3
Mai aikin ta Jamila ta zo suka gyara gidan a ka yi abinci sannan ta wuce. Ita kuma ta koma daki dan ta mike ta huta dan da su Siyama sun dawo ba sauran hutu garai ta.
Ta na cikin bacci ta ji hayaniya, a hankali ta budai idon ta wanda bacci ya rufe su dan baccin bai dadai da daukara ta ba. Ta tashi zaune tare da kokarin budai idon ta gabaki daya ta na korar baccin. Ta sauka daga kan gadon ta fito parlour. Iske Fatima tayi ta na bin Siyama a kan kujera da ta bata baby doll din ta.
Ammi ta karaso wurin tare da ce wa "Ku da kun dawo gida shi ke nan babu wani sauran nitsuwa."
Fatima na jin muryar Ammi ta wuce wurin ta ta na kuka ta na ce wa "Ammi tell her to give me my baby doll."
Ammi ta dubi siyama da ke tsaye bisa kujera ta ce "Siyam oya give her back, ina ta ki ta ke?
Siyama ta kara rike baby doll din ta ce "Ammi wannan ta wa ce, is not her own."
Fatima da ke kuka ta ce "Lier is mine not yours."
Tsale tayi ta sauko kusa da Fatima ta kai mata duka. Fatima ta kara fashe da kuka. Zata ruga Ammi ta janyo ta tare da amshe baby doll din ta ce "Ta ki ba babba ba ce?
Siyama ta turo baki ta na kokarin janye hannu ta daga rikon da Ammi ta mata. a lokacin Ammi ta dubi parlourn yan da suka hargitsa shi ta ce "Ban ce ma ki da kun dawo ki dinga maida komi in da yake ba didn’t I told you. "
Ta karasa maganar cikin tsawatarwa. Pick your school bags and lauch bag.
Ta saki hannun na ta ta koma ta zauna kan kujera fatima ta biyo ta ta zauna a gefen ta ta na kuka. siyama tayi tsaye wurin ta na hura hanci.
Ammi ta kara mata Magana "Ba Magana na ke mik ba."
Ta zunburo baki ta durkusa ta dau lunch bags din su ta kai kitchen Ammi ta bita da Allah ya shirye ki. Sannan ta koma lallashin Fatima. Sannan ta cire mata uniform ta wuce da ita dakin su ta mata wanka ta sa mata kaya ta dau comb da kibiya su ka koma parlour.
Ta kunna mata cartoon sannan ta fara mata tsifa domin Fatima in ta na kallon cartoon kamar wadda a ka cire wa komi na ta gangan jikin ta da ran ta duk za su koma kan cartoon din.
Ta na tsife mata na biyun ta kira siyama. Siyama da ke playing game ta turo baki ta sauko da ga gadon ta wuce parlour tare da wayar a hannun.
Ammi ta ce mata ta dauko mata school bag. Ta koma dakin na su ta dauko mata.
Ta ce ta ba ta ipad din.
Ta taka baya ta na ce wa "Ammi ki yi hkr."
Ammi ta ce "Kar ki bari in tashi, zo zauna ki yi assingment din yau."
Ta na playing game din ta ce "Ammi yau ba a ba mu ba."
Ammi ta ce "Mai karya?
Ta amsa ta "Dan aljannan.” Dan ta san an ba su assingmebt din, ta kara da "Ammi da na dawo daga islamiya zan yi promise."
Ammi ta ce "Kar mu bata maza ki zauna ki yi assignment din ki ko kuma na yi seizing ipad din."
"Ammi in.."
Ammi ta kaste ta "Zan fa za ne ki."
Ba arziki ta aje ipad din dan ta san tabbass ammin ta za ta iya seizing wayar kuma ko da ta fadawa Abi ba abin da zai yi mata. Ta fiddo assignment din ta fara yi, ta nayi ta na tashi ta na wasa har dai ta gama.
3:20pm
3 a ke tada su Qawwma zuwa 3:20 sun dawo gida. Ta yi sallma ta shigo suka amsa. Ta karaso tare da tambayar Ammi "Ammi salon za mu?
Ammi ta amsa ma ta da "Eh."
Siyama da jin haka sai murna ta ce "Yau ba zamu islamiya ba."
Ammi ta ce "Sai kun je."
Da jin haka ta bata rai ta cigaba da playing game din ta.
Qawwma kuma ta wuce da ki ta cire uniform din ta ta yi wanka ta sa wandon iislamiya da top. Ta fiddo wa sauran na su sannan ta kwada dakin dan ba ta kaunar ganin kaya a daki.
Ta fito ta nufi kitchen a kofar kitchen ta tsaya ta kira Ammi.
Ammi da ke parking kan Fatima ta amsa ta.
Qawwma ta ce "Ammi kin ga yanda suka mi ki da kitchen."
Kafin ammi ta yi Magana Siyama ta ce "Ba ruwa na Fatima ce."
Ammi ta tambayi Qawwma mi su ka yi.
Ta karaso ta na ce wa "Manja suka zubar."
Fatima da idon ta na kan tv ta ce "Siyama ce."
Siyama ta ce "Karya ne ke ce ki ka zubar da shi."
Ammi ta dagatar da su dan yanzu ya koma fada ta ce wa Qawwama ta goge shi.
Qawwma ta ce "Ammi ba ki dukan su that why they do all what they want." Ta juya ta koma kitchen ta goge man sannan ta zuba abinci ta ci a nan dining.
Bayan ta tsince ma Fatima ta tsince na siyama duk da ana yi ana fada har loakcin islamiya yayi.
Qawwma ta shirya kanta da Fatima, ta ka ma a ka ida tsincewa siyama Ammi ta sharce mata shi ta daure.
Qawwma da Fatima suka fita waje kamar dai da safe suna cikin mota suna jiran siyama sai dai in za a islamiya siyama da Fauzan are always late.
Bayan sun dawo ko shigo da motar driver bai yi ba Qawwma ta shigo ta kira Ammi, su Farhin kuma suka shiga gidan su. Ammi ta fito ta amsa key din motar wurin Adamu ta shiga ta tada motar suka wuce salon din da suke zuwa.
Kasancewa da maraice ne ba kowa hakan ya sa aka fara da Siyama da Fatima. Da farko Fatima ta ki yarda sai da Ammi ta kunna mata cartoon a wayar ta sannan ta yarda a ka dora ta saman kujera a ka fara wanke mata lausasen bakin gashin ta. Qawwma kuma Ammi ta fara tsince ma ta kai.
Bayan an gama wanke masu a ka fara masu kitso kasancewa masu aikin hudu ne a saloon din so lokaci daya a ka fara masu sai dai duk tsiwar Siyama wurin kitso ba a Magana ta na kuka tana danbe da mai kitson kuma in an gama ta fi kowa nuna gayu da shi.
A takaice sai bayan isha’I wurin 10 a ka gamawa kowa Abi ya iske su a nan daman ya kira Ammi a kan zai zo ya samai su.
Siyama da Fatima suka shiga motar abi Qawwma kuma ta tsaya da Ammi suka wuce eatry su duka dan yin dinner daga nan suka koma gida.
A parlourn shi suka tsaya, suna isa Siyama ta cire hijab din ta tare da ce wa "Abi see my hairstyle. Ta nuna cike da kasaita.
Abi ya ware ido tare da ce wa "Wooo my princesse its beautiful."
Fatima ita da ta fi ta ta hau bisa cinyen sa tana ce wa "Abi mine is more beautiful then her own, see my hena. " Ta karasa maganar ta na nuna masa lellen hannun ta ja da bakin.
Siyama ta ce "Abi da na wa da na ta wanne ya fi kyaum
Abi ya dube dukan su ya ce "Na Yaaya ya fi kyau."
Qawmma da ta zaune a gefen kujera ta bata fuska jin Abi ya ce na ta ya fi kyau ta saki murmishi ta karso kusa da Abi. Siyama kuma ta bata rai.
Qawwma ta ce "Abi na dauka ba zaka yi prising na wa ba." Ta karasa maganar ta na turo baki.
Abi ya ce "Ni na isa Yaaya guda gimbiyar gida."
Ta kara fadada murmushin ta. sai ya fuskanci rain siyama ya baci.
Ya dan mata chakukulo ya na ce wa "Na mamana ma yayi kyau, kowa na shi yayi kyau."
Ya yi kissing din hannun ta sanna na Fatima sai na Qawmma. Sannan ya ce "Is getting late go take shower and sleep akwai school gobe."
Siyama ta ce "Abi wannan school ba a gama ta i'm tired of it."
Abi ya ce "Ana gamata amma sai wanda ya dage, and this time duk wanda ya take first postion he have a gifts."
Qawwma ta ce "Abi you know i'm always first is last term that boy overtake me." Ta ida maganar cikin baccin rai.
Ammi dai kallon su kawai ta ke dan in Abi ya na tare da su toh na ta kallo ne.
Yayi murmishi ya ce "Don’t worry put more effort."
Ta ce "Abi abin haushin ma new comer ne he just join us last term."
Abi yace "Kar ki damu. " Mamana ke kuma ki rage wasa ba na son na biyar din nan put more effort.
Siyama ta ce "Abi karatun ba da di."
Yayi karamar dariya ya ce "Daman karatu bai da dadi, sai an jure a ke cin Moriya by some years you will be proud of yourself." Chop knucle. Ta mika mashi hannu. Fatima ma haka sannan ya ce "Yaaya ku je ayi wanka a kwanta."
Siyama da Fatima suka yi kissing din sa tare da ce mashi good night Abi.
Sannan suka sauka da ka kan cinyarsa. Abi ya ce "Good night my queens pry before sleep."
Suka wuce Qawwma ta ce "Mashi good night."
Ya ce "Good nighrt dear, ki yi wa Kannan ki adu’a." Ta amsa shi da toh sannan ta ce "Ammi good night." Ammi ta ce "Allah kai mu."
Ta amsa da Amin sannan ta wuce.
Ta na fita yayi murmishi cike da farin cikin ganin farin cikin yaran. Sai a lokacin hankalin shi ya dawo wurin Ammi. Ya mike tare da komawa wurin ta yana ce wa "Banga na ki ba ko ba za a nunamin ba." ya karasa maganar cikin zolaya.
Ta dan kauda kai kafin ta ce "Sai yanzu ka san da ni."
Karamin murmishi yayi ya ce "No ina begen ganin adon ki but those kids sai suka dauke min hankali." Ya karasa maganar ya na jawo hannun ta da ta rungumai saman kirjin ta.
Ya dubi tafikan hannun ta da suka zannu da jan lalle har wani sheki yake na daka maroon, murmishi yayi masu bayyana hakora ya jawo gudan hannun ya budai tafin yace "Woooo, this is beautiful desing duk ni kadai. As if I will lick the palm, ya juya zuwa bakin lalle ya ce "Masha Allah." yayi kissing kucles din ta.
Sannan ya dago kan shi ya dan ja cheeks din ta ya ce "Give a smile now." Please...
Ta mashi karamin murmishi ya ce "Ko ke fa."
Sannan ya ce "Your hair ko shima sai na roka toh dan Allah a budai min shi na ga shekin sa."
Ta ce "Ba ka na da hannu ba."
Ya mai da mata "Har sai ma na bata wa kai na lokaci." Ya ida maganar tare da cire chogen da ke kanta.
Wanni zum ya ji a zuxiyar sa gannin yanda a ka yi packing gashin, gashi baki sai sheki yake ya kai hannun sa kasan jelan kashin ya ce "Awwwn wannan duk na ki ne like an Indian hair." Ya ida maganar ya na wasa da jelan gashin.
Ta ce "more than an idian hair."
Ya yi murmushi ya ce"Ko ke fa da kin tsaya my unborn baby ya chanza ki."
Murmishi ta mashi cike da son mijin na ta dan ba karamin dadi ne ba mijin ka ya nuna maka kulawa musanman wurin ado da kwaliya.
They were dalliance, flirting, toying, they had wrangled, by the kids. A hankali ta ambaci sunan Siyama kasance wa signals din da yake aikawa jikin ta wanda suka kashe mata jiki.
Ko a jikin shi ya cigaba da toying din ta. sautin kukan Fatima da ta ji ta yi kokarin tashi yamaida ta tare da tambayar ta "Where are you going?
Qawmma na nan za ta ji da su.
Ta ce"Wancen fadan ya fi karfin ta. Ta karasa maganar tare da kokarin tashi. Ya maida ta a karo na biyu ya mata peck sannan ya ce "Bari na je." Ya sauka daga bisan ta ya bar parlourn shi ya wuce dakin yaran.
Ya na shiga ya iske siyama na fada da Qawwma, ta na ganin Abi ta yi saurin janye hannun ta daga saman Qawwma ta cigaba da kuka.
Ya karaso ya jawo kujerar karatun su ya zauna Fatima ta matso wurin shi ta na kuka, siyama kuma ta zauna kasa ta na kuka. Ya dauki Fatima tare da tapping bayan ta yana tambayar ta "Who touch my darling?
Cikin kuka ta ce "Siyama ce."
Siyama da ke kuka kasa ta ce "Abi she has her own chocolate she picked mine, wai kuma Yaaya ta duke ni dan na duke ta.”
Ta cigaba da kuka
Abi ya kalli Yaaya sannan ya kalli Siyama ya ce "Sai ta duke ki sai ki rama?
Ta ce"Ita ta fara, kuma fah Fatima ta shanye min ita duka."
Ya ce "Naji come here."
Ta cigaba da kuka ta yi zaman ta. Dan ta san fada zai mata dan ya hanai ta da dukan yayar ta in ta duke ta.
Cikin tausansan lafazi ya ce "Zo mamana."
Ta mike ta karaso wurin sa. Ya ce "wipe up your tears."
Ta sa hannun ta goge hawayen ta.
Ya ce "Yaaya ba ta grime ki ba, is she your mate?
Ta girgiza mashi kai.
Ya ce"Ban hana ki dukan ta ba?
Ta na kuka ta amsa "Ka hana."
Ya ce sai kuma ki ka yi
Ta ce"But..
"Shhh! Yayi nuni da yar yatsar shi sannan ya ce"from today ki ka kara daga hannu ki ki ka duki yaaya za mu bata, she is your elder, you have to respect her okay."
Ta gyada mashi kai. Ya goge mata hawaye tare da ce wa "Ok stop crying."
Ta ce "Abi toh ta biya min chocolate di na."
Murmishi yayi tare da ce wa"Mamana ba ki yafiya, she is your young sister."
Ta ce"She has to appolgise to me."
Ya dubi Fatima dake saman sa ya ce "Oya Fatima say sorry to your sister.
Ta ce"Sorry."
Ya ce"Again."
Ta kara maimaitawa.
Ya ce saura ke apologise to Yaaya.
Kamar ba za ta yi ba sai kuma ta ce sorry wadda iya baki ta tsaya. Ko kallon ta ba ta yi ba.
Abi ya ambaci sunnan ta sanna y ace ki na so mu bata??