegari da Asuba ya shiga dakin su Qawwma ya tada su sallah sannan ya leka dakin matar shi duk da ya san ta tashi amma dabi’ar shi  ce kafin ya tafi sai ya tabbatar da dukkan su sun tashi musanman siyama sai ya ga ta shiga toilet ya ke fita. In ko Abi ba ya gida Ammi ta dinga fama da ita wurin sallah dan duk sangantar da su da yake da anzo maganar sallah Siyama ta san ba wasa a wurin Abi.


Ta na gama sallah ta koma ta kwanta. Qawwma kuma sai da tayi karatu rana na fitowa ta tashi ta shiga ta wanke toilet din su as usual, tayi wanka sannan ta tada Fatima ta mata wanka ta shiryata. 


Ammi kuma na kitchen ta na shirya masu breakfast da kuma abincin da za su tafi da shi. 


Qawwma ta shigo kitchen din Ammi ta tambaye ta idan siyama ta tashi.


Qawwma ta ce: “Na ta da ta kin san halin ta.”


“Allah ya shirya mi ita.” Ta furta ta na rinsing hannun ta da ta gama soya masu irish. 

Sannan ta kara da "Zo ki soya maku eggs din sai ki zuba  maku ke da Fatima bari na tada ta.”  


Qawwama ta amsa da “toh.” Ita kuma ta fita daga kitchen din ta wuce dakin su dan tada siyama wadda duk safiya sai anji su da Ammi.


Karasawa ta yi kusa da siyama dake kwance ta rufe jikin ta da duvlet. A hankali Ammi ta janye duvlet din ta na tapping din ta. "Siyam, siyam wake up you are gating late."


A hanakli ta budai idon masu nauyin bacci ta juya ta re da ce "Ammi please ki bari na Kara one minute.”


Cimaka Ammi ta dauke ta ganin ba ta da niyar tashi ta na ce wa daman baki kawanciya da wuri dole ki kasa tashi. 


Siyama kam lafe kanta tayi bisa kafadun Ammi ta na son cigaba da bacci. Ammi ta budai toilet din ta shiga ta aje ta cikin waterbath ta shiga cire mata kayan baccin ta.

Tura baki Siyama ta yi ta na ce wa "Ammi da kai na zan yi."


Ammi ta ce "Miyasa ba ki tashi da wuri ba."


Ammi na gama cire mata kayan siyama ta sa mata rigima ita ta girma da kan ta za ta yi.


Ammi ta ce "No za ku yi late din zuwa makaranta."


Ruwan dake cikin bucket Ammi ta fara zubaww siyama ajiki.

Siyama ta dau sponge din da sabulun da sauri ta nace wa "Ammi ki bar ni na yi na fah iya."


Ammi ta ce "Two minute ki gama ki yi brush if not zan shigo na miki." Da haka ta wuce ta bar dakin siyama kuma ta fara wanka.


Da sauri tayi wankan dan kar Ammi ta shigo ta mata ta na gamawa ta yi brush ta fito ta shirya cikin uniform din da Ammi ta fiddo mata dan in har ba a fiddo mata uniform fa zata lallata wardrobe din musanman ta socks.


Ta shirya ta fito ta iske su Qawwma na breakfast. Ammi kuma na zaune a kujera ta mike kafa. Ta karaso ta ja kujera ta zauna ta fara taking breakfast. 


Qawwama kuma tana gama ci ta koma ta gyara dakin na su. Ammi kuma ta shirya masu lunch din su suka fito waje dan already Adamu ya fidda motar waje Yana jiran fitowar su. 


Qawwma ta kama hannun Fatima tare da ce wa "Ammi mun tafi."


Ammi ta ce "Sai kun dawo Allah ya kiyaye." Suna fita parlourn Ammi ta kira Siyama tare da tambayar ta mi ta ke yi a dakin ta fito suna yin late."


Siyama tayi shiru dan hankalin ta na kan Verbal assignment din da ta ke yi cikin sauri.


Qawmma da Fatima suna cikin mota wasu jeren yara guda dauke da irin school uniform din su, su uku su ma suka fito daga gidan da ke jinki gidan su Wanda komi iri daya ne ba banbanci.


Qawmma ta budai masu motar baya tare da ce wa "We are the first."


Farhin ta shigo tare da ce wa "Don't be so happy cos is once in a while also siyama bata fito ba."


Qawmma ta rufe kofar mota ta ce "You know siyama da shiririta. She is always late."


Maza biyun da suka fito tare da farhin zaid da fauzan suka zauna gidan gaba.

Suna zaune cikin mota suna jiran fito war siyama. 


Ammi jin shiru yayi yawa ta mike ta shiga dakin na su ta iske ta ta na assignment ta ce "Ba ki isa ba." Ta karasa kusa da Siyama ta amshe pencil din hannun ta tare da janye littafin ta nace wa "Jiya ba ki yi assignment ba sai yanzu.


Siyama da ta maraice ta ce  "Please Ammi wlh aunty will flog me."


Ammi ta ce "Gwara ta bige ki gobe ba kin kara kin yin assignment ba."


Ta ida maganar ta na zipping din jikar. Ta ja hannun ta Siyama na mata magiyar ta bar ta ta gama ta kusan gamawa amma Ammi bata saurare ta ba har sai da ta fito da ita wurin gate ta ta sa mata jikar a bayan ta ta n ace wa "Be a good girl stop this bad attidue of yours." Maza je ki suna jiran ki. 


Ta tsaya ta na kallon aminta. Ammi ta ce "Go Siyama kar rai na ya ce before I count 3. Ammi ta daure fuska ta fara counting daga 1. 


Siyama ta fita ta bar gidan ta na isa motar ta d…