4
Haka yaran suka tubure su ba za su gidan aunty zulaiha ba duk da akwai jikoki sa’anin su, amma kaf cikin jikikoin ya’an Asif kadai suke shiri shima dan suna jikin gida daya makaranta daya both arabi da boko, sai yan' an Aunty salma wanda su xun girme su, apart from them ba mai yi da su daga masu jin haushin su sai masu masu hassada.
Bayan da Ammi ta iya ta sa ma su ido haka suka ki zuwa kamun
Abin haushin ba su je ba amma har an samu wani munafikin da ya fadiwa Abi ay matar shi ta na nisanta yaran shi wurin yanuwan su, bata so suna intraction da sauran yara gani ta ke yaran ta sun fi na su. Duk da ya gwale wanda ya kawo mashi labarin akan hakan nan ba za su ki zuwa ba, wani uzuri zai hana su zuwa.
Hakan na bakan ta masu rai dan so da dama za su kawo mashi gulma ko makirci sai dai ya gwale wanda ya kawo mashi in kuma ya koma gida ya haw Ammi da fada ba ta ce mashi komi sai in ya sauko sai ta fadi mashi gaskiyar sai ya bata hakuri.
Haka ma yau sai dai yau yaran ne suka amsar wa mahiafiyar su.
Suna zaune bisa dining gaba ki daya suna cin abinci ya ce "Ammi na ji an ce ba ku je Kamu ba ko zan iya sannin dalili kin zuwan ku bayan kin san bikin huda a ke.
Kafin Ammi tayi Magana siyama charab ta amsa tambayar "Mu muka ce ba mu zuwa."
"Siyama! Ammi Ta kwabe ta.
Qawwma ta ce "Abi ba fah laifin Ammi ba ne mu muka ce ba za mu ba."
Ya aje spoon din hannun shi ya ce "Dalili?
Ammi ta ce "Abi kayi hakuri ba wai.."
Siyama ta katse ta "Abi gidan ba dadi duk ba su son mu."
Duban Ammi yayi cikin mamaki, ya san family din ba sa son ta amma miyasa zata nunawa ya’an shi haka, bai yi tsanmanin haka ba.
Za ta yi Magana ya dagatar da ita, "Kin yi daidai." Ya mike ya wuce ya bar dinning ya koma parlourn sa.
Rai ba ce Ammi ta ce "Ban hanaku tsoma bakin ku in muna Magana da Abi ba?
Siyama fitsarara ta ce "Ammi we didn’t interrupt we just told the truth, kuma kin ce babu kyau karya." Ta ida maganar kamar ta na turke mahiafiyar ta. Qawmma dai shiru ta yi ba ta ce komai ba.
Ammi ta ce "Daga yau ina Magana da Abi wani ya sa min baki sai na fasa bakin." Daga haka ta mike ta wuce parlourn shi.
Syama ta ce "Chab a dake mu a hana mu kuka."
Qawwma bata ce ko mi ba dan tin ba yanzu ba ta ke monitoring din su, ta na bin su a jiki amma ko da yaushe family din basu da aikin yi sai zagin Ammi.
Ta isa parloun shi bai ciki sai ta wuce dakin sa bai na sai ta wuce balcony din dake dakin sa. Tsaye ta gan shi yana kallon ilahir unguwar. Da ga kofa ta ambaci sunan shi bai amsa ba ta kara kiran shi yayi shiru sai ta matso kusa da shi tare da hugging din sa ta baya. Ta dora fuskar sa saman bayan sa hannunwan sa saman kirjin sa cikin sanyi lafazi ta ambaci sunan sa "Darling ba wai haka nan muka ki zuwa.."
A fusace ya juyo ya ce "Ban damu da dalilin kin zuwan ku ba, habibty ban tsanmani haka daga wurin ki ba why will you tell the children the issues between you and my family, mi suka sa ni? Ina suka yi hankalin sanin dai dai da ba daidai ba?
Kwalar da ta dan sauko ta goge ta tare da yin murmishi mai ciwo ta ce "Yaran daa da yanzu ba daya suke ba, yanzu ba sai ka fadi wa yaro abin da ke wanzuwa ba zai gane, idan na fadi masu gakiya, mi zata kare ni da shi? Mi zata rage ni da shi? Kai karan kan ka ne a bayyane suke nuna min kiyaye da hassada mi zai sa yara ba za su fahimci haka ba, nayi imani ko rantsuwa zan yi bazan yi kaffara ba su Farhin su ma sun san da haka, amma ba komi, sun din yan’uwan ka ne kuma dole ka goyi bayan su.
Ta goge hawayen ta ta sauke ajiar zuci ta fashe da kuka. Ta juya zata wuce da sauri ya chafko ta ta fada saman kirjin sa, kukan ta ba karamin tada mashi hankali yake ba, ganin yanda yayi hugging din ta ta kara fashe wa da kuka, cikin kuka ta ce "Mi zai sa in fadi masu gaskiya bayan su da kan su suka gano haka?
Siyama yarinya ce mai wayyo, kai ma shedane, kaima shedane yanda muke fama da ita, idan Qawwma bata budai baki tayi Magana ba karan kan ka ka san siyama zata yi, in har Qawwma zata yi Magana akan abu kai ka san ya na ci mata tuwo akwarya."
Sosai ya rungumai ta yana bata hakuri dan zuciyar sa bata iya juran kukan ta. sai da ta yi mai Ishan ta sannan ta dago ta goge hawayen ta shima ya kara goge mata sauran. Ya ce "I'm sorry bai kamata in yi questioning din ki haka ba."
Ta ce "Ba komi ina so gobe ka dauke su ka kai su dan ni ba sa jin maganata."
Yayi karamar dariya yana ce wa an gama ranki yadadi my crying pet.
Ta dan bata rai tare da cewa bana so
Ya ce toh shi ke nan Allah kai mu gobe ta amsa da amin.
Washe gari kasan cewa juma’a bayan yayi sallah juma’a sai ya dawo gida ya ci ambaci sannan ya ke komawa company.
Ya na yin sallama duka biyun suka tashi suka mashi oyoyo sannan suka amsa leader hannun shi. Ya ce "Ku je Ammi ta raba ma ku." Suka mashi godiya ya wuce parlourn shi na kasa.
Su kuma suka wuce kitchen inda Qawmma, Jamila da Ammi suke abinci. Siyama ta mika wa Ammi ledar tare da ce wa "Abi yace a raba mana."
Ammi daake slicing cucumber ta ce ba Yaaya ta raba maku.
Siyama ta mika wa Yaaya da ke zaune genfen kitchen din saman small dining chair.
Ta aje wayar ta ta bude ledar ta fiddo yougut, sai kuma rake, kwakwa da dabino.
Daman yogurt a lissafe yake kananu na siyama da Fatima medium na ta sai big na Abi da Ammi. Ta ce wa siyama ta dau nata haka ma Fatima, sai ta raba raken ga kowa har da Jamila haka zalika kwakwa da dabinon.
At around 2pm lunch ya kammala ta sallami Jamila su kuma suka yi na su har da Abi da yi joining daga baya bayan sun gama ya ce su shirya za su fita in ya dawo da dare. Suka mashi murmishi cikin son fita da mahaifin na su.
Ya dubi Ammi ya ce mata "A masu kwaliya su yi kyau."
Ta amsa shi da "Toh." sanna su ka mashi Allah ya kiyaye.
Kasancewa yau Friday ba islamiya sai wasa da rishin ji da bari bari. Around 4:30pm siyama ta hau sama, parlourn Abi ta wuce balcony, ta nufi gudan balcony din wadda itace parlourn baban su Farhin tayi knocking ba a budai ba ta sauko kasa a chan backyard wurin Qawwma, ta na zaune saman swing chair dake kallon pool da karamin kur'ani a hannun ta ta na bitar hardar da za ta bada gobe.
Siyama ta karaso wurin ta ta ce "Yaaya dan Allah kira Mummy ki ce ta budai min I want to play with Farhin."
Qawwma dake karatu ta kalle ta, ta yi waqafi a cikin ayar da ta ke karantawa, ta maimaita abin da Siyama ta fadi cikin iskigili.
Daya ke ita ke so cikin ladabi ta ce"Please."
Qawwma ta ce "KI bi ta gate dole sai balcony."
Siyam ta ce "Kin san malan isa na nan ba zai bar ni na fita ba."
Ta ce "Ki ce mashi gidan su Farhin zaki."
Ta ce "Dan Allah ki kira."
Qawwma ta ce "Kar ki ishe ni, ina karatu kin dagatar da ni. " Tayi tsaki ta shiga call ta yi dailing number Mummy bayan sun gaisa ta ce a budai masu su shigo mummy ta amsa mata da toh. Su ka mata godiya.
Siyama ta wuce da gudu. Qawmma kam sai da ta fadi wa Ammi zata shiga gidan su Farhin, siyama kam ta saba bata fadi wa Ammi, ko da wani gida za ta je cikin unguwar, mafarin ke nan a ka ce wa malan isa ya dai na barin su suna fita.
Suka wuce sama, Mummy ta budai masu balcony suka rungumai ta tare da gaishe ta, ta amsa, ta sake su tana masu nuni su karasa.
Ta rufe kofar ta bi su suka sauko kasa kasancewa gidan iri daya ne da nasu komi da komi furniture ne kawai ya ban banta shima ban da na kitchen. Suka sauka parlourn, ta iske Farhina na assignment Qawwma ta ce "See serious student ke kuma ba ki komi sai shirme." Ta ida maganar tare da sa hannu cikin swing baby bed ta dauki little Qawmma ta nace wa "My namesake."
Siyam ta ce "Ay there’s weekend."
Farhin ga baby dolls zo muje mu yi wasa.
Zata tashi Mummy ta ce kar ta sake ta tashi har sai ta gama. Farhina ta koma ta cigaba da assingment din ta duk da hankalin ta ya koma wurin wasa.
Qawmma ta ce "Ke ma da assignment din ki ka yi da ya fiye maki wasa. "
Ko sauraran ta ba ta yi ba Ta wuce waje wurin su Fauzan.
Mummy ta tambayi Yaaya "Yau ba za ku kamun ba?
Qawmma ta dan bata rai sai ta ce "Mummy ni ban jin dadi."
Mummy ta ce "Ay na ga jiya ma baku je ba ba dai yau ma baza ku ba??
Qawwma ta ce "Mummy ni harka family ne ban san shiga gwara kowa yayi zaman sa a gida."
Mummy ta ce "Ay zumunci ne."
Farhina ta rufe note book din tare da ce wa "Mummy na gama."
Mummy ta ce "Miko min in gani kuma ki kayi ba daidai ba sai kin sake shi."
Farhin ta miko mata mummy ta duba ta mika mata littafin tare da cewa kwashe min targachen ku.
Farhin ta kwashe littafanta da school bag din ta ta kai su daki ta wuce waje wurin su dama sauri ta ke ta gama.
Qawwma ta ce "Wani zumuci, zumuncin da ake nuna ba a san ku."
Mummy tayi karamar dariya tare da cewa wa wa yai bai san ku?
Qawmma ta ce "Kowa ma. i'm exusted with the family issues."
Mummy ta ce "Toh ya za kiyi daman zama ya gaji haka, dan'uwa dan'uwa ne ba a fushi da shi.
Qawwma ta ce "Dan Allah Mummy miyasa ba su san Ammi? Abin nan na damuna I can't ask Ammi non Abi.
Mummy tayi shiru kamar ba za ta amsa mata ba sai kuma ta ce "I don’t know, what I want from you ki ja su ajiki, ki yarda suma yan"uwan ki ne ba wai su Farhina nai kadai na ku ba, kowa da kowa wata rana sai labari."
Qawwma ta tabe baki. Chan kuma sai ta ce "Mummy I think she is hungry sai faman budai baki ta ke."
Mummy ta kalli small qawmma tana ce wa"Yunwa ki ke ji."
Kamar ta na jin abinda Mummy ta ce ta fara yi mata dariya.
Mummy ta mike tare da cewa bari na hada masu madara, sai shegan ci dazu fa na basu suka sha suka yi bacci amma ji ta na tashi ta fara neman abinci na san sawwama yanzu zaki ga ta tashi.
Qawmma ta ce "They are kids what they know is their mothers' milk."
Mummy ta wuce kitchen ta hadawa Qawwma madara, ta na fito wa ta ga sawwama ta tashi. Ta ce "You see, I told you yanzu zaki ga itama ta tashi."
Qawmma ta mike ta amsa madara daga hannun Mummy ta ce yau dai ni zan yi feeding namesake di ta.
Karamar dariya ta yi ta ce "Okay bari naji da sawwama. Ta koma kitchen ta hada wa sawwama madara dan ta san yanzu itama zata naimi Abinci dan twins din mahaifar su daya komi tare suke yin shi in daya ta tashi daya ma sai ta tashi in daya ta fara kuka daya ma za ta fara.
Suka yi feeding din 4month twins din. sai da a ka kira magriba suka koma gida su Mummy suka fara Shirin dinner.
Ko da suka koma ba su naimi abincin dare ba dan sun san za su fita da Abi, cartoon suka fara kalla bayan sun yi sallah magriba kafin isha’I su shirya.
Suna cikin kallon carton Abi ya shigo. As usulal Fatima da Siyama suka mashi oyooya Qawwma da Ammi suka mashi sannu da zuwa.
Ya tambaye su "Have you pray isha?
Da sauri Siyama ta girgiza kai ta wuce dakin su dan tabbass fada Abi zai mata kuma bata kaunar fadan shi.
Fatima kuma ta ce "Abi ni da kai zan yi."
Ya ce "Ni na yi tawa, go pry so that we can leave early."
Zai wuce dakin shi ya ce "Ammi a shirya su kar mu makara." Ta amsa mashi da toh ya wuce sama.
Ya na wuce wa ta mike tare da cewa Qawwma ta taso su shirya. Ta wuce dakin yaran ta iske siyama na sllah ta wuce press din su ta dauko masu gown sannan ta daga wardrop ta dauko wa siyama hula Fatima headband.
Siyama na sallama sallah ko azkar ba tayi ba ta mike tare da ce "Ammi wannan gown din zan sa??
Ammi ta ce "Eh." Siyama ta rungumaita cike da murna dan sabuwar gowan ce. siyama ba abin da ta ke so sama ta ga ta sa sababin kaya.
Ammi ta janye ta tare da ce wa je ki shirya.
Ta tube wa Fatima kayan jikin ta ta sa mata gown din sannan ta shafa mata powder, kajal da lipban. Tayi jelling front hair din ta ta sa mata headband. Ta na ida mata Fatima ta wuce madubi da sauri dan ta ga kwalliyar ta.
Ta na isa siyama ta ga kwaliyar Fatima ta sauka daga kan stool ta na cewa "Ammi ni ma ki min."
Ammi ta ce "Ba ce wa ki ka yi za kiyi da kanki ba."
Ta turo baki chan kuma ta ce "Dan Allah." Ammi ta mata nuni da ta karaso. Ta karaso wurin ta cike da murna. Ammi ta fara gyara ta.
Fatim kuma ta ce "Zan je in nunawa Abi." ta fita da gudu a lokacin Qwwama ta shigo. Ammi ta dubai ta ta cigaba da gyara fuskar Siyama chan kuma ta ce "Yaaya bana san bakin halin ba za ki wuce ki shirya ba.”
Ta aje wayar hannun ta ta mike ta shiga toilet. Ita ta san wurin dinner za su ba wai fita za su yi da Abi ba duk da da shi za su je dinner.
Ammi ta gyara fuskar Siyama ita ma ta sa mata jel. Za ta sa mata hula siyama ta ce no headband.
Ammi ta ce "A’a kin girma da sa hedband kuma dare ne ba zaki fita ba hula ba."
Ta ce "But Fatima.."
Ta katse ta "Fatima karama ce."
Da jin haka ta juya ta nace wa "Sai na fadi wa Abi." Ta wuce ta bar dakin.
Qawwma ta fiddo kayan da zata sa Ammi ta ce "Ba su ba zaki sa, sabuwar atanfan nan zaki sa."
Rain Qawwma a dakule, ta ce "Ammi ni fah ba zan je wannan dinner ba."
Ammi ta ce "It is an order from your father." Ta mike ta wuce.
Qawwma bata sa antamfar anko ba ta shirya cikin butterfly shirt and pants. Ta yi rolling veil ta koma ta kwanta.
Ammi na shiga parlourn ta wuce dakin Abi, Abi ta iske shi shi da yaran sa, yana ganin ta ya ce wa su Siyama su jira su a parlour ya shirya shima. Suka amsa da toh suka fita.
Su na fita shi ma ya mike ya karaso wurin Ammi tare da ce mata gashi dai kin shirya su ke kuma baki shirya ba.
Ammi ta ce "Yanzu zan shirya, I think you should go talk to Qawwma sai wani dacin rai ta ke."
Ya tambaya "A kan mi?
Ammi ta ce "Ina tunanin ta san in da za ku, nace ma yaran nan wayo garai su."
Murmshi yayi yace bari na mata Magana ki je ki shirya.
Suka bar parlourn shi ya shiga dakin su Qawwma ita kuma ta shiga dakin ta.
Yana shiga ya iske ta kwance ta na amfani da wayar ta.